Shi kuwa Rocky cigaba ya yi da taɓa mata jiki, tsoratar da ta yi sosai ne yasa take jin kamar wannan taɓa mata jikin da yake yi cin namar jikin nata yake yi, hakan yasa take wannan ihu na ya cinye mata kafa, shi kuwa ina ruwansa? Yasan ma me take cewa ne? Ai kawai taɓata yake yi da bakinsa, kuma ya saba yi wa Kamran ko Mamma irin hakan, shiyasa ita ma ya yi mata.
Taɓa mata wajen cinyarta da ya yi ne yasa ta zunduma wani irin mahaukacin ihu, nan take kuma ta ɗauke dif kamar an ɗauke wutar nepa, da alama tsoro yasa ta sume, ta zaci cikye mata cinya zai yi. Ammafa ni banga laifin Pretty ba, Damusa fa aka ce? Kai ai tama yi ƙoƙari, wannan shegiyar dabba ki sabon? Tab ai Kamran ma badan ya buɗe idanu ya sami Mamma da Rocky ba da zai sha fama kafin ya saba da shi, hmmm waɗan nan dabbobi ba'a sake jiki da su, kuma ba'a sabo da su ato.
Duk sun rikita Kamran bawan Allah, ya rasa ma ta kan waye zai fara, ga Sweetie tana ta rera nata kukan tana ambatar sunan Pretty, ga kuma Pretty wadda ta sume mashi a jiki ya tallabota da hannu ɗaya dan kada ta zube ƙasa.
Shi kuwa Rocky duk wannan abin da ya faru bai sa ya dai'na taɓa jikinta da bakinsa ba. Dama kuma a kaidar dabbobi ire iren waɗan nan idan har ka nuna kana jin tsoronsu to fa sun rinƙa tsorata kenan, duk da shi Rocky ba da gangan ya yi mata hakan ba, kawai yana taɓata ne saboda ya saba yi wa su Kamran.
"Sweetie please ki yi shiru babu abin da zai yi maki, Rocky ne fa, is my friend, baya cutar da mutane".
Cewar Kamran ɗin kenan.
"Ina Pretty take to? Ina ta tafi? Damusar ya cinye mun ita ne? Na dai'na jin kukanta ne!". Cewar Sweetien
Tana magana gabaɗayanta a ruɗe take, duk ta rikice, muryar tata ma baya wani fita, sai in da in da take faman yi, ga hawaye wani na bin wani a saman ƙuncinta, ita da kanta bata san me take faɗa ba!.
"Sweetie Pretty tana nan lafiya, wannan Damusan ba mai cin mutane bane, please ki yi shiru".
Ya kai karshen maganar tare da kwantar da Prettyn a ƙasa, dan ya samu dama ya zaunar da Sweetie ɗin ma!. Shoulders ɗin Sweetien ya riƙo da hannunsa dukka biyu, cikin sigar rarrashi ya zaunar da ita a ƙasa wajen wannan farin yashin (ƙasa) yana mai cigaba da rarrashinta.
Sai tambayarsa ina Prettynta? Take yi. Shi kuwa takaici yasa bai ma san time ɗin da ya wurgawa Rockyn wani irin ɗan iskan kallo mai kama da harara ba, Rocky ya kawosa har wuya saboda bakin ciki, to shi Damusa ina ruwansa?.
Miƙewa tsaye ya yi ba tare da ya sake amsawa Sweetie magana ba, ya nufi hanyar ƙoramar nan dan ya ɗebo ruwa. Da sauri Rockyn ya bi bayansa yana tafiyar ƙasaita na cikakken Tiger mai lafiya a jiki.
"Kada ka biyoni". Kamran ɗin ya faɗa cikin wannan yare tasa da ni kai'na na ƙasa gane wani irin yarene, wannan sai Mammarsa da kuma Alkalamina ne kawai suka san wace yarece!.
