sararin samaniya ruwan nan yake yi, saboda haskensa! Sai dai kuma tsakanin tekun da wannan dutse da take a kai, akwai nisa sosai, sannan kuma, akwai dogayen bishiyoyi ta gefe gefe ruwan, bayan haka akwai abubuwa da dama dai irin na ko wace babbar daji da ta amsa sunanta daji.
Dakatawa ta yi daga gudun da take yi tana mai kallon wannan tapkeken tekun, tana sakin wahalallen nishi. Wannan shi ne gaba babu hanya baya ma babu hanya, gaba teku baya warriors! Ya kenan?.
A hankali tamkar mai tsoron juyowa ta juyo dan ta kalli waɗan nan masu bin nata, wanda suma a daidai lokacin suka cin mata, har lokacin tana cije da laɓɓanta bata saki ba, hakan zai fahimtar da kai tana cikin azaba.
Juyowarta ya yi daidai da ɗaya daga cikin warriors ɗin ya ciro kwari da baka daga bayansa, ya ɗana kifiyarta tare da ja da karfi, ya saitata, kai tsaye ya harbeta sai saman katon cikin nan nata ta gefen hagu.
Wani irin jini jajazir ne ya fallatsa ya fito daga jikinta, da alama jinin nata ma, ya jijjiga sosai, dan kuwa yanda ya fallatsar nan tamkar jira yake yi a huda mishi hanya ya fito.
(*PRINCESS TEEMA CE....✍️🔥💘* )
Saboda gajiya da kuma bakar azabar wahalar da ta sha, muryarta baya fita sosai, wani irin wahalallen ihu ta saki wanda sautinsa bai fita ba, cikin bakin azaba da wahala ta sanya hannunta bibbiyu ta dafe cikin nata tare da riƙo kifiyar da suka harbeta da shi ɗin gam tana nishi, lokaci guda fuskarta ta sauya, har wani kumburi ta yi cikin ƙanƙanin lokaci, dama kuma ga na ciki a gefe, sai abin ya haɗu ya yi mata yawa, duk wanda ya kalleta a halin da take a ciki, komai rashin imaninsa matuƙar musulmi ne yasan kalmar shahada, kai ko ba musulmi ba sai ya matsa mata kwallah ba kaɗan ba, domin tana cikin wani irin bakin mawuyacin hali wanda baki ma ba zai iya misilta shi ba.
Su kuwa waƴan nan shaiɗanun azzaluman, ko a jikinsu, tamkar ba mutane bane, tamkar babu zuciya a kirazansu, tamkar wasu dafaffun karafuna ne ko ace duwatsu ne a matsayin zukatansu ba zuciya ba, saboda tsantsar zallar madarar rashin Imani dake tattare da su, sai ma ƙoƙarin ciro wani kifiya ɗaya daga cikinsu ya yi domin ya kara sake mata a cikin nata, duk da halin da take ciki basu da niyar raga mata ko su tausaya mata.
Cikin fitar hayyaci ta saki wani marayar wahalallen kuka tare da yin baya baya ta faɗa kasan wannan katafaren kogi ko ace teku, dan ko rani ya yi damina ya ɗauke, wannan tekun bata ƙafewa, shi kuma kogi yana iya kafewa a lokacin da ba damuna bane.
Faɗawarta kasar wannan dutsen ya yi dai'dai da kecewar ruwan sama kamar da bakin kwarya, ga tsawa da walkiya mai karfin gaske.
Tsakanin wannan dutse da kuma ruwan dake a ƙasansa, zai iya kai a kallah 3.6 meter, amma haka ta faɗa kasan, hakan kuma zai kara tabbatar muku da cewa tabbas bata son mutuwa a hannun waƴan nan azzaluman, tabbas tana da bukatar cigaba da rayuwa.
Ganin ta faɗa kasan ne yasa suka ƙariso waje ba tare da sun sauƙa daga kan dawakansu ba, babu alamar tsoro, tausayi, imani a tattare dasu, sai ma alamar jarumta tare da taurin zuciya.
