x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 13 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 36001 words
  • 39000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 409

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
yana son ganin sarki.

Cikin hanzari sallama ɗin ya ƙariso gaban stage da King yake a kai, a nutse ya haura sama, a daf gabansa ya zo ya zube gwiwowinsa a ƙasa, cikin girmamawa tare da zubawa King kirari kafin nan ya sanar da shi cewa Sarkin yammaci yana neman iso a gare shi.

Shiru na ƴan mintocin da akallah zasu kai uku King ya yi, da alama fa King jinin mulkin nan ta ratsa shi sosai, dan izzar bala'i ke gare shi, magana cike da class, maganar mai sifirin ce, ana yi kamar ba'a son yi, ana yi kuma ana hutawa.

"Daddy in tafi ko?". Cewar auta, dan ita sam bata son hayaniya, yanzu ta san idan sarkin yammacin nan ya shigo sai an yi ta zuba mashi kirari, kuma sarkin yammacin matsayin wa yake ga marigayi King ABDUL MALIK BADEEN, dan dai a tsarin mulki idan mutun ya fika matsayin kujera to ya fika ne, ba dan haka ba ai da King Zuhair ɗin ne ma ya dace da ya je ganin Sarkin yammaci ba wai shi ya zo ba, idan kuka yi duba da kasancewar Sarkin yammaci a uncle na King Zuhair ɗin kenan, amma da yake kujerar yammaci tana a ƙarƙashin mulkin king Zuhair ne, dole sarkin yammaci ya zo da kansa idan yana da buƙatar ganin King.

"Kin gaji da zama ne?". Har lokacin kallonsa yana fuskantar cikin tsakiyar fadar, bai juyo gareta ba.

"Daddy ai naga kaka zai shi go ne, shi ne yasa zan tafi, sai can yamma ai zan dawo".

Jinjina mata kai kawai ya yi, ba dan yana son ta bar kusa da shi ba, sai dan kawai zai so ya gana da uncle ɗin nasa ne cikin nutsuwa da mutunta juna ya kuma bashi hankalinsa waje guda.

Har lokacin Sallama yana duƙe a saman gwiwowinsa yana jiran amsar da king zai basa, dama a tsarin KINGDOM OF POWER wlh babu wanda ya isa ya shigo fada ta kofar can taba family ba ba tare da izini ba sai, mulki mai karfi ke garesu, kuma suna gudanar da mulkin nasu ne bisa ga bin dokokin da suka tsarawa masarautar, idan kun san abin da ake cewa ba sani ba sabo, to shi ne yake aiki a cikin dokokin wannan masarauta, babu sani kuma babu sabo, duk wanda ya yi ba daidai ba hukunci kawai ake yanke mashi, koma waye shi, hakan kuma ita ce adalci, ita ce dai'dai, wannan dalilin ne kuma yasa masarautar ta tara ɗinbin makiya na kin karawa, ba'a taɓa masarauta wadda ta tara maki a tarihi ba irin wannan masarauta, dama kun san idan mutun ya ce zai yi aiki bisa gaskiya da amana, zai yi mulki kamar yadda ta zo a Shari'ance, to ba shakka zai tara makiyan da shi kansa sai ya ji ya tsani duniyar ma gabaɗaya, dan duk in da ya juya makiya ne ta ko'ina, burin kowa kawai ya kaisa ƙasa, saboda kawai wannan gaskiya tasa, zata zamana harta makusantarsa ma basu barshi ba, wata kila ya taɓa hukuntasu dan sun yi laifi, suma sai su shiga sahun makiyansa, to a takaice dai haka King Zuhair yake da waɗan nan tarin uban makiyan ta ko'ina, sai dai shi mutum ne da ya riki Allah hannu biyu, sannan kuma mulki yake gudanarwa dai'dai da koyarwar addini, baya damuwa da kowa da komai, koda ɗansa ne ya yi laifi sai ya hukunta shi, adalci kawai ya sani, kuma duk wanda yasan tarihin modarawa dama yasansu da wannan ɗabi'ar, suna da adalci, basu taɓa mutum haka kawai sai in har shi ya taɓosu, idan kuwa ya yi gigin taɓosu fa sai dai mu ce sunansa sorry, dan gangan ma sai ta fishi dakuwa, gari sai ta fishi niƙuwa, MODARAWA No be wasa Wlh!!.

