Saura kaɗan Hajiyarsu ta yanke jiki ta faɗi ƙasa saboda mamaki game da bakinciki, ta san dai tun da take da baban Zee, tun da ya kai shekaru goma a duniya, ya fara mallakar hankalin kansa ba ta taɓa yin magana ya ce a'a ba, komai ta ce mashi da daɗi da ba daɗi hakura yake yi ya amsa mata da to, kuma ya aikata abin da ta ce ɗin cikin biyayya matuƙar bai saɓawa Allah ba, dan ba'a bin umarnin kowa a aikata saɓon Allah, ko alamar ɓacin ran baya so ma ba zaka gani a face ɗinsa ba, kawai zai aikata umarninta, amma yau rana tsaka shi da bakinsa da girmasa yake mayar mata da martani? Abin da bai taɓa yi tun yana yaro ba!.
Wannan abin ya gigitata kuma ya zame mata izina a rayuwarta, yau ta ga ayar Allah ƙarara. Shiru ta yi tana tunani, gani take yi laifinta ne, sam bata kawo a ranta cewa Hauwa ta asirce shi bane, faɗi take a cikin zuciyarta koma me ya yi a halin yanzu laifinta ne, bawan Allah mai biyayya, ta takurawa rayuwarta shi da familynsa, ta hana shi sakat, ta ɓata mashi farincikinsa bayan kuma shi kullum ƙoƙari yake yi ya ga ya sanya ta farinciki, ta cusa mashi damuwa da tunani, duk wani walwala da yake yi sai da ta toshe mashi wannan kofa ya dai'na samun yinta, yanzu ga shi tura ta kai shi bango har ya juyo yana iya kallonta ido cikin ido ya gaya mata ta ɓatawa matarsa rai dan haka ta fita mashi daga gida? Wato ya gaji da irin cin mutuncin da suka rinƙa yi wa Maman Zainab shiyasa yanzu ba zai bari su yi wa amaryarsa ba, yau ga ayar Allah ido da ido ta gani..... Ita fa take wannan tunanin a cikin zuciyarta.
Wannan ba aya ce ga iya Hajiyarsu ba, ina fatan ya zama izina a garemu mata gabakiɗaya, idan yaro yana yi maki biyayya, yana binki sau da kafa, to fa ki yi ƙoƙari kiga kin kyautata mashi kema, kuma ki yi ƙoƙari taya shi neman farincikinsa kamar yadda yake yi maki, in dai ba abin cutarwa kika ga zai aikata ba kada ki matsa mashi wajen ganin kin hana shi yi, zuciya wani lokaci wawan abu ne, kuma wannan ɗabiarmu ce mata, idan munga mutun yana yi mana biyayya yana kyautata mana sai kawai mu yi ta bashi umarni ba kakkautawa, komai sai mu nuna mashi iko, mu hana shi sakat, tabbas wannan ɗabi'ar kaso tamanin cikin ɗari na mata suna aikatata. Ki sani idan kika takura mashi, yana yi maki biyayya kika matsa mashi ke kuma, kika hana shi sakat da wasu umarninki da ba wahayi ne daga sama ba, wlh a kwana a tashi zuciyarsa zata juya maki baya, musamman idan ya haɗu da abin da yake matuƙar so ke kuma kika hana shi, tabbas zuciya bata da ƙashi, ko bai yi maki rashin kunya ba zai ja baya dake, zai ji baya sha'awar ya rinƙa zuwa in da kike, zai ji kin fita a ransa!. Ga kuma shaiɗan a gefe da zai ƙara ingiza zuciyarsa da ya gujeki!!.
