x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - SU WAYE SU

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 144

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
saboda ita ƙatuwar cikin tasu beyerabiya ce gata ƙatuwa ga ƙarfin tsiya da take dashi....

Beenish ce tayi ƴar dariya tace Allah ya shirye ki Zeeee wanda baisan kiba ya shiga uku.

"Wallahi ko ɗaya mutum bazai shiga ba bare har uku, tana maganar tana wani irin tafiya kai kace wajen biki take, har ta kusa fita daga wajen Ameela tace "bakiji ba?

Cikin wani irin salo ta juyo tana fari da ido tace ko baki faɗa ba nasani kinsan inkiyar tawa tunda na rufe fuska ai bamaƙi taku me kyau ba, kunsan ko ina muke akwai iya taku,

Ƙatuwar cikin su tace "ai munsani basai kin faɗa ba,

Juyawa ta ƙarayi tace to ke ya kika ganni gaba da baya komai daidai, duk da acikin babbar rigace amma hakan ma wanka ne,

Ameela ce ta shiga tafawa tanayi mata jinjina da babbar yatsar ta......

Juyawa tayi da niyar tafiya sai kawai ta kuma tsayawa tare da juyowa tana kallon Aunty Babba tace ƙawar yimin inyi miki kyaut...

Tun kan ta rufe baki ma Ameela ta shiga cewa "ZEE BARAZANA ZEE FASHION KO BA KUƊI AKWAI IYA TUKU.....

"Bare ma akwai komai tabata amsa ta na ci gaba da takun ta ta fice daga gurin...

Aunty Babba tace "Zee..! Zee..! hmm saidai fatan shiriya.

Ameela tace kunga ta fita dan na matsu mu koma gida wallahi zanyi baƙo,

Harar ta sukayi a kusan tare su ka ce; "A'a kin mata baƙi zakiyi da yawa ba baƙo ba,

Daga nan ba ɓata loƙaci, kamar yanda kuwa Barazana tace haka kuwa sukayi Aunty Babba ce ta ɗaga sa suka fita dashi daga gurin cikin motar sa sukaje suka buɗe baya suka sakasa Aunty Babba ce ta shiga gaban motar sa sai Ameela a gefenta ita kuma Beenish taje wajen ƴan rigima da ta shiga, Barazana ce zata tuƙasu Babyn baby kam tunda ta shiga baya take ta faman kuka koda Zee ɗin tazo ƙin kulata tayi,

A guje suka bar geto area ɗin da suka shigo daɗin tama babu mutane da yawa bayan sun fita daga cikin unguwar suka sami can wajen da ba mutane a gun, sannan sukayi parking motocin nasu, su Ameela ne suka fito daga tasa motar sannan suka rufe sa aciki tare da jefa masa wayar sa kan cinyar sa, suka bar wajen motar suka koma wajen tasu motar, basu damu da hannun sa dake ƙulle ba kawai sukayi tafiyar su, suka bar sa agun,

Ji yayi kamar yayi hauka ga bakin sa da yake a ƙulle ga hannunwan sa a ƙulle kuma ko kaya babu a jikin sa, sunci masa mutuncin da tunda yake a rayuwar sa babu wanda ya taɓa yi masa makamancin sa, abun da yake ƙara kona masa rai shine idan ya tuna mata ne sukayi masa haka sai yaji ya tsani kansa ma gaba ɗaya, zaune yayi a cikin motar shi kaɗai yana ta tunanin mafita dan ko wayar sa bazai iya ɗauka ba bare ya kira gida azo a ɗauke shi.........✍️

_*Ƴan WhatsApp me son group yayi min magana in saka sa dan bazan ringa share ɗin sa tare da link ba saboda bana son mutane su ringayi join batare da karantawa zasu yi ba, gwanda duk wanda yasan karantawa zai yi sai yayi magana ta number ta 08124226526*_

*Ƴan facebook kuma kuyi searching ɗin Su waye su group ku shiga anan zan ringayi kullum, dan gaskiya ba kullum zan ringa posting group group ba sai lkcn da na samu free time.*