Ruwan saman na dukansu, haka suka tsaya a cikinsa dan cimma burinsu, sai wani irin numfashi mara daɗin ji dawakan nasu suke fitarwa, su kansu warriors dake a saman dawakan, sai wani numfashin suke yi alamar sun wahala a gudun da suka sha.
Suna ƙarisowa ɗaya daga cikinsu ya sauƙa daga saman dokin nasa yana wani irin taku wanda yake nuna cikakken warriors ne, wato (Mayaki) lafiyayye mai jini a jika, duk in ya taka kasa, sai wajen ya amsa, yana da tsawo ga faɗin kirji sosai, sannan ga cikar halittar namiji, wanda yake nuna maka cewa cikakken gwarzon mayaki ne, ya horu ainun.
Kasan dutse ya zo ya leƙa a yayin da su kuma sauran suke a saman dawakansu suna jiran su ji me ake ciki.
Ko alamarta bai ga ni ba, da ya leƙa, alamu sun nuna ruwa ya tafi da ita, a nasa tunanin, katafaren teku ne wanda ya kai har mararrabar Masarautar su da kuma ƙasar dake makwabtaka da su, ma'ana wannan tekun ya zama kamar itace bordersu kenan.
Juyowa ya yi ya nufi bujumin dokinsa yana girgiza masu kai, alamar su je kawai babu wata matsala.
Juya kan dawakan nasu suka yi, a guje suka bar wajen suka nufi hanyar da suka fito.
Sun ɗan yi gudu mai nisan kafin su zagayo ta kasan dutsen, wajen ruwan kenan, dan su duba ko za su iya ganin wannan matar.
Duk da idanunsu ya gane masu faɗawarta kasar tekun, ba gaya masu aka yi ba, gani suka yi, amma basu yarda da cewa ruwa ya tafi da ita ko makamancin haka ba, shi ne yasa suka zagayo dubawa.
Warriors (Mayaƙa) guda biyu ne suka sauƙa daga saman dawakansu, suka nufi bakin ruwan dan su duba da kyau da kyau.
Kash ko alamar wannan mata babu a wajen, da alama ruwa ya tafi da ita da gaske ne, ga kuma baiwar Allah tana nakuda, ga kifiya a cikinta, ya ilahi ya lalliahi.......😭
Juyawa ɗaya daga cikinsu ya yi ya dubi waƴan da suke akan dawakan.
"Da alama fa ruwa ya tafi da ita, ku muje kawai, domin ina da tabbacin ba zata taɓa rayuwa ba, ba'a taɓa wanda ya shiga cikin wannan ruwan ya fita da rai ba! Ko da kifiyar da muka harbeta da shi bai kasheta ba, mugayen dabbobin cikin ruwan nan za su hallakata!".
Ya yi maganar cike da nuna jarumta da izza, kalaman nasa akwai kaushi, kuma suna nuni da cewa ya jima a sadaukan yaki, domin kuwa babu tsoro ko ɗar ɗar a tattare da shi, ko ace da su bakiɗaya, babu wani shayi a maganarsa.
Ɗaya daga cikin waƴan da suke a kan dawakan ne ya girgiza kai yana faɗin
"No, ya zama dole mu nemota, mu fasa cikinta mu ciro abin da yake ciki mu koma da shi masarauta, idan dai muna son rayukanmu da lafiyarmu!!".
Kenan hakan yana nufin abin da yake cikin cikin nata suke da buƙata?.........🤔...... Kenan ba niyar kashe abin da yake cikin nata suka yi ba? To in dai haka ne meyasa zata gudun masu? Meyasa ba zata tsaya ta haifa ta basu ba tun da ba kashewa zasu yi ba? Su meyasa suke son karɓar babyn dake a cikin natan? Me zasu yi da shi? Waye ne ma mamallakin cikin nata? Ma'ana uban cikin?. Tab akwai cakwakiya ba kaɗan na. PRINCESS TEEMA ce taku ta amana🤍
Da alama wanda ya yi magana yanzu shi ne babbansu, dan tun da ya fara magana suka wani sunkiyar da kai, suka kara nutsuwa tamkar masu karɓar umarni.
Jinjina kai suka yi suna mai nuna alamar sun ji maganarsa sun kuma gamsu. A tare dukkansu suka diro ƙasa daga saman dawakan nasu, ji kake yi dip, dip, dirowar manya.
