tsawonta sosai zurfi, da wannan katon cikin nata kuma ba zata iya buɗe kafafunta ta taka gefe da gefensa dan ta fita ba.
Komawa ta yi ta zauna sai a lokacin ta lura da ta kukkuje a hannunta, jajir kuma lallausan fatarta na singalalin hannu zuwa yatsunta duk sai jini yake yi, dama ga fatar luwai luwai da shi, zai yi saurin jin ciwo, ba iya hannu ne kawai ta kukkuje ba, har da kafafunta da sauran sassa na jikinta.
Har lokacin bata iya wani numfashin kirki, runtse idanuwanta ta yi a inda ta fara karanto addua'o'i kala kala dan neman taimakon mahaliccinmu, domin kuwa idan ba Allah ba, babu wanda ya isa ya ceceta daga cikin wannan hali da take a ciki.
A hankali ruwan sama ya fara cika wannan rami, da yake a gangaren tekun ramin yake, sai ruwan gudu ya fara shigowa. Jin hakan na ruwa na shigowa ne yasa ta yi yunkurin ta sake gwada miƙewa a karo na biyu, amma ina, ko motsin kirki ta kasa yi. Hasbunallahu wani'imal wakil shi ne abin da take ta maimaitawa a cikin zuciyarta.
Wani irin azababben murɗa da cikinta ya yi ne yasa bata san lokacin da ta kwallah kara wanda har sai da muryarta ta fita duk dashewa da ta yi ba, da yake ta sha ruwa ne sai muryar tata ta ɗan saki har sauti yana fita.
Dafe cikin nata ta yi tana mai cigaba da furta sunan Allah a ranta.
Da kaɗan da kaɗan ciwon cikin nata yake karuwa yayinda mararta ya kulle gam yana yi mata wani irin azababben ciwo. Nan take idanuwanta suka kara raina fata a in da a wannan karon suka yi jajir kamar wuta, saboda azaba.
Cigaba da murkusoso tayi a wajen tana damke ganyayyakin dake kusa da ita, ta ciza laɓɓa gam da kyawawan fararen hakwaranta tas kamar audiga, tamkar zata fasa laɓɓan nata da hakwaran, idan cikin nata ya murɗa sai ta kara ciza laɓɓanta da karfi, Baiwar Allah, kamar laɓɓan ne suke yi mata laifi.
Haka ta yi ta fama na tsawon mintocin da a kallah zai kai arba'in zuwa hamsin, duk ta galabaita ta fita a hayyacinta, duk wasu sauran albarkatun karfi da suka rage mata sun kare, harta ciyayin da take rikewa ma yanzu ta kasa rikewa, saboda babu wani karfi da ya rage a tattare da ita, sunan Allah ma yanzu a iya zuciya kawai take iya furtawa, bakinta banda kerma tamkar wanda ciwon sanyi ya kama babu abin da yake yi, ruwan sama na cigaba da gangarowa izuwa cikin ramin, a yanzu haka yanda take zaune ruwan ya kai mata har zuwa kugunta daga zaunen.
Nakuda gadan gadan take yi, da kyar ta samu ta iya cire kayan jikinta, bata rage komai a jikin nata ba, duk ta kwaɓe komai saboda azabar wahala, Baiwar Allah sai take ganin kamar kayan ne suke kara mata zafin da wahala, duk wasu gwala-gwalai tayi wurgi da su gefe guda, ta yi ƙoƙarin ta yaga rigarta ko alkyabbar ta dan ta ɗaure cikin nata in da suka harbeta da kifiyar da kyau, amma ina ta kasa, bata da karfin iya yaga komai, haka ta daure ta hakura tare da dafe wajen kawai.
Ganin cewa kamar lokacin mutuwar tane ya yi saboda azaba yasa ta daure cikin wani irin mawuyacin hali ta fara faɗin.