*Yawan comment yawan typing idan anaso a ringa ganin update akan loƙaci kuma me yawa to nima sai naga an fara comment in bahaka ba kuma nima sai sanda aka ganni*

Ina fa ƙara faɗa muku tafiyar ta dabance yanzu duk a makafi kuke babu wanda zai gane hanya yanzu sai nayi muku jagora zuwa guri me nisa,

Amma idan kai na dabanne kamar ni to idanunka zasu buɗe da wuri mutafi tare da kai cikin littafi nadaban,

*Zee barazana zee fashion ko ba kuɗi a kwai iya taku.....Haka naji ance nima amma dai banyarda ba ko hakane zainabobi?*

My WhatsApp number 08124226526

Please comment and share, Saboda Allah
[3/5, 11:28 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________


*_episode 3💧_*


💧💦محمدالرسوالله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

"A fusace ya miƙe tsaye tare da dukan tebur ɗin dake gaban sa, da ƙarfi ya furta "BILAL..! Never......!!!

Gaba ɗaya mutanen dake gefe gefen sa suma suka muƙe tsaye suna me duban wanda yayi maganar,

"Sir what happen..?? Me yasamu Bilal ɗin bashida lafiya ne?

Ɗagowa yayi yana kallon su yama manta a inda yake, cikin ɗan kiɗemewa tare da fara fita hayyacin sa gaba ɗaya ba nutsuwa a tattare dashi,

Glass ɗin idon sa ya ɗauka yasaka tare da gyara zaman hular kansa, sannan yace "Zama ya ƙare zanneme ku gobe, So, u can go, yayi maganar yana barin wajen yayi waje, ya kusan fita kenan wani yace "Amma sir kamar.....

Juyowa yayi a fusace yace "Amma me? Eh nace zannemeku idan kuma hakan beyiba kowa sai yakama gabansa buƙatar kuce batawa ba, danma kunci Sa'a mtssww ya ja tsaki yana ƙarasa fita daga gurin,

"Oh Allah gamu gare ka wai ɓarawo a hannun mata, ƊAN IJJE baida tausayi wallahi, mutumin nan yagama raina mana hankali wallahi,

"Salisu kade iya bakinka dan maganar nan zata iya komawa kunnen sa kasan shidai kamar me aljanu haka yake wajen jin magana,

"Mtsww ai saidai wani munafukin ya faɗa masa amma babu ta yanda zaiji kuma koma yaji aidai bai isa yayi min abun da Allah beyi min ba, ni wallahi ma na kusa dena zuwa wajen sa, ku da baku da zuciya sai kuyi tazama ana wulaƙan taku mtsw yana kaiwa nan yana ƙafafun sa ya fice daga wajen shima yana ta faman huhhura hanci,

Babu wanda ya ƙara yin magana acikin su suma sukaja ƴan matan ƙafafun su suka fice daga gurin, suna me jinjina ƙarfin hali irin na Salisu ko ɗar bayajin tsoron Ɗan ijje basu san me yasaba kodan baitaɓa kamasa da irin waɗannan maganganun ba ne ya hukuntashi shiyasa yake faɗar duk abun da ya ga dama a bayan idon sa,

************************

"Mutumin da ya fito daga gurin yana fitowa ya nufi inda motar sa take buɗewa yayi ya shiga tare da jan motar da gudun tsinya yabar unguwar cikin matsanancin ɓacin rai.......

Baizarce ko ina ba sai ƊAN IJJE'S house, tunkan yaƙarasa bakin gate ya fara doka horn me ƙarfin gaske, saura kaɗan yabi takan wasu ƴan mata guda biyu dake gefe suna tafiya Allah ya kare su sukayi saurin matsawa ɗaya har faɗuwa tayi a ƙasa saboda sun tsorata,

"Wayyo sannu sister Allah yasa dai bakiji ciwo ba, miƙewa tayi tana karkaɗe jikin ta harda ɗan guntun hawayen ta tace "SIYAMA waye wannan dan Allah yake irin wannan gudun acikin unguwa baya tsoron yayi kisan kai yanzu da bamu matsa bafa takan mu yake shirin bi to wallahi Allah ya isa dan bazan yafe masa ba, wannan ai shiga haƙƙin ɗan adam ne,

