x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 65 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 192001 words
  • 195000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 382

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ki ga parlourn da zaki yi aiki a ciki, sai bedroom ɗin Aunty Sharifat da zaki rinƙa gyara mata, nata ita da Guyson, bedroom biyu ne kawai zaki rinƙa gyarawa, Ummie ta sanar da ni shi ne aikinki".

Nan ma ƙasa ƙasa Leesharh ta amsa mata da. "Okey amma dan Allah ina ce alkibla a wannan gida?".

Da hannu Fadila ta nuna mata gabas tare da sa kai ta fice abinta. Saman carpet ta yi tsaya ta fuskanci alkiblar, sannan ta tada sallah da iya wannan veil na kanta da ta yi rolling.

Bayan ta idar ta yi addu'oi sosai da sosai, lokacin da ta ɗauka tana zuba addu'ar ma ya fi lokacin da ta ɗauka wajen gabatar da sallar. Bayan ta shafa ta matso kusa da abincin nata, dama yunwa take ji, tun safe bata ci komai ba, sai kuka ƴaƴan hanjin cikinta suke yi.

Abincin ta fara zaɓar wanda zata ci, cikin nutsuwa ta zuba a cikin plate, ba ɓata lokaci hannu baka hannu kwarya ta fara cin abincin. Wani tunani ne ya faɗo mata, tunawa da yadda taga yawan Cameras tun daga kan titin da zai kawoka gidan nan har izuwa cikin gidan ta yi. A hanzarce ta ɗaga kanta sama ta fara neman camera a cikin room ɗin nata, dan ta tsorata, a tunaninta akwai camera, kada ya zamana duk abin da take yi masu gidan suna kallonta.

Ganin bata ga alamar camera a room ɗin bane yasa ta cigaba da cin abincinta tana tunanin yadda zata kaya mata a wannan gida.

After some minutes. Ta kammala ci tas, ta ci abincin sosai, sannan ta tattare komai kamar ba'a taɓa cin abinci a wajen ba, ta kwaso kayan abincin ta fito waje. Nan ta bar wayarta a saman bed ɗin tata, ita da aka ce ta ɓoye wannan wayar, kada ta fitar kowa ya gani, ta bari za'a bata wayar amfani a gidan, dan duk masu aikin gidan suna da wayoyi da Ummie ta saya masu wanda zasu iya kiran ƴan uwansu, haka tsarin gidan yake, amma ita Leesharh tun ba'a je ko'ina ba ta baro wayar sirrinta a saman bed wangalam ba sakayawa ta yi waje abinta.... Toh fah, akwai fa ƙura, da alama Leesharh dai ita da kanta zata tonawa kanta asiri a wawtarta da shiriritarta.

Fitowa haɗaɗɗen parlourn nasu ta yi, yadda part na masu aikin gidan yake ma sai ya baka sha'awa, parlourn ne haɗaɗɗe mai cike da komai na more rayuwa, sai bedroom manya manya guda huɗu a cikin parlourn a hawa na farko kenan, a na biyun ma hakan ne har karshe, so ƴan aikin da suke hawa na farko suna amfani da part ɗin, ƴan aiki na hawa na biyu ma haka, in da Leesharh zata yi aiki shi ne ainahin family part, in da ɗakin barcinsu da komai da komai nasu yake kenan, to masu aiki uku ne kacal a wajen, da Leesharh ta zo yanzu sun zamana su huɗu, Fadila da Radia ƴan mata ne da a shekaru ma zasu iya zuwa mate, sai kuma babbar su wadda take kamar matsayin uwa a garesu, ita kam bazawarece wadda a kallah zata kai shekaru 40 haka a duniya, ita take kula da su da kuma aikin da suke yi idan ya yi kyau, sannan tana ɗaya daga cikin masu yin girki a gidan, a hawa na ƙasa ake yin girki ba'a family part ɗin ba, dan Ummie ta ce bata buƙatar kamshin ingredients komai ƙanƙantarsa a hawan nasu, dan haka ba za'ayi amfani da kitchen na part ɗin ba, sai dai ayi girkin a kasa a ɗauko a hauro da shi sama a jere masu a saman table, haka tsarin gidan yake, suna da tsari sosai da sosai, kuma a kan tsarin suke tafiya.

