canji kenan, baka isa ka ce baka so ba, dole ka karɓa, shikenan Allah ya kawo lokacin yin aurenka na yi farinciki sosai da hakan, amma kasan me yaya?".
A'a Rizwan ya amsa mashi da shi. Ɗan murza yatsun hannun Chuchu dake cikin nasa da ɗan karfi ya yi, hakan yasa ta ɗago kanta tare da kallonta izuwa kansa tana mamakin wai dama yana magana har haka? Bata san sai dai idan basu haɗu ba, ko shi da Jaish suna hira sosai idan suka zauna.
"Ina ga idan kazo tare kawai za'a haɗa auren namu ayi a wuce wajen". Yana magana yana kallon face ɗinta.
Ita ma ta lula duniyar tunani tana kallon face ɗinsa a zahiri, a baɗini kuma tana duniyar tunani tare da mamaki a kan yau dai ɗaya ta ji yayyunta suna maganar aure, abin da bata taɓa ji ba a bakunansu.
"Kai Jawad a ina ka samu mata kuma? Ko dai kaima Mammie ta yi maka irin abin da ta yi mun ne? Ita ta zaɓa maka ko?".
Girgiza kai ya fara yi kamar yana a gaban ɗan uwan nasa, sannan ya saki hannun Chuchun tare da ɗan rungumo shoulder ɗinta, ya dai'dai nutsuwarsa kafin ya cigaba da yin magana.
"Babu wanda ya zaɓa mun ita, ni da kai'na na zaɓota, ita ɗin ta daban ce".
"E lallai Jawad ba shakka kana cikin soyayya, to dai shikenan zamu yi waya anjuma". Yana kai karshen maganar ya katse kiran diff, da alama yana yin wani abin ne.
Shiru shi kuma Jawad ɗin ya yi yana jin wani irin a cikin zuciyarsa, haka kawai yau tun da suka fara waya da yayan nasa yake jin babu daɗi a cikin zuciyarsa, yanzu kuma Rizwan ɗin yana katse kiran sai ji ya yi ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, bai taɓa jin irin hakan a tattare da shi ba.
Hasbunallahu wani'imal wakil ya furta a cikin zuciyarsa tare da sakin shoulder ɗinta, ya miƙa mata ɗayar wayarsa yana faɗin. "Wayarki babu caji ta mutu, ki rike wannan nawan idan kin gama shiri sai ki kirani da ita, bari nima na je na duba daddy sai na je na shirya yamma tana yi".
Yana kai karshen maganar ya miƙe tsaye tare da nufar hanyar fita haka kawai yake jin zuciyarsa babu daɗi tun da suka yi waya da yayan nasa.
Cike da murna ta miƙe tsaye hannunta rike da wayar tasa, bin bayansa da kallo ta yi har ya fice hannunsa na rike da wayarta da ɗayar tasa. Yana fita ta dawo da kallonta a kan wayar tasa, kunna hasken screen ɗin wayar ta yi, a hankali ta kai hannu ta fara taɓa wayar, da alama sai da ya cire password ɗin wayar kafin ya bata, domin babu password.
Cikin wayar ta fara shiga kamar ya aiketa, dube dube ta rinƙa yi mashi har ta shiga cikin gallerynsa, ita da ya ce ta shirya da wuri.
Ta sha madarar mamakin ganin uban tulin pic's ɗinta a cike a gallery ɗin nasa, iya pic's ɗinta da kuma design na gine gine da companynsa take fitarwa ne kawai suka cika galleryn nasa, sake baki ta yi tana kallon pic's ɗin, mamaki take yi a ina ma ya samosu? Wasu pic's ɗin ma bata sani ba aka ɗauketa, wani suna saman dining table suna cin abinci tun bata kai shekarun haka ba, wani tana sanye da uniform zasu tafi school, wasu tana kwance a gadon Akka, wasu kuma a fada wajen King, hotuna ne dayawa iri daban daban da duk ba wanda ta san da su a cikinsu.
