x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 43 - SU WAYE SU

  • 126001 words
  • 129000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 198

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
wahala zaku ci baza ku taɓa iya fita daga gidan nan, zaifi muku kyau da ku koma ɗin, amma in kunji shawarata in ba haka ba kuma jiki magayi.

Yana kaiwa nan yaja karnukan sa suka tafi.

Babu wanda ya samu damar tashi akan loƙaci saima ƙara bajewa da sukayi suka kwanta agun, Salma ce ta kalli Bilal dake gefen ta, taga yanda yake ta faman sharar hawaye, yana gogewa da hannun kamar wani ƙaramin yaro bata san loƙacin da ta kwashe da dariya ba tana nuna sa da yatsa tare da tashi zaune,

Suma tashi sukayi zaune suna taya ta dariyar duk da basu san me takeyiwa dariyar, Bilal kam da yasan dashi take sai yayi saurin haɗe rai cike da jin haushin ta.

"Dan Allah ku kalli wannan ragon ko ni banyi kukan da yake ba, sai kace mace amma kaidai rangwanta tayi maka yawa abun kuka baya maka wahala.

Zaid yace kaɗan ma kika gani indai wannan yaronne babu abun da ya iya in banda bacci.

Bilal najin su bai tanka musu ba saima miƙewa da yayi ya tashi ya zare igiyar dake ƙafarsa aikwa gurin har yayi ja, yana ganin yanda gurin yayi yaji kamar ya kuma sakin wani kukan amma ganin yanda suke masa yasa ya juya kawai ya fara tafiya yana wani haɗe rai.

Da sauri Salma ta tashi itama cikin sauri tabi bayan sa tana cewa haba ɗan Boy sorry na dena tsaya mu tafi tare, tana tafiyar kuma still tana yi masa dariya bai kulata ba yaci gaba da tafiya,

Su Zaida ma tashi sukayi suka bi bayan su da sauri harda ɗan gudu- gudun su, dan har sun ɗanyi musu nisa.

Salma tana zuwa ta riƙo hannun sa tace; "sorry fa nace maza, kaiɗinne kake abun mata, yanzu daka haɗe rai har ka koma namiji wallai.

Ƙwace hannun sa yayi ƙoƙarin yi saita ta riƙesa sosai tace "Allah bazan sake ka ba salon kaje ka ɓata Hajja Mama ta huce akanmu tunda ance tafi ji dakai, ni lallaɓaka zanyi wallahi ko ta soni nima.

Bai kuma yunƙurin ƙwacewa ba ya rabu da ita tana ta zuba shidai tafiyar sa kawai yake.

Su Zaida ci gaba sukayi da kunna sa suna tsokanar sa, musamman Zaida ya saba daman, saida suka gama yi masa sannan suka dawo kan maganar fitowar tasu sunayi suna dariya suna maida yanda akai, Bilal ma a loƙacin ya saka baki saidai shi baiyi dariyar ba, shi daman baifiye yi ba, indai ba a wajen mahaifinsa yake ba, anan zakaga dariyar sa sosai, duk tafiyar da suke Salma na riƙe da hannun sa.

Tun suna tafiyar cikin daɗi har suka fara gajiya gashi basu kusa zuwa ba.

Suna cikin tafiya Bilal ya tsaya da tafiyar tare da marairaice fuska yace nifa wallahi bazan iya tafiya ba, na gaji bantaɓa irin wannan tafiyar ba.

Duk tsayawa sukayi shima Zaida yace to da waye ya taɓa yin irintar muma duk babu wanda ya taɓa yi ɗin, da haka zaka daure yaro duk bama kai kaja mana ba, muna zaman mu lafiya ga abun da ka jawo mana, da baka buɗe ƙofar ba ai da tuni hakan bata faru ba.

Faheema tace "eh da laifin sa amma muma da namu laifin me yasa bamuyi tunani ba muka biye masa yanzu ai gashi abun da ya faru, ni wallahi ma bansan ta inda zamu koma inda muka fito ba.

Dariya Salma tayi tace "ta inda muka fito tanan zamu koma ko zamu kwana a hanya.

