dan ki samu ki je wajen babanki ku koma ƙasarku, kada ki yi wasa, kin dai ɗauki duk abin da aka koya maki ba?".
Kai ta gyaɗa mata kamar kan ƙadangaruwa alamar e ta ɗauki komai.
"Good girl, to kada ki yi wasa kin ji? Ga wannan wayar idan kin je ki tabbatar kin ɓoyeta kada kowa ya gani, zan kara jan kunnenki Leesharh, ban yarda ki yi hira da ma'aikatan gidan ba bare har ki je kiyi suɓutar baki ki saki layi ki sanar da su abin da ya kaiki, nasan ma'aikatan gidan ba kakanun masu ilimi bane, wasu ma zasu yi maki dabara su bugi ruwan cikinki, kin dai ji abin da mai koya maki aikin nan ta ce ko? Kada ki yarda ki saki baki kiyi hira da wata, idan ya wuce gaisuwa ina wuni shikenan kada ki kara kada ki rage, sannan bayan Ramish ban aminta da ki kula kowa a cikin gidan ba, shi kaɗai zaki sakawa ido, kibi a hankali".
Ta kai karshen maganar tana kallon Leesharh har cikin ido.
"Aunty zan yi duk abin da kika ce da kuma abin da kuka koya mun In Sha Allah, amma Aunty ya za'ayi na gane wanene Ramish ɗin? Sannan kuma a wajensa zan yi aiki ne?". Ta yi tambayar cike da fargaba, tsoro take yi kada Aunty tata ta ce mata ta cika tambaya sosai.
Shiru matar ta ɗan yi kafin ta ce. "Ramish! Ramish! Ramish, kina ganinsa a jikinki zaki ji cewa shi ne, domin shi ɗin ganinsa ba kowace zuciya take iya ɗauka ba, amma dai zan turo maki hotonsa ki gani a cikin wayar, ki kula sosai, and yana da wasu kanne da ba zasu wuce mate ɗinki a shekaru ba, i think ba zasu wuce 13 years ba, kin ma fisu shekaru, they're twins, (Obaid and Omaid) and they're very very stubborn, basu cika zuwa gidan ba, amma na tabbata duk ranar da suka je idan kika yi wargi kaɗan zasu iya gano cewa ke ƴar leƙen asiri ce ko kuma akwai abin da ya kawoki gidan, because they're very very talented and suna da sharp brain fiye da tunaninki, kamar aljanu haka suke, ki kula sosai, idan sun zo gidan kada ki yarda ki yi wani kwakkwaran motsi, idan da dama ma kada ki bari ku haɗu da su kin ji?".
"To Aunty amma ta yaya zan gane sune har na guji haɗuwa da su ni da ban sansu ba?".
"Ai waɗan nan twins ɗin idan suka je gidan dole ma kisan sun je, saboda kamar yadda na gaya maki yadda kika san aljanu haka suke, kuma kowa a gidan sonsu yake yi, har shi kansa mai girma Abu Abdussalam bin Badeen kaunarsu yake yi, idan suka ce zasu je gidan ma har wani shagalin murna ƴaƴan Abu Abdussalam suke haɗawa, dan suna kaunarsu, ai zaki gani idan kika je, yawanci weekend ne suke zuwa gidan su ɗan yi hutu, kwana biyu kawai suke yi a gidan Saturday and Sunday, amma wlh sai ki rantse da Allah wani shugaban ne yaje gidan, saboda kauna da ake nuna masu, ke dai ki kula dasu, dan sun fi bala'i iya bala'i, makirai ne na karshe!".
(Yo ai dole ayi mata kashedi a kan Obaid and Omaid 😅 hmmm yaranda kamar ba mutane ba, anya Momma lafiya aka bar maki ƴaƴan nan naki kuwa?🤔 Na fara tantanma, dan sun fita zakka a cikin ƴan uwansu, ai kuwa Leesharh tana yin wani wargi zasu kamata waɗan nan yara, da kuwa sunanta sorry wlh baiwar Allah)
Da okey ta amsa mata, saboda a yanzu an koya mata dabaru kala kala. Ji take yi kamar ta tambayi Auntyn nata wanene wanda ya zo yanzun nan? Sai kuma ta basar da maganar gudun kada ta jama kanta wani abin.