Ta jima a tsaye tana ta ganin hotunan, wani waje ita da kanta idan ta gani sai ta kwashe da dariya, dan duk hotunane da aka ɗaukesu a sace, so dole wani ya baka dariya. Ta ɓata lokaci sosai wajen ganin hotunan kafin ta tuna cewa yana jiranta, dan haka sai ta yi sauri ta wuce izuwa room nata da yake a ɓangaren Akka ɗin dan ta shirya.
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️
🏞️FOREST🏞️
Kamar yadda Kamran ya tsara hakan ya yi, ya yi tafiyarsa har sai da Mamma ta sauko daga dokin zuciya da ta hau ta bazama nemansa a cikin dajin, dama ashe yasan ba zata iya hakura ta share shi ba, shiyasa ya yi mata wannan tsiya, yasan halinta in and out.
Ai kuwa ko da ta je ta same shi kwance a saman irin bishiyoyin nan masu fitowa a kwance, cikin sanyin murya ta fara lallaɓa shi a kan ya tashi su koma.
Amma da yake ya san lagonta, yana fa jin yunwa kamar me, amma dan tsiya sai ya kafe mata a kan shi babu in da zai je ta kyalesa kawai a nan tun da bata sonsa, komai ya yi mata sai ta yi magana, yanzu ta dai'na sonsa, shi wai me ya yi mata ne da ko waje bata son ya rinƙa leƙawa? Shin ita bata son farincikinsa ne? Ba zata barshi ko ɗan yawon nan ya rinƙa zuwa yana rage kewa ba?!.
Lallaɓa shi dai ta cigaba da yi, tuni ta mance da batun kitson da Hajiya Pretty ikon Allah ta yi mashi, yanzu burinta kawai ya dawo gida, dan tasan shi da shegen zuciya, ba ƙaramin aikinsa bane ya kwana a wajen nan, tana matuƙar kaunarsa, dama annabi ya ce abin da kake so a nan jarabawarka take, duk abin da ka sanya a ranka kana son shi to wlh a nan Allah yake gwada imaninka, nan jarabawarka take, to ita ma dai Mamma Kamran shi ne rauninta gaskiya, bata iya jure ganinsa cikin ɓacin rai, dan dole take hakura idan ya yi fushi ta hau lallashinsa.
Yana jin yunwa kamar me, amma sai da ya tsaya ya ja mata rai sosai, sannan ya miƙe suka nufi gida. Yana zuwa bai tsaya yin wanka ba kawai ya fara neman abinci, dama a hannu yake, kawai juriya ce saboda ya waskewa mamma, amma yunwar tana nan.
Sai da ya ci ya ƙoshi sannan ne ya miƙe da nufin ya je ya yi wanka. Da ido kawai Mamma take binsa, sai dai ba irin kallon yau da kullum take yi mashi ba, wannan kallo akwai alamar tambaya sosai a cikinta.
Wanka ya yi ya wuce makwancinsa ya kwanta abinsa, zuciyarsa cike da tunanin su Pretty barci ta yi awon gaba da shi.
Can cikin barci da yamma sosai rugugi da tsawar ruwan sama suka tada shi daga barci, a hankali ya waro idanuwansa da suka yi mashi nauyi sosai saboda barci. Jin yadda garin yake ta famar haɗewa da hadari ga tsawa da walkiya ta ruwan sama yasa ya kara waro idanuwansa waje tare da miƙewa zaune, a hanzarce ya zuro kafafunsa ƙasa tare da miƙewa tsaye.
Kamar wadda ya yi wani ajiya a waje haka ya nufo wajen da zafinsa. Mamma tana barci, dan ta sha aiki ta gaji. Kai tsaye fita ya yi, gari ta yi bakinkirin da hadari, sai walkiya dake tashi, iska suna ta kaɗa manya da kananan bishiyoyi, ruwan ƙoramar na kaɗawa.
