dining table ɗin, abincinsu kawai suke ci cikin natsuwa, sai ka rantse da Allah babu su a cikin room ɗin, auta duk ta damu na rashin ganin gimbiya Chuchu a room ɗin, ita kuma Sarina sai faman hararar Aneesa take yi sarakai waɗan da basa shiri, sai mayar mata da martanin hararar Aneesa ɗin ma take yi.
Obaid and Omaid dai har yanzu suna nan suna shirya kalar azabar da za su yi wa Mama, basu janye wannan kuduri nasu ba.
King ne ya ɗan yi gyaran murya tare da fara yin magana kamar haka. "Omar dai uncle Abu Abdussalam ya ce ba zai dawo this week ba, na yi na yi amma ya ce wlh na fita idonsa na bar mashi guyson ɗinsa ya kara mashi hutun koda na one month ne kafin ya dawo ya cigaba da karatu, so mummynsa sai ki yi hakuri da shirya mashi walimar sai next month, ku kuma Obaid and Omaid sai next week zaku koma, dama saboda Omar zai dawo ne yasa na yarda zaku koma, to tunda an sake riƙe mun shi nima bari na sake riƙeku a nan kaɗan tun da ma ku baku koma school ba, ke kuma Sarina ina son ki mayar da hankalinki da kyau, kada na kara ji ko ganin wani bako ya zo wajenki, nasa a saki su Yusuf bayan Zafar ya horasu da kyau". Ya kai karshen maganar yana kallon Mommar Zunaira.
Momma ɗin dai bata ce komai ba, domin yayanta ne Abu Abdussalam ɗin, kuma shi ya hana Omar dawowa, ya zata yi da ya wuce ta yi shiru, bata da ta cewa, ita kuma mummy sai cewa ta yi. "Kai gaskiya uncle Abu Abdussalam ya yi hakuri ya bar nana Guyson ɗin mu ya dawo, muna kewarsa sosai fa".
Mama ce ta wani ɓalle masu kallon banza tare da turɓene fuska kamar wadda taga wani abin kyamar.
"Daddy please ka barni mana na je wajen su Uncle ɗin, ba sai mu dawo a tare da Yah Omar ɗin ba". Cewar auta, ta yi maganar tana turo baki.
"Wani zuwa kuma bayan an buɗe school?" King ya bata amsa.
Turo baki kawai ta yi, ta ji babu daɗi, tun kafin a buɗe makaranta take ta son zuwa, amma aka hanata.
"Bari na dubo Aunty Chuchu". Cewar autar, ta yi maganar tare da miƙewa ta nufi hanyar fita daga room ɗin. Sauri sauri ta yi ta fita dan ma kada daddyn nata ya ce ta zawo sai sun ƙarisa cin abinci, dan Akka ta gaya mashi cewa Chuchu ta ce tana ƙoshe bata jin yunwa da ya tambaya.
Kai tsaye part ɗin Akka ta nufa, dan tasan a can zata sameta, bata jin daɗi ne a duk lokacin da take waje ba tare da Chuchu ba, sun yi matukar shaƙuwa.
Ta zo wucewa ta part ɗin Yah Jaish ne Yah Jawad ya fito daga ciki, bayan ya yi sallolin da suke a kansa ne ya yi wanka ya yi shirin barci sai ya nufi part ɗin Jaish kamar yadda suka saba, a nan suka ci abincin dare suka ɗan yi hira kaɗan, kasancewar yana da aikin da zai yi sosai shi ma kuma Jaish ɗin akwai wani bincike da yake yi a kan wata ma'aikata da suke zargin tana haɗa kwayoyin cuta da kwayoyin magunguna na shan al'umma, suna watsa cutar ta wannan hanyar, a matsayinsa na babban ɗan jarida ya kuma samu information sosai a kan ma'aikatan, shi ne yake ƙoƙarin bincikarsu ya tabbatar da abin da jama'a suke zargin gaskiya ce kafin ya fitar da bayanan, wannan dalilin yasa yau suka yi sallama da juna da wuri, saboda duk suna da tulin aiki a gabansu.
Yana fitowa suka ci karo da auta. "Good evening Yah Jawad". Ta faɗa tana ƙoƙarin wucesa.
"Zunaira ina zaki je kike sauri haka? And then ban hanaku yawo da kayan barci babu hijabi haka a cikin gidan nan ba?".
Dakatawa ta yi daga tafiyar da take yi, ɗan turo baki kaɗan ta yi kafin ta ce. "Kayi hakuri ba zan sake ba, na manta ne".
Shiru ya ɗan yi mata na ƴan sakani kafin ya ce. "To ina zaki je haka?".
"Wajen Aunty Chuchu zan je, bata zo dining room bane, tana part ɗin Akka, shi ne zan je in dubota". Ta bashi amsa.
