x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - RAWANIN ZALINCI STEP 1

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 297772 words

Category: Love Stories

Views 431

10 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
hankalinta baya a kan Tv, sai tunanin islamiya take yi, dan an kara masu karatu yau, kuma da daddare ne kawai take samun damar yin karatun, da safe zasu tafi makarantar boko, ba zasu dawo ba sai karfe uku, idan suka dawo kafin su ci abinci su yi wanka haɗe da shirin islamiyar, karfe huɗu ta yi, dole islamiyar zasu wuce a dai'dai wannan lokacin, so babu time, yanzu haka Khadijah tana primary 2 a makarantar boko, ita kuma Zainab primary one zata shiga yanzu, suna da ƙoƙari sosai, saboda kula da suke samu daga wajen iyayensu, babansu ba wai ɗan kasuwa bane kawai, degree gare shi a fannin electric engr, kuma ya fito ne da first class, kawai yanayin kasar ce tasa ya zama ɗan kasuwa mai sayar da atamfofi, lace, shadda, da dai sauransu, babu aikin yi, ya gama karatu bai sami aiki ba, shi ne ya zaɓi ya fara kasuwancinsa kawai, ya tattara result na makarantar ya ajiye a gefe guda.

Mammansu kuwa ta gama secondary school nata, tana da ilimi dai'dai gwargwado, sannan macece mai ilimin addini, ga saukin kai da tausayi tare da fawwalawa Allah komai nata, so a takaice dukkansu daga maman har baban duk ba jahilai bane ba, suna da ilimi, shi ne yasa suke kula da karatun su Khadijah sosai da sosai.

Sai misalin ƙarfe 9:30 su Khadijah suka miƙe suna yi wa iyayen nasu sai da safe, dama already sun rigada sun sani, karfe 9:30 suke shiga su kwanta, saboda tashi zuwa makaranta, tun suna yara mamansu ta tsara masu tsari mai kyau na rayuwa, wani abin ba sai ance su yi ba, sun riga da sun saba yi.

"Mamana kada ku manta ku yi addu'ar kwanciya, nima zanzo in yi maku nawa idan zamu shiga". Cewar babansu.

Da to suka amsa mashi tare da wucewa cikin ɗakin nasu. Wata riga da wando mai laushi sosai Khadija ta ɗauko masu daga cikin drawer saka kayansu, iri ɗaya ne kayan launin navy blue.

Miƙawa Zainab nata ta yi, karɓa ta yi suka hau canza kayan ba ɓata lokaci, kayan barcinsu ne.

Bayan sun canza Zainab ta haye saman gado, ita kuma Khadijah ta ɗauko takardun islamiyarsu tare da ɗauko littafinta na Nahhu ta buɗe shafin filul mahdi dan ta kara duba karin karatun da aka yi masu.

Ta ɗauki a kallah minti goma tana ta karanta wannan filul mahdi'n kafin ta rufe takardar ta mayar cikin jaka, sannan ta mayar da jakar mazauninta, a lokacin har Zainab ta fara zuba barcinta abinta.

Zama ta yi a tsakiyar gadon ta fara karanta kulhuwallahu kafa uku, falaki da nasi suma kafa uku uku, sai ayatul kursiyu kafa ɗaya, sannan amanar rasulu shi ma kafa ɗaya, ta tofa a hannunta kafin ta shafa a jikinta gabaɗaya, ta juya ta shafawa Zainab ma, kamar wata babban mace, bayan ta shafa mata ne ta jawo masu bargo, dan garin akwai sanyi sosai, gari ne na damina, Khadijah tana tsananin son Zainab over to over wlh, ita kaɗai ce ke gareta.

Su kuma iyayen nasu, sai da suka kai har karfe 11 suna kallo, sai da suka ƙarisa kallon wannan film ɗin, shi ma Haidar saboda tsabar gulma yaki wucewa ɗakinsu, yana nan a tare suka ƙarisa kallon, sannan ya miƙe ya nufi ɗakin nasu yana yi masu sai da safe.