Duk surutan su bai damu Bilal ba saima tsugunnawa da tayi agun da yaji hakan bai masaba sai ya zauna kawai yana miƙe ƙafa yana kallon ƙafar tashi da yaga duk ta kumbura.

"Ɗan Boy wai meye hakan ka tashi mutafi dan Allah.

Yatsina fuska yayi kamar zai fashe yace "wallahi da gaske nake bazan iyaba kinga fa yanda ƙafata tayi gashi sai zafi take.

"Faheema tace "to pha wata sabuwa yanzu ya kake so ayi kenan anan zamu barka ka taho daga baya ko kuwa.

Zaid yace "eh hakan za'ayi mana, da tafiya a gabanmu amma mu zauna ai wannan hutun jaki da kaya zamuyi gwanda kawai mu ƙarasa, idan munje ma samu mu huta gaba ɗaya.

Salma ce ta tsugunna a gaban sa tace "kayi haƙuri muje kaga bazasu jira mu ba, indai ta nice zan jiraka ka huta, kuma kaga yamma nayi kar dare yayi mana a hanya mu kasa gane inda zamu koma, gashi karnukan nan kar su kuma dawowa.

"Wai baku da ido ne bakuga me ƙafata tayi ba nace muku bazan iya ba bazan iya ba amma kunƙi yarda, ku bari idan na huta wataƙil in iya takawa.

Tsaye sukai kowa baki sake suna kallon sa, basu san ma ya zasuyi da shi ba,

Zaida ne yayi gaba yace "nidai kunga tafiyata idan zaku jirasa sai ku zauna, dan bazan bari yamma tayi ba ina wajennan kun mantama tafiyar dake cikin gidan kafin mu fito saida muka daɗe.

Faheema da Salma duk yanda suka so da Bilal ya tashi amma ya ƙi sai haƙuara sukayi suma suka bi bayan Zaid, a tunanin su idan yaga sunyi gaba ai dole ya tashi ya biyo su, amma har suka ɗanyi nisa baida niyar tashi saima kuka da yafarayi dan dagasken yake bazai iya tashi ba.

Salma ce "gaskiya bai kamata mu tafi mubar sa ba tunda kukaga haka dole kasawar yayi, idan muka koma babu shi mu kanmu bazamu ji daɗi ba, kuma komai ya faru dashi ɗayar matar zata iya ɗaukar mataki akanmu, duk da gaba ɗayanmu babu wanda yayi kalar wahala ko saba irin tafiyar amma shiɗin yafi mu rangwanta mu zamu iya finsa dauriya bamu san waye shi ba bamu san wacce irin rayuwa ya taso ba, dan Allah mu tsaya mu samu mafita akan hakan kunji dan Allah.

Suma daman duk tausayin nashi sukaji musamman da suka fara jiyo kukan sa, Zaid ma kuma yasan halin shi da rashin juriya babu abun da ya iya na ƙarfi ko wahala, hakan yasa suka sauya tunani, sukayi na'am da shawarar Salma suka juyo, amma duk da haka suna tafiya suna mita.

Yanda suka barsa haka suka same ya miƙe ƙafafu yana ta dirzar kuka sai yau yake ta tuna abubuwa da dama, yaji kewar mahaifinsa na taso masa sosai, kukan sa yake bilhaƙi ko tunanin mafita ma bayayi.

Suna zuwa sai ya kuma daɗawa kukan nasa volume, yana kawar da kai gefe shi a dole sun bashi haushi da suka tafi suka barsa.

Duk sunji tasauyinsa amma abun da yayi saida ya basu dariya, Salma ce ta cire ɗan kwallin kanta ta tsugunna tana bashi haƙuri sannan ta kamo fuskarsa ta shiga goge masa hawayen da duk ya ɓata fuskar tasa har tayi ja idon sa ya kumbura.

"Yaya Bilal yanzu ya kake so ayi duk so kake mu zauna sai sanda ka gama ko kuwa ɗaukar ka zamuyi.

Da sauri ya ɗago ya kalle sa jin wai ko ɗaukar sa zasuyi da girman da taya zasu iya ɗaukar sa, a fili kuma sai yace "ba tafiyar ku kukayi ba, to ku tafi mana ni nace ku dawo.

