yin wani abu wai shi aure? Ki bari idan lokacin yi ɗin ya yi zamu zo, but now ayyuka sun yi mana yawa, bamu da lokacin kanmu ma bare na wata mace, just ki bari kawai.........".
Cikin hanzari ta katse shi da cewa. "Naki na bari ɗin, sai fa anyi, bari ma zan turo maka hoton Chuchun sai kaga yadda ta girma ta kara kyau, nasan ma kana ganinta zaka ce ka yarda kawai daddynku ya ɗaura maka aure, dan ta girma, kuma nan da two weeks kawai na baka kazo ka ganta da idonka".
A takaice ya amsa mata da. "Okey Mammie yadda kike so hakan za'ayi, yanzu dai aiki nake yi, anjuma zamu yi waya, dama nakira ne na ji ya kike? Tun da kina lafiya shikenan".
Da haka suka yi sallama, wani irin murmushi mai wuyar fassaruwa ta saki tare da miƙawa wannan kuyangar wayar, sannan ta gyara ta ɗan kishingiɗa a saman wani throw pillow dake kusa da ita, ta kai hannu ta ɗauki tuffa guda ɗaya, a hankali ta fara jujjuya tuffa ɗin tana sakin murmushi, sai Allah kaɗai yasan tunanin me take yi.
A can cikin gid kuwa, kwance Auta da Gimbiya Chuchu suke a saman bed ɗin Akka, dogayen riguna iri guda ne a jikinsu, kayan ya yi masu kyau sosai, babu ɗan'kwali a kansu, kamar kullum ɗauri biyu suka yi wa arab hairnsu, sai hira suke zubawa kamar wasu ƙawaye, sai labari Gimbiya Chuchu take bawa autar a kan yadda suka yi da Yah Jawad, sai murmushi auta take yi mata.
Jin wani daddaɗar kamshin perfume ya daki hancinsu ne yasa suka ɗan ɗago kai a tare suna bin kofar shigowa da kallo.
Yana tsaye ya harɗe hannu a kirji yana ta kallonsu, Allah ya gani yana kaunar kannen nan nasa sosai, ko su Sarina da suke uwa ɗaya uba ɗaya ma baya jinsu sosai a ransa kamar yadda yake son Chuchu da Zunaira, saboda kyan halinsu, sam baya shiri da Sarina, ya fi kaunar Fanan a kan Sarina, ita ta cika rashin ji ne sosai shiyasa.
Cikin hanzari suka miƙe zaune a tsakiyar gadon. "Yah Jawad good evening". Cewar auta.
Ɗan sake fuskarsa kaɗan ya yi tare da ƙarisowa cikin room ɗin yana amsa mata gaisuwar. Saman bedside drawer ya zauna tare da tambayar su ina Akka?.
Still auta ce ta bashi amsa da Akka tana fada, suna can suna zama ne a kan yakin da King Zuhair yake son su yi da wancan masarautar, so Akka tana wajen, kunsan halinta sarai ba wasa, Akka bata son wargi, akwai zafin nama, tana can tana bada shawarar ayi yaki, nan ko takobi ba iya riƙewa zata yi ba, sai baki .........😅
"Auta jeki room nawa ki kwaso mun wayoyina dukka kin ji?". Ya faɗa yana dawo da kallonsa kan fuskar chuchu da ta yi ƙasa da kai, ko gaisuwa bata ɗaga mashi ba, ta tsorata ne dan tana tunanin ya ji hirarta ita da auta, idan ya ji tasan zai hukuntata, saboda ya ce kada ta gayawa kowa ya bata punishment, amma ta zo ta bawa auta labari har da cemata ai ta tsani Yah Jawad ɗin nan, to tana tsoron ace ya ji ne, dan basu san tun yaushe ya shigo ba, ita kuma a gaskiya ba zata iya ɓoyewa auta komai ba, komai aka yi mata sai ta bata labari, haka ita ma autar take, komai sai ta gayawa Chuchu ɗin.
