x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 94 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 279001 words
  • 282000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 381

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
bata taɓa nuna mashi wani mugun abu ba tun yana yaro, ta riƙe shi kamar ɗan cikinta, bai san da cewa Allah ne ya taimakesa yake tsalle rijiya da baya daga tarkonta har ya kawo yanzu da Allah yasa ya girma ba, bai taɓa kamata tana ƙoƙarin cutar da su ba ko da sunan wasa, to wannan soyayya da ta nuna masu a zahiri kamar uwarsu yasa suke yi mata biyayya sosai. Baɗininta kuma Allah ne kaɗai masani, Allah ne kaɗai yasan me take shirya masu na mugunta? Kuma menene kudirinta a kan Kingdom namu, Allah masani sai alƙalamina, makirar mata ce sosai, ta iya makirci ta yadda ko baka so sai ka yarda da ita ba muguwa bace ta Allah ce, ta iya takunta sosai.

So a takaice dai yanzu ga shi tasa dukkansu biyu suna matuƙar kaunar Chuchu ba tare da sun san da cewa ɗaya yana sonta ba, ita kanta Chuchun tana kaunarsu dukkansu biyu, sai dai kaunar da take yi wa Jawad na matsayin yaya da kanwa ne, shi kuma Rizwan bayan yaya da kanwa akwai na masoyi a gefe, wlh Mammie ta cucesu over, a yanzu haka duk wanda ya auri Chuchu daga cikinsu zuciyar ɗayansu wanda bai aureta ba sai ya cutu, koma dai ya zama sanadin ajalinsa, kuma su biyun duk randa ɗaya ya gane ɗaya yana sonta to ba shakka ɗayan zai hakura ya barwa ɗan uwansa..... Akwai matsala kam babba ma kuwa. Gaskiya Mammaien ba ƙaramar muguwa bace wlh! Ta cika bakar azzaluma! Dan ba ƴaƴanta bane shi ne ta gwara kansu a kan mace ɗaya! Ko me dalilinta na yin hakan? Wato su mutu idan ma zasu mutu, Allah sarki shi kuma Rizwan yana ganin kaunarsa take yi sosai har yasa ta zaɓa mashi kyakkyawar mata na gani na faɗa, wadda duk namiji mai lafiya dole ya sota! Har da kara kaunar Mammaien ya ji yana yi da ta yi mashi hakan, bai san rami mai zurfi ta tona ta kuma kunna wuta a cikin ramin sannan ta tura shi ciki ba, shi ya ɗauka madarar kauna ce zalla.
(Wai nikam na ce ba ko dai so take duk su haɗiyi zuciya su mutu dan ita bata ɗa namiji ne? 🤔 Ku tayani duba my people's)

STORY🔥

"Babu komai Yah Rizwan".

Daga other side Rizwan ya ce. "A'a Jawad, babu komai kuma? Ni zaka ɓoyewa abin da yake damunka? Idan baka gaya mun ba waye zaka gayawa? Ko kana son ne nima ka hanani yin barci, ka hanani yin komai? Kasan ba zan iya aikata komai ba matuƙar kana cikin damuwa ko?".

"Yah Rizwan please kada ka kwana da damuwa, zan gaya maka, bana son naji wani abin yana damunka". Ya yi maganar tare da nufo kofar fita. Har zai fita kuma sai ya tuna kada Chuchu ta ji abin da zai ce, dan haka sai ya koma ya tsaya a in da yake tsaye ɗazun.

"To gaya mun menene yake damun zinariyar zuciyar ɗan uwana?". Rizwan ya faɗa.

"Yah Rizwan ba komai bane face kewar ɗan uwana Jaish, haka kawai na ƙasa samun nutsuwa a tafiyar da ya yi, kada ka gayawa kowa fa ya yi tafiya, tafiyar sirrice, amma duk na damu sosai, sai nake jin kamar na bishi, mun yi waya da shi ɗazun yake ce mun yana kewata sosai, da tunanina ya yi barci ya tashi, ina jin kamar bani da lafiya ne haka".

