x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 32 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 93001 words
  • 96000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 366

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
kyakkyawar bakin gashin kan nan nata ya yi kafin ya ce. "Pretty meyafaru ne? Where's the warriors?".

Sai a lokacin ta ɗan ɗago kanta daga saman kirjin nasa, ɗan bakin nan nata har yanzu yana kerman tsoro, kyakkyawar red lips ɗin nan nata sai ɗan ɓari suke yi. Har yanzu ɗan siririn zazzaƙar voice ɗin nan nata rawa yake yi, da kyar ma ta iya bashi amsa da.
"Someone killed them all, i don't know who's he, he closed his face with veils, only his eyes i saw".

Ta bashi amsa tare da sake komawa ta kwantar da kanta a saman faffaɗar kirjin nasa, saboda shegen son jiki ne da ita kamar mage, ga bala'in tsoro, amma akwai wayo kuma sosai da sosai!. Ta wani lafe mashi a jiki, da yake shima yana cikin damuwa da tashin hankali sai bai yi mashi kamar a jikinsa ta kwanta ba, hankalinsa da nutsuwarsa basa a tarrare da shi!.

Jin abin da ta ce ne yasa ya tuna da wannan mutumi da ya taimakesa a yanzu, wanda ya bari suna fafata yaki da warriors ɗin can kenan. Tunani ya fara yi na cewa in dai haka ne kenan wannan matashin shi ne ha taimaki Pretty ya kashe warriors da suka biyota kafin ya ƙarisa wajensa shi ma ya taimaka mashi kenan? To waye shi?. Ya tambayi kansa tambayar da bashi da amsarta.

Kamar wadda aka mintsina ya ce. "Pretty let's go, I want to see that man, I have some questions that I want to ask him, and I want to see his face".

Ya kai karshen maganar yana shafa kyakkyawa kuma lallausan curly hairnta!.

"Kamran ina tsoro, i don't want to go they again, this people's aren't a human being at all!".

Ya fahimceta sosai, ya fahimci ta yi tsananin tsorata ne, baiwar Allah bata taɓa ganin makamancin hakan ba. Abin da bata sani ba shi ne, waɗan nan warriors da suke shigowa cikin wannan daji duk su suke nema, idan baku manta ba tun farko mayaka ne suka biyo mummynsu, kuma da suka biyota ba ita suke son kamawa ko kashewa ba, abin da yake cikin cikinta suke son ɗauka, which means kunga su Prettyn kenan suke nema ido rufe ko ta halin ƙaƙa, tsawon shekaru goma kenan yanzu kullun sai sun shigo cikin wannan dajin neman su Prettyn, sun kasa hakura su yarda cewa mum twins da cikinta sun mutu tun lokacin da suka harbeta da kifiya, sun ki yarda ta mutu, da alama sun lura da cewa wannan mayakin da ya harbeta ɗin bai harbeta a in da zata mutu ba, hakan yasa suka kasa yarda da ta mutu ɗin, shi ne yasa kullum basa gajiyawa wajen zaryar neman su twin's ɗin! Sannan idan kuka yi duba da yadda Mamman Kamran ta ce bata taɓa ganin warriors a cikin wannan dajin ba sai yau, hakan zai sa ku gane e lallai dole akwai abin da suke nema wanda yasa a koda yaushe suke zuwa, to ba komai suke nema ba face su Pretty, a haukace suke suna nemansu ido rufe, ko araye ko amace, su dai kawai su gansu, sai dai kuma duk cikinsu babu wanda yasan su Pretty ɗin ai, basu san kamanninsu ba! Suna dai nemansu, a tunaninsu za su iya ganesu ta hanyar mum ɗin su tun da sun santa ita kam!!.

Abin tambaya a nan shi ne, me zasu yi wa twin's ɗin idan suka kamasu? Meyasa basu buƙatar mamansu sai dai su? Meyasa zasu iya kashe mum ɗin tasu dan kawai su fasa cikinta su ɗauke su? Ina zasu kaisu? Shin turo su aka yi ne ko kuma bisa radin kansu ne? In turosu aka yi to wanene ya turo su?. Waɗan nan amsoshi duk sai alkalamina ne kawai zai warware maku wannan cakwakiya!!.