Miƙa mata dalleliyar wayar hannunta matar ta yi, waya ce mai tsada ga kyau, sannan ta miƙe ta nufi waje tana gaya mata cewa mai koya mata aiki ta tafi, aikinta ya kare yau.
Haka kawai Leesharh ta tsinci kanta da jin faɗuwar gaba a lokacin da ta ji zancen mai aikin..... Ni kaina na ji wannan faɗuwar gabar, fatana dai shi ne Allah yasa ba kashe mai aikin zasu yi ba, dan sun ce babu mai jin sirrinsu kuma ya rayu, kunga kuma ita mai aikin ai ta ji sirrinsu, dan sai da suka gaya mata abin da zata koyar da Leesharh ɗin, to Allah dai ya nuna mana lokaci ya kai mu mu ji komai a tare.
Zubawa wayar idanu sosai Leesharh ta yi tana kallonsa, a cikin wannan sati biyu da suka yi an koya mata yin amfani da waya, sai dai abin da bata sani ba shi ne an saka mata abubuwa biyu zuwa uku a cikin waya. Na farko an saka mata na'urar bi diddigi a cikin wayar, na biyu ansaka mata abin sauraren magana, matuƙar wayar tana kunne ta yi magana a kusa da wayar to waɗan da suka bata wayar suna sauraren duk abin da zata faɗa, abu na uku kuma shi ne anyi setting na wayar ta yadda duk wanda ta ki zasu sani. Hmmm wlh akwai cakwakiya ba kaɗan ba a wannan part ɗin. Duk Leesharh bata san da waɗan nan abubuwa da suka sanya mata ba fa tab! Waya sani ma kila akwai wasu abubuwan da basu bari muma mun sani ba.
Yanzu ita Leesharh duk bama wannan bace a gabanta, face ɗin wannan mutumi da ya shigo a yanzu take son ta sake gani, tana son sanin wanenen shi? Ko ba komai yau karo na farko ta ɗan ga face ɗin wani a cikin gidan, duk da tasan tabbas ba ɗan gidan bane, dan a yanayin yadda ya shigo ya nuna cewa koma wanenen ya fi ƴan gidan nan kuɗi da ji da isa, saboda idan ka lura da irin kallon da yake yi wa gidan, kallo ne na raini da kuma ƙasƙanci, kuma fuskarsa ta nuna kamar dole aka yi mashi zuwa wannan gida ba da son ransa ba, sannan idan ka kalli yanayin motocin da suka rako shi da masu tsaronsa, haɗe da motocin ƴan'sanda har guda uku zai nuna maka ba ƙaramin mutun bane, ya fisu komai da komai, kuma yana bala'in ji da kansa sosai, duba da yadda ya shanya waɗan nan shirga shirgan bodyguards ɗin suna a tsaye suna jiransa tsawon lokaci yana cikin mota, sai lokacin da ya ga dama ya fito, ko mutun ɗaya daga cikin waɗan nan ƴan'sanda da bodyguards ɗin babu wanda ya nuna alamar ya ji wani abin, alamu sun nuna cewa lallai ba yau bane farau, halinsa ne shanya mutane suna jiransa, sai dai a jirasa amma shi baya jira.
Sosai Leesharh tasa ƙwaƙwalwarta a cikin tunanin tana ƙoƙarin haɗa abin da tasan sam ba zai yi wu ba, dan wannan matashi shi ne kawai ta kalli face ɗinsa a cikinsu, shi ma ba sosai ba, ba lallai ma idan ta sake ganinsa a wani waje ta ganesa ba, amma ta dage tana ta ƙoƙarin haɗa idanun ƴan gidan, ita a yanzu da idanu da kuma murya take son ta gwada iya gane su wanene su, shiyasa take ta ƙoƙarin haɗa idanun wannan guy da bata gani da kyau ba da kuma idanun wannan matashiyar mata tare da mamarta, dan ta gane shin wannan matashi yana da alaƙa ta jini da su ko kuma bashi da shi? Leesharh kenan, akwai ƙwaƙwalwa, wani lokaci kuma akwai iya shirme da shiririta, ga yarinta da yake ratsowa ta cikin ƙwaƙwalwar tata.