Shiru Rizwan ɗin ya ɗan yi na ƴan sakani kafin ya ce. "Shikenan my pleasure, ka yi mashi addu'a, kuma ka cire duk wani banzar tunani a ranka, babu komai In Sha Allah, bana son ganinku cikin damuwa, amma idan kaga ka damu sosai to da safe ka bishi kawai, dan ba zan lamunci ganinku cikin damuwa ba"

"In Sha Allah Yah Rizwan zan dai'na damuwa kuma zan yi mashi addu'a". Ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya.

"To shikenan ka kula mun da kanka sosai da sosai".

Da okey ya amsa kafin shi ma ya ce yayan nasa ya kula mashi da kansa, suna kaunar juna sosai, da haka suka yi sallama. Suna sallama ya nufo waje.

Kasancewar ɗakin da duhu dan King ya kashe wutar yasa sai ya kunna hasken wutar wayarsa, nan take haske ta gauraye wajen, gaban bedside drawerta ya je ya zauna.

Hannu ya kai ya yi ƙasa da bargon da King ya rufeta da shi ita kuma ta kara ja har sama ta rufe kanta gabaɗaya. Ƙasa ya ɗan ja bargon zuwa dai'dai kirjinta, hasketa ya yi da hasken wayarsa, ta lumshe idanu kamar mai barci.

Zubawa kyakkyawar fuskarta idanu sosai ya yi, a nan ne ya fahimci ba barci take yi ba, da gangan ta lumshe mashi idanunta. Siririn murmushi ya saki kafin ya kai hannu ya ɗan shafi face ɗinta. "Tashi to, na gano baki yi barci ba".

Kin kula shi ta yi, irin ita a dole ta yi barci da gasken nan, ga kuma idanunta yana gani suna rawa duk da suke lumshe. Jin taki kula shi ta dake a zaman dole ta yi barci ne yasa ya kifa wayarsa a saman bed ɗin ta wajen hasken, nan take duhu ya karaɗe ko'ina. Hannu ya kai ya toshe mata hanci saboda tsokana.

A firgice ta buɗe idanun haɗe da cewa. "Wayyo Yah Jawad zaka kashe ni, wai me nayi maka?".

Zame hannunsa ya yi ba tare da ya yi magana ba. Ajiyar zuciya ta sauke tare da yunƙurawa ta miƙe zaune. Wayarsa ya ɗauko daga kifata da ya yi, haske mata fuska ya yi tana ta aikin turo baki.

"Awww ashe baki yi barcin ba, amma meyasa kika yi mun barcin karya?".

Tana aikin turo baki ta ce. "Ni fa wasa na yi maka, amma shi ne ka kusa kashe ni?".

"Da gaske wasa aka mun?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e.

"Jannat ya za'ayi in kashe ki? In na kashe ki ai kai'na na kashe! Dan nima ba zan kai labari ba! Kina mutuwa zan biki! Nima da wasa na toshe maki hanci, baki ga na sakeki da wuri ba? Ai na sake ki da wuri ne dan ma kada wani abin ya samun min ke". Yana magana yana kara kare mata kallo daga sama har ƙasa, dan iya shege sai kalle mata kirji yake yi a cikin sleeping dress ɗin, da yake kayan sun zauna a jikinta dai'dai ita, sai alamar komai ya bayyana.

Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Amma fa Yah Jawad akwai wahala idan aka toshewa mutun hanci!".

Ɗan zaro idanu ya yi tare da cewa. "Kunji wahala ne?".
Kai ta gyaɗa mashi alamar e.
"Kaɗan fa na ɗan rike maki hancin, amma kin ji wahala?".

Kai ta gyaɗa mashi still tana turo baki. Hannu ya kai ya ɗan shafi kumatun nata. "Sorry my Jannat, ba zan ƙara ba, to yi murmushi".

Haɗaɗɗen murmushi ta sakar mashi wadda ya sanya shi sakin murmushi shi ma. "To shikenan ni zan wuce bedroom ɗina, sai da safe ko?".

Ƙasa ƙasa ta ambaci sunan. Lafiya ya amsa mata da shi. "Allah Yah Jawad bana son ka tafi, ina jin daɗin yin hira da kai".