"Pretty kada ki ji tsoro, mu je kawai". Ya faɗa tare da sanya hannunsa ya ɗago haɓarta.

Jinjina mashi kai ta yi, magana ta gaskiya ta amsa mashi da okey ɗin ne kawai, amma wlh tana tsoron zuwa wajen fiye da tunaninku, mayyar tsoro ce ga shegen son jiki, yanzu da wuya idan bata yi mafarkin wannan abin da ya faru ɗin ba, kaɗan daga cikin aikinta ma ta yi mafarkin warriors ɗin sun kasheta, ga shi dai a zahiri basu kasheta ɗin ba, ko taɓata ma basu yi ba, amma a mafarki tsab zata yi mafarkin sun kasheta!.

Miƙewa ta yi daga jikin nasa tare da saukowa kasa daga saman dutsen, sai narai narai da idanu take yi kamar zata yi kuka. Lallaɓata ya rinƙa yi yana karfafa mata gwiwa, sai dai ina, wannan bata san karfafa gwiwa ba, tsoro kawai ta sani a rayuwarta kamar farar kura, tana gani a gaban idanunta wannan matashi ya yi wa waɗan nan mayaka biyu da suka biyotan kisan killah na rashin imani, sannan ace mata ta sami kwarin gwiwa? Ai ba wannan magana, a dai yi sha'ani kawai...........😅

Hannunta ya riƙo cikin nasa suka nufi wajen da suka fito, izuwa yanzu ya warware ya koma normal, sai maƙoshinsa da ta bushe kwalam yana buƙatar ruwan sha, kishi yake ji sosai da sosai, sai dai babu ruwa a kusa, dole sai sun je wajen wannan ƙoramar zai iya samu ya sha.

Pretty dai bata yarda da iya hannunta kawai da ya rike ba, gani take yi fa warriors ɗin nan zasu kasheta, dan haka sai ta matso jikinsa sosai ta rikesa ta wajen ƙugunsa domin ta rage tsoro. Wani irin shock ya ji a jikinsa na rungumo mashi kugu da ta yi, wannan yarinya akwai son jefa mutun cikin bala'i, ya faɗa a cikin ransa tare da ɗan riko shoulder ɗinta, saboda ta ɗan kara nutsuwa mashi!.

A haka suka nufi wajen nasu, sai baya baya take yi duk da ta wani dungume mashi kugu kamar nata, da alama ma ita sam bata san amfanin wajen da ta runguma ɗin ba, ita fa kawai ta ɓuya kada mayakan nan su ganta, a kan haka koma inane zata runguma babu ruwanta, to bama dan Kamran ɗin ya yi mata daɗin baki ba ai wlh da babu in da zata je, sai dai duk wacce za'ayi ayi!........ Pretty manya! Yanzu ma da kuka ganta zaune a saman dutsen nan wannan matashin da ya kashe mayakan da suka biyota ɗin ne ya zaunar da ita a wajen, ya kuma ce kada ta tashi har sai Kamran ya zo! Shi ne yasa kuka ga ta daure ta zauna shiru a wajen, amma a tsananin tsorace take sosai kafin Kamran ɗin ya zo.

Abin mamaki tun da suka doshi wajen suka ji shiru babu wani hayani ko kuma motsin wani bil adama, tsit kake ji kamar babu waɗan da suka taɓa yin faɗa a wajen. Hakan yasa Kamran ya kara saurin dan ya iso wajen.

Wayam babu kowa a wajen, ga gawarwakin warriors ɗin dukka a zube a kasar wajen, amma babu wannan matashin a wajen, babu shi kuma babu gawarsa, hakan na nufin basu kashe shi ba kenan, shi ne ya kashesu kuma ya yi tafiyarsa, to wanenen shi?.

Ɗan waige waige Kamran ya fara yi ko zai hango giftawa ko kuma wani motsi na wannan matashin. Amma ina, sam babu ko mai kama da shi a arear wajen. A hanzarce ya saki Pretty tare da faɗin. "Wait for me here am coming".