Ta jima tana kallon wayar da aka bata ba tare da ta shiga cikin wayar ba, bata ma sha'awar shiga cikin wayar, saboda tasan babu komai a ciki.
Sai hidima take ji ana ta famar yi a cikin gidan, amma ita babu halin ta fita taga me ake yi, dan idan bada izinin wannan hajiya ba ko kofar ɗakin bata leƙawa baiwar Allah. Tana ƙunshe a ciki kamar daddawa!.
Tana dai ji anata kai komo tsakanin hawan kasa da sama, elevator sai zarya yake yi, amma haka ta cigaba da kwanciya shiru.
Wunin ranar dai haka ta wuni a takure, ta takure kanta da burin son fita ta leƙa me ake yi a cikin gidan, amma babu hali, haka ta wuni babu wanda ya leƙo in da take har can yamma. Kamar daga sama ta ji motsin jama'a a harabar gidan. Ai a dubu ɗari ta diro ƙasa daga saman bed ɗinta ta nufi wajen window dan taga menene?.
Wannan matashin saurayin ne zai tafi, ga mamakinta sai taga mata wajen huɗu ne suka rako shi wajen motarsa, ita dai tasan mata biyu kawai ta sani a cikin gidan, sai mai koya mata aiki wadda kuma tun da rana ta koma, to su kuma saura mata biyun nan daga ina? Ta tambayi kanta.
Ga wannan Hajiya da kuma ƴarta waɗan da already Leesharh ta rike kamaninsu ta yanayin idanunsu duk da suna cikin nikaf, kuma wata basira irin tata ko basu yi magana ba tana iya gane da waye take a tare ta hanyar idanunsu. Sam basu kawowa ransu cewa Leesharh zata iya yi masu wannan sani ta haka ba, a tunaninsu ai ba zata taɓa iya ganesu ba.
Kamar dai ɗazun, yana sunkuye da kansa yana kallon ƙasa ya nufi motarsa, sosai Leesharh ta baza idanu tana son kallon face ɗinsa da kyau da kyau, amma sam hakan bai samu ba, saboda yana ƙasa ita kuma tana sama, ya kuma sunkuyar da kansa ƙasa, ba halin ta gansa sosai!.
Tana ji tana gani suka bar wannan gida, sam ranta baiso haka ba, ta so dai taga wannan haɗaɗɗen guy ɗin mai cike da shegen isa da izza.
Sai da ta ga tafiyar motocin nasu ne ta juyo ta koma wajen bed ɗinta cike da haushi, sai kuma ta fara tambayar kanta a kan cewa kenan ko da wannan matashi ya zo basu cire nikaf ɗin da yake face ɗinsu ba? Ko dai sun cire a cikin gida da zasu rakoshi waje ne suka sake sanyawa? Waɗan nan tambayoyi shi take ta jerawa kanta wadda kuma har lokacin sallar mangariba ta yi bata samu amsarsu ba.
Jiki ba kwari ta tashi ta yi sallah ta dawo ta cigaba da kwanciya tana tunanin irin rayuwar da suke son jefata a ciki, ga shi sun yi mata kashedi da kada ta yi kusa da kowa a wannan gidan aiki da zata je, sannan kuma sun ce kada ta yarda ta rinƙa sanya hijab irin nasu na Africa, a kayan da zasu saya mata ma ba za'a sayi irinsa ba, sai dai arab hijab zata sanya wanda iyakansa kirjinta ya tsaya, abin ya ɗan ɗaure mata kai da har ta fara tunanin kenan tallar jikinta zata yi wa Ramish ne ko yaya? Ta ƙasa gane komai, waɗan nan mata akwai shegu, duk sun birkita mata ƙwaƙwalwa ta yadda ta kasa iya kamo zaren bakin abu guda ɗaya a cikin waɗan nan matsaloli ta warware ta gani, anya kuwa waɗan nan mata su suke shirya wannan plan ɗin kuwa? Saboda abin ne ya wuce tunani, dole akwai sama da su, to waye? Wannan tunani Leesharh ta fara yi a cikin ranta.
