x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 53 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 156001 words
  • 159000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 374

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
dai menene lokaci zai nuna mana...... Mu dai bari mu leƙa FOREST mu dawo, wata kila kafin nan hankalin Leesharh mu ya ɗan kwanta, baiwar Allah marainiyar Allah duk da bamu san asalinta ba.

🏞️FOREST🏞️

Tafiya Kamran yake yi cikin jarumta, amma kuma zuciyarsa na raya mashi kada ya je wajen su Pretty, haka nawai ya tsinci kansa da zargin cewa Mammarsa ta biyo bayansa. Kawar da wannan zargin ya yi daga zuciyarsa, dan yana ganin kamar karya ce kawai, ba dai'dai bane, Mamma ba zata biyo bayansa ba.

Ƙara tsanan ta mashi zargin hakan zuciyarsa ta yi, lokaci guda ya ji jikinsa ya mutu da tunkarar wajen na su Pretty, da yake yana da kaifin ƙwaƙwalwa ya kuma san wacece Mamma, sai ya fara tunanin irin tattaunawar da suka yi da ita jiya da kuma yadda aka yi yau daga ce mata bari ya je cikin daji babu musu ba komai ta amince, ita da wani lokaci sai sun kai ruwa rana take aminta ta barshi ya fita, amma yau kai tsaye ba wata kwana kwana or ƙunbiya ƙunbiya ta ce ya je kawai? Dole akwai abin da take shiryawa.

Tuna hakan ne yasa ya canza hanya daga kan hanyarsa na zuwa wajen su Pretty izuwa wata hanya ta daban. Yana tafiya yana kasa kunne yadda ko zai jiyo motsin Mamma a bayansa. Amma shiru bai jiyo ba, kuma yaki yarda ya juya baya dan kada idan ta biyo shi ma ta gane ya fahimci tana binsa, hakan yasa ya samu waje a ƙarƙashin wata itaciyar ɓaure ya zauna tare da ɗan jinjina da jikin itaciyar.

Laɓewa Mamma ta yi a can nesa da shi in da take iya hangosa daga wajen, ta laɓe tana kallonsa yadda ya jingina da jikin itaciyar tare da lumshe idanu. Shiru ta ɗan yi tana tunanin dama nan wajen yake zama kenan?....... Wannan shi ne ɗan na gada ya fi ɗan na koya, yau Kamran ya yi wa Mamma wayo duk kaifin ƙwaƙwalwar tan nan, tab akwai cakwakiya kuwa duk ranar da ta kama shi tsamo tsamo a wajen su Pretty, ina ga daga ranar rabasu zata yi, kuma da wuya idan bata koresu daga cikin Forest ɗin ba, dan ita fa bata da ɗigon tausayi a ranta.

Almost 20 mins suna a haka, daga karshe dai tsabar basaja da iya waskiya na Kamran harda kwanciya, ya karkata ya gyara ya kwanta a wajen, domin tun zamansa a wajen ya hango Mammar tasa a can bayan itaciyar da ta laɓe, yaga kayan jikinta, amma bai ga face ɗinta ba, shi ne har da kwanciya dan ya tabbatar mata da shi babu in da yake zuwa.

Sanɗo Mammar ta fara yi tana son ta lallaɓa ta koma wajen kogonsu tun da taga babu in da yake zuwa. Tana sanɗo yana kallonta da mamaki, tunani ɗaya kawai yake yi yadda aka yi wannan tunani na tana bin bayansa ya faɗo mashi a cikin ransa, kullun yana zuwa wajen su Pretty, amma bai taɓa jin irin wannan zargin a ransa ba sai yau, ga shi shi bai san Allah ba bare ya ce Alhdulillah, sai dai kawai ya miƙe cikin sanɗo ya fara lallaɓawa zai je ya leƙa ko Mammar ta yi nisa.

A hankali yake tafiya har izuwa bayan wata itaciyar mangoro ya laɓe, yana ganin Mammar tasa har sai da ta kurewa ganinsa, sannan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da juyawa da sauri ya bar wannan yankin.