Fara kewaye wajen suka yi, dan su ga ko zasu yi nasarar samun wata makama, dukkansu basu da wani burin da ya wuce ace sun ga wannan matar, kowannansu burinsa ace shi ne ya yi nasarar ganinta ya kuma ciro babyn dake cikin cikin nata ya mayar da shi masarauta, da alama ba karamar kyauta aka sakawa duk wanda ya kawo babyn dake a cikin wannan matar ba, saboda yadda suka zage da iya karfinsu tare da kwarin gwiwa suna aikin nemanta.
Amma duk da hakan kuma sun kasa yin gigin yunkurin shiga cikin ruwan, dan sun san zurfin ruwan nan ya wuci tunanin mai tunani.
Sun jima suna kewaye a wajen, amma babu komai a cikin ruwan sai manya da kananun jiragen ruwa dake shawagi a can nesa da in da suke, ta tsakiyar ruwan.
Daga karshe dai suka hakura ba dan sun so ba, suka haye saman dawakansu, suka kutsa ta cikin wasu dogayen bishiyoyi dake a wajen, suka tafi.
*TO FAH, FARKO KENAN DAGA CIKIN LITTAFIN RAWANIN ZALINCIN, KU DAI KASANCE DA ALKALAMIN PRINCESS TEEMA DAN JIN YANDA ZATA KASANCE, KUN DAI JI TA YADDA LABARIN NAMU YA SOMA, NA SAN ZAKU SO JIN AINAHIN KAN LABARI, WACECE WANNAN MATA? MEYASA SUKA KASHETA? SU WAYE SU? MEYASA SUKE SON ABIN DA YAKE A CIKIN CIKINTA? ME ZASU YI DA SHI? ITA MEYASA TA ZAƁI MUTUWA A KAN TA BADA ABIN DA YAKE A CIKIN CIKIN NATA? SHIKENAN YANZU RUWA YA TAFI DA ITA? TA MUTU DA GASKE? GA KIFIYA A CIKINTA SUN HARBETA DA SHI? GA SHI TANA NAKUDA BAIWAR ALLAH. TO DAI MU KASANCE A TARE DAN WARWARE WANNAN SARKAKIYA A TARE, KADA FA KU YI WANI TUNANI TUKUN NAN,🥱 MASU YI MUN PREDICTION ME ZAI FARU A GABA NA LITATTAFINA SAY HII😂 KAMAR YANDA TRIPLETS YA RIKITA MAKU TUNANI, KUKA KASA HASASHEN GABA, TO WANNAN KO FARA HASASHENSA BA ZAKU YI BA, DAN KUWA SALONSA DABAN NE!🔥 AKWAI RIKITA KWAKWALE, MU JE DAI ZUWA, NAYI GABA SAI KUN ZO!!.*
*PRINCESS FATEEMAH, PRINCESS TEEMA DUKKA SUNANA NE, DAN NAJI WASU SUNA TAMBAYA💫❤️*
To!! To!! To!! Ina masoyana? kai harma da makiyana, ina kuke? Ina masoyan littafin TRIPLETS? Ina masoyan Noorish and Meesha? Ina masoyan babyn baby and his baby? Ina masoyan Heartbeat and Heartbeat? Ina masoyan Sudais and Anaya? Ina masoyan Uncle T and Aafia? Ina masoyan sir Arvin and Maryam?, Ina masoyan Alex and Adiva?, ina masoyan Imran and jelly, Akila and Umaisha, Irfan and Pinky, masoyan Hjy gwaggo mai zamani, duk dai Ku matso da sauri, dan a yau PRINCESS TEEMA ta sake dawo maku da wata zazzafar littafin mai tashin kai, shi wannan ba zazzafa bane ba, tafasa yake yi yana bada tiriri, salonsa daban ne, ina mai tabbatar maku salonsa daban ne, ku my peoples kun sani already ba sai na sake faɗa ba, PRINCESS TEEMA taku mai abin ban mamaki ce, kun san zaku sha mamaki a wannan karon ma, kun san idan nace salonsa daban ne, to fa daban ɗin ne, trust me ya sha banban da sauran labaran da kuka sani, dan fa a shiryena na taho In Sha Allah,🤍 zan tashi kanku