x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - SU WAYE SU

  • 24001 words
  • 27000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 147

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
na commissionan ƴan sanda kana yin abun da bai dace bane da har kake expecting ɗin zamu ɗauke maka yaro, idan kana tunanin haka ai kai jami'in tsaro ne me kare haƙƙin jama'a ko waye bare kuma ace an taɓa naka ai kamata yayi kayi gaggawar ɗaukar mataki amma har ka ɗauki masu laifi a motar ka kayi driving ɗinsu batare da ka ɗauki ko wane irin mata ki ba, wannan ai abun kunya ne baka cancanci muƙamin kaba, da masu sharar gida ka dace ta yanda zaka zama marar gata akuya da kare su ɗauka sannan......

Ameelaaa...!!!

Ya daka mata tsawa tare da cewa; "fice min daga mota right now......

Dariya ta kwashe da ita harda tafawa tare da cukwikwiye masa riga tana sauya kalar fuskar ta zuwa ai nahin yanda ya santa.......✍️

Please ayi maleji ba yawa.

*(Duk me son in saka shi a group yayi min magana ta number ta a WhatsApp, dan Allah idan kasan ba karantawa zakayi ko zaka tambaye ni wani littafin to kar kayi min magana Please 🙏08124226526)*

*(ƴan facebook kuma da basa WhatsApp kuyi searching ɗin SU WAYE SU HAUSA NOVEL GROUP kuyi join anan zan ringa posting kullum amma idan kana wani group ɗin zaka iya ganin sa saidai baizama lalle kagani kullum ba kuma ba ajere ba.)*
[3/5, 11:45 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________


*_episode 9💧_*


💧💦محمدالرسوالله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

Ameelaaa...!!!

Ya daka mata tsawa tare da cewa; "fice min daga mota right now...!

Dariya ta kwashe da ita harda tafawa tare da cukwikwiye masa riga tana sauya kalar fuskar ta zuwa ai nahin yanda ya santa.

Stop shouting at me before inyi maka a bun da baka tsammani na rantse da Allah ka kuma ɗaga min murya anan gurin sai ka gane shayi ruwa ne, har Ni zaka cewa in fitar maka a mota, Ni zaka kora daga motar ka, akan wani ɗan iskan ɗanka, kasan ba tsoran uban kowa muke ba, da idan mu muka ɗauka zamu ɓoye, mu ɗauke sa mu ɗorawa kanmu kaya, ai mutum nayi mana zamu ci ƙaniyar sa jikin mutum yagaya masa basai anɗau loƙaci ba, bare ma kuma shi yayi kaɗan muyi dashi saidai muyi da Baban sa ko Baban Babban sa... Tana faɗar haka ta sake sa tana watsa masa harara tare da buɗe murfin motar ta fita tana banko masa ƙofar kamar zata ɓalle ta, dan har saida yaɗan razana kaɗan da jin ƙarar ƙofar, hannu ya dunƙuli ya kaiwa sitiyarin ɗin motar duka yana me sakin ƙara kalmar ta ta ƙarshe ba ƙaramin tasiri tayi ba a zuciyar sa, maganar ta dake shi sosai, saidai tayi da Baban Baban sa, lalle Ameela dole ta gama rainasa, amma idan sun san wata basu basan wata ba, zai ɓullo musu ta bayan gida zasu gane basu da wayo.... Haka yayi ta kunce da warwara shi kaɗai saida ya kai tsawon wani loƙaci a haka kafin ya iya tayar da motar yabar wajen zuciyar sa cike da ta ƙai ci.

*Ameela*

Can inda take tunani ganin su ta nufa cikin wani restaurant dake gefen inda suka tsaya, tana shiga kam ta hango su suna kwasan waku, ita ma ƙarasawa tayi tayi join ɗin su daman plate ɗin ta yana gurin hana jiran ta dan haka ta hau ci kawai tana basu labarin yanda sukayi da commissionana, har suka gama cin abin cin suka tashi daga gurin tare da biyan kuɗin suka bar wajen.

Washe gari.....

Kamar kullum yauma haka suka shirya suka tafi makaranta duk wanda ya gan su sai yayi mamakin ganin nasu domin ana tunani yanzu suna sale a ƙulle amma kuma ko kwana basuyi ba a gansu sun dawo makaranta, amma saidai gulmar tasu dan babu wanda ya iya tunkarar su bare ya tambaye su yaji ya akai suka dawo.

Suna shiga duk suka rabu kowa yayi nasu department ɗin su.

"Kai amma fa sun burge ni wallahi amma ina tunanin ta ina zan fara yi musu magana karfa su wulaƙan tani kasan ba ɗauka zanyi ba kar a zo a samu matsala, ganin neman gira a rasa ido.