Kai tsaye wajen su Pretty ya nufa abinsa, sai dai yana tafiya yana fargabar kada ace ita ma Mamma wayo ta yi mashi ta yi kamar ta koma alhalin bata koma ba, ta bari ne taga ko zai je wani waje. Yana tafiya zuciyarsa na harbawa cike da tsoro.

Ko da ya isa wajen su Pretty ɗin ma sai da ya jima a tsaye a waje kafin cikin sauri kuma cikin dabara ya buɗe ramin nasu ya afka ciki a hanzarce.

Zaune ya isko Pretty a saman dutse ta buga uban tagumi, ita kuma Sweetie tana kwance a saman bed. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da idanuwansa suka sauka a kansu, Allah ya gani yana kaunar yaran nan sosai da sosai, jinsu yake yi har cikin ransa.

Ya ɗan ji wani irin ba daɗi a ransa na ganin Pretty zaune ta buga uban tagumi saɓanin yadda ya saba samunta a kullum cikin nishaɗi da annasuwa.

Jin motsin mutun yasa Pretty ɗago da waɗan nan idanun nata ta bi hanyar shigowa da kallo, ganin cewa shi ne yasa ta miƙe a hanzarce, kana ganin face nata kasan a matuƙar tsorace take. Da sauri ta nufe shi tun kafin ya ƙariso, tana zuwa kuma ta faɗa jikinsa tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Miƙewa zaune ita ma Sweetie ta yi, baiwar Allah da yake bata gani sai ta fara cewa. "Pretty meyasa kike sake yin kuka kuma? Ko dai mutanen ne suka biyoki har cikin nan mun shiga uku?". A ruɗe ta yi maganar, daga jin muryarta kasan ta sha kuka ta ƙoshi.

Sosai Kamran ya ruɗe tare da shiga tashin hankali na ganin Pretty tana kuka ita kuma Sweetie daga jin voice ɗinta kasan ta sha kukan ne har ta ƙoshi.

"Pretty what happened? Why are you crying? Please stop this crying and tell me what happened". Ya yi maganar cikin tsananin damuwa, dan a yanzu ya fi shiga damuwa idan aka taɓasu sama da idan aka taɓa shi, ya fi shiga ɓacin rai idan su suna cikin ɓacin rai sama da ace idan shi ne ransa ya ɓaci.

Jin zazzaƙar voice ɗinsa yasa Sweetie sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da lumshe idanuta kamar wadda aka jefa a cikin ruwan sanyi a sahara mai tsananin zafi.

"Pretty talk to me now?". Ya yi maganar a hankali sosai.

Cikin kuka ta amsa mashi da cewa. "Ba waɗan nan mutanen da ka yi faɗa da su ranar bane na je ɗebo mana ruwa a ƙoramar nan suka kamani".

Zaro idanu waje ya yi, a hanzarce ya ce mata. "To da suka kamaki sai me ya faru? Ya aka yi kika kuɓuta daga hannunsu har kika dawo nan?". A ruɗe ya yi maganar.

"Wannan mutumi mai rufe fuskar ne wanda ya taimakemimu ranar ne ya zo ya kashesu dukka, sai ya ce mun na gudu na tafi, na gudu shi kuma ya fara faɗa da su".

"Ina mutu min yake?". Ya tambayeta cikin ƙaguwa.

"Nima ban kara ganinsa ba ai, daga ya ce in gudu shikenan na gudu na dawo, ban san ya suka kare ba".

Sarkin tsoro ta tsorata ne sosai, dan a wannan karon kamata suka yi zasu tafi da ita, ta je ɗebo masu ruwa, su kuma mayakan sun je wajen domin dawakansu su sha ruwa suma, shi ne suka ganta, sai suka kamata, wannan mutu da ya taimaka masu ranar ne yau ma ya zo ya taimaketa ya kuma ce ta gudu, shi ne ta gudo ta dawo. Toh fah! Ko waye wannan mutumi? Wannan sai alƙalamina ne kawai zai warware maku wannan cakwakiya, kedai kada ki bari a baki labari, yanzu labari zai fara ɗaukar zafi.