in sanya maku hayakin kwakwalwa my peoples, yanzu dai ba QUADRUPLE bane fa😂 kada ku yi mani irin ruɗewar da kuka yi a TRIPLET'S🥺 wannan ina kara gaya maku yasha banban da kowani irin littafi, dan haka kada ki yarda ki bari a baki labari, da a baki ai gara ki bayar, gani ya kori ji, dan haka ki hanzarta maza ki kasance a cikin tafiyata, dan ki gani ba ki ji labari ba👌 ina kara jaddada maku wlh ba zaku taɓa yin danasanin bibiyar wannan littafi mai suna RAWANIN ZALINCI ba In Sha Allah, tabbas zaku yi alfahari da ni fiye da tunaninku, kun sani Alkalamin PRINCESS TEEMA alkalamina mai ilmantarwa, fadakarwa, wa'azantarwa, tare da nishaɗantarwa ne, na san kun san da hakan, dan kune ma kuka shaideni da hakan, bani na faɗa da bakina ba, shaidarku ce wannan, kun shaidani bana rubuta shirme da abubuwan banza a labarina, bana rubuta abin da hankali ba zai ɗauka ba! Bana rubutu kamar tatsuniya! Ina rubutu ne kamar gaske, abin da yake kewaye damu!! Kada dai na cikaku da surutu, mu haɗe daku a cikin littafin RAWANIN ZALINCI page 2 kawai.🔥🌹 Ku daga jin sunan RAWANIN ZALINCI kun san da akwai abubuwa ba kaɗan ba wadda baki ya yi kaɗan ya kwatantasu.
*Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.*
Baƴan lokaci mai tsawo da tafiyar waƴan nan jiga jigan worries ɗin, har lokacin ruwan sama na cigaba da zuba tamkar da bakin kwarya, ga garin sai kara wani uban duhu na hadari yake yi, tamkar yanzu za'a fara ruwan ma, wani irin walkiya mai matuƙar haske ne yake ta famar walwali a sararin samaniyar, ga wani irin uban rugugin tsawa mai sanya hanjin cikin duk wata halitta razana, sai ka rantse da Allah tsawar nan zata faɗo kasa ne.
Da kaɗan da kaɗan haki da nishi yake tasowa daga ɗan nesa da bakin wannan teku, da sauri da sauri nishin yake fita tamkar idan mutun ya rike numfashinsa na ɗan lokacin daga baya ya saki, to a wannan lokaci numfashin zata fita da sauri sauri kuma da karfi karfi, dan hanya da ta samu, haka wannan numfashi da hakin yake tashi!.
Kara yawaita wannan numfashin yake yi, daga can nesa da wannan tekun.
Wasu ramuka ne masu ɗan zurfi kamar rijiya a ɗan nesa da bakin ruwan, mafiya yawan manyan dajuka irin hakan ana samun irin waɗan nan ramuka sosai, wasu ramukan zaka tarar irin bishiyoyi masu fitowa a kwancen nan suna rufe kofar shigarsu, wasu kuma ganyayyaki da dogayen ciyayine ke cika rakukan, bare yanzu da ya kasance gari na damuna, akwai yelwar ganyayyaki koraye shar a ko'ina a dajin, hakan yasa baka iya ganin wasu ramuka ma sosai.
Kwance take a cikin wani katafaren rami mai kama da rijiya, ramin yana da ɗan zurfi kuma yana da faɗi, haka zalika akwai yelwar dogayen ciyayi a cike a ciki wanda suka rufe har baki, muddin mutun yana ciki ba zaka iya ganin shi ba har sai idan shi ya yaye waɗan nan ganyayyaki ya leko kansa waje, sannan ne zaka gan shi.