"Faheema bama abun da zai faru ni inaji ajiki na ba abun da zasu yi miki zasu karɓeki hannu bibbiyu saidai kawai kar ki bari su san ko ke ƴar waye sannan karki rinƙa zaƙe musu da yawa ki bisu a sannu sannu nasan zasu kaɓe ki amma fa sai kinyi haƙuri kin daure zamu samu abun da muke so.

"Tom yaya zandai yi kawai saboda kai, amma fa gaskiya ba komai zan jura ba zandai gwada mugani Allah dai ya rufa asiri kawai komai ya tafi yanda kake so, amma zanbi waɗancan ukun da naga sun shiga can dan naga kamar zasufi sauƙin kai musamman wannan me red kayan nan, (Beenish)

Jin wacce ta faɗa har saida ya ɗan lumshe idon sa jin kamar ra'ayin su yazo ɗaya dan shima yafi jin Beenish ɗin a cikin ransa, cikin zumuɗi yace; Yauwa nima na fahimci zata fi sauƙin kai, ita ce wacce tayi kukan nan har na nakaita office ɗina,

"Okay tom bari in wuce saura 3 minutes mu shiga lecture any way idan na fito ma haɗu zan duba inda suke zama, tana faɗar haka ta buɗe motar ta fito, shima fitowa yayi cikin sauri, nan sukayi sallama kowa yayi nasa guri....

*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*

*ƊAN IJJI'S HOUSE*

Alhaji ɗan ijje ne zaune a falon sa shida matayen su kowannen su yayi rafka uban tagumi tunda aka ɗauke Bilal komai ya tsayawa Alhaji ɗan ijje dan ya ɗorawa ɗan so bana wasa ba, ko abinci yaƙi ci, saboda baya cikin kwanciyar hankali, musamman idan ya tuno hoton ɗan nasa da aka turo musu ana mishi barazanar kashe shi yana cikin mawuya cin hali ga bindugu da suke saitin sa, gashi ance indai yana so ɗan sa ya dawo sai ya tura musu billoin talatin da biyar zasu bada ɗan shi kuwa yana tunanin ta ina zai fara basu kuɗin nan duk da yana dashi amma sunyi yawa, idan ya basu karayar arziƙi zata iya kamasa, saboda sai yacire rabi za kwata na kuɗin sa,

Miƙewa yayi daga inda yake a zaune yana ɗan tafiya kaɗan kaɗan yana tunanin mafita gurin wazai je ya taimaka masa, su haɗa kuɗin nan in yaso sai ya ci gaba da neman wasu ya haɗa ya biya,

Hajiya Khattume ce tace; Alhaji, ni kam in baka wata ƴar shawara mana, me zai hana kayiwa tsohon governor maganar mana nasan zai taimaka maka bazaiƙi baka wani abun ba, mussaman idan yaji halin da kake ciki, ina ganin ko bai baka ba zai iya sawa a binciko duk inda suke ko ɗan sane zai sa a gaba kadan dai ɗansa ba wasa zai iya lalubo su kuma idan ya lalubo su bazai musu ta daɗi ba, ko jin sunan shima a cikin lamarin zai iya sawa su tsorata su dawo dashi batare da sun cutar dashi ba, amma kayi tunanin kaga meye mafita,

Shiru yayi yana nazarin maganar ta kuma ta wani fanni yaji daɗin wannan shawar ta ta, "Gaskiya ne maganar ta hanyar sa kawai zan samu Bilal in ba haka ba nasan sai na shiga wani hali wallahi gaba ɗaya kaina ya ƙulle nama rasa wane kalar tunani zanyi a kai in samu mafita, take wani irin farin ciki ya lulluɓe sa kamar ance masa Bilal ya dawo, saboda murna baisan loƙacin da yaje ya mannawa Hajiya Khattume kiss ba a gaban Jannat, rufe ido tayi kawai tana watsa masa hararar da baisan tana yi ba, kuma ko inda take bai kalla ba, ya kuma juyawa yana ta farin ciki ya fice daga gidan dan yace baiga ta zama ba sai ya gansa a gaban tsohon governor hankalin sa zai kwanta.

Yana fita Jannar ta daka tsaki tare da miƙewa daga gurin tabar wajen, Hajiya Khattume kam binta da kallo tayi kawai tana jinjinawa lamarin ta, yanzu sai ta ƙullace ta ɗan wannan abun da me gidan yayi mata a gabanta sai kace ita tace yayi mata, itama taɓe baki tayi haɗi da maƙe kafaɗa, a fili tace to ba mijina bane koma me ya min, ita ma gurin tabari ta nufi hanyar kitchen..