Mamance kawai ta amsa, baba bai amsa ba, dan shi har ga Allah baya son wannan hali na Haidar, kawai ba yadda zai yi ne, ya yi iyaka bakin ƙoƙarinsa a kan yaron nan ya canza hali, ya koma makaranta lokaci bata kure mashi ba, amma sam yaki yarda, ya zauna sai shirmen banza da wofi yake yi, yana mayar da kansa irin local matan nan masu shegen tsugudidi. Ga shi babu halin baban Zainab ɗin ya kore shi daga gidan, dama yaya lafiyar kura bare ace ta yi zawo? Yanzu ma ana cewa maman Zainab ta yi mashi asiri ta mallake shi, to ina ga kuma idan ya kori Haidar? Ai shikenan abu ya sake kwaɓewa, sai aje ayi ɓatattciya da dangi, zaman lafiyarsa kawai ya cigaba da bin Haidar ɗin da idanu har lokacin da zai girma hankalin manyantaka ta shigesa, wata kila a lokacin zai iya gane dai'dai da ba dai'dai ba.

Miƙewa baban Zainab ya yi ya je ya rufo masu kofar parlourn bayan tafiyar Haidar ɗin kenan, dama already ya rufe masu kofar gida kam tun tuni, suna dawowa daga sallar issha suke garƙame kofar gidansu, saboda tsaro, akwai gurɓatattun matasa ɓata gari a unguwar tasu sosai, shi ne yasa basu wasa da rufe kofar gida.

Kowannensu ɗakinsa daban, baban nasa daban, ita ma Maman nata daban, amma dayawa lokuta a ɗaki ɗaya suke kwana, inma na maman or na baban, a dai ɗaki ɗaya suke kwana, yau ma ɗakin baban suka wuce a tare bayan sun kashe kayan kallon nasu tare da wutar parlourn haɗe da tattare komai nasu, suka shiga wajensu Zainab suka yi masu addu'a, sannan ne suka nufi ɗakin barcinsu. A suba ta gari............

♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥♥︎♥︎♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥

🏞️Forest🏞️

Tun da Kamran ya yi wannn barci bai farka ba har washegari da safe, abin abin ban mamaki mai rikitarwa, ko da ya farka kuma ya jima sosai idanuwansa biyu ya kasa motsawa, jikinsa duk wani irin azabbabben ciwo yake yi mashi, duk ya ji wani irin tamkar ba shi ba, kamar wanda ya sha kayan maye overdose suka sanya shi barci, jin jikinsa yake yi tamkar ba shi ba, kamar an canza shi, da kyar ya iya samun dama ma ya waro idanuwansa waje, wani irin nauyi idanun nasa suka yi mashi, da farko ma ji ya yi tamkar an manne mashi su da super glue, sai da ya yi da gaske ne ya iya buɗesu.

A hankali hankali ya fara kallon wani irin jiri jiri tana ɗebarsa daga kwance, saman ɗakin nasa ne ya fara juya mashi kamar fanka.

To me ya sami Kamran ɗin mu?.

Dishi dishi idanuwansa suka fara ganin masa, like idan mutun yana ƙoƙarin sumewa, haka zai fara gani dishi dishi, yunƙurin miƙewa ya fara yi domin ya lura abin tana so ta fi karfinsa, sai dai ina, bai iya ko motsin kirki ba, tamkar an sanya igiya ne aka ɗaure shi ɗaurin goro, ƙoƙarin buɗe bakinsa ya yi domin ya kira Mamma, nan ma ina ya kasa, dan kuwa ji ya yi tamkar an ɗaure harshen nasa ne kam, ya kasa.

Sanya dukka ilahirin karfinsa ya yi da nufin ya miƙe da karfin gaske, duk da haka a banza man kare, ko motsawa bai iya yi ba, ya juyar da idanuwansa ya kalli gefe guda ma ya kasa, iya saman ɗakin nasa kawai yake iya kallah, duk wata jijiya a jikinsa sai da ta tsaya sak da aiki! Jinin jikinsa duk ya dai'na gudu, nan take idanuwansa suka kara firfitowa waje sosai tamkar zasu faɗi ƙasa, tamkar wadda aka matse sosai, sai ƙoƙarin ya yi magana yake yi, yana son ya kira Mamma ta kawo mashi agaji, amma ina ya kasa, harshensa ma a ɗaure take gam.

Dai'dai lokacin Mammar ta faɗo cikin ɗakin tana faɗin.