"Ya Ubangiji na, kai kaɗai zaka taimaka mun a cikin wannan bakin azabar da nake a ciki, ya Allah dan karfin ikonka ka kawo mun ɗauki cikin gaggawa, ka saukakamun wannan nakuda cikin gaggawa, ya Allah kada ka bari na mutu ba tare da na kalli abin da zan haifa ba, ya Allah ko bayan raina kasa abin da na haifa ya zamana shi ne sanadiyar rugujewar RAWANIN ZALINCI ya tayar da RAWANIN ADALCI da aka kwantar, ya Ubangiji ko na mutu ko ban mutu ba na baka amanar abin da zan haifa, Allah ka kula mun da shi, ka raya mun shi, ya Allah ka bashi basira da kaifin kwakwalwa da tunanin da zai iya tunkarar waɗan nan azzaluman da suka zaɓi ɗaura RAWANIN ZALINCI a kansu, ya Allah ka bashi iko cika mun burina, ya Allah ka sanya mashi tsoronka da kuma aiki da abin da kace, kasa ya zamana Zaki a cikin zakuna mai ruguje ZALINCI ya kafa ADALCI tamkar jinin ABDUL MUTALLAF na hakika, ya Allah kada ka bar mahaifinsa........."
Bata kai karshen addu'ar tata ba wani irin azababben nishi ya kwace mata wanda ya sanyata dakatawa daga addu'ar nan take.
Babu wani sauran karfi da ya rage mata, dan haka nishin ma bata iya yin shi sosai ba, amma a haka take ta ƙoƙari tana fama, abin gwanin ban tausayi. Sai dai kuma abin mamaki a nan shi ne yadda take faman tana son ganin ta haihu tamkar wadda ta taɓa haihuwa, kamar ta san komai dangane da haihuwa, ga dukkan alamu wannan ba shi ne haihuwarta ta farko ba, idan ma shi ne to tabbas tana da sani sosai a wannan ɓangare, ko kuma likita ce ma.
Jim kaɗan ta saki wani nishi wanda ya zo mata da karfinsa, nan take baby ya faɗo cikin wannan ruwa, ya kuma faɗo duniya da kukansa na nuna alamar lafiyayyene.
Cikin sauri ta sanya hannu ta ɗauke shi, dan saboda kada ruwan ya kashe mata shi. A saman kirjinta ta manna shi sai kuka yake yi, ita ma sai a lokacin ta sami damar yin kuka sosai.
Jim kaɗan bayan faɗowar baby kamar da minti ɗaya wani sabon nakuda ya taso mata gadan gadan, kankame babyn nata ta yi a saman kirjinta tana salati a cikin zuciyarta tare da ciza laɓɓa, murkusoso ta fara yi, tana wani irin numfashi mai matuƙar ban tausayi.
(Kai ko ni Princess Teema ina son sanin labarin wannan mata, kuma ina yi mata fatar Allah ya amsa mata addu'arta ta samu mai kwata mata ƴanci kamar yadda ta buƙata😭 irin wannan azabar zalunci haka?😭)
Duk kuma wannan wahala da take ciki taki sakin babyn da yake hannunta, haka ta kankame abinta gam. UWA KENAN BA WANDA ZAI IYA YIN HAKAN SAI ITA!.
A nakuda na biyu bata wani wahala sosai ba, ba ta ɗauki lokaci ba shi ma sai ga nishi ya zo mata da karfi, nan take baby na biyu ma ya sake faɗowa, ga na farkon sai kuka yake yi mata, da faɗuwar baby kamar da minti ɗaya sai ga mahaifa ya biyo baya.
Mahaifa na faɗowa kuma ta nemi duk wani ciwon kaf ta rasa, Allah ya sawwaka mata.
A hanzarce ta ɗauko ɗayan babynma ta haɗe su a saman kirjinta, sai dai baby na biyun sam bai yi kuka ba, bai kuma yi motsi ba, tamkar babu rai a jikinsa, bata damu ba, kuma bata ma lura da babayn bai yi kuka ba, saboda kukan na farkon ya toshe mata kunne kuma ya ɗaga mata hankali, dan tana tsoron kada ace waƴan nan dakarun yaki da suka biyota ɗin suna kusa su jiyo kukan jariri su zo su hallakata su karɓe mata baby's su rabasu, saukin abin ma ɗaya da akwai karan zubar ruwan sama na tashi kuma suna cikin rami, so kukan baya tashi zuwa waje sosai.