"Wallahi haka yake me wannan gidanne babban mutum dashi amma yana abu kamar ƙaramin yaro daga shi har yaransa babu wanda suke ɗauka da mutunci kowa bi takan sa suke saboda suna taƙama da kuɗin da Allah yabasu, bakiga yanda sukeyiwa wata ƙawata dake aiki a gidan ba ƙaramin yaro ya iya bura'uba acikin gidan, gashi bata isa tabar gidan ba inadai suka ɗauke ka aiki ba ƙaramin abune zai fito dakai daga cikin gidan ba,

"Ke Siyama..!! kamar ya bazai bar gidan ba?

Hmm kedai bari kawai idan kinajin labarin cikin gidannan zaki sha mamaki kisha mamaki kisha al'ajabi sannan kisha dariya....

"Dan Allah mu shiga ni na yarda zanyi musu aikin indai zasu ɗauke ni da yaseen sai na nakasasu,

"SHA'IBA dan Allah mubar wannan maganar anan gurin dan bamai yiyuwa bane,

Suna tafiya suna ta surutun su har suka ƙaraso waje Jen gate ɗin dan shi kuwa tuni ya daɗe da shigewa ciki,

Sosai ta tsaya tana bin gidan da kallo, sannnan ta kalli ƙawar tata tace "Siyama shiga gidan nan kamar nayi nagamane me hanani shiga cikin gidan nan sai Allah amma sai na shiga ko za'ayi tsirena abawa kaji sai na shiga,

Taƙaici ma bai barta tabata amsa ba tayi tafiyar ta tabarta a awajen saidaga baya tayi saurin bin bayan ta suka ci gaba da tafiya tare tana me yi mata shirme da shiriritar zance, dan kawai jinta take tanayi mata kallon mahaukaciya.......,

***********************

Yana shiga cikin gidan ya nufi Part ɗin cikin gidan da motar Saida yaje bakin ƙofa sannan ya tsayar da ita tare da ɓalle murfin motar ya fito daga ciki cikin hanzari ya nufi wajen ƙofar kai tsaye, yana zuwa yasa ƙafar sa ya tura ƙofar da ƙarfi....

Duk waɗanda suke cikin falon nan Saida suka tsorata tare da maidai dubansu ga bakin ƙofar,. Gaban wasun sune yayi mummunar faɗuwa sakamako tozalin da sukayi dashi...

"Whare is BILAL!?

Dukansu shiru sukayi dan babu wanda yake da ƙarfin basa amsa,

Da sauri Mubeena tace "Ya ɓata.....,

Ko kallon inda take baiyi ba yaci gaba da takowa cikin katafaren falon da ya gaji da haɗuwa iya haɗuwa komai akwai,

Tambayar ku fa nake babu me bani amsa ne.!? Me yasa kuka barsa ya fita da izinin wa ya fita..!? Yayi maganar cikin ɗaga murya, yana daka musu tsawa. Kowa kamewa yayi awaje ɗaya cike da jin tsoron abun da zai biyo baya duk da ba laifin su bane amma bazai gane hakan ba sai ya haɗa dasu,

JANNAT da bata cikin falon jin muryar sa yasa ta saukowa daga upstairs cikin sauri tare da mayafi akan ta, cikin nuna damuwar tace "Ƴallaɓai ka gafar ce mu sannan ka fahimce mu kabari muyi maka bayani muma bamu san ya fita ba, nima da na fito neman sa zanje na kira police na sanar dasu za'afara binciken inda yake, nasan za'agansa bazai taɓa bata ba acikin garin nan kona su waye su dole su dawo dashi,

"Laifin waye me yasa baku kula da shiba har ya fita baku sani ba, wallahi idan ya mutu gaba ɗayan ku sai na ɗaureku sai nasa an rataye min ku....shin kunsan wane hali yake ciki a halin yanzu ku kalla ku kalli BILAL kunga yanda suka maidashi, ya ƙarasa maganar yana nuna musu videon da aka turo masa,