Miƙewa auta ta yi tare da cewa sallama ya sanar da Hoorain ita zata bi ta kofar nan da zai sadata da part nasu, ba zata fita ta kofar da kowa yake shigowa ba, wato kofar da ta shigo kenan, da yake kunsan da akwai kofar da zai iya sadaka da part na King a cikin fadar, dayawan lokuta ta nan ma family suke shigowa cikin fadar.

Kun san dai yadda tsarin mulki take, kuma ku daga gani kunsan madarar mulki ziryar ake bugawa a cikin wannan masarauta babu wasa. Dan haka ƙasa auta ta duƙa dan yi wa mahaifin nata sallama, wannan ma ɗaya ce daga cikin dokokin masarautu, ko da mahaifinka ne a kan mulki dole ka bashi girma fiye da tunaninku, kamar dai yanzu ita auta da ta zube gwiwowinta a ƙasa, ƴa ce mafi soyuwa a wajen babanta, amma dole ta bi dokar masarauta, shiyasa na ce maku king Zuhair harta ƴaƴansa idan suka yi laifi yana hukunta su, ba sani ne kuma babu sabo.

Sai da King ya bata izinin tafiya, sannan ta miƙe tsaye, cikin tsantsar so da kauna ta manna mashi kiss a kumatu kafin ta juya ta nufi step na sauka ta bayan King ɗin, dan kofar tana ta baya ne ba ta gaba ba.

Dawo da kallonsa a kan sallama dake tsugunne ya yi, cikin sanyin murya tare da magana ɗaya ya furta an bashi izini, daga haka ya mayar da hannunsa da ya fitar daga cikin alkyabbarsa dan shafa kumatun Auta, sannan ya mayar da kallonsa a kan tsakiyar fadar.

Kirari sosai Sallama ya fara zuba mashi tare da ɗaga hannu sama ya dunƙuleta yana aikin zuba mashi jinjin da kuma faɗar kyawawan fararen halayensa.

Yana dake a saman kujerar nan bai ko motsa ba, ya hakince abinsa. Almost 2 mins Sallama ya ɗauka yana zuba wannan kirari kafin ya miƙe ya nufi kofar fadar dan ya isar wa da sarkin yammacin saƙon King.

A bangaren ita kuma Auta, tana fita cikin ainahin part nasu ta koma, ta baro su Chuchu a garden suna aikin yanka mata fruits. Akwai bayi sosai da suke ta faman safa da marwa a part ɗin nasu, kowace baiwa da aikin da take yi, duk idan auta ta zo wucesu sai sun tsugunna mata ƙasa alamar girmamawa.

Kai tsaye wani babban part ta shiga, tun daga kan yanayin tsarin wajen kasan wajene na mutane na musamman a cikin masarautar, saboda tsari ne mai matuƙar kyau da aka tsara shi, harta kwalliyar jikin bangon ginin wannan part ɗin kwalliya ne na musamman.

Ciki ta shige abinta, a babbar parlourn ƙasa ta tsaya, parlourn ya tsaru iya tsaru, dukiya ta yi kuka a wannan waje, komai na cikin parlourn launin dark blue and gold ne, kalar kuma ta yi matuƙar bada abin da ake so, dan ta kara bayyanar da cewa lallai nan gidan sarauta ne.

Kuyangu ne suke ta faman aikace-aikace na gyara a cikin parlourn, ƴan mata ne su huɗu, kowacce da abin da take yi, daga mai gyara shinfiɗun alfarma dake saman kujeru, sai mai shirya pillows, ɗayar goge wajen Tv take, ɗayar kuma goge katafaren parlourn take ta faman yi.

Suna ganin auta suka zube gwiwowinsu a ƙasa tare da sunkuyar da kai ƙasa.

"Inan Akka?". Shi ne tambayar da autar ta jefa masu.

Cikin girmamawa har suna haɗa baki wajen cewa. "Akka tana sama".