Saukowa kasan gadon auta ta yi tare da nufar kofar fita tana faɗin okey.
A hanzarce ita ma Chuchu ɗin ta sauko da nufin ta fake da raka auta ta gudu.
"Come here". Ya faɗa a sanyaye.
Jiki ba kwari ta juyo ta dawo. Da hannu ya nuna mata saman bed ɗin ta kusa da drawer da yake kai a kan ta zauna. Ba musu ta zauna tare da takure jikinta waje guda ta sunkuyar da kanta ƙasa.
"Yau ba zaki gaishe ni bane Jannat?". Ya yi maganar yana mai da kallonsa a kan ƴan yatsun hannunta dake ta faman ƴan kerma.
"Ka yi hakuri na manta ne good evening". In a cool voice ta yi maganar.
Hannu ya kai ya riƙo ƴan hannayen nata cikin nasa. "Meyasa kike jin tsorona har haka Jannat?".
Girgiza kai ta yi tare da cewa babu komai.
"Meyasa kika gayawa auta na baki punishment? Kuma meyasa zaki ce mata kin tsaneni? Me nayi maki da zaki tsaneni?".
Yadda ya yi maganar ƙasa ƙasa kamar wadda aka yi wa dole yasa ta yi saurin ɗago kanta.
"Meyasa kika ce kin tsaneni e Jannat?". Ya sake jefa mata tambaya a karo na biyu.
Kai ta fara girgiza mashi tare ce mashi..........
*Masu tambayata cewa sunan Raj na musulmai ne koma krista, sunansa ba Raj ba ne, SURAJ ZUHAIR ABDUL MALIK yake, ƴan uwan nasa ne suka yanke sunan daga DR SURAJ zuwa RAJ, so sunan musulmai ne fatan kun gane?. Duk wani suna da na saka a cikin littafin nan suna ne masu ma'ana mai kyau, sunan larabawa ne, kuma kowanne zan rubuta maku ma'anoninsu, zaku iya sakawa yaranku idan ya yi maku.💘🌼*
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 27/8/2024.....✍️📚🌹
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
Those who are asking me for complete of RAWANIN ZALINCI babu complete ɗin, yanzu nake posting ɗinsa, hakuri zaku yi ku cigaba da bibiyar su Kamran ɗin nan har muga me Allah zai yi🥱 much love my people's 💘🔥
"Meyasa kika ce kin tsaneni e Jannat?". Ya sake jefa mata tambaya a karo na biyu.
Kai ta fara girgiza mashi tare ce mashi. "A'a ban tsaneka ba Yah Jawad".
"Amma ai na ji da kunnuwana kin cewa auta baki sona, duk cikinmu ni kika fi tsana why?".
Shiru ta yi bata da bakin magana, ta kuma kara yin ƙasa da kanta sosai. "Ɗago idanunki ki kalleni sai ki bani amsa ta ko?".
Bata iya ɗago idanun nata ba, sai dai ta ce mashi. "Ka yi hakuri ba zan sake ba, kuma ni na dai'na tsanar taka daga yanzu".
"To amma me nayi maki da yasa tun farko kika fara tsanar nawa?". Ya kai karshen maganar tare da sakin hannunta guda ɗaya, ya kai hannun nasa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna.
Ƙasa ta yi da idanunta tare da yin shiru. "Me na yi maki tun farko Jannat da yasa har kike ikirarin kin tsaneni?".
Ɗan turo baki ta yi kafin ta amsa da. "To Yah Jawad ba kai ne kake saka ni kneel down ba, kuma sai ka rinƙa ja mun ga shi kan......". Shiru ta yi ta ƙasa ƙarisa maganar sakamakon ji da ta yi ya saki ɗayar hannun nata ma, a tunaninta wani laifi ta sake yi yasa ya saki hannun nata zai daketa.
"Shi ne yasa kika ce kin tsaneni ni?". Yana magana yana kara ɗago haɓarta da kyau.
Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar e. "Okey to buɗe ido mu yi magana". Ba musu ta ɗan buɗe idanun nata, sai dai taki yarda su haɗa ido.
"Am so so sorry da punishment da na rinƙa baki, na yi haka ne nima ba'a son rai na ba, amma ki mun alƙawarin abu guda ɗaya, ni ma kuma ba zan sake baki punishment be kin ji?".
Ɗago idanu ta yi zata saci kallonsa, sai ta tarar da ita yake kallo. "Na yi maka alkawari In Sha Allah". Ta amsa mashi tun ma bata ji me zai ce ba ko akan me zata yi alkawari ba ta riga da ta yi.
Shiru ya yi bai gaya mata alkawarin me yake son ta yi ɗin ba, tun da ta amsa mashi da ta yi sai ya kawar da zancen da cewa. "Kada ki sake cewa kin tsani wani daga cikin gidan nan, bama ni ba koma waye, mu ba ƴan uwanki bane? Idan kika tsanemu to su waye zaki so? Amma tukun nan ma anya Jannat kin san me kalmar tsanar nan take nufi ma kuwa?".
Shiru ta yi tana tunanin ya zata gaya mashi yadda ta ɗauki tsana a nata tunanin.
"Me tsanar mutun yake nufi?". Ya jefa mata tambaya yana sakin haɓar tata ya koma ya riƙo hannayen nata a cikin nasa kamar ɗazun.
"Tsana yana nufin kamar idan mutun yana yi maka abin da baka so sai kana jin babu daɗi sai kawai ka tsane shi". Ta bashi amsa a kwakkwaɓe. Sai yanzu ma ya fahimci ita bama ta san ainahin menene ma'anar tsanar ba, haushin mutun shi take ɗauka a matsayin tsana, tsana kuma daban jin haushin mutun daban, mutun zai iya yi maka abin da baka so a lokacin ka ji haushinsa, daga baya idan ka huce komai ya wuce ku koma normal, shi kuma tsana daga zuciya yake, idan mutun ya tsaneka da gaske to mawuyacin abu ne ya dawo daga baya ya soka ko me zaka yi mashi kuwa.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan matsowa kusa da ita kaɗan, sannan ya kai hannunsa ɗaya yana shafa arab hairnta. "Da ga yau ba zan sake baki wani punishment ba, amma kema ki dai'na yin duk wani abin da bana so kin ji?".
Cike da murna ta ce. "Da gaske Yah Jawad ba zaka sake bani wani punishment ba?".
Kai ya gyaɗa mata alamar e. Cikin sauri ta faɗa jikinsa tana dariya, kamar ba ita bace yanzun nan take ƙoƙarin saka mashi kuka, Allah sarki ashe wannan punishment ɗin da yake bata abin yana matuƙar damunta, yana yi mata ciwon da kullum yana ranta, to yau dai an dena, ai sai murna kawai.
Ɗan rungumeta kaɗan ya yi tare da cewa. "To ai ni kuma baki tambayeni me bana so ba domin ki dai'na aikatawa".
Tana kwance a jikinsa ta amsa da. "Ai na dai'na komai ma, amma dai tom gaya mun sai na kara dai'nawa".
Shirmenta ya fara saka shi farinciki da murmushi, wai komai ma ta dai'na, ita da bata san ainahin dalilin da yasa a kullum suka haɗu sai sun sami saɓani da shi ba, amma wai ta dai'na, har da wani zata kara dai'nawa.
Murmushi kaɗan ya ɗan sakar mata kafin ya ce. "To promise me that za'a rinƙa sanya ɗan'kwali one! Two kuma za'a rinƙa sanya hijab idan za'a fito da sleeping dress!".
Ita dai tun da babu zancen punishment a yanzu ai shikenan, dan haka sai ta ce "I promised you ba zan sake yi ba dukka".
Kara rungumeta da kyau ya yi. "Yah Jawad to hoto fa?".