"Tun jiya barci yaki karewa kamar ba lafiya ba, maza ka tashi lokacin motsa jiki ya yi, ka kama ka tafi yawonka ba dole ka gaji ka yi ta barci ba, kafa baya zama waje ɗaya, baka bawa jikinka hakkinsa na hutawa!".

Jin motsin shigowar Mamma tana waɗan nan surutan ne yasa gabaɗaya ya ji jikin nasa ta sake, nan take ya ji ya koma normal kamar ba shi ba, abin da ɗaure kai da kuma mamaki.

Waro idanuwnsa da suke jajir saboda barci ya yi a kan Maman tasa dake tsaye a kusa da bed ɗin nasa tana faɗin ya tashi su tafi, ya zo sai wani zuba barci yake yi tun jiya da yamma, da daddare ta tashe shi har ta godewa Allah yaki ya tashi, har ruwa ta shafa mashi a fuska, amma yaki tashi, sai dai ya ɗan motsa kaɗan ya sake cigaba da barcin abinsa, da farko abin har ya fara bata tsoro, sai daga baya kuma ta kyale shi kawai ta je ta ci abincinta ta kwanta, to shi ne fa bai iya farkawa ba sai yanzu, e gaskiya kam abin da abin mamaki sosai Wlh, akwai kuma ɗaure kai!.

Kada ku manta daga cikin littafin RAWANIN ZALINCI wanda alkalamina ni PRINCESS TEEMA ya rubuta maku kuke karanta wannan daddaɗar labari mai cike da ruɗu da ɗaure kai, to yanzu muka fara, bamu ma fara kutsawa cikin labarin ba tukun nan, bamu ma yi komai ba, ku dai ku kasance dani, na tabbata In Sha Allah ba zaku taɓa yin danasanin karatan wannan littafin ba!.

Har yanzu lokacin harshensa ta yi mashi nauyi wajen magana, da kyar ya iya furta.

"Mamma ya naji kina cewa tun jiya nake barci sai yau na tashi? Kina nufin kwana ɗaya ta wuce kenan?".

"E mana Kamran, kwana ɗaya ta wuce, wai me kasha jiya ne? Ka je ka sha ƴaƴan wata itaciyar mai bugar da mutun ko? Ina ta tashinka daga barci kaki ka tashi" .

Zaro idanuwansa ya yi tare da furta what?! Da ɗan karfin, kwana ɗaya ta wuce kuma? Ya sake tambayar kansa.

Ganin haka yasa Maman ta ce. "Kamran anya are you okey kuwa? Menene kuma ya faru?".

Ɗago dara daran idanuwan nan nasa ya yi a in da ya sauke su a saman fuskarta, shiru ya ɗan yi kafin ya ce.

"Mamma yau ba zan motsa jiki ba, ina zuwa, bari na je nan baya yanzun nan na dawo, sai na zo na yi wanka......."

Wani irin kallo da ta wurga mashi da waɗan nan sexy eyes ɗin nata ne yasa bai san lokacin da ya haɗiye sauran maganar tasa bai ƙarisar ba.

"Wuce muje ka fara aikin motsa jiki, idan ka gama ka yi wanka ka ci abinci sai ka tafi in da zaka je, dama zaka je kawo mana nama ai, babu abin da zai hanaka yin training, wai shin ni ina ma ka je jiya da ka dawo mun kamar a buge ne?".

Da kyar ya iya miƙewa zaune yana turɓune fuska tare da ɓata rai. "Mamma ni ina kuma zanje da ya wuce in da muka saba ni da Rocky, wai Mamma please yau ki kyaleni da zancen motsa jikin nan mana".

Shiru ta yi mashi bata sake ce mashi ko uppan ba. Yasan fassarar shirunta, hakan yana nufin dole sai ya motsa jikin nan ko yana so ko baya so, ga kuma ciwo a yatsarsa.

Dole tasa ya miƙe jiki duk ciwo take mashi, gaɓɓansa duk suna yi mashi zafi, haka ya wuce gaba yana kara turɓu ne fuska.

Rufa mashi baya ta yi, a saman tsaunin ta bayan kogon nasu suka tsaya, ga wasu manya da kananan duwatsu a wajen, a nan suka tsaya ya fara aikin training da waɗan nan duwatsu, ita kuma Mamma ta wani tsaya kamar jarumar sadaukiyar yaki, yacce kuka san wata commender masu bawa mayaka horo, haka ta wani tsaya tana aikin kirga sau nawa ya ɗaga wata katuwar dutse.