Ƙara rikicewa sukayi gaba ɗayan su sun rasa inda zasu tsoma ransu ganin halin da yake ciki wasu harda kuka saboda jin tausayin sa ganin suke ma kamar za'ace musu ya mutu, ga kuma furucin da yayi musu idan ya mutu suma duk sai sun mutu,

Da ƙyar ya tsaya ya saurari bayanin su yanda suma Bodyguard ɗin suka basu labari,

Mamaki da al'ajabi da taƙaicin jin waɗanda sukayiwa ɗan sa haka yake ji,
Da ƙarfi yace "MATA..! MATA..! MATANE SUKA KAMASA, mace dai har suka iya yin wannan abun to kuwa sunjawowa kansu bama iya sukaɗai ba gaba ɗaya familyn su sai nasa an ƙulle su, shiru yayi yana ƙara jinjina maganar da yake ganin abun kamar ba gaske ba,

Can ya kuma cewa "Tabbas ina son sanin ko SU WAYE SU? ina son sanin gidajen su iyayen su da inda suke raywa gaba a yau nake son sanin komai, daga nan zuwa dare, in bahaka ba kuma, to kuka da kanku, dan hukuncin da zan ɗauka ƙwaƙƙwara.

Yana tsaye agun yafara kiran ƴan sanda yana sanar dasu saida ya kira wajen mutane biyar harda gidan radiyo da gidan TV,.....

Suma al'ummar gidan kowacce bazama tayi ta fita daga gidan babu wanda ya tsaya saboda idan ka tsaya rankane zai ɓaci da yawa,

Shima fita ya ƙaragi tare da shiga mota ya kuma janta yafita daga cikin gidan,

Kan kace ne acikin ɗan ƙanƙanin loƙaci maganar ɓatan nasa ta fara bazuwa cikin unguwar abunka na manya da kuɗi a ƴan daƙiƙun loƙaci gari ya ɗauka cewar wasu mata sun sace ɗan gidan Mas'ud Ɗan ijje.

Bodyguard da suka fita tun ɗazu har yanzu dai basuyi nasarar ganin saba,

Suna cikin tafiya akan titi bayan suna hau wata hanya da su kansu basu san ina suka dosa ba, tundaga nesa suka hango motar sa, cike da jin daɗi suka ƙarasa gurin, har suna rige rige wajen fitowa daga cikin mota, su biyar ne suka kai hannu wajen motar zasu buɗe ta amma ɗaya ne da yafisu zafin nama ya riga su buɗewa,

Yana buɗewa sukaga wayam babu kowa acikin motar gaba da baya duk suka duba amma babu kowa acikin ta, take murnar su ta koma ciki da tunanin kuma shikenan tasu ta ƙare tunda har ga motar sa babu shi aciki to basu san kuma wacce hanya zasu bi ba su kama su,

Kallon kallo kawai ake sun kasa cewa komai, suna cikin haka saiga motar ƴan sanda ta ƙaraso gurin , Nan suka shiga tambayar su game da motar, suma amsa suka basu da abun da suka gani.....

Saida suka ɗaiyi dube duben su acikin motar sannan sukace su tarkata kawai su koma gida dare ya fara yi ,

Tun akan hanya police ɗin ya kira Alhaji Mas'ud Ɗan ijje ya sanar dashi,

Tofa Familyn Ɗan Ijje ba lafiya sama ko ƙasa an duba ba'aga Bilal ba, ta tabbata an ƙwamasheshi kenan, abudai kamar wasa har zuwa wajen ƙarfe ɗaya na dare ana ta abu ɗaya ba'agansa ba, ko me kama dashi ba'agani ba,

Washegari......