*$$$$$$$$$$$$$$$$$$*

*COMMISSIONA*

Can ofishin ƴan sandar ya koma tare da gargaɗi kowa da jan kunne akan abun da suka gani game da abun da yafaru tsakanin sa da ƴan matan, ya hana kowa ɗaga maganar da gargaɗi me ƙarfi, yace duk wanda yasake maganar ta fito a bakin aikin sa, hakan kwa babu wanda yayi gigin tunanin zai bari maganar ta fito, haka yagama jan kunnen su sannan ya nufi asibiti inda aka kwatar da ɗan da suka ɓallawa hannu.

Tunda ya shiga asibitin ake gaida shi saboda sanin matsayin da yake dashi, Saida sukaje bakin ward ɗin sannan sauran ƴan sandan suka tsaya abakin ƙofar ɗakin da zai shiga, shi kuma ya ƙarasa shiga.

"Yana shiga ya tsaya yana kallon su yaron ne a zaune ga hannun da aka naɗe masa da bandeji, sai wata mata dake basa abinci a baki, bisa ga dukkan alamu kamar mahaifiyar sa ce dan suna ɗan kama da ita, sai wata yarinya dake tsaye a gefen su, itace ta ɗago ta kalli mahaifin na su, dan duk basu san da shigowar sa ba, da sauri tace; Abba hakan yasa mahaifiyar tasu sa da ɗan saurayin suka ɗago suna kallon bakin ƙofar.

Saida ya sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya sannan ya iya takawa zuwa inda suke, gaida shi sukayi gana ɗayan su, sannan matar ta ɗora da cewa; "Abban su ya akayi da yaran da aka kama, ina fatan dai za'a ɓallawa yarinyar da ta ɓallasa su kuma sauran ayi musu hukunci me ƙarfi da zai hanasu ƙara yiwa wani haka bare kuma zuri'ar da ta shafe ka.

Yarinyar ce tace; "Gaskiya dai Abba dan bazamu barsu dan ko anyi musu hukunci in suka fito sai na kuma ɗaukar wa yayana fansa dan bazan ƙyale su ba nima,

Maganar mahaifiyar tasu bata dame sa ba kamar yanda yaji batun ƴar tasa, tunda ta fara maganar yake binta da kallo yana jinjina kai a ransa yana ƙara maimaita kalmar ta ta kusan ƙarshe, fansa, fansa sai na ɗau fansa zagayawa yayi ta inda take sannan ya riƙo hannun ta, ƙasa yayi da murya sannan ya ce; Kinsan dai meye aiki na, ko kuma duk ne ɗaukan hukunci da kansa shima me laifi yake zama dan haka kar na kuma jin wannan furucin a bakin ki, ɗaukar hukunci a dakan ka ya saɓa shari'ah bare ma kuma an riga anyi musu hukunci kizo ki ƙara ɗauka, kinga nema zaki zama me laifi, ko kina so kema a sakaki a sale?

Da sauri ta girgiza kai tana tutturo baki dan ranta baiso ba da dakatar da ita ɗin da yayi, amma duk da haka ko bata ɗauki mataki ba sai tasan abun da zatayi musu batare da kowa yasan itace tayi ba.

Shi kuma yayi mata hakane saboda halin su da yasani yasan ko hauka suke bata isa ta iya ɗaukar fansa a kan su ba, kawai zata kuma jefa sa cikin matsala ne tsakanin sa da su, shiyasa gwanda yayiwa tifkar hanci tun wuri baya so familyn sa su saka ƙafar wando ɗaya da yaran nan dan mugayen mutane ne riski ne da su, shi baima san me ya kawo su garin ba, baitaɓa tunanin zasu zo har inda yake ba, gashi kuma suna ƙoƙarin takura rayuwar sa....

"Abban su.!"

Matar ta kirasa hakan ya katse tunanin da yake, zuba mata ido yayi yana kallon ta batare da yace komai ba.

Cikin yanayin damuwa sosai tace; Wai har yanzu ba a gano inda suka kai min Zaid ba haka zamu zauna muna zuba, ya kake so inyi da rayuwa ta wancan sun ɗauke sa wannan sun karyasa wai me hakan yake nufi meye haɗin su da ƴaƴa na, me suka tsare musu da zasu ringayi min haka ta kara sa maganar ta ɗan matsar ƙwalla, cike da damuwa.