Ina ai kara ƙanƙame shi ta yi tare da ƙoƙarin saka mashi kuka a kan kada ya tafi ya barta.

"Pretty nothing will happen, you hear? Please be strong kin ji? Zan duba mutumin nan ne da ya taimaka mana, maybe bai yi nisa ba sai mu san who's he ko?".

Ina ai kara ƙanƙame mashi ƙugunsa ta yi tare da kwantar da kanta a saman kirjinsa tana faɗin.
"No Kamran, i can't stay here, ina tsoro sosai, let's go together kawai!".
Tana magana hawaye na bin saman lallausa kuma jajir ɗin kumatun nan nata!.

Ganin yadda ta tsorata sosai kuma har yanzu tana cikin tsoron ne yasa ya ji muguwar tausayinta ya kama shi, duk sai ya ji wani iri babu daɗi, ya ji ba zai iya tafiya nan da can ya barta ba, ta rigada ta tsorata sosai, dan haka sai ya rungumeta da kyau a jikinsa tare da kai hannunsa cikin dabara ya cire hannayenta data harɗesu a ƙugunsa, ya mayar mata da su saman cikinsa ta wajen kirji, saboda zaman hannayen nata a ƙugunsa fa suna saka shi yana jin wani irin yanayi.

"Is okey Pretty, I can't go anywhere na barki, mu je mu duba Sweetie tun da mai taimakon ya tafi, kuma i promise you that zan kula da ku sosai, sannan zan rinƙa zuwa wajenku sosai da sosai, gobe ma idan zanzo zanzo tare da kwari da bakata in fara koya maki harbi kin ji ko?".

Tana daga kwance luf a saman kirjin nasa ta ɗaga mashi kai alamar e ta ji. Shafa kanta ya yi har izuwa bayanta kafin ya ce to. "Let's go ko? Mu je wajen Sweetie".

Nan ma jinjina mashi kai kawai ta yi, ita dai koma me ba zata rabu da jikinsa, dan gani take yi tana sakinsa tabbas waɗan nan warriors ɗin za su tashi su kamata, shiyasa ta kara ƙanƙame shi!!.

Cikin ramin nasu suka nufa, tana rike da shi har suka je bakin wajen, sannan ne ya ce to ta sake shi ta fara shiga ciki. A hanzarce ta sake shi ta yi maza ta buɗe kofar ta faɗa ciki abinta, Allah ya rufa masu asiri warriors ɗin da suka kalli wajen ɓuyar tasu ma dukka an kashesu, yanzu babu wanda yasan in da suke.

Sai da ta shiga shi ma ya rufa mata baya, kai tsaye wajen Sweetie suka nufa, baiwar Allah tana kwance a saman gadonsu shiru, kamar mai tunanin wani abin, ta ɗaga idanu tana kallon sama yadda kuka san tasan abin da take kallo.

Jin motsin shigowa wajen ne yasa ta fara faɗin.
"Pretty meyasa kika daɗe haka?".

Da gudu ta ƙarisa wajen ƴar uwar tata tare da hayewa saman gadon, dai'dai lokacin ita kuma Sweetien ta miƙe zaune tana jiran amsar da Prettyn zata bata, tana zuwa ta rungumeta sosai tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

A matukar ruɗe Sweetien ta fara tambayarta. "Pretty lafiya kike kuwa? Meyafaru? Meyasa kike kuka? Please tell me kada kisa zuciyata ta buga!".

Ƙarisowa wajen gadon Kamran ya yi tare da zama a kusa da su. "Pretty why zaki tayarwa da Sweetie hankali? Me kuma abin sake yin kuka a nan tun da komai ya wuce?". Cewar Kamran kenan!.

Cikin kuka ta ce. "Dole zan yi kuka Kamran, da yanzu sun kashe ni shikenan ba zan sake ganin ƴar uwata ba? Shikenan mun rabu da ita? Da waye ita zata zauna idan bana nan? Waye zai kaita toilet? Waye zan bata abinci? Waye zai bata kayan sakawa? Waye........."