Kasancewar har lokacin ruwan gudu nan na gangarowa cikin ramin ne yasa ruwan ya kai mata har izuwa saman cikinta a yanzu. Ganin hakan ne yasa ta yi yunkurin miƙewa tare da baby's ɗin suna manne a kirjinta.
Amma ina sam ta kasa tashi, wani irin kuka ne ta ji ya zo mata, yanzu idan wannan ruwa ya cika ramin ya zasu yi? Ƴaƴanta mutuwa fa zasu yi, abin ku da jarirai mutuwarsu ba zai yi wahala ba.
Tuna cewa idan ruwan nan ya cika ramin nan baby's ɗinta mutuwa zasu yi ne yasa ta sake yin yunkurin tashi, amma ina ta kasa, kara ƙanƙame ƴaƴan nata tayi tana ambaton sunan Allah da ya kawo mata ɗauki, ruwa kuma yana ta kara cika rami, ga ruwan sama sai kara karfin zuba yake yi, walkiya da kuma tsawa ya yawaita a sararin samaniya, duniyar ta yi duhu sosai tamkar dare ne.
TO KO TA YA YA WANNAN MATA ZATA FITA DA ƳAƳAN NAN NATA⁉️
A hankali ta dawo da kallonta a kan wannan baby daketa zuba kuka tamkar makoshinsa zai ɓalle. Wasu zafafan hawayene ta ji sun fara zubo mata a saman kuncinta gwanin ban tausayi, yanzu shikenan tana ji tana gani baby's nata zasu mutu a hannunta? Ita sam bata damu da kanta ba, burinta kawai ƴaƴanta su rayu, koda kuwa ita zata mutu, dan tana da yakini da kuma sa ran Allah zai amsa mata addu'arta.
Ga baby's ɗin kuwa, jajir da su, haskensu ma irin hasken Koreans ne, dukkanninsu idanunsu a rufe gam, kyawawan gaske ne na wuce misali, dogon hancin nan sak irin na mahaifiyar tasu, wannan mai ihun ɗan bakinsa ɗan karamin, bata duba me ta haifa ba, mata ne ko maza or mace da namiji, sai hankali a kwance ake wannan, ita dai ta rungume kayanta, amma fa ba karya kyawawa gaske ne baby's ɗin, bare ma wannan mai tsallah ihun, ɗan bakinsa jajir sosai, da yake yanayin fatarsu kalar madara kalar Koreans, sai jan lips ɗin ta kara bayyana over. Ɗayan baby dai shiru har yanzu bai motsa ba, da alama dai kamar babu rai a jikinsa, shi kuma lips nasa dark purple ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali.
Wannan baby da bai motsa ba gashin kansa launi ne mafi tsada a duniya, wato launin white color, ba irin normal white da kuka sani ba ne, a'a na babyn ya yi wani irin gold white ne a kwance yana ɗaukar idanu, mai azababben kyau da shi, ba kasafai aka cika samun masu irin gashin a duniya ba, sai ɗaiɗaiku, ɗaiɗaikun ma sai ta can ƙasashen AREWACIN DUNIYA, ta yanki Asia ta Arewa kenan, kuma a bincike ya nuna mafiya yawan masu gold white hair nan, ba karamar baiwa da basira ke garesu ba, amma sai dai kash baby baya motsi, yaki ya motsa, babu rai a jikinsa.
Ɗayan baby dake ta tsallah kukan kuwa, gashin kansa bakinkirin ne mai bala'in tsantsin gaske, ya yi tamkar an kifa mishi hula ne a kan nasa, tsabar bakin gashin nasa har ya yi tamkar dark blue, yana wani irin kyalli na daban, ga gashin nasu yar'yar sai tsawo ba cika, kana iya ganin farin fatar kansu, saboda rashin cikar gashin, tsawo kuma ya sauko musu har gaban goshinsu, ya kusa rufe masu idanu. A takaice dai dukkansu biyu suna da tsananin kyau na wuce misali.