Sun san kawai faɗe yake amma ƙarya yake yace so yake su tafi,

Faheema ce ta zauna kusa da ƙafafunsa hannu ta ɗora ta danna ƙafar da ƙarfi, take ya saki ƴar ƙaramar ƙara, yana riƙe hannun ta.

"Ka tsaya mana idan aka ɗan matsa maka zakaji sauƙin ta sai ka lallaɓa mu ƙarasa.

Salma tace "eh Boy ka bari a matsa maka bari inyi maka ɗayar zakaji sauƙi sosai Sa'a mu tafi.

Shiru yayi baice musu komai ba suka shiga mammatsa masa ƙafar, tun yana jin zafi kuma har ya fara jin ba zafin.

Zaid kam gefe ya koma ya zauna ya zuba musu ido.

Sunkai wajen minti ashirin suna yi masa sannan suka barshi haka, suka ce ya gwada miƙewa, sosai yaji raɗaɗin ya tafi yana miƙewa ma yaji ya iya tsayawa.

A hankali ya furta musu "thanks.

Ɗan murmushi kawai sukayi masa sannan Salma ta kuma riƙo hannun sa suka shiga tafiya.

Zaid kam taɓe baki yayi yana cewa; "rago kawai.

Harara Bilal ya jefa masa batare da yace dashi komai ba suka ci gaba da tafiya....


$$$$$$$$$$$$$$$$$$$

*BULAMA*

Suna ƙarasawa cikin falon yacewa Commissioner ya shiga ɗayan falon bari yaje ya kaita ɗaki ya dawo.

Shidai bin duk abun da yace yayi yake, haka ya shiga falon yayi zaune yana tunani abun duniya duk ya isheshi yauɗinna, ya daɗe zaune cikin falon kafin Bulama ya shigo ciki, guri ya samu ya zauna yana facingvɗin shi fuskar sa ɗauke da murmushi da kamar ɗabi'ar sace yawan yin murumishi dan ko mugunta zaiyi sai yayi wannan murmushin a jikin sa yake.

"Commissioner da kansa meke tafe dakai Allah ya taimake ka ina cikin garin dan jiya jiya na shigo.

Saida Commissioner ya ɗan numfasa kafin yace "wai sun kore ni daga aiki yau suke aiko min da takarda harda gargaɗin in banmu su gida sun ban 24 hours.

Murmushin dai Bulama ya kuma saki me ƙayatarwa dan har haƙoransa na bayyana, yana jinjina kai yace to kuma shine me? Shine zaka ɗaga hankalin ka, ni daman tun farko nakyi maka sha'awar aikin nan ba dande ka nace yasa na shiga ciki aka baka, ga ayyuka nan kala kala da zaka samu kuɗi fiye da wannan da zasu biya ka, ƙarewa ma a gidan su kake zaune, yanzu kuma idan ta kasance suka kore ka saika koma ina, wannan gangancin ne Malam Khamis nifa da zaka bi ta shawarata kar ka kuma ɗaga murya akan maganar ka banmusu ka shigo sana'ar mu a dama dakai zaka samu alkhairi kaine kaƙi don kayi kuɗi tuntuni amma da yanzu kafin haka, amma ka tsaya kana fama da aiki a ƙarƙashin wani haba Khamis, amma zan baka loƙaci kayi tunani akai idan kuma kaga can ɗin kafi so kayi min magana zansa a mayar dakai.

Nauyayyiyar ajiyar zuciya commissioner ya sauke cike da nazarin maganar da Bulama yace masa, shi bawai kuɗinne baya so ba, yana so amma tasu harkar ce kamar bazai iyaba, baya so ya fiya wasa da rayukan mutane su kuma abun su kenan yana jin tsoron ranar da asirin su zai tonu azo a haɗa dashi, su basu da iyalai shikam ƴaƴan sane abun ji, ya tabba sace ɗansa da akayi yana da alaƙa da zargin sa yana cikin su shi yasan hakan ce zata faru shiyasa ma yabar lamarin da tunanin sa masu zaman kansu ne amma yasan bamuyi haka ba, loƙaci guda zasuyi maka abun da kayi musu ba wani jan loƙaci dan basu da tsoro, shiyasa ya daina zargin su, amma rashin sanin su waye suka yi hakan na matuƙar ɗaga masa hankali...