Sai da ya ɗaga sau hamsin cif tana kirgawa, sannan ta ce ya fara press up, haka ya fara yi kamar zai yi kuka, yau duk jikinsa ciwo take yi mashi, ga shi Mamma ta zo tana kara mashi azaba a kan azaba, haka dai ba yadda ya iya, dole ne ya yi idan yana son zaman lafiya.

Da Mamma ta lura fa baya yi da sauri zai ɓata mata lokaci, sai ta koma cikin ƙogon nasu.

Tana tafiya ya yi zamansa yana tunanin maman twins, sai wani mai da numfashi yake yi da sauri da sauri, irin ya sha aiki ya ƙoshin nan.

A hanzarce ya tashi ya cigaba da yi jin alamar takun dawowar Mamma wajen, ba shiri ya ɗaura daga in da ya tsaya.

Kusa da shi ta zo ta tsugunna hannunta na rike da wata iriyar doguwar takobi na mayaƙa, sai dai takobin tana a cikin gidanta, bata fito da ita ba, da ƙotar gabaɗaya ta ɗauko. Ɗaga takobin ta yi ta fara kai mashi wajajen hannunsa, hakan yasa ya fara yi da sauri, dan idan ya bari takobin ta taɓa hannunsa zata ji mashi ciwo, dama ga ciwo a yatsar hannunsa tana yi mashi zogi, dan ma dai da diddigen tafin hannu ya dafa ƙasan ne, bai isa ya tsunsa sun taɓa kasa ba, saboda ciwon yatsar nan.

Mamma ta wata fuska idan ka gani sai kaga kamar bata son ɗan nata, amma kuma ita ce ainahin mai sonsa da gaske, yanzu duk in da ya shiga zai iya kare kansa ba sai ya jira wani ya zo ya kare shi ba, sai dai ni PRINCESS TEEMA ina ganin akwai wani dalilin da yasa Mamma ta zaɓi Kamran ya zama jarumi sosai har take bashi irin horo haka mai haɗari, hannunsa yana ciwo ma ba zata kyale shi ba, sai ta sanya shi yin wannan abin, haba mana Mamma..........💔😭

Yau sai da ya kusa saka mata kuka, sannan ne ta rabu da shi tare da kama ƴatsar tasa dan ta cire wannan bandejin nasa ta kara yi mashi dressing na wajen.

Shi dai burinsa ɗaya kawai, shi ne ta barshi ya je ya ga maman twins, ko yunwa ma baya ji, yana son ya koma ya sake ganin yaran ne, amma bai isa ya tirjewa Mamma ba, dole ya bita a yadda take so dan kada ta yi zargin yana aikata wani abin a ɓoye, dan haka sai ya hakura ta sake yi mashi dressing na wajen ciwon nasa, ta gasa wajen sosai da ruwan ɗumi, sannan ta ce ya je ya yi wanka ya zo su yi breakfast.

Ba musu ya je ya aiwatar da duk abin da ta ce cikin zafin nama, dan ya yi sauri ya gama ya laƙa mum twins.

Zama suka yi suka ci abincinsu kamar yadda suka saba, sannan Mamma ta ce mashi ya je gonarsu ya kawo masu masara ɗanya, ya duba ƙosassu ya ciro, sai ya haɗo masu da nama, daga karshe ta yi mashi kashedi a kan ya kula da yatsar nan tasa sosai, dan yatsar kamar tana son samun matsala.

Okey kawai ya amsa mata da shi kafin ya miƙe ya koma cikin ɗakinsa, kwari da bakarsa masu lafiya ya ɗauko domin farautar nama, sai wata ƴar wuka mai kaifin gaske da ya ɗauka dan tsaro, a kugunsa ya sanya ƴar wukar, ita kuma kwari da bakar ya ratayota a bayansa, sannan ya sanya takalmarsa mai kama da waterproof shoe, a hanzarce yake yin komai, duk dan ya yi sauri ya fita.