Kamar a mafarki muryar babanta ya fara yi mata yawo a cikin kunnuwanta in da yake ce mata. "A'isha duk abin da zaki yi a rayuwar nan ki riƙe gaskiya da amana, in dai kika rike waɗan nan abu biyun to Allah ba zai taɓa bari ki taɓe ba, Allah zai ji ƙanki, ki tabbata baki cutar da kowa ba a rayuwarki, hakan zai sa Allah ya sanya bargon ni'imarsa ya lulluɓeki daga kowani irin cuta da ɗan adam zai yi maki, kada ki bari mutuncinki ya zube ta hanyar cutar da wani, gara maki ace mutuncinki ya zube wajen ƙoƙarin tsayar da gaskiya".
Sai gizo kalaman babanta suke yi mata a cikin kunnuwanta, gabaɗaya ta rasa madafa, hankalinta ya yi mummunar tashi gobe za'a kaita gidan aiki, ji take yi kamar ba zata iya ba, duk da wannan mata ta ce mata ba cutar da kowa zata yi ba, amma ita a jikinta tana jin cewa kamar cutar Ramish ake son yi, to amma koma cutar ce a wannan gaɓa dai bata da zaɓin da ya wuce dole ta yi wannan aiki, idan ba haka ba ita kuma zata rasa babanta wanda shi kaɗai ya rage mata a duniya. Tashin hankali, duniya ta ɗau mata zafi fa.
Cikin ƙoƙarin neman mafita da tunanin ina zata sanya ranta ne Jasrah ta ratso mata ta cikin tunaninta, daɗaɗan kalam Jasrah ta fara tunawa a in da take ce mata. "Leesharh a duk lokacin da kika rasa mafita, kika shiga damuwa, kina ganin kamar baki da mafita, kina ganin kamar komai ya lalace maki, a dai'dai wannan lokaci ki fara furta Hasbunallahu wani'imal wakil, domin babu wanda zai iya kawo maki ɗauki sai Allah, kada ki tunkari kowa da ya ya ye maki damuwarki, ki tunkari mahaliccinmu kawai ta hanyar ɗauro alwala ki yi nafila raka'a biyu tare da karanta Alqur'ani mai girma koda shafi biyu ne, zaki ji sauki sosai a ranki, domin Allah shi ne kawai mai kowa kuma mai komai, shi ne kawai zai iya fitar dake daga zafi izuwa sanyi, duk tsananin da zaki shiga kada yasa ki manta Allah".
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, zamanta da Jasrah babban alkhari ce a gareta, ta koyar da ita abubuwa da dama. Tunano da kalamar ƴar uwar tata ne yasa ta yunƙura zata tashi ta ɗauro alwala kenan wannan matashiyar matar ta shigo cikin room ɗin bakinta a ɗauke da sallama. Tare suke da wani babban likita da yake biye da ita a baya, yana sanye cikin ƙananan kaya ya ɗaura rigarsa na likitoci a saman kayan, hannunsa na ɗauke da A box, babban mutun ne da zai iya haura shekaru 45 a duniya, farin balarabe ne tas da shi.
Leesharh matar ta nuna mashi da hannu tare da zama a saman bedside drawer tana faɗin. "Doctor Suhail this is the patient".
Ɗan zaro idanu Leesharh ta yi tana tunanin ita a yaushe ta ce bata da lafiya to? Ita dai tasan lafiyarta ras, to me za'ayi mata kenan?.
"Zaki iya bamu waje". Dr Suhail ya yi maganar cikin harshen larabci.
"No Dr, ka yi aikinka kada ka damu da ni, ina son bata kulawa ne sosai". Ta faɗa cike da nuna mashi cewa tana kaunar Leesharh ɗin sosai.
Sai kallon face ɗin Dr da yake sanye da farar face mask na likitoci a face ɗinsa Leesharh take yi. Ko kaɗan alamu basu nuna cewa waɗan nan mata suna da wata alaƙa ta jini da wannan Dr ba, saboda shi yanayin idanunsa daban da nasu, amma fa a tunanin Leesharh ne hakan.