"Idan kin je ki ce ta zo ina son ganinta, ta same ni a part ɗina". Yana kai karshen maganar yasa kai ya wuce abinsa. Ita ma cikin sauri ta wuce izuwa wajen elevatorn da zai kaita part ɗin Akka.
Kwance ta isko Chuchu a saman bed, tana sanye cikin kayan barci riga da dogon wando masu kyau launin maroon color, kayan barcin yana da hula mai kyan gaske, so ta sanya hular a kanta, sai latsa wayar Akka take yi dan Yah Jawad ya kwace mata nata wayar idan baku manta ba.
Saman bed ɗin auta ta haye tare da cewa. "Aunty Chuchu shi ne baki nemeni ba ko? To Yah Jawad yana kiranki".
Zaro idanu waje Chuchu ta yi tare da miƙewa zaune. "Nashiga ukuna! Me kuma na sake aikatawa Yah Jawad da yake nemana?! Ni wlh Allah sai na kai shi kara wajen daddy in dai ya sake bani punishment, kuma sai na gayawa Akka ma, na gaji da shan wannan bakin azaba, haba wai ni kaɗai ce a gidan?". Cikin tsiwa ta yi maganar.
Kwanciya ita dai auta ta yi tare da jawo pillow ta rungume haɗe da karɓar wayar Akka dake hannun Gimbiya Chuchun, sannan ta ce. "Allah ni ban san meyasa Aunty Chuchu kike ganin laifin Yah Jawad ba, yana da saukin kai fa, kuma yana da kirki".
Duka ta kaiwa autar a baki tana faɗin. "Tun wuri ki yi istigifari, dan Yah Jawad kam sam bai bi hanyar da saukin kai ya bi ba, mugu ne na karshe, kuma wlh sai na gayawa uncle Abbas duk muguntar da ya yi mun, Allah har na fara tsanarsa sosai, amma fa kada ki gayawa kowa na ce na tsanesa fa".
Hannu auta ta kai ta toshe ɗan bakinta da shi tare da zaro idanu waje. "Yah Jawad ɗin kika tsana Aunty Chuchu? Yayan mu ne fa, innalillahi". Tana magana tana zaro idanu!.
"Ke zaki yi mun shiru ne ko dai kina gaya mun yayan mu ne? To ni dai bana son shi, mugu ne, kuma idan kika faɗawa wani ko wata nace hakan daga yau mun bata".
Girgiza kai auta ta fara yi tana faɗin. "Ba zan gayawa kowa ba, amma dan Allah Aunty Chuchu ki dai'na cewa kin tsanesa, please, wlh ni bana son jin wannan kalma".
Ƙoƙarin sauka kasa daga saman bed ɗin ta yi tana faɗin. "Zan daina faɗa, amma dai ba zan cire tsanarsa a rai'na ba, sai ya yi ta azabtar da mutane dan mugunta, Allah bari na je na amsa kiransa, idan ya bani wata punishment ɗin kamar a gaban uncle Abbas aka yi, sai na gaya mashi, kuma in gayawa Akka da daddy dukka". Tana kai karshen maganar ta sauko kasa, sai turo baki take yi ta nufi waje, haushi yasa ta manta da cewa kayan barci ne a jikinta kuma bata ɗauki hijabi ba, haka ta nufi part ɗinsa tana kunkuni a cikin ranta, sai faɗi take in dai ya ci zalinta yau to wlh sai ta kai kararsa wajen uncle Abbas, sai dai ya yi duk abin da zai yi mata mugu kawai.
Bakinta a ɗauke da sallama ta shigo part ɗin nasa. Daga jin yadda ta yi sallamar kasan a ƙule take da bakinciki har wuya.
Babu kowa a parlourn, kuyangu masu yi mashi gyara ma sun kammala aikinsu sun fice. Kai tsaye bedroom ɗinsa ta nufa. Ƙasa ƙasa ta yi sallama tare da tura kofar ta shiga ba tare da jira izininsa ba, dan ita fa haushin da take ji yasa ta manta ma a ina take tukun nan, sai kunkuni take yi tana tsine mashi a cikin ranta.
Yana zaune a saman bed ɗinsa, ya tasa laptop a gaba yana aiki a kan aikin da King ya ba wa Companynsa na gina gidan marayu, aikin yake ta fama da shi. Ta wutsiyar idanunsa ya kalleta. Wani irin bakinciki da kishi ne ya taso mashi, hakan yasa ya ɗaure fuska sosai kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa, yauma da kayan barci ta fito kenan? Ya..................
Lokacin shan Maltina ta yi🥱
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
Yana zaune a saman bed ɗinsa, ya tasa laptop a gaba yana aiki a kan aikin da King ya ba wa Companynsa na gina gidan marayu, aikin yake ta fama da shi. Ta wutsiyar idanunsa ya kalleta. Wani irin bakinciki da kishi ne ya taso mashi, hakan yasa ya ɗaure fuska sosai kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa, yauma da kayan barci ta fito kenan? Ya tambayi kansa da kansa a cikin zuciyarsa.