A wajen madafa ya isko Mamma, kwandon da suke ciro tomatoes a ciki ya ɗauka dan zubo mata masarar da ta ce ya ciro masu a gonarsu, sannan ya ɗauki wata karamar kwando ma wanda zai zubo masu fruits, dukka kwandunar da itace aka saƙasu, sai dai sun saƙu da kyau.

Sallama ya yi wa Mamma tare da nufo kofar fita. Sosai ta sake yi mashi kashedi a kan kada ya yi wasa da hannun nan nasa fa, ya kula sosai.

Okey ya amsa mata da shi tare da ficewa, yau ya fito sak maharbi. Wajen wata bishiyar lemu ya tsaya ya fara ciro lemun da suka nuna, yana cirowa cikin nutsuwa. Ɗan dai'dai ya ciro kafin ya je wajen bishiyar gwaiva, ita ma ba dayawa ya cire ba, sai mangoro da ita ma bata fi biyar ya tsinko ba, dukka nunannu yake bi yana cirowa, haka ya tara fruits ɗin dayawa, sannan ya nufi hanyar wajen mum twins dan ya je ya kai mata fruits ɗin, ita ya cirowa wannan, na Mammansa sai yana dawowa zai ciro mata, yaron kirki...........😅

Tafiya yake yi cike da jarumta, yana wani bubbuɗe kirji kamar wani mayunwacin zaki, ko alamar tsoron wannan daji babu a idanunsa, tsuntsaye sai shawagi suke yi abinsu, shi ma sai tafiya yake yi abinsa.

Wani irin mahaukacin birki ya ja lokacin da ya isa wajen da mum twins ɗin take, sam bai san lokacin da ya saki kwandon fruits na hannunsa ta faɗi ƙasa ta tarwatse ba, fruits ɗin duk suka watse a wajen.

Wani irin kara zaro idanuwansa waje ya yi, nan take fuskarsa ta bayyanar da alamar zallar madarar mamaki, cikin hanzari da zafin nama ya kara matsowa wajen dan ya tabbatar da gaske ne abin da yake gani.

Tabbas gaskiya ce, babu mum twins kuma babu twins, ɗakin bukkar da aka yi masu ma duk an kakkarya shi, an karya itatuwar gabaɗaya, tamkar waɗan da suka yi faɗa da Damusa ko kuma Damusa ya faraucesu, duk komai a kakkarye, ga kwaryar magangunanta a wajen duk a farfashe, an fasasu, ga kuma towel ɗin da aka rufe baby's ɗin duk suna nan, babu abin da aka ɗauka a wajen face baby's ɗin da Mamansu.

Tamkar a mafarki haka Kamran yake ganin wannan al'amari, tambayar kansa yake yi to ko Damusa ce ta shigo wannan yankin ta cinyesu? Kasancewar shi bai san da cewa biyo maman nasu aka yi daga masarauta za'a kwacewa mata baby's ba, sai bai yi tunanin ko mutanen masarautar tasu ne suka zo suka ɗauketa ba, shi dai tunaninsa wata dabbace a cikin wannan daji ta hallakasu ta kuma ɗaukesu suka tafi cikin dabbobi ƴan uwanta suka cinyesu.

To waye ya ɗauki mum twins? Shin da gaske wata dabbace ta cinyesu ko kuma dai waɗan nan warriors na masarautar tasu ne suka dawo suka ɗauketa? Allah mai iko, Allah masani sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA taku ta amana❤️

Wani irin bakin ɓacin rai ne ya bayyana a saman fuskar Kamran, tamkar ya saba da su, tamkar ƴan uwansa haka yake jin mum twins ɗin nan, kawai daga jiya da la'asar zuwa yau ace bata nan? Ina take?. Idanuwansa ne suka kaɗa suka yi ja sosai saboda tsananin ɓacin rai, har wani huci ya fara fitarwa. Cikin matsananciyar damuwa ya fara kewaye wajen yana nemansu, a cewarsa idan ma damusa ce ta faraucesu zai ga ragowar kasusuwansu, shi ne ya bazama ya fara nema, duk wasu lunguna da saƙuna, bayan bishiyoyi da bayan duwatsun, ƙoguna da ramukan itace dake arear wajen, ko'ina shiga yake yi yana leƙawa, nemansu a haukace kawai yake yi, duk yana kiɗi me, baya damuwa da in da yake shiga, ba
End Ads