Da sauri ya sauko kasan tsaunin nasu, Rocky baya nan, da alama ya yi gaba abinsa, ya tafi yawo.
Kai tsaye wajensu Pretty ya nufa, dan da tunaninsu ya yi barci, da kuma su ya farka a ransa, yana son kafin ruwan saman nan ta sauƙo ya je ya duba su, dan yasan wannan ruwa idan ta zubo tofa takan iya kai cikin dare tana zuba, so gara mashi ya je wajensu in ya so ya dawo cikin ruwan ta jiƙa shi, amma dai ya je ya gansu kam.
Sosai yake zuba sauri cikin takun jarumta, babu tsoro ko ɗigo a ransa. Yana zuwa ya yi maza ya afka cikin ramin nasu.
Sweetie ce kawai zaune a saman wani dutse hannunta na rike da wannan abin mai haske da suke farfasa abu da shi ko su daka wani abin da shi, ɗayan hannunta na rike da wani irin nau'in fruits mai kama da ruman tana sha. Baiwar Allah tana sanye da kayan da Kamran ɗin ya kawo masu na sakar audiga, ta yi matuƙar kyau sosai da sosai, kayan suna yi masu kyau, ga idanunta tas, wlh sai ka rantse da Allah tana gani, gasu tankar da su a buɗe, amma ba abin da take iya gani face duhu, yana ya rufe idon daga ta ciki.
Jin motsi yasa ta fara faɗin. "Kin dawo kenan? Dama na gaya maki ba zaki iya zuwa in da Kamran yake ba, ke da bama kisan daga ta ina yake zuwa ba, kawai ki ce ke kina kewarsa zaki je ki kirasa, Allah Pretty baki jin magana, wai da can kece kike kiransa ya zo ne? Ba shi da kansa yake zuwa ba? Sai kin je kin ɓata hanya ai zaki yi bayani".
Zaro idanu waje sosai ya yi tare da faɗin. "Sweetie ina Pretty ɗin ta tafi?".
Ita ma ɗan zaro ido ta yi kafin ta ce. "Kamran kai ne?".
E ya amsa mata tare da sake tambayarta ina Pretty ɗin ta je?.
"Wai ta tafi nemanka dan tana kewarka sosai, tun ɗazun da ka tafi baka dawo ba shi ne wai ba zata iya hakura ba ta je nemanka".
Dafe kansa ya yi tare da juyawa a guje domin ya bi bayanta.
"Kamran! Kamran!". Sweetie ta fara kiran sunansa. Ina ai tuni ya fice, bai sake bi ta kanta ba, dan kada ma ya biye mata Pretty ta je ta faɗa wani wajen.
Yana fitowa ya fara ƴan waige waige yana tunanin to shi yanzu ta wani hanya zai bi ya je ya nemo wannan rigimammiyar yarinyar?.
Fara nemanta a ɗan kewayen wajen ya yi ko Allah zai sa ya ganta bata yi nisa ba, har haɗa zufar dole ya fara yi, damuwarsa ɗaya shi ne kada ta je a garin nemansa ta isa ga in da Mamma take.
Sosai ya fara nemanta ta yankin waje, ya je ya dawo ya je ya dawo, duk ya wahala ya galabaita, ya kuma shiga cikin tsananin tashin hankali da damuwa, duk ya ruɗe, har idanuwansa sun yi jajir saboda shiga damuwa, ga hadarin ruwan sama yana ta kara tsananta.
Idan ka gansa sai ya baka tausayi, sai ka rantse an raba shi da Pretty ɗin kenan, wannan ya kenan idan aka ce za'a rabasu? Ya zai yi da ransa? Ina zai sa kansa? Sun rigada sun zama jinin jikinsa, suma ba zasu iya rabuwa da shi ba, kunga dai bai wani jima sosai da barin wajen nasu ba, barci ne ya dauke shi har lokacin da yake dawowa ya yi bai dawowa ba, amma Pretty ta kasa iya hakura har ta tafi nemansa, hakan zai kara tabbatar maku da suma ba zasu iya rabuwa da shi ba, dukkansu biyu suna kaunarsa sosai. Babbar magana akwai case ranar da Kamran ya bayyana da gaske waye yake so a cikinsu tab!!.