So kowani hawa ƴan aiki huɗu ake ɗauka kamar yadda part ɗinsu yake ɗauke da bedroom guda huɗu. Leesharh tana fitowa ta ci karo da su Fadila suna kallo Arabians film a makeken Tvnsu da yake a cikin parlourn nasu.

Sannu ta yi masu, Fadila ce ta miƙe ta karɓi trayn kayan abincin daga hannunta tare da ce mata ga waje ta zauna mana.

Okey kawai ta amsa da shi tare da nufar saman sofa ta zauna, ita kuma Fadila ta yi waje da kayan abincin.

Shiru ta yi bata yi magana ba, Radia ce ta ce "Ke baki yin magana ne? Gaki kyakkyawa".

Ƙasa kaɗan ta ɗan yi da kanta kafin ta amsa da tana yi. Kasancewar muryarta baya fita sosai yasa Radia bata iya gane me ta faɗa ba, sai kawai ta mayar da kallonta a Tv da suke kallah. Ko a iya kan masu aikin gidan kawai ya isa yasa ku fahimci shi Abu Abdussalam bin Badeen shugaba ne adali, duba kuga yadda masu aikin suke shanawarsu, idan sun kammala aikinsu suna da damar zuwa part ɗinsu su yi wanka su sha kwalliya kamar ƴan gida, su kunna Tv da Ac su samu waje su zauna suna kallo. Akwai emergency phone a gidan ta ko'ina wadda duk wanda yake buƙatar wani abin daga wajen wata ƴar aiki koma a hawa na nawa yake zai iya kiran emergency phone ɗin nan, cikin ƙanƙanin lokaci masu aikin zasu bayyana su kawo mashi abin da yake buƙata, sam Abu Abdussalam bai ƙasƙantar da ƴan aikinsa dake a ƙarƙashinsa kamar yadda saura suke yi ba, ya basu jin daɗi da hutu suma kamar ƴaƴa, har sun dai'na jin kansu a matsayin ƴaƴan talakawa marasa gata, ga shi a duk karshen shekara yana basu dama su je ganin iyayensu bayan ya cikasu da alkhairai dayawa, zai basu abubuwa da dama su kaiwa iyayen nasu, a kaisu da mota a kuma dawo da su, ita ma Ummie ta kara masu, Sharifat da Omar ma wato Guyson ba'a barsu a baya ba, suma in dai masu aiki zasu je ganin gida sai sun basu kyauta mai tarin yawa su ce su kaiwa ƴan uwansu, Sharifat yarinyar kirki, haka zalika shi ma Omar ɗin Gimbiya Zunaira, yana da kirki shiyasa suke shiri da Sharifat sosai, duk gidan su biyun nan ne suke shiri sosai, bayan shi Sharifat bata shiri da kowa, ko sauran brothers ɗin nata, dan basu wasa da ita, kallo ma bata ishesu ba, amma fa suna bala'in kaunarta over, kawai dai basu wasa da ita ɗin ne.

Fadila ce ta dawo cikin parlourn baki a ɗauke da sallama, ta kai kayan abincin cikin kitchen ne ta dawo. "A'isha muje ki ga yadda abubuwa da kuma dokokin gidan suke ko? Daga nan sai na nuna maki parlourn da zaki yi aiki a ciki".

Da mamaki Leesharh ta ce. "Dama ba'a parlourn da muka shiga ɗazun zan yi aiki ba?".

Kallonta da kyau Fadila ta yi tana mamakin yadda take magana, ta ji voice ɗinta baya fita sosai, abin sai ya bata mamaki. Amma sai bata ce komai a kan yanayin maganar tata ba. Sai ta ce. "Wannan parlourn ai na hutawar Ummie ne, ainahin babban parlourn gidan mai ɗauke da part na kowani ɗan gida yana gaba dana Ummie, muje zaki gani".