Ƙasa ƙasa ya amsa mata da. "Ki cigaba da ɗaukar kayanki, ba zan takura maki ba, dan kada ki sake tsanata".
Ƴar dariya ta yi tana faɗin. "A'a ba zan kara tsanarka ba ai".
"Promise?". In a low voice sosai ya yi maganar.
Da sauri ta gyaɗa mashi kai alamar e. "Okey tom shikenan jeki shirya sai kizo ki rakani wani waje, amma kada ki bari kowa fa yasan cewa zaki rakani wani waje, kawai idan kin gama shi sai ki kirani a waya zanzo mu tafi".
Cike da murna ta zaro idanu tana faɗin. "Yah Jawad wajen Kingdom zamu fita?".
Basu taɓa fita waje haka wai yawo ba, sai dai idan Dubai zasu tafi, shi kuma Dubai daga cikin gida idan suka shiga mota sai airport kai tsaye, shi ma Dubai suna jimawa sosai, school nasu ma kunga a cikin kingdom ɗin yake, ba su taɓa leƙa waje su ga gari ba, suna son zuwa yawo suga gari, amma ba hali, ko shopping za su je yadda kuka san menene, a mota za'a kaisu, a jira su ɗauki abin da suke so, sannan a dawo da su har cikin gida, basu fita ko nan da can, su ko irin taro na sarakuna da ake yi kowa ya je da iyalensa King baya yarda, baya son yaga suna yawo cikin mutane, shi King ai sai dai a zo a same shi a cikin kingdom ɗinsa, ba kowani taro yake zuwa ba bare ma har ya je da ƴaƴansa, yana da doka mai tsaurin gaske ne shi ɗin, ga bala'in ji da kai kamar me, baya ɗaukar rai'ni ko wargi.
"Wajen Kingdom kike son mu je?". Yana magana yana cigaba da shafa arab hairnta.
A hanzarce ta ɗago kai daga kirjinsa tana faɗin. "E ina son mu fita waje naga ya yake?".
"Tom shikenan jeki shirya, kada dai ki bari kowa yasan zamu fita".
Tana ƙoƙarin miƙewa sai kuma ta dawo ta ce "Harda auta kada na gaya mata?".
Ya fahimci bazata iya ɓoyewa auta komai da ya danganceta ba, so ko ya hanata ma sai ta faɗa mata koda a sace ne, is better for him da ya kyalesu a yadda suka taso kada ya ce zai yi ƙoƙarin sakawa lallai sai chuchu ta ko ɓoyewa auta wani abin nata, idan ya ce zai yi hakan to tabbas zai haifar da matsala a tsakaninsu, gara ya kyalesu kawai, akwai gaɓar da idan anzo wajen da kansu ma zasu ɓoyewa juna wani abin ba sai an ce masu sirrinsu bane. So dan haka sai ya ce.
"Ki ɓoyewa kowa amma ban da auta, kin manta ke da ita ɗin hanta da jini ne? Ai bazama ki iya ɓoye mata ba na sani, da wani ɗan bakinki a wajen kamar da gaske idan na ce kada ki gaya mata ɗin ba zaki faɗa ba, ni da nasan ko a ɓoye sai kin gaya mata".
Ƙara shigewa jikinsa ta yi tana dariya kamar bakinta ba zai rufu ba, ya harbo jirginta, domin kuwa dama ko ya ce kada ta gayawa auta sai ta faɗa mata koda a ɓoyene kamar yadda ya faɗa ɗin, so sai abin ya bata dariya.
A haka auta ta shigo ta samesu, a kusa da chuchu ɗin ta zauna tare da miƙo mashi wayoyinsa kamar yadda ya ce ta ɗauko mashi. Karɓa ya yi ita kuma Chuchu ta tashi daga jikinsa tana mai cigaba da murmushi.
"Aunty Chuchu dariyar me kike yi?". Auta ta tambaya.
"Yah Jawad ya ce zamu je wani waje".