Jinjina kai Dr ya yi tare da cewa Leesharh ta gyara kwanciyarta bari ya dubata ya kuma duba maƙogoronta me yasa maganarta baya fita sosai?......... NI KAM NA CE ANYA BA WANI ABIN ZA SU SANYA MATA BA KUWA?🤔 BAFA A YARDA DA IRIN WAƊAN NAN MUTAEN!.
Ba musu ta gyara ta kwanta, dan ma dai bata da wata zaɓin da ta wuci hakan. Alluran barci Dr ya ciro daga cikin A box ɗin ya fara haɗawa, amma kafin ya yi mata sai da ya tambayeta ya akayi maganarta bata fita sosai? Shin haka aka haifeta ne ko dai daga baya ne ta samu wannan cuta?.
Kallon wannan matar ta yi alamar tana jiran ta ji me zata ce. Cikin sanyin murya matar ta ce. "Ki saki jikinki ki bawa Dr duk wani amsar tambayar da zai yi maki, ta hakance kawai zai sa a iya yi maki magani cikin sauki, ba sai an shawahalar wani dogon bincike ba". Cikin harshen larabci ta yi maganar.
Bayani Leesharh ta fara ƙoƙarin yi masu, sai dai ga dukka alamu a tsananin razane take da maganar da ta fara yi ɗin, alamu sun nuna bata son yin maganar, in fact bala'in jin tsoron yin maganar take yi, hakan zai tabbatar maka da cewa akwai babban abu dangane da ita da take tsoron faɗarsa ga duniya, dole akwai abin da ya faru da ita a rayuwarta ta baya, baiwar daga tambayar meyasamu voice ɗinta duk ta ruɗe, ta shiga tashin hankali kamar ba ita ba.
Kasa iya yi masu bayanin ma ta yi, daga fara wa sai ta fara kuka da hawaye bibbiyu. Ganin hakan yasa wannan mata ta matso kusa da ita tare da ɗan rungumota ta fara rarrashinta a kan ta yi hakuri.
Cikin kuka take faɗin. "Ni dan Allah kada ku tambayeni meya samu voice ɗina, kawai dai abin da nasani shi ne ba'a haka aka haifeni ba, last year ne ma abin ya faru da ni, kuma garwashin wuta ne silar komai, garwashin wuta ne ya shiga bakina har maƙogorona ya kona mun baki da yasa muryara bata fita, please kada ku tambayeni wani abin kuma".
(Garwashin wuta zai shiga bakin mutun da kafafunsa ne?🤔)
Ganin yadda ta ruɗe ta fita a hanyacinta daga cewa ta bada labarin abin da yafaru da muryarta ta dai'na fita yasa Dr Suhail ya fahimci lallai yarinyar nan gabaɗayanta tana under barazanar mutane ne, dole dole akwai gagarumin abin da ya faru da ita a rayuwarta ta baya wanda kuma take a ƙarƙashin barazanar kada ta yarda ta tona wannan abin da ya farun, hakan yasa da suka tambayeta ta yi wannan ruɗewa har haka, da alama kuma wannan dalili yasa ta ƙasa iya buɗe baki ta yi magana a kan mutuwar mahaifiyarta da ake ta cewa ita ta kasheta, dole wani abin ya saɓa, rayuwarta akwai abin dubawa sosai, amma kada ku ji komai, ni PRINCESS TEEMA ba zan gaji ba sai na je na leƙo masu asiri na binciko maku tarihin rayuwarta koma ta halin yaya ne, ai ba za'a barmu a baya ba, daga jin wannan abin kasan tarihin rayuwarta akwai darasi da abubuwan karuwa, dan haka dole na binciko mana dan muji komai mu kuma ƙaru..........😎
"Dr Suhail ina ganin kada ka sake yi mata wani tambayar kuma, tun da ta ce ba'a haka aka haifeta ba, kuma ta ce last year ne abin ya faru da ita sannan garwashin wuta ne ya shiga bakinta yasa voice ɗin nata baya fita, ina ganin ka bata magani