Ba musu ta miƙe, Fadila ta ɗan yi gaba kaɗan ta na ce da Radia ko zata zo su je ne. Sai kun dawo Radia ta yi mata alamar ba zata je ba kenan.

Fitowa suka yi Fadila tana nuna mata komai daki daki tare da yi mata bayanin yadda komai yake dallah dallah.

Sosai Leesharh ta kasa kunne take naɗan komai da ake gaya mata tare da hanyoyin da suke bi. A haka har suka isa izuwa babban parlourn, sai dai sun ɗan sha tafiya sosai daga part ɗinsu zuwa parlourn, sannan ne suka isa.

Ai a nan ne Leesharh ta zama cikakkiyar ƴar kauye sosai, ko a film bata taɓa ganin parlourn mai girma da haɗuwar wannan ba, gari guda, ya haɗiye sofa set kala kala har set biyar, ya ƙawatu iya ƙawatuwa kamar parlourn shugaban ƙasa. A nan ne part ɗin kowane ɗan gida yake wadda shi ma akwai ɗan madaidaicin parlourn a cikinsa kafin sleeping room ɗinsu.

Ganin yadda Leesharh ta saki baki tana karewa parlourn kallo ne yasa Fadila ta ɗan yi dariya kaɗan kafin ta ce. "A'isha wannan parlourn zaki rinƙa gyarawa, amma ba ke kaɗai bane, Ummie ta gaya mun ke kaɗai ba zaki iya ba, ta ce na rinƙa tayaki, sai kuma part ɗin Aunty Sharifat wanda ga shi can shi ne na tsakiya, na Guyson shi ne a kusa da nata, su ne zaki rinƙa gyarawa ke kaɗai, parlourn kuma zamu gyara a tare".

Jinjina mata kai kawai Leesharh ta iya yi, amma ta kasa yin magana, haɗuwar wannan parlourn ya ruɗar da ita.

Ta yi shiru tana kalle kalle ne can idanunta suka hango mata wani katafaren frame na hoto, yana da girma frame ɗin, an ƙawata shi ya yi kyau sosai. Wani irin zaro idanu waje sosai Leesharh ɗin ta yi a lokacin da idanunta suka sauka a kan hoton da yake a jikin frame ɗin, a hanzarce ta runtse idanunta ta sake warosu a kan hoton. Sam Fadila bata lura da yanayin da Leesharh ɗin ta shiga na ganin wannan hoto ba, hankalinta ita yana can kan yi mata bayanin lokutan da zata yi aiki, bata san Leesharh kam bata a tare da ita ba.

Hoton wani kyakkyawan matashi ne number ɗaya, kyakkyawa ne sosai ɗan wanka, ya sha wanka da idan ka gansa sai ka so ka sake ganinsa, ya fita iya fita a hoton, kamar ka kirasa ya amsa, kansa na sunkuye a ƙasa ya ɗago da dara daran fararen idanunsa, yanayin smooth skin ɗinsa kamar madara, dark black arab hairnsa kamar wadda aka kifawa hula har gaban goshinsa, yana da ɗan ƙaramin lips sosai, hasken fatarsa tasa launin lips ɗinsa ya kara fitowa sosai, a shekaru ba zai wuce 15 to 16 years ba, ya sanya wata ƙatuwar Bluetooth a kunne, da alama dai ɗan gayun ne na gasken gaske, ko kaki ko kaso daga ganinsa kasan ya ci sunan da suke kiransa da shi wato Guyson, dan fa guy ɗin ne da gaske.