Bai iya bari ya kai ƙarshen jero mashi maganganun nata ba yasa tafun hannunsa ya rufe mata ɗan bakin nata, wannan yarinya sai shirin Allah, kawai ta zo ta ɗagawa ƴar uwarta hankali a banza bayan komai ya rigada ya wuce.

"Kamran Please tell me me ya sami Pretty? Who attack her? Who want to kill her da na ji tana faɗa? Meyake faruwa ne?".
Tana magana kamar zata yi kuka baiwar Allah, har fararen idanunta su cika tab da kwallah, duk ta ruɗe!.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Sweetie calm down, nothing happen, kawai wasu ne suka so raunata mu". Daga nan ya kwashe labarin abin da ya faru ya gaya mata ba dan ya so ba, sam bai so ta san komai ba, dan baya son abin da zai ɗaga mata hankali har ya sanya kuka, saboda matsalar idanunta!.

Jin abin da ya faɗa ne yasa ta kara ƙanƙame Pretty suka manne juna kamar zasu shige jikin juna, nan take ita ma jikinta ya soma kerma, ta tsorata, cikin damuwa take faɗin. "Nashiga ukuna, my Pretty kashe mun ke suke son yi kenan? Me kika yi masu? Wayyo mummynmu".
Tana magana tana ruwan hawaye, ita ma Pretty ruwan hawayen take yi.

Yau dai Kamran ya ga ikon Allah, haka ya hau rarrashinsu su biyun dukka, baya son Sweetie ta yi kuka ko kaɗan, dan yana gudun idanun nan nata su lalace gabaɗaya, yanzu a point ɗin da taken nan za'a iya yi mata magani, da Mammarsa zata yarda ma ai da ita ma zata iya yi mata magani, amma ba zata taɓa yarda ta taimaka masu ba, so yana so ne dama ya lallaɓa Mamar tasa ta gaya mashi menene maganin wannan itaciya mai gubar idan ta taɓa idanun mutun ya dai'na kallo, idan ta gaya mashi zai zo ya yi mata ganin da kansa, so idan tana kuka tana mussuƙe idanun wajen goge hawaye za'a iya samun matsala su lalace gabaɗaya su ki gyaruwa, hakan yasa hankalinsa ya tashi da ya ganta tana kuka.

Ba kakkautawa ya hau rarrashinta yana bata hakuri, ga shi sun haɗu su biyu sai yi suke yi, ba abin ka sami bulala ka zanesu ba........😅

Kawai sun saka bawan Allah cikin damuwa, Sweetie ta ce kashe mun ke suke son yi, Pretty ta ce rabani dake suka so yi, haba sai su kara sautin kukan nasu tare da kara manne juna, na gaya maku kamar a sami bulala a zanesu, amma ya za'ayi? Dole ne kawai Kamran ya lallaɓasu ya basu hakuri ya samu su yi shiru!.

Da kyar ya iya samu ya lallaɓasu suka yi shiru, sannan ne ya samu damar gaya masu cewa gobe zai zo ya fara koyawa Pretty harbi da kifiya, yanzu zai je gida kada Mammarsa ta nemesa, dan ya ce mata ba zai wuce one hour ba, yanzu kuma yasan awa ta wuce.

Pretty kamar zata yi kuka, bata son ya tafi ya barsu, tana tsoro sosai, amma ya zata yi? Dole haka ta hakura suna ji suna gani ya tafi. Yana tafiya suka kara mannewa junansu saboda tsoro.

Lallai da alama yau su Pretty babu ko iya cin abinci, dan naga alama tsoro ba zai barsu su iya raba jikinsu da juna ba😅 to mu dai bari mu leƙa KINGDOM OF POWER mu ga me ake ciki?.