Sosai ya galabaita sai haki yake yi, amma babu ita babu alamarta, kai kamar ma ba'a taɓa yin mai kama da ita ba a duniya. Har kusa da gidansu ya je nemanta, amma shiru. Nufar wajen ƙoramar da suke zama ya yi yana ta mayar da numfashi tare da sauke ajiyar zuciya.
Tun daga nesa ya hangota kamar wata macijiya tana tsaye a samar dutse kamar ƴar tsana tana aikin data saba, wato dai tana sanya hannunta a cikin ruwan koramar ruwan yana fallatsuwa mata a saman fuskarta, hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba, mayyar son ruwa ce sosai, ko da yake dama dole ai su so ruwa sosai, duba da in da suka taso. Ita ma Sweetie ba baya ba wajen shegen son ruwa, shi ne abin wasansu da kuma ɗebe masu kewa, idan suna jin kewa cikin ruwan ƙoramar suke zuwa su shiga yana jiƙasu suna jindaɗi.
A dubu ɗari ya ƙariso wajen yana sauke numfashi dan ya tabbatar da cewa ita ɗin ce ko ba ita ba.
Wani irin daddaɗar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya kalli cewa ita ɗin ce, tana sanye da riga da sket wanda ya fara ganinta da shi, ta ɗaure gashin kanta kamar dai ranar da suka fara haɗuwa.
Cikin wani irin farinciki ya ambaci sunanta tare da ƙarisowa wajen yana murmushin da shi kansa bai san yana yi ba, ya ji daɗin ganinta, da bai ganta ba yau ina zai sa kansa? Ta wahalar da shi ashe tana nan tana aikin da ta saba.
Jin voice ɗinsa yasa ta juyo tare da dirowa kasa, da gudu ta faɗa jikinsa tana dariya tare da gaya mashi ta yi kewarsa sosai.
Rumgumeta ya yi shima yana murmushi mai ƙayatarwa, alamar suna cikin tsantsar farinciki da ganin juna.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 28/8/2024.....✍️📚🌹
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
Rumgumeta ya yi shima yana murmushi mai ƙayatarwa, alamar suna cikin tsantsar farinciki da ganin juna.
Ruwan sama ne mai karfin gaske ya kece kamar da bakin kwarya. A ɗari ta sake shi tana faɗin. "Kamran mu gudu cikin raminmu ruwan sama".
Hannunta ya riƙo shi ma yana faɗin. "Me ruwan saman zai yi maki sarkin tsoro? Babu komai, zu mu zauna a saman dutsen nan kina mana busa ruwa na jiƙamu".
Ɗan turo baki ta yi. "Kamran akwai sanyi fa ruwan".
Jan hannunta ya yi suka koma saman dutsen suka zauna. "Ai haka kike so, shi ma ruwan ƙoramar da kike shiga kullum ai akwai sanyi".
Kwantar da kanta a saman shoulder ɗinsa ta yi tana faɗin. "Not like rain, shi sanyinsa daban ne, but is so sweet kuma fa".
Tafukan hannunsa ya buɗe ruwan na zuba a samansu. "The water is so very very fresh and cool". Ya yi maganar yana ɗan watsa mata shi a saman face ɗinta.
Jinjina mashi kai ta yi. "Yah ikon Allah kenan, ko iya ruwan saman nan idan ka kallah ya isa ya sanyaka ka kara jin tsoron Allah, ka kara ganin girman Allah, Allah buwayi gagara misali, yanzu idan ka ɗaga kanka ka dubi sararin samaniya sai ka rasa ta ina ruwan yake fitowa, hmmmm wani abin sai Ubangiji, yanzu fa a saman nan akwai ruwan da zai iya cinye duniya da abin da yake a cikinta, kaf duniya babu wanda ya isa ya tare ruwa kada ya wuce idan ya doso waje, amma shi Ubangiji ya rike ruwan da zata iya cinye duniyar nan tas ba tare da ta zubo ta cinye duniyar ba, kai komai ma fa ka gani a duniyar nan idan kana da hankali ya isa yasaka ka kara jin tsoron Allah!!".