Da sauri ta haye saman ba tare da ta sake bi ta kansu ba, wajen kyakkyawar elevator ta nufa, sama ta haye, sai faman farinciki take yi kamar wadda aka yi wa wani kyauta mai girma, daɗi take ji yayanta ya kammala secondary school zai dawo.

A hawa na ukku ta tsaya, sauka ta yi ta nufi cikin katafaren parlourn saman, cikin wani katafaren bedroom mai girman gaske ta shiga.

Wani shinfiɗaɗɗen king bed na alfarma ne a cikin wannan ɗaki, bed ɗin yana da girma sosai, kayin wannan King bed ɗin ya kai kusan taɓa sama, dan ya fi rabin bango, kuma iya wannan bed ɗin ne kawai a cikin wannan katafaren bedroom ɗin, sai wasu gajerun luntsuma luntsumar Dubai carpet dake shunfuɗe a kasar floor na ɗakin, tiles na cikin ɗakin gabaɗaya launin sky blue ne, sun sha gyara, sai ka ce kafa bai taɓa bi ta kansu ba, saboda tsafta, ga wasu triplets door masu kyau a jere ta ɓangaren dama a cikin ɗakin, ɗaya door ɗin toilet ne, ɗayan kuma na balcony, ɗayan kuma dressing room ne.

Akwai kuyangu guda biyu a cikin ɗakin da suke yi wa mamallakin wannan ɗakin hidima, ƴan mata ne kuyangun masu jini a jika.

Wata kyakkyawar farar balarabiyar dattijuwa ce ke kwance a saman wannan katafaren bed ɗin, kuyanga ɗaya tana aikin matsa mata fararen kafafun nata, abinku da jiki na tsufa, ɗayar kuyangar kuma tana matsa mata hannunta, ita kuma tana kwance shiru abinta.

Hayewa saman bed ɗin auta ta yi bayan ta gabatar da sallama kenan.

"Akka, Akka tashi ki ji wani labari". Shi ne abin da autar take ta faɗa.

Buɗe idanuwanta wannan dattijuwa ta yi, kwayar idanunta sak irin na autar, duk da take tsohuwa kyakkyawar gaske ce.

"Wani labari ne wannan haka Auta?". Ta yi maganar tana ƙoƙarin miƙewa zaune.

Cikin hanzari kuyangun nan nata suka ja da baya kaɗan tare da cire hannayensu daga tausan da suke yi mata.

"Akka Yah Omar ya kammala secondary school, kuma daddy ya ce zai dawo nan"

Akka zata yi magana sallamar Gimbiya Chuchu ya katse ta.

"Wato ke auta a nan kika zo kika yi zamanki kin barmu muna ta jiranki a garden ko? To ga can Aunty Fanan tana jiranki da fruits a hannu, ni ba zan iya ba na taho na yi wanka". Cewar Gimbiya Chuchu kenan.

"Aunty Chuchu ni fa na fasa shan fruits ɗin, kuma ba yanzu zan koma garden ba, yanzu ina nan tukun nan". Ta kai karshen maganar tare da kwanciya a saman bed ɗin ta tada kai da cinyar Akka.

Juyawa Gimbiya Chuchu ta yi ta nufi waje tana faɗin. "Ke dai kika sani, ni kinga wucewata, bari naje bedroom ɗin can na yi wanka hai". Ta kai karshen maganar tata ma a kofar waje, dan tana tafiya ne tana maganar.

Bedroom na kusa da na Akka ɗin ta shige, tana shiga kuma ta hau cire kayan jikinta kamar wadda take sanye da ƙaya dama. Toilet ta nufa dan yin wanka, kasancewar wannan part ɗin na kakansu ce, Akka ita ce ta haifi King Zuhair, so kowa daga cikinsu yana da damar shigowa cikin wannan part ɗin ya yi abin da yake so, babu wanda zai yi mashi wata shamaki.

Ita kuwa auta, ta yi kwanciyar suka cigaba da hira a tare da Akka, shi kuwa Hoorain ya koma cikin mayaƙa ƴan uwansa, dama sai ta fito yake kula da ita, idan ta koma ciki shi ma komawa wajen ƴan uwansa mayaka yake yi.