Rarrashinta Kamran ɗin ya fara yi yana ɗan bubbuga bayanta a hankali a kan ta yi shiru to tun da ta samu ta tsira. Sarkin son jiki, kara kwanciya mashi a jikinsa ta yi tana tunanin yadda waɗan nan mayakan suka damko gashin kanta, da yake tana nan ƴar piritu ba nauyi sai suka ɗagata da gashin kai saboda rashin imani, yau ta ga bone ai ƴar kaniya, shi ne yasa ta tsorata sosai.

Da kyar Kamran ya samu ta yi shiru, sai dai bata tashi daga jikin nasa ba, ta cigaba da kwanciyarta a saman kirjinsa tana mai da numfashi. Daga Kamran har su Prettyn dukkansu fa babu wanda yake tunanin yana da uba a cikinsu, dan dukkansu uwa kawai suka buɗe idanu suka kallah, basu san da ma cewa sai mutun biyu bane suke haifan ƴaƴa, su dai kawai iyayensu mata suka sani, basu san me aure ba, kuma basu ma san a cikin ciki mahaifiya yaro yake rayuwa har izuwa wata tara a haifesa ba, duk basu san wannan ba, saboda idan kuka yi duba da yanayin yadda suke dukkansu basu da kanne bare ace sun san lokacin da mahaifiyarsu take da cikin kannen nasu, duk basu san wannan ba, gara ma shi Kamran ya yi karatu wajen Mamma, amma fa ba ta wannan fannin ya karanta ba, ya dai san abin da ya sani, kuma ya taɓa kallon wani maharbi yana wucewa rike da ƙaramin yaro a hannunsa, a nan ne ma ya fara sanin ashe akwai kananan yara a duniya, shi da duk a tunaninsa kowa da girmansa kamar yadda ya yi wayo ya gansa da girmansa a tunaninsa kowa a haka yake zuwa duniya......... Da kuwa an shiga uku😅

Su Pretty sune mutane na uku da ya taɓa gani suna kanana a rayuwarsa, su kuwa su Prettyn basu taɓa ganin kananan yara ba, shi kawai suka sani sai mum ɗinsu, sai kuma yanzu da suke ganin waɗan nan warriors ɗin time to time, shiyasa kuka ga dukkansu suke a haka, basu taɓa yin tunani ina iyayensu maza ba? Ba su taɓa yin wani tunani makamancin hakan ba........ E lallai akwai cakwakiya kuwa, ko waye zai koyar dasu sanin hakan?.....🤔

Sweetie da take a saman gado ne ta ce. "Kamran sannu da zuwa".

Sai a lokacin ya kai kallonsa a kanta, amsa mata da yauwa ya yi kafin ya ɗaura da cewa. "Pretty sakeni bari na je na duba wannan mutumi a wajen ƙoramar ko? Ko zaki rakani?".

A hanzarce ta fara girgiza mashi kai alamar ita ba zata je ba. Hannu ya kai ya ɗan shafa lallausan gashin kanta da yake bakin kirin ta ɗaure shi kashi biyu gwanin birgewa kafin ya ce. "To bari na je na dawo, na kawo maki wani kyauta, ki jirani ko?".

Gyaɗa mashi kai kawai ta yi ba tare da ta amsa ba.

Raba jikinsu ya yi tare da juyawa a hanzarce ya nufi waje, ita kuma ta yi maza ta koma saman gado tare da kwanciya ta tada kai da cinyar Sweetie tana goge hawayen nata.

Kai tsaye wajen ƙoramar Kamran ɗin ya nufa ba tare da tsoro ko shakkar komai ba, cike da jarumta tare da fata da kuma yakinin son ganin wannan mutumi ya nufi wajen. Yana ƙarisawa wajen ya wani ja uban birki babu shiri, a razane ya zaro fararen idanuwan nan nasa waje kamar zasu faɗi ƙasa........