Wani irin gurnani Rockyn ya yi alamar irin a banza Kamran ɗin ya yi magana, wato sai ya bishi kenan. Banza da shi Kamran ɗin ya yi bai sake bi ta kansa ba, dan gabaɗaya haushin shi ma yake ji. Sai dai kuma a dake Rockyn namu na amana ba zai daku ba, a zage ma ba zai zaku ba, sai dai Kamran ya yi ta fama da kuncin zuciya.....😅🥱
Har ya je wajen ƙoramar kuma sai ya rasa da me zai ɗebo ruwan, bai ɗauki komai ba, wani karin takaici ya ji kamar ya kifawa Rockyn wani wawan mari, amma haka dai ya daure ya juyo ya dawo. Har lokacin sai kuka Sweetie take yi tana ambatar sunan Pretty, baiwar Allah babu halin gani.
Bai kulasu ba ya wuce izuwa cikin ramin nasu domin ya sami abin da zai ɗebo ruwa a ciki ya zo ya zubawa Pretty ta farfaɗo.
Shi kansa da ya jima a cikin wannan daji tsawon shekaru ya sha madarar mamakin ganin wannan dutse da su Prettyn suke daka da shi, yana gani duwatsu masu abin al'ajabi, wasu ku ga kamar mutun, wasu kamar halittar wata dabba, amma bai taɓa ganin irin wannan ba, hannunsa ya kai ya ɗauki dutsen yana binsa da kallo, wani irin haske mai bala'i kashe kwayar idanuwa ne yake fita daga jikin ɗan dutsen, in dai zaka kalli dutsen kai tsaye, to kana kawar da idanunka ba zaka iya ganin komai ba na tsawon mintoci, haskensa zai kashe karfin ganinka, sannan yanayin abin dai ga shi nan ne kamar ba dutse ba.
Kamran ya ɗauki tsawon a kallah 10 mins yana ta kallon wannan abin mamaki a cike fal ransa, tunanin su Pretty ɗin ne ma ya faɗo mashi a ransa yasa ya mayar masu da abinsu ya ajiye, sai Allah kaɗai yasan daga ina suka samo shi kuma menene wannan abin?.
Yasha madarar mamakin ganin abubuwa dayawa a cikin wajen nasu, ciki kuma harda sarkar gold na mamarsu wanda ya ɓace mata time da ta haifesu, da alkyabbarta, da dai sauran abubuwa, duk gasu nan sun dawo, mamaki ne ya kama shi a kan to ya aka yi ta gane waɗan nan abubuwa nata dukka? Abin dai akwai ɗaure kai sosai, domin wani lokaci idan kaga wani abin sai ka rantse da Allah mum twins ba mutun bace, yanzu dai ga shi ta ɓata ɓat, sama ta yi ƙasa ta yi wallahu a'alam, amma dai a yadda take son twin's ɗin nan nata, a kuma yadda ta rayu dasu tsawon shekaru tara, ta basu kulawa fiye da kanta, ta sha bakar wahala, ta gudunwa mayaƙan nan saboda su, to mawuyacin abu ne ta yi tafiyarta haka kawai bisa radin kanta ta barsu, koda kuwa basu da mahaifi, ina nufin koda kuwa ba ta hanyar aure ta samesu ba, to ba shakka ba zata iya tafiya ta barsu ba, dole dai akwai abin da ya saɓa, sannan bugu da ƙari ga masu nemanta tun farko waɗan da suka yi sanadiyar shigowarta cikin wannan dajin ma har yanzu suna nemanta, har yau har gobe suna shigowa cikin dajin nemanta, hakan na nufin kenan har yau basu ganta ba, da sun ganta ba zasu biyo sahun nemanta ba, to wannan abin dai akwai ɗaure kai sosai, sannan kuma wanenen wannan Jarumin jarumai da ya taimaki su Kamran? Kada ku manta idanunsa ne kawai aka iya gani, kuma babu in da idanun nasa suka banbanta dana Pretty akwai fa ɗaure kai......🤔
Kamran da ya je ɗaukar abin da zai ɗebi ruwa, sai ya ɓige da al'ajabi tare da mamakin abubuwan da yake gani a cikin ɗakin nasu, abubuwa ne da bai taɓa ganin irinsu ba, kada ku manta shi bai taɓa fita daga cikin wannan daji ba, so kayan da Mammarsa take kerawa kawai ya sani, su Pretty kuma kayan da suke amfani dasu dukka kaya ne da aka kawosu daga gari, abubuwa ne masu bala'in tsada ba kaɗan ba, hakan yasa Kamran ɗin ya zama kamar wani ɗan kauye a cikin wajen, ya taɓa wannan ya taɓa wancan, ga mamaki sosai a saman fuskarsa.