Abin da ya faru shi ne, a lokacin da ta faɗa kasan dutsen ne iska ya kwasheta zuwa cikin ramin, dama kunsan idan kazo faɗawa waje irin wannan akwai igiyar iska mai karfi tamkar ta ruwa da take fisgar mutun, bugu da kari ga iskar ruwan sama mai karfin gaske, Allah ya taimaketa ya kuma ceceta ta yi sa'a a in da ta faɗa cikin ciyayin ba tare da ta ji ciwo ba, ta kuma faɗa ta baya baya ne ba ta gaba ba, Allah ya kare mata cikin nata, ikon Allah kuma bata ji wani jiri ko wani abu makamancin shi ba, sai dai suma da ta yi saboda razana na irin tsayin wajen da ta faɗo ɗin, dama kunsan irin wannan akwai razana zuciya.
(Sai dai ni Princess Teema ban yarda da cewa ita ta shiga cikin ramin nan ko iska ya kai ta ba, dan dole akwai ayar tambaya, amma dai bari mu cigaba da bibiyarta mu gani!)
Bayan faɗawarta da ɗan tsawon lokaci ne ta farfaɗo daga sumar da ta yi saboda ruwan sama dake zuba yana taɓata, har a lokacin babu alamar hawaye a idanunta ko kaɗan, idanunta suna bushe, da alama ta saba da wahala sosai, zuciyarta ta bushe sosai, dan duk wannan abin da ya faru bata sare ba, bata karaya ba, muradin cigaba da rayuwa ne ziryan a cikin kwayar idanunta, da alama jaruma ce ta gasken gaske! Dan kuwa ko da ta faɗa cikin ramin babu alama na wahala ko nuna gajiya a tattare da ita, tana da taurin zuciya da taurin rai, da alama an gwabza abubuwa da ita ba kaɗan ba, an kara da ita ba kaɗan ba a baya, ga dukkan alamu ba karamar yaki aka buga da ita ba kafin a iya kaita ƙasa ko in ce a iya samun nasarar jefata cikin wannan hali da take a ciki!.
Jini ne yake zuba sosai daga cikin nata, sai dai da ikon Allah ta iya cire kifiyar da suka harbeta da shi, kuma ta yi sa'a kifiyar bata soketa sosai ba, da alama wanda ya harbeta da kifiyar duk yadda aka yi akwai wani abin a ƙasa tsakaninta da shi, domin kuwa bai harbeta a in da zata raunata sosai ba, bai harbeta a in da zata mutu ko kifiyar ta yi mata illah ba, kuma da alama kwararren maharbine, yasan kwari da baka sosai, yana da saiti, domin kuwa yadda ya harbeta a gefe guda babu saɓa saiti ko kwana kwana, alamu sun nuna yana sane ya kaucewa harbinta a in da zata iya mutuwa ko ta cutu, wata kila da wata manufa ya aikata hakan, amma lokaci ne zai nuna mana komai.
Tattare iya karfinta ta yi tare da miƙewa zaune ta cire alkhabbar jikinta, sai haki take yi sosai, dan a lokaci da ta farfaɗo ta fahimci waɗan nan azzaluman mayakan sun nufo in da take suna nemanta, hakan ne yasa ta rike numfashinta ta hanyar toshe hanci da bakinta da gefen alkyabbar tata, shi ne yasa yanzu take numfashi sama sama, dan sai da ta ji motsin barinsu wajen, sannan ta saki numfashinta, kunga kuwa dole ta yi haki sosai, dan rike numfashi ba wasa ba.
Da kyar ta iya zare alkyabbar daga jikinta, a in da ta ɗaure gefen cikin nata da yake zubar da jini da shi, sai buɗe baki take yi alamar kishin ruwa kamar zata mutu. Idan ya jima ya jima sai ta ɗaga kanta sama tare da buɗe baki tana tarar ruwan sama dan ta samu ruwan ya shiga bakinta ta ɗan sha, so abin ku da ruwa idan ba'a indararo yake ba, sam baya zuba sosai duk karfin gudun ruwan sama, amma Alhadulillah ta ɗan sha sosai har ta ji duniya ya ɗan saki mata ta dawo cikin hayyacinta.
Ƙoƙarin miƙewa ta yi dan ta fita daga cikin ramin, lokacin ta ji ta ɗan sami sauki bayan wasu mintuna kenan, amma ina ta kasa miƙewa, koda kuwa ta miƙe ba zata iya fita daga cikin ramin ba, saboda yafi