Shi kuma King Zuhair suna can suna tattaunawa da Sarkin yammaci a kan yanayin halin rayuwa da al'umma suke a ciki, suna ta faman neman mafita, dan samawa mutanensu saukin wahalar rayuwa da ake ciki.

Idan muka waiwaya gidansu Zainab kuwa, and kafin mu waiwaya let me tell you one think about me and my story, ina son ku sani kowace marubuciya a duniyar nan da yanayin tsarin salon rubutunta wadda ta tsarawa kanta, kowacce da abin da ta fi karkata a kai, to abin da nake son ku sani a kai'na shi ne, ni salon rubutuna yana tafiya ne a kan part, part! Wato labaraina suna da ɓangarori da dama, nasan da dama daga cikin waɗan da suka karanta littafin TRIPLETS sun san yana da parts parts daban daban, a fita wannan a shiga wannan, idan ban yi karya ba a kallah akwai parts mabanbantan sama da guda 13 a cikin littafin TRIPLETS, parts nasu Abba ne, nasu Abbi daban daddyn jelly da dai sauransu, kuma kowani part kun sani da nashi roll ɗin da yake playing a cikin littafin, ba'a banza nake sako parts da dama ba, so ni haka salon nawa rubutun yake, kowacce writer da nata salon, ina maku albashir da cewa shi ma littafin RAWANIN ZALINCI tafe yake da parts mabanbanta da zasu ƙayatar da ku matuƙa, duk da cewa ba lallai ya kai yawan parts na TRIPLETS ba, sannan kowani parts da nasa cakwakiyar, kuma duk wanda kuka ga sako a cikin labarina da rawar da zai taka, ba haka kawai nake sakosu dan jin daɗin kai'na ba, fatan kun gane?.

❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥❥

GIDANSU KHADIJAH🧡

A yanzu Khadija an zama ƴan'mata, kyau ya kara bayyana, ga surar jiki komai masha Allah, su Zainab iyayen san kyalliya ma an zama ƴan'mata, mamansu tana matuƙar kula da su, kamar yadda kuka sani ne babansu yana kula da su sosai, kuma tun daga kan Zainab mamansu bata sake haihuwa ba har yau, dangin miji sun sakota a gaba a kan cewa shiru shiru bata sake haihuwa ba, dama su jama'a ba'a iya masu, ka haifi dayawa ace ka cika haihuwa, idan kuma Allah ya dakatar maka da haihuwar, nan ma su isheka da shirun ya yi yawa yakamata ka kara, sai kace akwai wanda yake bada haihuwa ne a duniya, wlh jama'a muji tsoron Allah, ban cire kowa ba muji tsoron Allah! Mu dai'na takurawa waɗan da basu haihuwa da wuri ba ko kuma waɗan da basu samu haihuwa ba kwata kwata, domin kowa yasani cewa babu wanda ya isa ya bada haihuwa sai Allah mahalicci mai kowa mai komai, amma saboda son zuciya sai a murje idanu ayi ta takurawa baiwar Allah wai har yanzu bata haihuwa ba, to kada dai a manta mai bada haihuwar yana sama yana jin duk abin da ake yi kuma yana gani, ku ta cin zarafin yarinya idan bata haihu da wuri ba, a dai rinƙa jin tsoron Allah, wata ma idan ta haifi maza ace ta cika haifar maza, ta cikawa mutane gida da maza, idan kuma mata ne nan ma ace ta cika gida da ƴaƴa mata kamar dai Maman Zainab a yanzu, su maman Haidar sun sakota a gaba wai ta tara ƴaƴa mata kuma daga su ta lafe shiru ba kari, to gaskiya su shirun ya yi masu yawa, ko ta kara haifar wasu ko kuma baban Zainab ya karo aure daga cikin family, abin mamakin kuma duk wannan bala'i da maman Haidar ɗin take yi fa ita ma ƴaƴanta biyu rak, amma saboda son zuciya bata duba nata ba ta sakawa wata ido, da yake dama ba kaunar maman Zainab ɗin suke yi ba, dama ance laifi tudu, ka taka naka ka hango na wani, wannan matsala ta haihuwa ko rashinsa yana ɗawainiya da mata dayawa, to wlh mu ji tsoron Allah, mu sani Allah shi ne mai iko da komai, shi haihuwa idan Allah ya tsara ga lokacin da zai zo to fa babu uban da ya isa ya hana shi zuwa, ko uban magani kike sha dan hana ɗaukar ciki, wlh idan lokacin da Allah ya rubuta zaki haifi ɗan ya zo duniya, to fa ba makawa sai kin haife shi a lokacin, and lastly su ƴaƴa ai ba'a ƙayyadewa kai ga iya adadin da ake so, sai dai bawa ya faɗa kawai dan jin daɗin bakinsa, amma Ubangiji ya riga ya tsara maki ƴaƴa nawa zaki haifa a rayuwarki, dan haka ba sai kin wahalar da kanki ko kin wahalar da ƴar wasu a kan zancen bata haihuwa ba! Ki sani kema watara zaki iya haifar ɗiya mace, nasan babu wadda zata ji daɗi a sako ƴarta a gaba da cin mutunci a kan rashin haihuwa, to ki sani alkawari ne duk abin da kika yi wa ƴar wani sai anyi wa taki.