So ita Leesharh ba wai kyansa ne ya ruɗata ko kuma wankar daya ɗauka ba, dukka ba wannan ba, abin da ya ruɗa ta shi ne yanayin kamaninsa, tabbas yana kama da wancan matashin da ta gani a gidansu masu nukaf wanda ya je ranar, duk da bata sami damar ganin face ɗinsa da kyau ba kasancewar kansa na kallon ƙasa, amma tabbas a yadda Guyson ya duƙar da kansa ƙasa tare da ɗago waɗan nan kyawawan idanun nasa ba makawa sun yi yanayi da wancan guy ɗin, tabbas sun yi mata kama, wannan shi ne abin da ya ruɗar da ita.

Wani irin wahalallen yawu ta haɗiye tare da fara tunanin wanene ma Guyson ɗin nan tukun nan? Idan har da gaske ne abin da idanunta suka gaya mata na yanayin kamanceceniya a tsakanin Guyson da wancan matashi hakan na nufin kenan already dama makashin Ramish yana nan a tare da shi? Ko dai yaya abin yake ne? To amma idan har makashin nasa yana a tare da shi meyasa za'a turota leƙen asirin motsinsa? Kai ina hakan ba zai yi wu ba.

Wani tunanin ta sake yi a kan to anya wancan matashin da ya je gidansu mai nikaf ɗin nan yasan da abin da suke shiryawa kuwa? To wannan wani irin al'amari mai bala'in rikitarwa ne?.

Ya ilahi ya lilliahi, shi ne abin da Leesharh ta furta a cikin zuciyarta tare da dafe kanta da yake yi mata barazanar tarwatsewa. Sai magana Fadila take ta yi mata, amma ina ko kalma ɗaya bai shiga mata cikin kunnenta ba. Haka Fadila ta gama surutun bayanan nata abanza, ta ce su tafi. Ta yi maganar tare da wucewa gaba.

Ganin tana tafiya ne yasa Leesharh ta rufa mata baya, yadda kuka san wadda kwai ya fashewa a ciki haka take jan kafafunta, duk jikinta ya yi sanyi, sai tunani take yi a kan masu nikaf ɗin nan, faɗi take yi a cikin ranta anya masu nikaf ɗin nan basu da wata alaƙa da wannan gida kuwa? Anya ba ƴan uwan juna bane?.

Nima dai PRINCESS TEEMA an jefani a cikin ruɗani, dan haka bari na bar part ɗin su Leesharh ɗin nan kada su sanya ƙwaƙwalwata ta tarwatse, bari na je na sha Maltina mai sanyi sannan na leƙa mana su Kamran, wata kila kafin na dawo ƙwaƙwalwata zata ɗan huta na samu na cigaba da kwaso maku labarai a kan Leesharh tamu... Amma dai akwai cakwakiya ba kaɗan ba!.

🏞️FOREST🏞️


🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)






🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 14/8/2024.....✍️📚🌹




For information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️








E____________35🔥




🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼


🏞️FOREST🏞️

A zaune suke wajen ƙoramar nan, Kamran yana zaune a saman dutse mai ɗan faɗi ita kuma Pretty tana tsaye a bayansa tana ta famar yamutsa mashi kyakkywar gashin kansa, sai busa mai daɗi yake yi masu da abin busarsa. Sweetie kuma tana cikin raminsu tana barci, bata fito ba yau, ta ce zata kwanta ta huta.

Kayan sakar da ya kawo masu Pretty ta sanya a jikinta, ta yi matuƙar kyau over, sai ta zama kamar wata ƴar tsana a cikin kayan, ta kara zama ƴar karama da ita, kamar dai kullum kyakkywar dark black curly hairnta a ɗaure kashi biyu, ta saki jelar gashin har bayanta, sket ɗin kayan ya tsaya mata a iya gwiwarta.

Sai watsa mashi gashin kansa take yi kamar an aiketa, wai zata ɗaure mashi irin yadda mum ɗinsu take ɗaure masu nasu, haka take ɗaurewa Sweetie ma nata, to shi ne wai shi ma zata ɗaura mashi nasa. Ta yi mamakin ganin yadda gashin nasa yake da yawa bakin kirin da shi, ya yi baki sosai kamar tata.