Dafe kansa yayi da yaji ya fara sara masa dan shi tunanin sa ya fara tsayawa da matsayin da komai amma wasu suna ƙoƙarin maida shi ƙaramin mutum, saida ya shaƙi iska sannan ya furzar da me zafi yana cije baki, sannan ya ce; ba haka bane kar kiyi tunanin laifin kine ko laifin su, shi wannan laifin sa ne tunda shi yaci zarafin ta tunda ya mare ta shiyasa suma sukayi masa haka, shi kuma Zaid basu suka ɗauke sa ba, yaran basu isa ɗaukar mutum ba, kawai dai basaji idan an taɓa ɗaya daga cikin su, amma ɗaukar Zaid baida alaƙa da su, wasu ne daban suka ɗauke sa kuma kinga ai bashi kaɗai aka dauke ba harda ɗan gidan Alhaji ɗan Ijje, zai iya yiyuwa sunyi mana hakane saboda sunga muna dashi ko kuma abokan adawa dan kana rayuwar ka baka shiga ta kowa ba amma zaka tsokane wa wasu ido da basu da burin da ya wuce suga sun ƙuntata maka rayuwa, amma dai kiyi haƙuri har yanzu ana nan ana bincike matsalar kuma daman basuyi waya ba bare abi diddigin inda suke saidai muyi ta addu'a Allah ya kare su a duk inda suke daga shi har ɗayan, Allah ya bayyana mana su.

"Ameen tace yana ƙara goge hawayen da ya cika mata ido taf,

"Kai kuma na dawo gare ka ya maida kallon sa gare shi, sunkuyar da kansa yayi saboda duk tsiyayar da yake tsulawa baya bari mahaifin sa, yasani saboda yana jin tsoron sa,

"NA'EEM" kar kayi tunani bansan me kake ba rabuwa nake dakai kawai idan baka shiga hankalin ka sai nayi maganin ka, ni da kaina zan kuma ɓalla ɗayan hannun, akan kawai ta bugeka bata sani ba, dan me yasa zaka ɗaga hannu ka mare ta wannan ai shashanci ne da shirme, daga yau bakai ba su ka fita a harkar su kar naji wani abun ya kuma tasowa magana ta ƙare ankashe ta tun ɗazu kaji ni?

Jinjina masa kai yayi alamun eh amma a ransa ba haka bane dan acike yake dasu baya jin zai iya rabuwa dasu.

Shima mahaifin na sa daɗi yaji aransa dan yana ganin kamar ya kawo ƙarshen abun dan bayaso maganar taci gaba da tafiya.....✍️

🫣🫣🫣🫣 Wlh kunyar ku nake ji kuyi haƙuri in sha Allah zan faran ta muku a satin nan dan har weekend ma sai nayi muku sorry please
[3/5, 11:46 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________


*_episode 10💧_*


💧💦محمدالرسوالله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

*Alhaji ɗan Ijje*

___Tun yana kan hanya ya kira number sa yasanar masa da zuwan sa, dan haka tun kan ya ƙaraso aka sanar da masu gadin gidan, bai wani tsaya ba yana zuwa suka basa hanya, ya wuce ciki, gida ne tafkeken gaske me girman gaske wanda yaci uwar na Alhaji Ɗan Ijje a girma da haɗuwa da komai, wajen gidan da cikin gidan duk cike yake da matakan tsaro sun zagaye ko ina na cikin gidan, wasu harda bindigu a hannun su irin zabga zabgan nan,

Motar sa na tsayawa a wata farfajiya, wani daga cikin masu tsaron gidan yazo da sauri ya buɗe masa ƙofa, yana fitowa wanda ya buɗe masa motar yayi yana yi masa iso yana nuna masa inda zaiyi, sai kuma wasu mutum biyu a bayan sa suna mara masa baya, saida sukayi tafiyar kamar minti 3 sannan suka ƙaraso bakin wata ƙofa me ɗan faɗi suka buɗe suka shiga wani dogon corridor suka kuma miƙewa ba wata tafiya me tsawo sannan sukayi kwana tun anyi kwanar sauran biyun suka tsaya daga gurin da ɗayan suka ƙarasa bakin wata ƙofa nocking yayi sannan ya matsa daga gurin tare da juyawa ya matsa can nesa dashi,

A hankali a ka buɗe ƙofar wata mata ce ta buɗe tare da sunkuyar da kai ƙasa tace barka da zuwa bismillah ta faɗa tana basa hanya, shiga yayi tare da yin sallama ta amsa masa, tare da barin wajen, cikin tanƙameman falon ya ƙarasa ya samu ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman royal chairs ɗin da suka gaji da kyau ya samu ya zauna, babu kowa a falon sai kan center table ɗin da aka cika da kayan marmari, shiru yayi yana ɗan bin falon
End Ads