To dan haka ni dai shawarata a gareku iyaye masu ƴaƴa ƴan albarka masu biyayya, da ma mata da basu rigada sun zama iyaye ba, shawarar da zan baku shi ne, duk wanda yake sonku yake kyautata maku, yake yi maku biyayya, yake bin umarninku, ku daure ku so duk abin da yake so matuƙar ba cutarwa ce a gare shi ba, ku daure ku so nashi farincikin shi ma, kada ku yi la'akari da ku kuka haifesa dole ya bi umarninku, Allah da ya halicci mu gabaɗaya ma bai ce dole dole mu bi abin da ya halicci mu dominsa ba, saboda yana da wuta da aljanna! Ki sani idan har zaki daure ki bi farincikin ɗanki mai yi maki biyayya, ki so shi ki so abin da yake so, wlh a kullum sonki karuwa zai rinƙa yi a cikin zuciyarsa, zai ji yana son ganinki a kusa da shi, zai ji shi idan ba gida ɗaya tare da ke bama ba zai iya zama ba, bare ace kina son familynsa, ƴaƴansa ma suna sonki, wlh duk yadda zai yi sai ya dawo dake kusa da shi domin ya cigaba da samun farinciki, ba ƙaramin daɗi yake ji ba idan yaga kina kaunar familynsa, ji yake kamar ya haɗiyeki dan soyayya, zaki ga komai kika ce cikin rawar jiki zai amsa maki, sai kiga ya fi umarnin da kike zama ke Hajiya two seater ki ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya ki zayyana mashi su kamar wadda aka saukowa da wahayinsu, ke sam ba zaki yi tunanin halin da zai shiga ba, bukatarki kawai dai ta biya kamar dai Hajiyarsu baban Zainab....... Abin da yasa na yi maku wannan magana saboda rayuwar gidansu Zainab abu ne wanda yake faruwa a cikin al'umma sosai da sosai, to fisabilillahi mata ku ɗauki hanyar gyara domin farincikin kanku da ƴaƴanku haɗe da jikokinku, Allah ka yafe mana kura kuranmu ka iya mana da iyawarka, ka jikan iyayenmu da suka rigamu gidan gaskiya, waɗan da suke raye kuma Allah ka kara masu lafiya da nisan kwana, Allah kasa mu cika da imani, na so na bawa ƴan'mata ma shawara, amma babu lokaci zaku cinye mun filin page ɗin, sai wani lokaci idan alkalamina ya zago ta makamancin hakan.
Sosai Hajiyarsa ta shiga yin danasanin abubuwan da ta yi wa Maman Zainab, dan ita a tubaninta ita ce ta hasasa komai, kuma ba shakka tana da hannu a ciki kam, domin idan da bata biyewa son zuciyarta ba, ta tsaya ta yi mashi addu'a, tana son ganin farincikinsa wlh da wane mutu, wane kaniyar Hauwa ta iya yi cin nasara a kansa, wai kun san karfin addu'ar iyaye kuwa? Musamman ma uwa! Wlh da tana yi mashi addu'a ko shi baya yi sosai babu abin da ya isa ya taɓa shi, amma ta tsaya biyewa son zuciyarta maras amfani, to yanzu ga shi an raba ta da shi, kuma shi ɗin nan dai shi ne mai ciyar da su, shi yake rike da ita da ƴan uwansa su maman Haidar, to yanzu ba dukkansu sun yi rashi ba? A yadda yake ɗin nan ina wani zance kula da su? Ai sai dai kowacce ta ciyar da kanta a yanzu, dan yanzu dai Hauwa ce mai mulki da komai, kuma kunsan Hauwa ƴar tijara kam ba yi masu zata yi ba, sai dai ma ta hana ayi masu! To mata bana son ko wacce readers ɗin litattafaina ta faɗa irin wannan aikin danasanin maras amfani, kun ga aya a fili, da mamarsa tana son abin da yake so, tana zaune cikin kwanciyar hankali da shi tana zuba mashi ruwan addu'oin ai da wane uban Hauwa ta yi nasara a kansa. Dan Allah mata mu gyara.
...........Ni kam anya Hajiyarsu ma bata fi shekaru goma rabon da ta yi mashi addu'a ba kuwa?🤔😅 Mata kullum cikin mashifa da kuntatawa familynsa, bata san idan ta kuntatawa familynsa shi ta kuntatawa ba, ta biyewa su Maman Haidar sun kaita sun baro, kai wato mu mata akwai shegen son girma🤔 kawai ki dake a saman kujera ki ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya kina jerowa yaro umarni babu ruwanki da halin da zai shiga🤔 Allah dai ya shiryamu wlh...............