Ɗan zaro ido autar ta yi tare da kai kallonta kansa. "Yah Jawad waje zaka kai mu?".
Gera kawai ya ɗaga mata yana ƙoƙarin kunna hasken screen ɗin wayarsa. "Zunaira jeki ki fara shiryawa ba ɓata lokaci kinga yamma ta yi". Ya faɗa yana kan bin screen ɗin wayarsa da kallo, miss call ɗin Yah Rizwan ya gani har uku a wayar tasa.
Da sauri autar ta miƙe ta nufi waje, sai murna take yi. Miƙewa ita ma Chuchun ta yi zata nufi waje da ɗan saurinta. Yana ƙoƙarin kiran number Rizwan ɗin ya riƙo hannunta da hannunsa ɗaya. Juyowa ta yi tana kallonsa, da ido ya nuna mata wajen da ta miƙe a kan ta koma ta zauna.
A hanzarce ta koma ta zauna sai sakin ƙayatattcen murmushi take yi. Murza ƴan yatsun hannunta a cikin nasa ya fara yi dai'dai lokacin da Rizwan ya yi picking na call ɗin.
"Assalamu alaikum Yah Rizwan". Ya faɗa yana dawo da kallonsa a saman face ɗinta. Murmushin nan nata yana ƙayatar da shi matuƙa.
Daga ɗayan ɓangaren ɗan uwan nasa ya amsa mashi da. "Jawad ina ka yasar da wayar taka kuma tun ɗazun nake kira baka ɗauka ba?".
"Sorry yaya na barota a ɗaki ne ina wajen Akka, amma lafiya kuwa?".
Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "E to kusan hakan dai, ɗazun na kiraka mu yi magana baka ɗauka ba, but yanzu ina yin wani aiki idan na gama zuwa dare sai mu yi magana".
"To amma Yaya lafiya dai ko? Ko dai na zo ne?".
"Kazo kuma?". Ya jefo mashi tambaya a takaice. "E mana yaya nazo idan da wata matsala".
"Ni nace maka da wata matsala? Ba zan kiraka mu yi magana ba sai idan da akwai wata matsala?".
A'a ya amsa mashi da shi.
"Okey tom babu wata matsala, nima ai na kusa kawo muku ziyara, Mammie wai ta yi mun mata, kuma wai dole na zo naga matar ido da ido, ka dai san halinta idan ta sako mutun a gaba, bani da lokacin yin aure a yanzu, amma zan zo ɗin kamar yadda ta buƙata, dan farincikinta kuma nasan ma ba kyaleni zata yi ba idan ban zo ba, ta rinƙa takura mun kena, idan na yi wasa ma sai ta shirya mun abin da ba haka ba, akan ta yi mun abin da zai sani ɓacin rai na har abada gara dai na bi umarninta a hankali mu rabu lafiya".
Guntun murmushi Jawad ya saki kafin ya ce. "Wlh gara kazo ka yi abu da kanka, idan ba haka ba kana can Mammie zata iya sanyawa a aura maka yarinyar da baka ma santa ba, kuma dole ka karɓa ba yadda zaka yi da ita, kaga kuwa idan hakan ya faru kana cikin ƙunci, so is better kazo kaga matar idan bata yi maka ba sai ka ce ta duba maka wata....."
Tarar numfashinsa Rizwan ɗin ya yi da cewa. "Ai kasan zaɓin Mammie ba yadda na iya da ita, dole zan karɓa, kuma nima ai ban isa in ce bana son matar ba ai, a cikin yaran daddy wai ta yi mun mata, kuma dai yarinyar like zata yi dai'dai da ra'ayina duk da cewa ban wani kalli pic's ɗinta da kyau ba, muna hira da Ramish lokacin da Mammie ta turo mun hotunanta, amma dai zuwa anjuma idan na nutsu zan sake duba hotunan da kyau, ko a iya yanzu naga yarinyar like ba laifi".
"Awww wai dama a cikin yaran daddy ta yi maka mata? Tab to ai wannan zaɓi babu