Sai fama take yi, gashin ya fi karfin ƴan hannayenta, shi kuwa sai busa yake yi masu. Da kyar ta iya samu ta raba gashin nasa gida biyu, kitsa mashi ɗayan ta fara yi, sam bai san me take ta faman yi mashi ba, shi dai har cikin ransa yana jin matuƙar daɗin wasa da gashin nasa da yake yi, dan a tunaninsa wasa da shi take yi, so hakan daɗi yake yi masa.

Ita kuwa kitsa mashi su ta yi kamar yadda mummynta ta koya masu, sannan ta nannaɗe jelar gashin nasa ta cusa mashi a ƙarƙashin kitson kafin ta mayar mashi da hularsa ta rufe mashi kan nasa.

A ta gabansa ta dawo ta zauna tare da kwantowa a jikinsa ta kai hannu ta karɓi abin busar. "Kawo bari na busa mana". Ta faɗa cikin sanyin murya.

Ba musu ya miƙa mata, dan shi ma yana jin daɗin busar tata sosai. Hannayensa dukka biyu ya ɗaura a saman shoulders ɗinta a in da ya zuro da su ta gaba ya kara jawota jikinsa yana faɗin. "Rocky fa yana nan zuwa?".

Kai abin busar ɗan bakinta ta yi tana girgiza kai, kafin ta fara busar ta ce. "Yazo nan sai na mare shi, gara mashi tun wuri yasan in da dare ta yi mashi". Cikin tsiwa ta yi maganar, dan fa ita bata kaunar Rocky, sam jininsu bai haɗu ba, har yau har gobe razana take yi idan ta ganshi.

Ɗan murmushi kaɗan ya ɗan yi wadda ba za'a iya kiranta da murmushi bama, dan sam bata fito ba, sannan ya sauke hannunsa ɗaya daga saman shoulder ɗin tata izuwa saman ɗan shafaffen cikinta. "Rocky fa baya da faɗa, kece nan kike sawa yake baki tsoro".

"Ko baya da faɗa bana sonsa, kuma ba zan taɓa sonsa ba". Tana kai karshen maganar ta fara busarta cikin kwarewa, a yanzu ta iya busar sosai da sosai, ga shi kala daban daban ta iya rera busar, har wani lumshe idanu suke yi daga ita har shi idan tana busa masu. Akwaita da ƙwaƙwalwa, cikin ƙanƙanin lokaci take iya koyan abu ta haddace, akwai su da baiwa twin's ɗin nan sosai.

Yanzu ma tsabar daɗin busar yasa suka lumshe idanu su dukkansu, ta kara lafewa a jikinsa tana mai cigaba da busawa.

Wajen ya yi shiru tsit, sai karar sautin zubar ruwa da kuma kukan tsuntsayen dake shawagi a wajen zaka ji, a hankali hankali sautin busar tata yake tashi a arear wajen, hakan ba ƙaramin daɗi da ƙawa ya yi ba, a yanzu akwai wata busa da suke yi wa junansu, wanda Kamran ɗin shi ne ya koya masu, idan suka cutsa cikin daji yawo, da wannan busar suke kiran juna, wani lokaci idan suka je yawon nasu Kamran da Sweetie suna zama a ƙarƙashin bishiya suna hira, ita kuma Pretty yawo take tafiya abinta, so idan Kamran zai nemota sai ya ciro abin busarsa ya fara busawa, idan tana kusa da shi zata mayar mashi da martanin irin wannan busar da tata abin, shi kuma zai bi sautin karar busar tata har zuwa in da take.

Idan kuma ta ji shiru bata mayar mashi da martani ba to ta ɗan yi nisan zango, sai ya kara gaba har sai ya samota.

Wani kyakkyawan parrot ne ya sauka a kusa da Pretty da ta lumshe idanu tana aikin busa mai kwantar da hankalin mai sauraro.

Cikin dabara Kamran ya shammaceta tare da shammatar parrot ɗin ya damko shi. Tana jin alamar hakan ta yi maza ta waro idanunta waje tare kuma da dakatawa
End Ads