Ita kuwa gabansa ta nufo, sam bata tuna komai ba. A ɗan nesa da shi kaɗan ta tsaya tare da cewa. "Yah Jawad gani nan".
Tamkar bai san da shigowarta room ɗin ba, aikin gabansa kawai ya cigaba da yi, sai dai kuma a zahirin gaskiya ya kasa yin aikin dai'dai saboda ɓacin rai, hankalinsa kuma yana kanta, tunanin kalar hukuncin da zai yi mata kawai yake yi.
Ta jima a tsaye a wajen almost 10 mins bai ko ɗaga idanu ya kalleta ba, aikinsa kawai yake yi na latsa laptop ɗin buge dan kada ta gane hankalinsa baya a kan aikin.
"Yah Jawad in ta fi ne?". Ta yi maganar kamar zata fasa kuka, saboda ta gaji da tsayuwa, ta ga bashi da niyar kulata, kuma yau ta sha alwashin wlh ba zata tsaya a cuceta ba, idan ya ce ta yi kneel down ko makamancin haka to wlh guduwa wajen Akka zata yi, sai dai ya bita can ya kakkaryata idan yana so...... Lallai Chuchu ta fara girma, abin ya fara kureta........😅
Sai da suka kara good 5 mins a haka kafin nan ya ɗan ture laptop ɗin daga gabansa izuwa gefensa, ba tare da ya ɗago ya kalli in da take ba ya ce. "Zo nan ki yi mun kneel down, domin yau sai na koya maki hankali sosai, ke kunnanki baya jin magana ko Jannat? To yau zai fara jin magana dole........"
Bai gama rufe baki ba ta watsa a guje zata nufi waje, dama ta ce wlh ba wani hukuncinsa da zata karɓa yau, yana yin yunkurin hukuntata zata gudu, aikuwa sai ga shi ta ruga a guje zata yi waje.
Wani irin miƙewa ya yi babu shiri, dan yasan idan ya barta ta gudu ya shiga tara da Akka na farko, na biyu kuma bai ga dalilin da zai sanya yana yi mata magana zata gudu ba, a cikin kannen nasu ma fa ita da auta sune kanana, amma tsabar ta rai'na shi ne yana magana zata gudu? Lallai yau dole ta ci duka, ba ma zai yiwu ya barta ta gudu ba ai, dole ya kamota ta karɓi hukuncin dama bai taɓa yi ma kowa daga cikin kannen nasu ba, ko Sarina da take sarkin rashin ji yau hukuncin da zai yi wa Chuchu bai taɓa yi wa Sarina ɗin ba, sannan ya ja mata kunne a kan idan ta gayawa Akka ko uncles Abbas sai ya karairayata........ (Ku ji mun mugunta, a dakeka a hanaka kuka, ya azabtar da ita kuma ya ce kada ta gayawa kowa🤔 Allah Yah Jawad ma mugu ne)
Bata kai ga isa kofar ɗakin ba ya damkota ta baya, duk da tasan cewa ko ta yi ihu babu wanda zai iya jinta a cikin gidan, saboda ainahin kofar shiga part ɗin nasa ma a rufe, tana shiga kofar ta rufe, ga shi izuwa yanzu tasan kowa ya rufe kofofin part ɗinsa, koda bama haka ba yanayin tsarin ginin gidan mawuyacin abu ne tana cikin wani part ta yi ihu a jita a wajen, hakan ba zai yi ba.
Amma duk da haka hakan bai hana ta waje baki zata kurma mashi ihu ba, domin ta tsarorata da kamota da ya yi, bata yi tsammanin zai yi yunƙurin bin bayanta har ma ya kamata ba, ta yi tunanin zata iya tsira ne ma yasa ta fara gudun, tasan ba komai yake kulawa ba, so a tunaninta idan ta gudu ma zai kyaleta ya ce wata kila da safe zai kamata, amma sai ta ji an damkota ta baya, shi ne abin ya razanata da har yasa ta waje baki da karfin gaske zata zunduma ihu, ga tsoron kalar hukuncin da zai yi mata, yanzu ma bata gudu ba ma ya ce ta yi kneel down bare kuma ya ce ta yi ta ki yi zata gudu? Ai ita da kanta tasan hukunci ya karu sosai!.