A hankali hankali fa ruwan nan sai haurowa sama yake yi, yanzu ya fara taɓa mata baby's ɗin nata.
Kara haurar da su saman wajen shoulders ɗinta ta yi, tana mai cigaba da kuka tare da ambato sunan Allah da ya kawo mata ɗauki. Bata gaji ba, haka take ta kokarin miƙewa dan ta ceci ƴaƴanta, amma duk wasu gaɓoɓi na jikinta sunki yarda su bata haɗin kai wajen ta iya miƙewa, kada ku manta tana da ciwo a cikinta na kifiya da aka harbeta, ga kuma haihuwa, ai ta auna babban arziki ma da har yanzu take cikin hayyacinta, har yanzu tana karkashin kariyar Ubangiji dan shi kawai take ambata a baki da zucinta, idan kuma ka riki Allah to wlh wani abin idan Ubangiji ya hukunta a kanka, sai mutane su rinƙa kallon kamar tsafi ko asiri, saboda irin baiwar da kuma iko na mahaliccinmu, babu abin da ya fi karfin Allah a duniyar nan.
WANNAN ABIN DA SANYA MUTUN CIKIN TASHIN HANKALI YAKE...
*Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.*
*Ga waɗan da basu sani ba, ni ina da tsayayyen lokaci na yin posting nawa, 5:30 dai'dai nake yin posting na littafina, duk wanda yake a grp nawa lokacin TRIPLETS ya sani, sai dai idan matsalar network aka samu, amma 5:30 na yamma dai'dai nake update 💘*
E____________3🔥
Tana a cikin wannan hali Allah ya aiko mata wani bawan Allah, da alama maharbine, matashin saurayi ne mai jini a jika, yana da tsawo sosai, ga faffaɗar kirjinsa kamar wani zaki, jajir da shi kamar tsada, a shekaru ba zai wuce 15 years ba, dakakken namiji ne, dan daga ganin irin yanayin tsayuwar da ya yi a bakin ramin, alamu sun nuna ba rago bane, namiji ne sosai, ko da yake dama rago ba zai iya kasancewa a cikin irin wannan daji ba, duk wanda ka gani a cikinta to jarumta ta ratsa jinin jikinsa sosai!.
Yana sanye da irin takalmar nan na maharba mai kama da waterproof shoe a kafafunsa, irin kayan nan da ake saƙawa da zare da audiga ne a jikinsa, wandoce mai matuƙar kyau da aka saƙata da audiga, sakar hannu ce mai kyau, ta saƙu sosai, wandon launin brown color ce, ta sama riga ce mai karamar hannu launin white color, ita ma ta sakar ce, yana sanye da hular sanyi ta saka a kansa, hular ta kasance brown color kalar wandonsa, daga kugunsa ya ɗaura wata kyakkyawar belt launin white color kalar rigarsa, ita ma ta sakar ce.
Kayan sun yi matuƙar yi mashi kyau sosai da sosai, ga su tsab tsab, babu datti ko kaɗan, tamkar yanzu ya sakosu, kamar ba maharbi bane ba, da alama yana da matuƙar tsabta sosai, dan babu alamar kazanta, datti a jikinsa.
Kyakyawan gaske ne wannan matashi, kamar ba mutun ba kuma, jajir da shi, kalar fatarsa tamkar madara, tamkar bai taɓa fita rana ba, skin nasa har wani kyalli take yi, tamkar wadda ya girma a cikin A.c da kuma rayuwa a manya manyan jiga jigan gidajen manyan muryoyi a duniya, sam bai yi kalar wannan dajin ba ko miskala zarratin.