Wani irin ƙatuwar envelope ya ɗauko daga cikin wani waje da aka keɓe shi sosai, alamar wajen ajiyar abubuwa masu mahimmanci ne, da alama kuma wannan envelope ɗin yana da matuƙar mahimmanci fiye da tunaninku, in da aka ajiye shi ma dole babban mutun ne ya ajiye shi, ba irin ajiyar su Pretty bane, da alama mum ɗinsu ce ta yi wannan ajiya kafin ta bar wajen.
Ya ɗauki tsawon a kallah two mins yana karewa envelope ɗin kallo kafin ya kai hannunsa ya fara ƙoƙarin buɗeta. Wani irin kukan da Rocky ya yi mai sautin gaske ne yasa ya dakata daga yunƙurin buɗe envelope ɗin, a hanzarce ya ɗaga kansa sama yana kallon wajen hanyar shigowa daga ramin.
A karo na biyu Rocky ya sake yin irin wannan kukan. Ai kuwa ba shiri ya yi wurgi da wannan envelope ɗin, ba tare da ya ɗauko abin da zai ɗebi ruwan ba ya fice waje da gudu sosai domin ya je yaga menene yake faruwa?.
Yana fitowa ya ja wani irin mahaukacin birki yana kallon wannan al'amari. Sweetie ma dai ta suma saboda tsoro, bayan shigar Kamran ɗin cikin ramin Rocky ya zo yana taɓa mata jiki da bakinsa kamar dai yadda ya yi wa Pretty, hakan ne ya tsoratata sosai har ta suma, shi fa Rocky idan yana wannan taɓa jikin burinsa kawai a rinƙa shafa mashi nashi jikin shi ma, shiyasa yake yi wa su Mamma ma haka, amma su Pretty basu gane ba.
Sweetie ta suma, shi kuma Rocky ya farauci wani mayaki guda ɗaya da ya zo giftawa ta wajen, mayakin ya yi yunƙurin harbin Rockyn da kifiyarsa a ciki, kifiyar ta same shi sai dai bata ji mashi ciwo sosai ba, dan fatar dabba daban take da na mutun, ba ƙaramin abu bane yake hudata, hakan yasa bata jiwa Rocky ciwo sosai ba, shi ne yasa ya daka waɗan nan uban ihun da ya yi tare da buga tsalle ya capko wuyar mayakin, daga saman dokinsa ya janyosa kasa, nan take ya tsinke mashi agarar wuyarsa, shi ne fa ya hau cin nama abinsa.
Shi dai Kamran a wannan point ɗin kansa ta ƙulle, tunani yake yi wai waɗan nan warriors ɗin basu karewa ne a cikin dajin nan?. Bai san cewa turosu ake yi ba, idan aka turo wasu, in aka ji shiru basu dawo ba, sai a sake turo wasu, haka suke yi, kuma a dokarsu duk wanda ya fita neman mum twins kada ya dawo ba tare da ita ba, idan ya dawo ba tare da ita bama kashe shi za'ayi, so yanzu haka wasu mayaƙa su takwas ɗin ne suka sake shigowa cikin dajin, shi ne suka rarraba hanya wai kowa ya yi nasa gun ko Allah zai sa su kama mum twins, ashe basu san rabon Rocky ne wannan da ya biyo ta hanyarsu Pretty ba, to ga dai shi nan Rocky ya ci nama abinsa, wani ma ya sake zuwa, ai shi Rocky ba zai gaji da cin nama ba.....😅
Izuwa yanzu Kamran ya fara tsorata da waɗan nan warriors ɗin, yaga yanzu almost goma sha biyu suka mutu amma wai wasu sun sake zuwa? Anya kuwa ba'a cikin dajin nan suma suke ba kuwa? Ya jefawa kansa tambayar da shi ma bashi da amsarta, tunani ya fara yi a cikin zuciyarsa na cewa yana da kyau ya kama warrior guda ɗaya ya ɗaure shi ya samu ya gaya mashi me yake kawosu cikin wannan daji, dan gaskiya ya fara tsorata da lamarinsu.