KINGDOM OF POWER💪🔥

Almost 10 mins Gimbiya Chuchu tana zube ƙasa a saman gwiwowinta, shi kuwa Yah Jawad yana cikin room ɗinsa yana shiryawa, kamar zata yi kuka, abin da bata sababa, duk kafafunta ciwo suke yi mata, sai wani irin raɗaɗi da zogi suke yi mata, tana son ta yi kuka ko zata rage jin raɗaɗi, amma kuma tana tsoron yin kukan kada Yah Jawad ya fito ya sameta, dan ya ce kada ta bari ya isko hawaye ko ɗigo ɗaya a saman face nata, so tana tsoron kara laifi a kan laifi, hakan yasa ta daure ta cije, amma fa ga fararen idanun nan nata sun yi jajir da su, alamar ta wahala.

Sai da ta kara 5 mins a haka sai ga shi ya fito shirye cikin wasu tsadaddun kayan barcinsa wando da riga, rigar mai karamar hannu ce wandon kuma zuwa dai'dai gwiwowinsa ta tsaya mashi, ya yi wa kayan matuƙar kyau sosai, ga shi fari tas da shi, launin kayan kuma brown color, hakan ba ƙaramin kyau ya yi mashi ba, ya fito a balarabensa, ga gashin kan nan nasa da ya sha gyara sai kyalli yake yi, gashin yana kwance luf, sai suba wani irin daddaɗar kamshi yake yi, bai sanya takalma a kyawawan fararen kafafun nan nasa ba.

Tun da ya fito sai kallonsa ta ƙasan ido take yi, ya yi kyau ba karya.

A saman bakin bed mattress ɗin nasa ya zo ya zauna tare da kai hannu ya ɗauko ɗaya daga cikin wayoyinsa.

Kamar zata yi kuka ta ce.
"Yah Jawad dan Allah ka yi hakuri, na tuba ba zan sake ba".

A hankali ya ɗaura waɗan nan dara daran idanun nasa a saman face nata, ta tsuke ɗan bakin nan nata kamar wadda aka yi yunkurin dallawa mari.

Shiru ya ɗan zuba mata idanu na ƴan mintocin da a kallah zasu kai 3 zuwa 4, sannan a nutse ya fara motsa lips nasa ya fara magana in a low voice sosai.
"Jannat tell me your problem first, what are you doing with all those pics that your talking anytime?".

Jannat shi ne ainahin sunan Gimbiya Chuchu, kuma sunane na kakarta wadda ta haifi mahaifiyarta, shi ne yasa mamanta ta ɓoye sunan nata suke kiranta da Chuchu. Amma banda dukka brothers ɗin nasu, su kam da Jannat ɗin suke kiranta!.

Narai narai da idanu ta yi, ita bata san me zata sake ce mashi ba, ita da kanta bata san me take yi da hotunan ba, ko kallon hotonan ma fa bata sake komawa ta yi idan ta ɗauki hoton, ita dai ta ɗauka ɗin ne kawai.
Manya kuke ji kenan ita dai ta ɗauka kawai abinta..........😅

"Sorry Yah Jawad ba zan sake ba, na yi alkawari zan dai'na ɗaukar hoto daga yau".
Ta kai karshen maganar cikin ɗan shagwaɓa.

"Okey zaki dai'na ɗaukar hoto ne ma ba kin daina ba? Wato zaki cigaba kenan".

A hanzarce ta girgiza mashi kai tana faɗin. "No I mean na daina not zan daina, nama dai'na, please yah Jawad".

Shiru ya yi mata bai sake yin magana ba, sai ma kunna wutar screen ɗin wayarsa da ya yi ya fara latsawa.

Shagwaɓe fuska ta yi kamar zata yi kuka, har ga Allah ta gaji, ba zata iya jurewa ba.
"Yah Jawad please am tired, ka yi hakuri dan Allah".

Yadda ta yi maganar a shagwaɓe sosai ne yasa ya dawo da kallonsa a saman fuskarta. Slowly ya fara binta da kallo from head to toe, kallon one min ya yi mata kafin ya kawar da idanun nasa izuwa saman screen ɗin wayarsa.

"We done with the case one, na ji na hakura, amma idan na sake kamaki a kan case ɗin pics zaki sha wahala, lest go to the second case, waye ya ce ki fito daga ke sai kayan barci? Are you out of your sense? Mutun nawa kika ci
End Ads