Jiki a mace Hajiyar tasu ta ce da su Maman Haidar su zo su koma gida. Da mamaki suke kallonta, a tunaninsu ai umarni zata bashi a kan lallai dole ya saki Hauwa, amma sai suka ga akasin haka!.
Juyawa ta yi ta nufi hanyar fita ba tare da ta sake yi wa su maman Haidar ɗin magana ba. Har ta kai bakin kofar parlour sai kuma ta juyo da kallonta a kan maman Zainab dake zaune shiru ta mayar da su Tv tana kallo.
Allah sarki maman Zainab sarkin tausayi, gabaɗaya sai ta ji mugu mugun tausayin tsohuwar ya kamata, amma ko sannu bata ce masu ba, dan koma me ya faru su suka ja wa kansu!!.
Ƙasa iya yi mata magana Hajiyar tasu ta yi, gabaɗaya kunyar Maman Zee ɗin ma take ji, sai kawai ta juya ta fice daga parlourn zuciya cike tab da danasani maras amfani.
Da sauri su Maman Haidar ɗin suka rufa mata baya. Suna barin gidan Hauwa ta dawo da tijararta a kan maman Zainab dake zaune shiru.
Ai tsabar tsanar da maman Zee ɗin ta yi masu ma ko tanka mata bata yi ba, dan cewa ta yi magana da Hauwa ma zunubi ne babba, dan haka ita bata sake buɗe baki ta kulata.
Sai tijara Hauwar take yi! Ko ci kanki Maman Zainab bata sake ce mata ba, yadda kuka san ta zagi sama ko kuma da mutun mutumi take magana ba Maman Zee ba. Da dai taga ba kulata zata yi ba, sai ta ce da baban Zainab lallai lallai yau sai ya zane Zainab a gidan nan ko kuma ta bar mashi gidansa.
Ta yi hakan ne dan ta ƙuntata zuciyar Mamam Zee, sai dai nan ma dai kamar babu Maman Zee a parlourn, sam bata nuna kamar ma ta ji me suke faɗa ba.
Da ta ga hakan sai ta ce da Baban Zee ɗin su je ɗaki su tattauna a kan batun auren Khadija da Haidar, dan wannan aure babu fashi wlh.
A wannan karon ne maman Zainab ɗin ta ɗan ɗago idanu ta kalleta amma bata ce komai ba. Wani irin shu'umi kuma munafukin murmushi Hauwar ta sakar mata, dan ta ƙara kona mata rai. A cikin zuciyarta kuma tana faɗin ai wlh tun da baki son Khadijah ta auri Haidar to ba shakka sai anyi auren nan cikin satin nan tun ubanta a hannuna yake, bani da burin da ya wuce in ga ina ƙuntatawa rayuwarki!!............Tashin hankali!! Hauwa fa ƴar iskace bata da mutunci ko kaɗan wlh!! Kowa yasan ko yau ta ce a ɗaura auren nan sai an ɗaura ba fashi, dan uban gayya umarninta yake bi!. Akwai matsala.
Kawar da kallonta Maman Zee ɗin ta yi, still dai bata tanka mata ba. Cikin ɗaki suka shige da baban Zainab tana gaya mashi yadda za'ayi tsare tsaren bikin, duk dan ta bakantawa baiwar Allah maman Zee rai. Shi kuma baban Zainab komai ta ce sai ya ce yadda kike so haka za'ayi ai Hauwa'u na!.
Suna shiga cikin ɗakinsu ita ma Maman Zee ta miƙe ta nufi ɗakin da su Khadijah suke a ciki.
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️
KINGDOM OF POWER 💪🔥💘
Zaune Yah Jawad yake a kusa da King saman bedside drawer, while King ya saman katafaren bed ɗinsa, suna ɗan fuskantar juna, King dai yana aiki ne a laptop ɗinsa kamar yadda ya saba, dama idan baku manta ba ya ce Jawad ɗin ya zo ya same shi.