Ya jima a tsaye a wajen yana kallon yadda Rocky yake watandarsa da namar wannan mayaki, ya kasa gaba ya kasa baya, har sai da ya fara jin motsi a kusa da shi, sannan ne hankalinsa ya dawo jikinsa, a hanzarce ya kai kallonsa wajen motsin. Pretty ce ta farfaɗo daga sumar da ta yi tana ɗan motsi.
Da sauri ya ƙarisa wajenta tare da zube gwiwowinsa a kasa kusa da ita, sunanta ya fara ambata a hankali hankali, fatansa ɗaya Allah yasa ta tashi a nutse, kada ta tashi a birkice. Pretty akwai murya innalillahi, idan ta yi ihu sai dajin kusan gabaɗaya ya amsa, kada ku manta ranar da aka haifeta ma sai da dajin yasan da zuwanta, saboda kuka, Sweetie sarkin hakuri ita kuma, har suka girman nan Pretty bata da hakuri da cin abinci, idan ta ji yunwa ya fara damunta zata fara yi wa Sweetie kuka ne kawai abinta, gata da ruwan hawaye kamar famfo ake buɗewa, dan hakan ne yasa Kamran yake addu'ar ta tashi cikin nutsuwa ba da hayaniya ba.
Jin muryar Kamran yana ambatar sunanta yasa ta yi wani irin zaro idanunta waje, kai tsaye sai cikin kwayar idanunsa, da yake ya tsuguna a gabanra ne yana kallon kyakkyawar face nata.
Ɗan lumshe idanunsa ya yi tare da sake buɗesu amma ba'a kan nata idanun ba, sai ya ɗan kawar da kallonsa gefe guda.
Ita kuwa ganin shi ne a kusa da ita yasa ta fara ƙoƙarin miƙewa zaune tana faɗin. "Kamran ina Sweetie take? Damisar bai cinyeta ba ko? Ina take?".
Tana magana tana tattaɓa kafafunta ta ji shin Rocky ya cinye mata kafafun ne ko kuma dai suna nan.
Ganin cewa bata lura da Rockyn dake can gefe yana watandarsa ba ne yasa Kamran ɗin ya ce mata.
"Pretty kin manta na taɓa gaya maki cewa Rocky baya cin mutane ne? Ai baya cin mutanen da suke tare dani, abokina ne fa, ke baki ga ni ma bai cinyeni ba ne? Dan haka ki dai'na jin tsoronsa ku kullula abota kin ji ko?".
Yadda ya yi mata maganar cikin sanyin murya yasa ta nutsu ta kuma fahimce shi sosai, dan haka cikin nutsuwa ta ce.
"To ina Sweetieta take?".
Da hannu ya yi mata nuni da ita yadda take kwance a gefensu a sume.
Da sauri ta rarrafa ta ƙarisa wajen ƴar uwar tata, sunanta ta fara ambata tana kallon face nata.
"Ta suma ne fa Pretty, ki barta sai an zuba mata ruwa".
A ɗari ta juyo da kallonta a kansa, zaro idanu waje ta yi, ai a dubu shi kuma ya kawar da kallonsa daga kanta, dama yaya bare kuma ta zaro mashi ido? Wannan yarinya tana birkita mashi ƙwaƙwalwarsa sosai, sai ya rasa a wani point zai ajiyeta.
"Meyasameta ta suma Kamran?". Ta yi tambayar ne a ruɗe sosai
Ba tare da ya kalli in da take ba ya bata amsa da cewa "Tsoro ta ji ita ma, yanzu dai tashi muje wajen ƙoramar can mu ɗebi ruwa mu zuba mata, bari na ɗauketa ko?".