Yadda ta yi maganar kamar wata babbar mace, ta kwantar da kanta shiru tana zayyano bayanai cikin natsuwa, ruwan saman na sauka a kansu, abin sai ya ƙayatar da masu kallon.
"Pretty ina son sanin wanene Allah? And ina son samun karin sani sosai a kan abubuwan da kuke yi keda Sweetie". Ya yi maganar tare da juyowa da kallonsa izuwa saman face ɗinta.
"Kamran Allah shi ne wanda ya halicceni ya kuma halicceka tare da sauran mutanen da kake gani suna giftawa a cikin dajin nan, sannan ya halicci sammai da ƙassai, halittun Ubangiji ba zasu kirgu ba, dan sun wuce gaban tunanin kowa".
Juyowa da kyau ya yi ta yadda zai sami damar ganinta da kyau da kyau. "To meyasa Ubangiji ya haliccemu kenan?".
"Bauta, domin mu bauta mashi, kuma sallah da ka tambayeni a kan mecece ita ranar da kasame ni ina yinta to ɗaya ce daga cikin abin da Ubangiji ya haliccemu muzo mu yi mashi, kuma ita ce ma a kan gaba, sai karatun Alkur'ani mai girma, ita ce littafin nan da ka ɗauka a wajenmu ranar, akwai azumi da sauransu, amma ni dai bana yin azumi gaskiya, ba zan iya yunwar nan ba, Sweetie ce kawai take yi, ni kam wlh dana ji yunwa zan ci abinci na, so ban taɓa yin azumi ba". (Sarkin cin abinci ba, yo dama ke a yanzu ai ba zaki iya yi ba, wata kila idan ya zama wajibi a kanki kyayi dan dole😅)
"E ina karanta littafin dana ɗauka a wajenku, kuma yana da matuƙar daɗi sosai, sai dai ban yi nisa a karatun ba, wannan littafin ma yana ɗaya daga cikin abin da ya hanani karanta diaryn da mummynku ta bani, wannan Alqur'anin ya ja ra'ayina sosai, ya ɗauke mun hankali da a kullum a ƙagare nake dana karanta shi".
Murmushin ta sakar mashi tare da kai hannunta ta ja karar dogon hancin nan nasa. "Ka yi ƙoƙari ka karanta zaka ji daɗinsa, aduniya babu abin da ya kaisa daɗin karantawa da kuma sauraran mai karantawa".
Shafa kumatunta ya yi kafin ya ce. "To ɗan karanta mun kaɗan na ji". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannunsa a cikin gashin kanta dake ta zubar da ruwa sosai, ga hadari sai kara haɗuwa yake yi, ruwan sama yana kara tsananta karfin zubarsa kamar da bakin kwarya, ga walkiya mai hasken gaske da yake haske arear wajen a duk lokacin daya wanzu a sararin samaniyar, sai tsawa ya biyo baya. Hankalinsu a kwance suke zaune a wajen abinsu, ko kaɗan basu damu da ruwan da yake zuba masu a kansu ba.
Rera mashi karatun Alqur'ani mai girma ta fara yi cikin suratul iklas, ga voice ɗin nata da zaki ga shegen daɗi. Shiru ya saurara yana jinta, har wani irin ni'imantaccen ajiyar zuciya ya sauke, Alqur'ani akwai daɗin saurara, ga kwantar da hankalin mai sauraro.
Ƙarar da suka fara jiyowa daga can nesa da su ne yasa Pretty ta dakata da karatun, a lokacin already ta kammala suratul iklas ta shiga falak,