Shiru Yah Jawad ya yi alamar ya luluƙa duniyar tunani, gabaɗaya yana jinsa babu daɗi, haka kawai yake jin baya son zuwan ƴan uwan nan nasa da za su yi gobe.
Sau uku King yana yi mashi magana bai amsa ba, ya luluƙa duniyar tunani. Sai da ya ɗan taɓa shi ne ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya tare da ɗago idanunsa zuwa saman face ɗin daddyn nasu.
"Daddy ka kammala aikin ne?". Ya tambaya yana tattaro hankalinsa da nutsuwarsa waje guda.
"Jawad menene yake damunka har haka? Tunanin me kake yi haka da har na yi magana baki uku baka ji ba?".
Ɗan zaro idanu ya yi yana mamakin jin daddyn nasu ya yi magana har baki uku yana can yana tunanin da shi kansa bai san me yake tunawa ba..... Tirƙashi.
"Daddy wlh ni ma fa ban san tunanin me nake yi ba, kawai dai ban ji me ka ce ba".
Shiru King ya zuba mashi idanu ba ƴan sakanni kafin ya ce. "Jawad ka gaya mun me yake damunka? Ina Jaish yake kuma yau bai shigo ba?".
Ɗan shafa arab hairnsa ya yi tare da ƙaƙalo murmushin dole. "Daddy babu abin da yake damuna, Jaish kuma i think ya fita shiyasa bai shigo ba, idan ya dawo da wuri nasan zai zo".
Ajiyar zuciya King ɗin ya sauke kafin ya ce. "Jawad meyasa baka jin tausayin maraicin ka ne? Meyasa kake son ɗaurawa kanka damuwa? Matsalar wajen aiki ce ko ta cikin gida? Ni fa daddynka ne, duk duniya baka da biyuna, ko Abbas bai kai ni kusanci da kai ba, dan shi kansa Abbas da hakwaranka sama da goma ya zo ya sameka tun bayan da ya miƙa mun kai kana cikin tsumma, a tunanina babu wanda ya fini sanin halinka, dan haka kawai ka gaya mun gaskiyar me yake damunka? Ko dai kana da wani mahaifin bayan ni ne?".
Da sauri ya fara girgiza mashi kai bawan Allah. "Daddy tabbas babu wanda ya kaika sanin halina, kuma tabbas bani da wani mahaifin da ya kaika, haka zalika babu wanda nake kauna number one a duniyarnan sai kai, kai ne farincikina daddy, kuma nasan ka sanni in and out, tabbas nasan kaga damuwa a tattare da ni ne yasa ka matsa mun sai na gaya maka menene? Amma daddy ka yarda da ni wlh ni ma ban san me yake damuna ba".
"Kana kewar mummynka ne?". King ya jefa mashi tambaya cike da tsantsar tausayinsa, yana kaunar Jawad over, kuma yana tausaya mashi saboda wasu abubuwa da suka faru a shekarun baya.
Guntun murmushi ya yi kafin ya amsa da. "Daddy ni da ban san ya kalar mum ɗin nawa ma yake ba meyasa zan yi kewarta har haka? Ina kewarta amma ba har haka ba, wanda ya rayu da uwa na ɗan lokaci ne idan bata nan zai yi kewarta, ni da na tabbata ko rayuwar 30 mins ban yi da ita ba ya za'ayi na ji kewarta har haka? Ban san daɗinta ba kuma ban santa ba, kai da Momma kune komai nawa, idan akwai wata uwa da zan yi kwatarta to Momma ce, kuma tana part ɗinta, a duk lokacin da na ji kewarta zan je in ganta, dan haka daddy ni bana wani kewar mum".
Haƙiƙa King ya yarda da maganarsa na cewa shi kansa bai san me yake damunsa ba, amma kuma abin ya tsaya mashi a rai sosai.
Ƙoƙarin kawar da zancen King ɗin ya yi ta hanyar sako wani topic dan ya ga ya kore mashi damuwar da take kwance a saman face ɗinsa.
"Aure kake so ko?". Ya jefa mashi tambayar yana kura mashi ido.