Taɓasan da Bulama yayi ne yasa shi dawowa cikin hayyacin sa, yana mai maida sunansa gare sa.

"Khamis 1tunanin me kake yi ne haka ina magana ko kina bakayi.

Murmushi ya ƙaƙalo ya aza a fuskar sa, tare da girgiza, yace "ina tunanin da kace nayi ne amma dai kaban loƙaci to amma inda matsalar take da akace nan da 24 hours in tashi idan na tashi bansan inda zanyi ba kasan ba wani planing ne da ni ba, ban ajje komai ba, a samu kawai a biyawa kai buƙata.

"Kar ka damu da wannan indai gida ne ka zaɓi duk wanda yayi maka a cikin nawa ka ɗauka na baka kyauta.

Cikin jin daɗi yace "gaskiya naji daɗi Alhaji nagode kuma sosai, sai yanzu naji hankalina ya ɗan kwanta, saidai akwai wani abu da zanyi akwai wasu ƴan mata da muka samu saɓani to sune suke yawan dagulan lissafi ina raba ɗayan biyu ma yanzu haka da haɗin kansu wajen korar nan tawa, dan dama sunce sai sun sa an koreni da aikin da na dogara dashi, saboda ɗan wani saɓani da muka samu da su tunda daɗewa.

"Ban fahimce ka ba, bansan inda maganar ka ta dosa ba, fahimtar dani, nan ya kuma yi masa bayanin su, yanda wasu abubuwan suka faru a tsakanin su saidai bai gaya masa asalin haɗuwar tasu ba.

"Ni banga abun wani tayar da hankali akan su ba, suna mata har zaka bari sufi ƙarfin ka, haba mana kayi maganin su kawai loƙaci ɗaya.

Shiru commissioner yayi na ɗan loƙaci kafin yace "amma akwai matsala fa, nayi mamakin ganin ka da wannan yarinyar, kuma tana ɗaya daga cikin ƴan matan da nake magana.

Sai loƙacin ma Bulama ya gama gane su tabbas su yake nufi kenan harda masoyiyyar sa aikwa bai isaba dole ya haƙura ma da case ɗin akansu gaba ɗaya.

"Ya kake ganin za'ayi yanzu? Commissioner ya tamabayata.

"Hmm babbar magana kenan da matsala to amma fa abun da baka sani ba wannan ba itace asalin wacce nake so ba, wannan wata yarinyar uban gida nace da ya daɗe da mutuwa shine ta manne min da ƙyar na yakice ta na gudu, garin neman waccen kuma na haɗu da ita, amma ba wani komawa zamuyi da ita ba zan aikata inda na aika ubanta, dan gangancine ka kashe muciji baka sare kansa ba, dole sai ta tafi itama, daman akwai wasu takaddu danake son tayi signing loƙacin batayi ba tana ƙarama, da zarar tayi min zan kawar da ita, ita kuma waccen so nake in ɗan ƙarama ta loƙaci kafin ingama shirya duk wani abu da zan shirya in wuce da ita na angwamce da amarya ta.

Mamakine ya kama commissioner lalle Bulama bazai taɓa daina halinsa ba, kashe mutum ba komai bane a gunsa, lalle dole ya raba hanya dashi tunkan loƙaci bai ƙure masa ba, yana iya shegen sa sosai da latse latsen ƴan mata kuɗinsa ma duk ana suke ƙarewa, amma shi bai iya ɗaukan ran mutum ba, yana tsoron wannan abun shiyasa tun wuri yaƙi sakin jiki da su Bulama kawai dai suna bashi cin hanci suna fakewa dashi ta wani wajen a matsayin sa na me muƙami, amma baya ga haka baya son sauran halayyar su.

Amma sai ya maze a fili yace; "gaskiya ne wannan, dole wataran zata gano gaskiya hakan kuma bazaizo da kyau ba, dan wallahi team ɗin nan nasu basa barin ta kwana musamman ita tana iya gwarawa da maza, riƙo ɗaya tayiwa ɗana ta karya masa hannu haka inaji ina gani na haƙura na rabu dasu, bakaga yanda suke faɗa da ƴan sanda ba.