Ajiyar zuciya ya sauke tare da duba time a wayarsa. 11:44, "Jannat dare ya yi fa, ki kwanta ki yi barci akwai school gobe".

Ɗan turo mashi baki ta yi kafin ta amsa mashi da to. Miƙewa ya yi zuciyarsa cike tab da tunanin zai yi kewarta, ɗan matsowa ya yi ya bata sumbata a goshinta kafin ya ce ta kwanta bari ya mayar mata da bargonta ya lulluɓeta.

Ba musu ta kwanta, ya lulluɓeta, zuciyoyinsu bai so rabuwa ba, amma haka ya yi mata sallama sai turo baki take yi ya fice zuwa nasa room ɗin. Yana tafiya ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita ba tare da ta kunna wayarta ba, daɗin hira da Yah Jawad yau yasa ta manta da hira da Yah Rizwan.

Shi kuwa a nasa ɓangaren ko da ya kwanta bai iya yin barci ba, tunani ne kala kala cike tab a ransa, har wuraren karfe 2 ya gagara barci, daga karshe ya miƙe ya ɗauro alwala ya zo ya fara gabatar da nafilfilu.

Washegari da safe misalin 6:30. Shirye yake cikin wandon Jeans baka, daga ta sama t-shirt fara ce tas, sai ya ɗaura long coat zuwa gwiwarsa a saman kayan, ita ma coat ɗin baka ce kalar wandonsa, takalmar kafafunsa ma bakake ne, matsayinsa na farar fata sai bakaken kayan suka yi mashi kyau, ga arab hairnsa bakin kirin da shi ya sha gyara.

Kai tsaye part ɗin Akka ya nufa sai zuba kanshi yake yi, office zai je yau da wuri, amma yana da buƙatar sanya ta a idanunsa kafin ya tafi, yasan kuma a part ɗin Akka kawai zai sameta by this time around.

Dai'dai zai shiga part na Akkar shi kuma uncle Taheer kanin Mama yana fitowa, kusan karo suka yi, da sauri ya ɗan ja da baya yana faɗin good morning uncle. Fuska ba yabo ba fallasa ya amsa mashi tare da tambayarsa ya ya kwana ya kuma ya wayi gari. Da Alhdulillah ya amsa kafin ya wuce ciki, shi kuma uncle Taheer ɗin ya fice ya nufi part na mama dan ya duba jikinta............. Allah sarki mama, su Omaid sun ja mata bala'i, sun barta da jinya, suna can gidan Abu Abdussalam, ko me suke aikatawa yanzu?...🤔

Baki a ɗauke da sallama ya shiga cikin ɗakin. Babu kowa sai Chuchu dake ta ƙoƙarin sanya uniform ɗinta, yanzu Akka ta shiga toilet bayan sun gama gaisawa da uncle Taheer, ita kuma Chuchu uncle Taheer ɗin yana fita ta hau shirin zuwa school, dama ta yi wanka shigowarsa ɗakin yasa ta zauna suka gaisa.

Ta zura rigar a kanta tana kokawar sauke shi ƙasa, da yake rigar dai'dai ita yake hakan yasa sanya shi yake ɗan yi mata wahala.

Cike da tsokana Jawad ɗin ya ƙariso ciki, samar rigar ya rike ya hanata janyo shi ƙasa. Ja da karfi ta yi sai ta ji kamar an rike, ga shi bata iya gani bare taga wanene? Dan ta zura rigar a kanta.

A ƙule ta ce. "Auta bana son walaƙanci fa, zaki sakar mun riga na samu na sauke shi kasa na shaki numfashi ne ko sai kin kashe ni?".

Shiru bai amsa mata ba, sai ma da shaiɗan ya ɗan ruɗesa ya zura hannunsa daga ta bayan nata izuwa saman plat tummynta.

Janyota ya yi ta zo jikinsa. Sai surutu take yi a tunaninta Auta ce, sai da ya ɗan wahalar da ita kafin ya sakar mata rigar tare da jan mata shi ƙasa har lokacin hannunsa yana saman cikinta.