Yana da doguwar hanci mai matuƙar kyau, hancin nasa bata yi irin doguwa zud ɗin nan ba, ɗan dai'dai mai matuƙar ɗaukar hankali, kasancewarsa fari kal da shi, sai yasa pink lips nasa suka kara bayyana sosai, tamkar lips ɗin mace, har wani kyalli suke yi, saboda ruwan sama da ya jiƙasu, bakin nasa ɗan karami, yana da dara daran idanu farare kal kal kamar audiga, bakin cikin kwayar idanun nasa kuwa, ya yi bakin kirin da shi, irin bakin nan da zaku ga har wani kyalli yake yi, saboda ya yi baki siɗif, sexy eyes ke gare shi, yana da gashin gera mai yawa sosai, a cike suke, sai dai suna kwance luf, saboda tsantsi, ga wani bakinkirin ɗin saje ɗan dai'dai a face ɗin nasa kamar babban mutun, face ɗinsa ya kasance kamar egg face, wato fuska mai ɗan tsawo ba cancan ba, face ɗin nasa kuma tana da cika, ba'a rame yake ba, alamar ya ci ya ƙoshi, sam babu alamar yunwa a tattare da shi, daga yanayin zubin halittarsa ma sam bai yi kala da wannan dajin ba, yafi kama ne da ƴaƴan manya manyan mutane waɗan da maƙudan dukiya suke yi masu mubaya'a, hakika wannan matashin kyakkyawan gaske ne, kuma babu tsoro ko miskala zarratin a cikin waɗan nan dara daran idanuwan nasa, dan a bushe suke, zara zaran eyeslashes nasa nan a tsai tsaye suke, alamar babu tsoron da yake ji.
Yana rike da wata iriyar lema wadda babu irinta a yankin nan, ƙasashen Arewacin duniya ne suke amfani da irinta, lema ce wadda aka kerata da itace, abin gwanin ban mamaki sosai, komai na jikinsa ba irin na yau da kullum bane, sabbin kere kere ne a zamanin nan.
Yana wucewa ne yaji kukan jariri a wajen wannan ramin, shi ne ya ƙariso wajen dan ya duba, yana leƙa ramin ya gansu.
A hanzarce ya kara waro dara daran idanuwansa yana kallonta, kamar mai tsoron juyawa ya juyo a hankali yana kallon gabas da yamma gudu da arewa, abin ya bashi mamaki ne, mace da yara a cikin wannan daji kuma cikin ramin nan haka, dole ya yi waige waige ko zai ga wani abin, fuskarsa a cike fal da mamakin ganinsu.
Ko da ya jujjuya bai ga alamar mutun ko wani abin mai rai a wajen ba, hakan yasa ya dawo da kallonsa a kanta.
Duƙawa a saman gwiwowinsa ya yi tare da miƙa mata hannunsa a kan ta miƙo mashi baby's ɗin, ga ruwan sama na zuba mashi a kansa sosai, dan ganinsu yasa ya saki lemar hannun nasa ya faɗi kasa ba tare da ya lura bama, sun bashi tausayi ne ainun ga mamaki da al'ajabin abin.
Da farko taki yarda ta miƙa mashi baby's ɗin, sai da ta kalli da gaske ruwa zai cika ramin, dan izuwa yanzu ruwan ya hauro mata har izuwa kirjinta ta sama, sam ba'a iya ganin breast nata, ruwa ya rufe, hakan ne yasa ta yi hanzarin miƙa mashi wannan mai tsallara ihun.
Karɓa ya yi tare da ɗan ɗago jikinsa daga kan ramin kaɗan. Sam bai iya rike jariri ba, ga kuma cibiya a jikin babyn ba'a yanke ba. Haka ya ɗan kwantar da shi a gefe, sannan ya cire rigar jikinsa ya nannaɗo babyn a ciki, duk da rigar tasa ita ma a jike take, amma tafi babu gaskiya.
Kwantar da babyn a gefe ya yi tare da komawa ya kifa jikinsa a bakin ramin, dan ya karɓi ɗayan babyn.
Yana miƙa mata hannu ta yi maza ta miƙa mashi babyn, karɓa ya yi tare da ɗago da jikinsa, ya haɗe baby's ɗin duk ya kudundunesu a cikin rigar tasa, sannan ya mike da su tsaye daga wajen,