Da sauri ta miƙe tana faɗin okey. Miƙewa shi ma ya yi tare da saɓar Sweetie ɗin a saman shoulder ɗinsa mamar baby, suka nufi wajen ƙoramar, ko kallon in da suke Rocky bai yi ba, ya samu nama ba ruwansa da su.......😅
Ita ma Pretty bata lura da Rockyn yana ɗan gefe yana cin namar ba, da ta gani ai kara haukacewa zata yi, za ta ce da Kamram ai ga shi nan Rocky yana cin mutane, ita ba zata yarda da shi ba, to sai Allah yasa bata gani ba, ta yi gaba shi kuma Rocky yana ta ɗan bayansu ne.
A kusa da ƙoramar ya kwantar da Sweetien, sannan ya wuce ya ɗebo ruwa a cikin kyawawan tafukan hannunsa, a hanzarce ya zo ya yayyafa mata a saman fuskarta.
A ruɗe ta farka tana mai kukan ambatar sunan Pretty, da saurin Prettyn ta ƙarisa kusa da ita tana ce mata gata nan babu abin da ya faru.
Haba rungume juna suka yi suna sauke ajiyar zuciya,. Shi kam Kamran da ido kawai ya bisu, ya rasa a wani matsayi zai ajiye yaran nan, da zarar ɗaya ta yi abu to ɗayar ma sai ta yi, yara kamar wasu chewing gum.
Sai kallon face ɗin Pretty yake yi, har ga Allah wannan ɗan bakin nata yana matuƙar yi mashi kyau, bakin kuka, a duk lokacin da ya kalli ɗan bakin nan nata abu ɗaya ne yake faɗo mashi a ransa, ba komai bane kuma face ranar da aka haifeta, irin ihun da ta rinƙa tsallarawa, da zarar ya tuna hakan kuma sai ya ɗan yi murmushi, yanzu ta girma kamar ba ita ba.
Ɗago kai Pretty ta yi daga jikin Sweetie da nufin ta kalli Kamran ɗin tana son yi mashi magana.
Ganin ta ɗago kai zata kalle shi ne yasa ya yi saurin kawar da kallonsa daga kanta, dan ma kada su haɗa idanu.
"Kamran mutafi ko?". cewar Pretty.
Sauke kwari da bakarsa dake a bayansa ya yi ya ajiye a ƙasa tare da nufar wata bishiyar ayaba dake ɗan nesa da ƙoramar kaɗan.
"Ina zuwa Pretty, zamu tafi amma sai mun ɗan huta a nan".
Ya bata amsa yana mai cigaba da tunkarar in da ya nufa.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da kafeshi da idanu tana kallon yadda yake tafiya a bubbuɗe cike da jarumta, shi ko tsoron namun daji baya ji, duk in da ya nufa tafiyarsa kawai yake yi ba tare da tunanin zai iya haɗuwa da muguwar dabba a wajen ba, babu ruwansa da wannan tunani, ɗan garama kwana biyun nan da yana samun saɓani da waɗan nan warriors ɗin sun fara jefa mashi tsoro da shakku a cikin zuciyansa, hakan yasa yanzu idan ya tunkari waje yana tafiya yana tunanin kada ya haɗu da wasu warriors ɗin, amma sam baya tunanin kada ya haɗu da wasu namun dawa.
Har ya ƙurewa ganin Pretty bata kawar da kallonta a kansa ba, sai da ya kure mata ne ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da raba jikinta dana Sweetie tana faɗin.
"Sweetie Kamran yana da kirki sosai".
"Sosai kam Pretty, mutumin kirki ne, nafara tunanin shi ne wanda mum ta ce mu nemo".
Miƙewa tsaye Prettyn ta yi tare da nufar wajen duwatsun da suke a bakin ƙoramar tana faɗin. "Sweetie bari na shiga cikin ruwa kaɗan ina zuwa, idan mun koma sai mu yi maganar Kamran ɗin, yanzu zai iya jin abin da zamu faɗa fa".
Jinjina mata kai kawai Sweetien ta yi, zuciyarta a cike tab da tunanin ya Kamran yake? Ya kamanninsa yake? Tana burin taga face ɗinsa!.
Shi kuwa abin tsakiyar ganyen ayaba ya ciro guda biyu dogaye, sannan ya dawo in da suke.