Bamu fara komai ba, dan har yanzu ba mu kai ga nemo RAWANIN ZALINCI ba tukun nan, yanzu labarinmu zai fara, ga Leesharh ta baro gidan AAJ babu shiri, ya Jasrah zata ji a ranta idan ta ji shiru Leesharh bata dawo ba? Shikenan sun rabu kenan? Wani irin rabuwa ne wannan mai tsananin ciwo haka? Leesharh dai zata yi aikin dole domin ta ceci rayuwar mahaifinta, ya kuke tunanin zata gudanar da wannan aiki? Shin asirinta zai tonu a kamata ne ko zata yi nasarar kammala aikin? Idan ta kammala waɗan nan unknown mutanen zasu cika mata alkawarin da suka ɗauka mata na sakar mata babanta da kuma maƙudan dukiyar su kuma mai da ita ƙasarsu?.

WAJEN SU KAMRAN. Ya kenan idan Mamma fifikon wayo ta nunawa Kamran ta yi kamar ta koma alhalin bata koma ba? Ya makomar su Pretty, su waye su? Ina ne usulinsu? Ina mum ɗinsu? Suna da uba ko babu? Meyasa ake farautar rayuwarsu kamar yadda ake kafautar ruwan sanyi a sahara mai tsananin zafi?.

KINGDOM OF POWER meyasa Momma take fuskantar barazana a cikin masarautar?. Meyasa Mammien Yah Jawad bata son shi a tare da Gimbiya Chuchu? Meyasa da Mamma da Mammie ɗin dukka suke kamar ƴan leƙen asiri a cikin kingdom ɗin? Ya makomar su Yusuf? Me su twin's Obaid and Omaid zasu ƙullawa Mama?.

GIDAN SU KHADIJA. ya makomar rayuwarsu a yanzu? Maman Zainab ya tabbata ta je wajen boka? Shin idan ma ta je zai sa a fasa auren baban Zainab da kuma Haidar and Khadijah? Zai sa su maman Haidar ɗin su fara sonta ne?. Kai akwai tarin tambayoyi amma bari na barku da iya waɗan nan ku farata caza brain naku zuwa gobe idan Allah ya kai mu mu ji me ake ciki.


🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍



🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)






🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 6/8/2024.....✍️📚🌹




For information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️








E____________29🔥





🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️


🏞️FOREST🏞️



Kai tsaye wajen ƙoramar Kamran ɗin ya nufa ba tare da tsoro ko shakkar komai ba, cike da jarumta tare da fata da kuma yakinin son ganin wannan mutumi ya nufi wajen. Yana ƙarisawa wajen ya wani ja uban birki babu shiri, a razane ya zaro fararen idanuwan nan nasa waje kamar zasu faɗi ƙasa.

Fara bin gawarwakin warriors ɗin da idanunsa ya yi, mamaki ne sosai ya kama shi na yadda ya ga gawarwakin nasu, babu wata gawa da zaka iya kallah da mutuncinta, kisan walaƙancin wannan mutumi ya yi masu, da alama fa wannan mutumi an sha fama da shi a fagen yaki, da alama ya sha gwagwarmayar rayuwa, domin daga ganin yadda yake farautar mayaƙannan yake kashesu kisa mafi muni ba makawa shahararren jarumi ne na kin karawa.

A hanzarce Kamran ya fara juyawa gabas da yamma kugu da arewa yana dube dube ko Allah zai sanya ya ga wannan mutumi.

Amma ina babu shi babu alamarsa. Mutum kamar aljani, nan take yake iya yaƙan mayaƙa komai yawansu, zai tarwatsasu kuma ya yi tafiyarsa abinsa, sai ka rasa ina ya shiga? Ko alamarsa baka sake gani. Abin akwai ɗaure kai, anyama mutun ne ma kuwa? Na fara tantanma!.