Ita dai Maman Zainab kome za'a faɗa sai dai ta kawar da kai tamkar bata san suna yi ba, dan ba yadda za ta yi da su, yayyun mijinta ne, dama kannensa ne to da sai ta iya saka baki, amma yayyunsa ne da mahaifiyarsa, dole ta ja bakinta ta yi shiru.

Wani babban abin bakin cikin kuma a nan shi ne, wai Haidar yana son Khadija, mamarsa kuma ta dage sai shi za'a bawa ita, kwata kwata yanzu fa shekarun Khadijan 17 years, shi kuma Haidar a yanzu yana da 27 years, amma haka yaron nan ya kafe wai sai ita yake so, yaga ta zama ƴan'mata yanzu, komai zam zam, gata da tsafta da son kwalliya, dan tun suna yara mamansu ta saba masu da kwalliya idan baku manta ba, so yanzu abin ya bi jikinsu, tsaf tsaf da su.

Khadijah sam bata son shi, dan idan baku manta ba a baya tun suna yara yake kyararsu, baya kyautata masu, kun san yaro kuma da iya rike abu, to Khadijah dai bata manta da irin harara, mari tare da zagin da ya rinƙa yi masu tun shekaru goma zuwa shaɗaya a baya ba, dan haka sai ta tsane shi sosai.

Bugu da ƙari Khadijah bata son shi ne saboda rashin iliminsa, kunga dama shi bai yi karatu ba, to yanzu ita kuma tana Ss2, ganin wani iri wawa ma take yi mashi, dan ko sunaye bai iya rubutawa ba, idan an kira shi a waya sai ya tambayi Sadiq wanene mai kiran nasa, Sadiq ɗin ne yake gaya mashi sunan mai kiran nasa, ko saving number mutane a kasuwa Sadiq ɗin ne yake tallafa mashi ya rufa mashi asiri ya yi masa, babu abin da ya sani, shiyasa Khadijah ta yi mugun rai'na mashi wayo take ganinsa a very local, ga shi kuma kakanta wadda ta haifi babanta da kuma maman Haidar ɗin sun zage a kan tabbas shi zata aura tun da ya nuna yana sonta ai ba zasu bawa bare ba. Tirƙashi!! Yau ake yinta.

Kullum cikin kuka take yi baiwar Allah, har abin ya fara shafan karatunta, da babanta ya fahimci haka shi ne ya ce ta yi hakuri In Sha Allah ba zata auri Haidar ba, zai yi magana da mamar tasa, wato kakansu kenan, sannan ta rage zuwa gidan kakan nasu dan ta ɗan huta da zancen Haidar ɗin da ake yi mata, ita kuma kakan ta rike wuta a kan lallai Khadijah ɗin tana gama Ss 3 sai aure kawai. Babbar magana, ko yaya wannan aure zai kasance? To mu dai namu ido.

Zainab dai sai dai ta bisu da ido abinta, babu ruwanta da su, a maimakon Haidar ɗin ya ce Zainab yake so tun da ita ce kara ma kuma ta fi Khadijah kyau, sai ya nace ya khafe lallai
End Ads