Zaro idanu sosai Jawad ɗin ya yi, sai kuma ya saki siririn murmushi sakamakon gera guda da King ɗin ya ɗaga mashi.
"Daddy ni fa ba wani auren da nake so". Ya yi maganar yana ƙoƙarin tuɓune fuska irin shi da gaske yake yin nan.
"Ai duk wanda zaka gansa a cikin damuwa, ka tambaye shi me yake damunsa ya ce maka bai sani ba, to tabbas aure yake so, aure kawai zan yi maka kai da Jaish, shi ne maganin damuwar da ba'a san mecece bace".
"Daddy aure fa? To ina zaka samo matan da zaka aura mana ɗin? Ni kam ma dai bana so gaskiya daddy, wata kila dai Jaish, kuma ni daddy Allah ba damuwar aure bace take damuna".
"To me yake damun naka? In dai baka gaya mun me yake damunka ba to ba shakka damuwar rashin aure ce take damunka, kuma zan yi maganin abin, dan ba zan iya cigaba da zuba ido ina ganin my son cikin damuwar da shi kansa bai san na mecece ba".
"Daddyyyyyyyyyy ka fara ko? Ni fa da gaske ba rashin aure bane yake damuna, wai daddy su Yah Ramish da suke manya ma basu yi aure ba sai mu ƴan yara? Kawai salon ka ja mu tsufa da wuri, ni Allah bana so". Yana magana yana kawar da kai, dan kada su haɗa ido da daddyn nasa ya saka shi dariya, saboda ya turɓune fuska ne irin ace da gaske yake yin nan.
"Da gaske baka so?".
Kai ya gyaɗa mashi alamar e da gaske yake yi.
"To shikenan, amma gaya mun me a tsakaninka da Jannat?".
Da sauri ya dawo da kallonsa kan daddyn nasu. "Jannat kuma daddy?".
Gera guda kawai King ya ɗaga alamar e ita dai.
"Kai daddy kai daddy, ni babu abin da yake a tsakanina da ita, sister mafi soyowa ce a gareni ita da auta, bayan haka babu komai".
"Da gaske?". King ya yi mashi gatse.
"Kai daddy wai ba zaka bar tsokanata ba? Da gaske mana babu komai".
Ɗaure fuska sosai King ya yi alamar babu wasan nan, cikin nuna isa ya ce. "Me kaje yi a bedroom ɗinta ranar wuraren karfe 11, ka san dai na kamaka a bedroom nata ba sau ɗaya ba sau biyu ba ko? Haka zalika na kamaka da ita a room na Akka, kai har room ɗin nan nawa baku bari ba, daning room ma baku bari ba, and da kuka fita ranar ina kuka je?". Yana magana yana kara ɗaure fuska.
"Daddy ni fa addu'ar barci nake zuwa yi mata a room ɗinta, kuma ba ita kaɗai ba har da Auta, wai to daddy laifine dan yaya ya ɗauki kannensa sun fita yawata gari? Kuma ai kaga a tare da auta muka je, ni daddy ba zaka barni na huta ba ko?".
Wani irin kallo ya wurga mashi wanda sai da ya saka shi sakin murmushi. "Kai daddy kai daddy ka fara ko? Ni Allah wani lokaci kamar nayi kuka nake ji idan kana yi mana irin wannan abin, gaskiya fa na gaya maka babu komai a tsakaninmu".
"To ka ji nace karya ka gaya mun ne? Ko dai ka tsargu ne? Babu rami me ya kawo maganar rami? Kai da kanka da yake kasan ba gaskiyar ka faɗa ba duk ka tsargu, ka ruɗe kana ta maimaita kalmar gaskiya ka faɗa, to shikenan na ji addu'a kake zuwa yi mata a room ɗinta, shi kuma room ɗin Akka da nawa room ɗin fa? Ko nan ma addu'a kake zuwa yi mata?".
Kamar zai yi kuka ya ce. "Daddyyyyy tom shikenan duk yadda ka ɗauki tsakanina da Jannat haka ne, amma dai ni nasan babu abin da yake a tsakaninmu, kuma zaka iya tambayarta ma ka ji, amma please daddy ka bar zancen auren nan