Kamran ya jima tsaye a wajen yana ta jimamin abin, kafin daga bisani kuma ya hango robar da Pretty ta zo ɗeban ruwa da shi ɗazun. Ɗauko robar ya yi tare da ƙarisawa wajen da ruwan ƙoramar yake zubowa daga saman dutsen, a nan ya ɗeba masu ruwa mai haske, sannan ya juya ya nufi cikin ramin nasu, zuciyarsa a cike tab da tunanin wanenen wannan Jarumin sadaukin? Su waye waɗan nan warriors ɗin? Meyasa ake ta kashesu kuma basu gajiya da sake shigowa dajin? Wanda yake turosu kuwa anya yana da imani? Duk wanda ka turo cikin dajin basa komawa, amma a haka kullum yake cikin turo wasu dan su nemo mashi kananan yaran da su kansu basu san kansu ba? Abin da ɗaure kai sosai gaskiya.

Cikin ramin ya koma gabaɗaya jikinsa a mace, tunanin canzawa su Pretty maɓoya kawai yake yi, sai dai shi kaɗai ba zai iya ba, ba zai iya irin wannan gini da Mammarsa ta yi a cikin ƙogonsu ba, suma su Pretty wannan gini da yake ramin nasu dakakkun jaruman maza suka yi shi, ba mum ɗinsu bace ta yi shi, dan wane ita, bata isa ta yi shi ba, dole maza madaka katti ne suka yi shi, dan ba ƙaramin aiki bane, ba aikin yara bane ba. Shi ma zai iya yi, amma za'a ɗauki tsawon lokaci yana yin wannan aiki, kuma ba lallai aikin ya kai ko rabin na mammarsa da ta yi ƙargo ba.

Sai tunanin mafita na ya zai yi yake yi har ya ƙarisa wajensu, a gefe ya ajiye masu ruwan tare da zama a saman dutsen da ya saba zaba.

Tun da ya shigo Pretty ta tsare shi da waɗan nan idanun nata masu rikitar da shi. Da yake shi ma hankalinsa baya a jikinsa sai ya tsareta a ido a zahiri, amma a baɗini ba ita yake kallah ba, hasalima bai san in da yake kallah ba, ya luluƙa duniyar tunani.

"Kamran ka kalli wani abin maras kyau ne a wajen?". Cewar Pretty sarkin ba'a gani ayi shiru. Ta kalli face ɗinsa ya sauya daga yadda ya bar cikin ramin ne, ya fita da annuri a saman fuskarsa, ya dawo cikin tunani da jimamin al'amarin, hakan yasa yanayin face ɗinsa ta sauya gabaɗaya.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, jin muryarta yasa ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka. "No I didn't see anything, kawai am thinking ta yadda zan yi na sauya maku waje ne".

A hanzarce Prettyn ta miƙe daga kwanciyar da take tare da cewa. "Do you see the man?".

Girgiza mata kai ya yi alamar a'a bai gansa ba.

Shiru ta ɗan yi kafin ta miƙe ta diro ƙasa daga saman gadon, wajen wani ma'ajiya da aka gina da taɓo ta nufa. Da kallo Kamran ya bita kawai.

Ita kuwa Sweetie ta jingina da jikin bangon dutsen baiwar Allah, bata iya ganin komai, sai dai shiru kawai take yi tana sauraron maganganunsu a kullum, abin gwanin ban tausayi, rashin idanu babban cuta ce. Allah Alhdulillah da ka bamu ji da kuma gani haɗe da lafiya, kafafu da kuma hannaye.

Ƴan dube dube ta fara yi a wajen kamar mai neman wani abin. "What are you looking for?". Kamran ya jefa mata wannan tambayar.

Ba tare da ta kalli in da yake ba ta amsa mashi da. "Am looking for my mum pen and book, I want to draw something, ina ganin zan iya zana face ɗin mutumin nan, with his eyes like mine".

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Waye ya koya maki rubutu ma bare kuma zane Pretty?".

Sai a lokacin ta juyo da kallonta a kansa, dan bama ta ga abin da take nema ba. "Mum ɗin mu mana,
End Ads