Zaune take gaban madubi sai faman kwaliya take tsantsarawa fuskar ta, ba laifi kuma tayi kyau abun ta ɗas,

"Zee ke kam dan Allah ki tashi haka mana kisaka kayanki, kinsan dai halin Beenish ba jiranki zata tsaya yiba, ke kika fara wankan nan amma kowa ga shirya ya barki kina zaune kina abu ɗaya,

Yabawa kulawa ancewa jaka adama duk ɗan baƙin ciki saidai ya mutu dan anfishi kyau sai anyi maka Black stomach,

"To kar ki gama da alama yau kin shirya tafiya a napep, cewar wata santaleliyar budurwa kyakkyawa fara ce sol tana da ɗan tsawo ga hanci har baka idanuwan ta kuma sunyi wani irin kala su ba blue ba su ba baƙaƙe ba su ba brawn kawai sunyi wata iriyar kala ta ban me ɗaukar hankalin duk wanda ya lalle ta sai ya kuma kallo, musamman idan ta ware su ka gano cikin farin idon ta sai kaji kamar ka curoshi ka matar jikin naka, sai gashin kanta da ta riƙeshi da wani towel tana gogewa,

Agogon dake manne ajikin bangon ɗakin nasu ta kalla tare da cewa "Inna lillahi wallahi kunga wai har bakwai da rabi tayi, wallahi idan nasaka kaya babu wanda zan jira, wacce ta fito daga wankan take kuma yin wannan maganar. Beenish kenan....

Wacce take kan gado ce ta duro daga kan nata gadon tana cewa "nidai ko yanzu ma mu tafi a shirye nake saidai ƴaƴan hanjina da suke cukurkuɗewa bari inje in samu Aunty babba a guncen,

Beenish ce tace daman ai kinfi ƙarfi anan tana faɗa tana zura rigar bayan ta ta ɗau mayafi dan mai ma a tsatstsaye ta shafasa ta ɗauki jaka da takalmi ta nufi hanyar waje tana cewa masu kwaliya da masu zaman cin abinci sai ku zauna kugama abunku a nutse kwa taho rabon zama awajen ne zai kama ku, Babyn baby inyi gaba ne kuma kina nan,

"Wallahi nina yunwa nake ji amma dai muje kawai, ta tashi tana gyara mayafin jikin ta,

"Haba ƙawata wai tafiya zakiyi ki barni wallahi na gama waccen rigar kawai zan saka, cewar Barazana....

Itadai Beenish ficewar ta tayi su kuma suka shiga yin sauri suka ƙarasa shiryawar suka bi bayan ta,

A bakin ɗan ƙaramin kitchen ɗin su suka tsaya suna kallon Aunty Babba da take ta ƙoƙarin dafa musu karin kumallo,

Itama sanye take da riga da wando saidai rigar ta wuce har gwiwar ta sai ɗan ƙaramin mayafi da ta naɗe kanta da shi, btibarkallah baƙace ita amma ƙirin ba, yoroba ce kunsandai yanda suke tana da ƴarfaffaɗiyar fuska sai tsagu dake gefe gefen fuskar ta, duk da haka kuma tana da ɗan kyaun ta ba laifi,

Ɗagowa tayi tace wai har kungama "mungama a daidai kenan, bari in wanke hannuna mu wuce,

Beenish tace yauwa kokefa kingama komai miƙo mukai mota, wani flaks ɗin silba ta miƙo musu sai jug duk ta haɗasu ta miƙa musu, suka fita dashi basu daɗe da fita ba su Barazana suka fito suma duk da tasan kiranta ake amma hakan nakasa ta ɗaga ƙafar ta ba tayi sauri a hankali take tafiya tana taku ɗai ɗai takalmin ƙafarta na bada sauti ƙwas ƙwas ƙwas....

A wajen motar su suka haɗu gaba ɗayan su ba ɓata loƙaci ko wacce ta shiga ciki Beenish ce take jansu yanzu saboda tafi sauri saura ƴan mintina su shiga test,

"Kai kunsan kwa me yake faruwa Ameela tayi maganar hankalin ta na kan wayar ta.

Beenish ce ta ɗan juyo ta kalle ta kaɗan tana ƙara maida hankalin ta ga tuƙin da take,

Ameela ce ta ɗora da cewa "Tabbb mun taka sahun ɓarowa ina wannan guy ɗin da muka bari jiya kunji cigiyar sa ake kuma a wajen mu ake nemansa ance wasu matane sukayi kidnapping ɗin muke nan,

Babyn baby tace munshiga aljanna muyi tsudum tsudum sharri kuma za'ayi mana to waye ne ya ɗauke
End Ads