Yana sakar mata rigar bayan ya sauke mata a hanzarce ta fara ƙoƙarin juyowa domin taga wanene? Hanata juyowa ya yi ta hanyar ƙara ƙanƙame mata ciki. A garin ƙanƙame ta ɗin kuwa hannunsa ya ɗan haura sama izuwa kusa da kirjinta, hakan yasa ta kurma ihu mai sauti wadda tasa dan dole ya saketa a ɗari ya shiga dressing na Akka.

Yana shiga Akka kuma ta fito daga cikin toilet cikin zafi tana faɗin. "Nashi uku! Jannat lafiya? Ihun me kike yi?".

Ƴar waige waige ta fara kamar mai neman wani abin, kuma fa ta gansa lokacin da ya shiga room ɗin, amma ta rasa ita kanta waige waigen me take yi, ta kuma rasa me zata gayawa Akkar.

Shi kuwa sai addu'a yake yi Allah yasa kada Jannat ta gayawa Akka shi ne ya taɓata ta yi wannan ihun, yasan halinta sarai, idan ba shi ya ce kada ta faɗa ba Akka na tambayarta zata shi ne ya zo ya taɓa mata kusa da kirji, yasan yanzu da wuya idan ba gaskiya zata gayawa Akkar ba, ya shiga talatin yau ba uku ba. Da alama addu'ar King na daren jiya ne ta kama shi, dama King ya gaya mashi one day one time Akka zata kama shi yana yi mata soyayya a ɗaki, kuma idan ta kama shi ya shiga uku, to da alama yau ranar tonon asiri ne.......

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

ABU ABDUSSALAM EMPIRE 🤍🔥

Ko da Leesharh ta shiga cikin kitchen ɗin sai ta rasa ina zata nufa, ma'aikata ne birjik suke maƙare a ciki suna ta aikin dake gabansu, babu wadda ta ɗaga idanu ta kalleta ma bare ta sa ran zata iya tambayarta.

Da farko a tunaninta abin da sauki ne, sai yanzu ta fahimci isn't easy ooooo, damuwa ta shiga sosai, ta rasa wa zata tinkara da zancen?. Ta juya gabas da yamma gudu da arewa a cikin kitchen ɗin nan bata ga ƴar aikin da fuskarta yake a sake bama bare ta tinkareta, ga shi babu wadda ta kulata, sai ka ce basu ji shigowar mutun ba.

Ita fa Leesharh bata ma san da cewa masu girki daban, masu shirya abinci a parlourn daban, sannan masu serving ƴan gida abinci suma daban, bugu da kari masu kaiwa zaratan samarin gidan abinci suma daban suke. To a gabaɗaya cikin kitchen ɗin nan a yanzu dai iya masu yin girke girke ne a ciki, a lokaci guda sai a girka abinci almost kala sha biyu, kunga kuwa dole masu yin girkin su kasance suna da yawa, kowacce da aikin da take kamawa, haka zalika kowacce da kalar girkin da take yi, kun san laraba da iya shirya abinci kala kala a saman table. Idan suka kammala yin girkin ne sai masu kwasa su kai dining room su shirya a saman table kuma su zo su fara aikin jidansu su kai, masu kaiwa su Ramish suma su zo su kwasa nasu, haka tsarin gidan yake,

Ta kai almost 30 mins a tsaye a tsakiyar kitchen ɗin babu wadda ta ce mata ko ci kanki. Da dai taga tsayuwa ba zai amfana mata da komai ba sai ta duba a cikinsu ta ga mai ɗan dama dama dan ta nufeta.

Can ta hango wata ƴar matashiyar yarinya da ba zata wuci 17 year ba a duniya, sai aikin yanka kayan lambu irin su Chinese cabbage, cucumber da dai sauransu take yi. Ita kuma sune aikinta, sai ta wuni tana aiki ɗaya, dan duk girkin da za'ayi ana amfani da haɗin salad dan cin abincin, da rana haka da daddare haka, ga gidan da girma da kuma yawa, cikin wani katon kwando mai girma take yankawa, da yake ta saba sai sam bata ganin wahalar aikin.

Sannu Leesharh ta yi mata, yauwa ta amsa da shi, ta amsa kuma ba tare da ta ɗago ta kalli Leesharh ɗin ba, saboda aikin da yake gabanta, daddatsa su cabbage ɗin take yi babu wasa, cikin sauri sauri saboda ta kware, kwararriya ce.