Murmushi Bulama yayi yace "harkar ai bata ƙarfi bace za'a nuna musu wayon dula a daji, babba babbane, bayau aka haifemu ba iyayen su ne, dan haka kar ka damu ka barmin komai a hannuna kawai, yanzu kaje kayi tunani zuwa gobe, zan koma ciki. Yana faɗar haka ya miƙe tsaye tare da miƙa masa hannu suka gaisa ya fita baima jira tashi fitar ba, shi ya fara fita.

Hakannan commissioner yaji jikin shi yayi sanyi a haka ya tashi yana tafiya yana tunane tunane har ya shiga mota ya bar gidan...


$$$$$$$$$$$$$$$$$

*ALGERIA*

___Su Hajja Mama sun sauka lafiya a ƙasar Algeria cikin dare, direct hotel suka wuce saida suka kwana da safe sannan suka fita suka sissiyi kayyakin da zasu buƙata da kuma kayan sawa irin na ƴan ƙasar, barin koman su suka yi a cikin hotel ɗin dan sai sun fara shiga gidan a haka, sannan saida ta gyara girar ta da ɗaure kanta sai ta samu wani abu ta ɗan yanka gefen idon ta sannan ta shafa wani baƙin abu take dai kamannin ta suka sauya bazaka taɓa cewa ita bace, indai ba mugun sani kayi mata ba.

Wajan ƙarfe huɗu suka isa bakin wani babban gida irin gine ginen garin, suna zuwa ita ta sauka daga motar shi kuma suka juya da motar za'a kaisa wajen wata unguwar daban, Hajja Mama tayi wata kalar shiga irin ta talakawan garin, daman tasan garin sosai ta taɓa zama a ƙasar shiyasa gurare da yaren su bai mata wahala ba.

Tana zuwa suka gaisa da me gadin gidan tace masa tana son ayi mata magana da Maha ƴar aikin gidan, duk cikin yaren suke maganar, taci sa'a kuwa me gadin baida wulaƙanci yace ta shigo ta tsaya agun sa zai shiga ya faɗa mata, daɗi ne ya kama Hajja Mama jinta a cikin gidan, bin gidan ta shiga da kallo babba ne sosai yana da part guda uku duk a kusan manne suke daga wajen, amma kuma ta ciki kamar rufin su ɗaya, main ƙofar shiga guda ɗaya ce.

Tana gurin taji ana horn ƴar ƙaramar ƙofa ta buɗe dan ganin ko waye, gannin wata jibgegiyar mota yasa ta saki murmushin gefen baki tare da saurin komawa sai ta shiga buɗe musu babban gate ɗin.

Tana buɗewa aka danno motar ciki da gudu saura kaɗanma a bugeta tayi saurin matsawa tana me mamakin meyin wannan tuƙin kamar yana filin tsere zai wani shigo da mota a haka yanzu da ta buge taba.

Saurin maida hankalin ta tayi ta rufe gate tana daga gurin tana hangen inda motar ta tsaya, tana gurin taga wata budurwa ta fito daga gaban motar sannan wasu maza biyu suka fito daga bayan motar juyowa tayi tana kallon inda Hajja Mama take da sauri Hajja Mama ta sunkuyar da kanta, budurwar ce ta shiga takowa zuwa inda take tana zuwa ta jefa mata wani zagi da yaren su, tare da tambayar ta wace ce ita.

Kafin Hajja Mama ta bata amsa tuni ta ta ɗauke fuskar ta da mari da yatsa ta shiga nunata akan me yasa tabari suka daɗe a waje bata buɗe ba.

Mamaki ne ya kama Hajja Mama daga zuwanta memakonma ta tambayi ina me gadin tundade tasan mata basa gadi amma shine zatayi mata haka tabb sai ta kuma shiri kenan wai daga zuwanta wannan yarinyar zata mare ta lalle da sake yau badan da dalili ba da yarinyar nan ta gane kuren ta, amma tayi mata uzuri.

Tana cikin yi mata masifar, gate man ɗin ya ƙaraso cikin sauri jikin sa na ɓari, ya shiga bata
End Ads