Ina duk da yasan ba wani jin ihun nata family zasu yi ba, amma bai bari ta yi shi ba, tana waje ɗan bakin yasa hannu ya toshe mata bakin nata, ransa ya sosu matuƙa, duk cikin sisters ɗinsu babu wanda ya taɓa yi mashi makamancin abin da ta yi mashi, bai san cewa idan ka cina takurawa mutun dama ya kansa ya rage tsoronka idan ma yana ji ba, takura mata da yake yi ne yasa ta rage jin tsoronsa da har ma take kiransa da mugu, yanzu da Yah Jaish ne ya kirata ai ko yankata yake yi ba zata tsallake abin da ya ce ba, saboda me? Saboda da ni da ku dukka mun san Yah Jaish dai ba wanda ya ishe shi kallo a cikin kannen nasa, baya kulasu kuma baya bi da kansu, kunga kuwa dole a ji shakkarsa sosai, shi ma dai Yah Jawad ɗin chuchu kawai ya sakawa ido, kuma dani da ku duk mun san dalilinsa na yin hakan.
"Stay quiet, if not a cikin daren nan zan kakkaryaki na zubar da kasusuwanki a dustbin". Ƙasa ƙasa sosai ya yi maganar, ya kuma kai karshen maganar tare da zame hannunsa daga saman ɗan bakin nata.
Wani irin kermar tsoro jikinta ya fara yi, danasanin abin da ta aikata ta fara yi, yau dai ta shiga uku ta lalace, haka take ta faɗi a cikin ranta.
Saketa ya yi tare da juyo da ita suna fuskantar juna, sannan ya kai hannunsa ya damko wannan arab hair ɗin nata, saboda hular kanta ya cire tun lokacin da ta watsa a guje zata yi waje, so sai ya zamana babu ɗankwali a kan nata, hakan ya bashi damar damko mata kyakkyawar gashinta da ta ɗaure shi kashi biyu.
Da karfi ya danki gashin nata tare da jan shi baya sosai, hakan yasa dan dole babu shiri sai da ta ɗago kanta sama, wani irin azaba ne ta ji ya ziyarceta lokaci guda.
"Kin girma ko Jannat? Har inai maki magana zaki gudu ko?".
Kai ta fara girgiza mashi ba bakin yin magana, sai wasu zafafan hawayen azaba da suka cika mata idanu, kan ka ce me sun fara wanke mata fuska, amma fa a cikin ranta faɗi take yi wlh yana sakinta sai ta sake watsawa a guje, kuma yau ba sai gobe ba sai ta gayawa uncle Abbas muguntar da yake yi masu ita da su Sarina, sannan zata gayawa Akka da daddy, wlh ba zata hakura da kudurinta na gaya masu ba, ko dan su samu sassauci a kan irin cin zalinsu da yake yi, duk sai ta ji ta kara tsanarsa sosai.
"Zaki yi mun shiru ne ko sai na ɗauko belt?". Ya yi maganar yana kai kallonsa izuwa saman bed ɗinsa, wayarsa ce take kara alamar shigowar kira.
Kara jan mata gashi baya ya yi da ƙarfi, tare da dawo da kallonsa a kanta. Ba komai ne yake kona mashi rai ba face fitowa da kayan barci da ta yi, kishi ne kawai yake cinsa a zuciya yasa yake azabtar da ita har haka. Izuwa yanzu shi da kansa ya fahimci cewa tabbas uncle Abbas gaskiya yake gaya mashi na cewa yana son Jannat, domin kuwa idan har baya sonta ba zai yi kishinta har haka ba, wannan kishi ya wuce na yaya da kanwa sai dai mata da miji, kuma ba zai rinƙa damuwa da son ya ganta har haka ba, yanzu da yasa auta ta kirata a fili idan ta zo dama wayarta zai bata, a zahirin abin da yake cikin zuciyarsa kuma ba wayar yake son bata ba, ganinta yake son yi, dan yana kewarta, shi ne gaskiya!!.
Amma kuma shi fa wai a haka so yake ya cire son nata a ransa, saboda a cewarsa ita ɗin sistersa ce kawai, kuma ta yi ƙanƙantar da zai iya cewa yana so, bugu da kari ba zai iya jawa kansa rai'ni na cewa zai aureta ba, idan ya yi haka ai yagama da kansa, ya jawa kansa rai'ni, shi ne yasa tun farko yake kaucewa yaki yarda da cewa yana sonta, dan bai son rai'ni, yanzu kuma da ya fahimci hakan yake ƙoƙarin cire son nata a ransa. Akwai cakwakiya ga Mammie ɗinsa ma kun dai ji bata kaunar wannan haɗin, uncle Abbas kuma fatansa kenan, wai ma to meyasa Mammien bata son haɗin Jawad ɗin da Chuchun? Akwai dai wata a ƙasa gaskiya.
Kasa iya yi mashi shirun ta yi, sai ma kara karfin gudu hawayen nata suka yi, sakamakon ya kara ja mata gashi kanta baya, zafi ya karu, dan haka ita ma sai ta kara kukan nata. Har cikin ransa yake jin