Shiru ta yi tana tunanin ta yadda za'ayi ta tambayi wannan yarinyar abin da take buƙata. Ta ɗan yi nisa cikin tunanin da take yi kawai ta tsinkayo muryar yarinyar a kunnenta tana faɗin. "Kina buƙatar wani abin ne? Da me zan iya taimaka maki?".

Tana ƙoƙarin yin magana wani tunani ya faɗo mata a cikin ranta, ba komai bane kuma face tunawa da ta yi da akwai cameras sosai a cikin kitchen ɗin, tambayar mai kaiwa Ramish abinci a wajen babbar barazace a gareta, dan ana ganinsu. Tuna haka yasa ta yi maza ta juya ta fita ba tare da ta sake cewa yarinyar ko sannu ba......... Kai Leesharh fa tana da basira sosai yarinyar.

Kai tsaye room nata ta nufa domin ta je ta sake yin tunani a kan mafitarta. A dai'dai lungun da ta yi wa Ramish laɓe ɗazun suka ci karo da mutun, kasancewar wajen babu wadatatcen haske dan a tsakanin ɗakuna yake, kuma wajen babu Camera.

Rashin haske yasa bata san da waye ta yi karo ba, sai dai koma wacece tabbas macece, dan karon da suka yi kirjin wancan ta buji kafaɗunta, to ta ji tana da breast. Wucewa ta yi da sauri ba tare da buƙaci sanin da waye ta yi karo ba. Ita ma wadda suka yi karon a hanzarce ta wuce kamar maras gaskiya.

Dakatawa da yin tafiya Leesharh ta yi tare da juyowa ta bi yarinyar ne ko matar za'a ce ne da kallo, haka kawai sai ta ji gabanta ya faɗi, ji tayi bata yarda da matar ba, duba da yadda ta wuce da sauri kuma bata yi magana ba, ita ce ta bugi Leesharh ɗin, amma bata ce mata ko uppan ba ta wuce da uban sauri har haka, hakan yasa Leesharh zarginta sosai.

Da sauri ta juyo domin ta bi bayanta ko idan suka fita haske zata iya ganin wacece?. Sai dai kash! Kafin ta fito wajen haske sam bata ga ko mai kama da alamar matar ba, ta ɓacewa ganinta, da alama wani lungu ta shiga ko kuma wani wajen.

Jiki ba kwari ta juya ta nufi hanyar koma ɗakin nata. Tana barin wajen matar ta fito daga in da ta laɓe ta kusa da hanyar shiga part ɗin su Ramish, ashe tasan Leesharh ɗin ta biyo bayanta, da gaskiyar Leesharh matar bata da gaskiya, kuma ɗaya ce daga cikin masu aikin gidan wadda take a hawa na biyu, ko me ya kawota nan? Ko me ta aikata take wannan uban sauri har da ɓuya haka?.

A bakin gadonta ta zauna tare da buga uban tagumi tana tunanin yadda zata ɓullowa wannan al'amari. Wayarta ta janyo domin ta duba ko matan nan sun turo mata wani saƙo.

Tana kunna hasken screen ɗin wayar sai ga saƙon kuwa ta ci karo da shi sun turo. Buɗewa ta yi ta fara karantawa duk da ba wani kwarewa ta yi a karatun ba. Ba wani saƙo suka tura mata ba face cewa da suka yi ta duba cikin akwatinta sun ajiye mata maganin da suke son ta zubawa Ramish a cappuccino, dan haka ta ɗauko maganin kuma ta kula.

Zaro idanu ta yi tana mamakin ta ya akayi suka iya kawo mata maganin kuma? To ko dai suna tare da ita a cikin gidan ne bata sani ba?. Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta nufi wajen akwatin nata. Tana zuwa ta buɗe akwatin da wuri, ga mamakinta sai ga maganin a saman kayanta kamar yadda suka faɗa. Ita dai tasan ɗazun da ta ɗauki kayan sakawarta babu magani a ciki.

Maganin a cikin wani ɗan ƙaramin kwalba yake, kamar kwalbar maganin
End Ads