"Ogah ai agun muka bar ta kawai da muka ɗauko abun da muke so, tana cen mun barwa karnuka...
"Good aikin ku yana kyau yanzu plane na gaba shine nemo wannan mutumin da suka kai asibiti da kuma yarinyar da akace angan su a tare, yanzu mutum biyu kawai ya rage mana mu kawar a gobe nake son ku aiwatar da wannan aikin, asibitin de zaku kuma dubawa, za'a same su anan, dan haka ayau zaku bar ƙasar nan, dan ku same su akan kari, zamuyi magana da Rabi idan kunje ku same ta...
Nan suka amsa masa sannan suka bar ɗakin nasa da yayi kama da office.......
Washe gari....
Kamar yanda ya buƙata ƙarfe biyar a ƙasa Nijar tayi musu, dan haka zuwa shida sun isa gidan sa, yana gaban window tun asuba yana jiran ƙarasowar su, suna ƙarasowa kuwa akan idon sa, sai loƙaci yabar gurin ya koma ɗakin da suke haɗuwa da yaran nasa,
Yana shiga suma suka shigo falon cikin dakin suka nufa, saida suka nemi izini ya basu damar shigowa sannan suka shiga, yana zaune ya saita system ɗin sa kawai jiran su yake ya matsu yaga abubuwan da ta ɗauka..
Miƙa masa sukayi a wata ƴar farar leda da suka saka sa aciki, karɓa kawai yayi batare da yace da su komai ba...
Buɗewa yayi sannan ya zaro flash ɗin sai ya ciro memoryn a jikin nasa ya saka memoryn sannan ya saka shi a jikin system ɗin,
Shiru gurin yayi duk suka koma bayan sa suna jiran sugani suma, shiga cikin memoryn yayi yafara dubawa, wajen audio ya shiga amma baiji ɗaukar komai ba, sai waƙoƙi da yagani kaɗai, fita yayi ya shiga file ɗin nan ma duk sai hotuna ɗayan hannun sa ya fara dunƙullewa rashin samu wasu abubuwan da yayi tsammani photos ya shiga shima sai hotuna kaɗai sai da ya shiga wata folder ɗinne ma sannan ɗaya daga cikin su yace "kai wannan ai hotunan waɗanda muka kashe ne, nan sauran duk suna suka fahimta hotunan su ne dashi da wasu da yawa dai...
Miƙewa yayi tsaye a fusace yana kaiwa na gefen sa naushi "wannan wane irin hauka ne kuma hauka ne kuka karɓo min memoryn sa me zanyi da memoryn sa, kun zauna ya maida ku mahauta yamaida ku lusarai, me yasa baku gane hakan ba, gaba ɗaya ya rikice sai sumbatu yake musu yana kaiwa wanda yaga dama duke.....
Suma duk abun ya basu mamaki taya hakan ta faru daman duk yanayin tsoron da ya nuna yasan ba abun da suke buƙata bane ashe yayi musu exchanging ɗin memory to ina yakai sa......✍️✍️
My WhatsApp number 08124226526
[3/5, 12:10 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
💪Jajirtattu writers association 💪
______________________________
*_episode 27💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
Bismillah....✍️
*NAREWA*
____Zuwa bayan sallar isha'i mazan gidan duk suka shiga dawowa duk wanda ya dawo tunda ga waje zai fara jin abun dake faruwa, mutum ukun farko da suka shigo ne suka yi part ɗin suna zuwa suka rufe su da faɗa me yasa basu kaisu asibiti ba zasu bar su a cikin gida, daga nan aka kwashe su akayi asibiti da su duk da babu tunanin zasu tashi dan gani suke kamar sun mutu....
An daɗe akan su ana duba su basu farfaɗo ba saidai andaidai ta musu numfashin su ya ɗan fara fita, musamman ma Mama saboda a yanda bincike ya nuna musu yayi doguwar suma, amma shi Kabeer anma kasa gane inda matsalar sa take, saidai kansa da ya bugu sosai amma bugun zuciyar sa na ɗan ƙaruwa....
Tun dare ake abu ɗaya har washe gari, a taƙaice dai, basu mutu ba kafin dare duk suka farfaɗo gaba ɗayan su, abun mamaki ma zuwa safe duk suka ware dake daman ba wani mugun duka sukayi musu, babu karaya babu targaɗe, kawai bugu ne akan su shima kuma ansamu ambasu kulawa sosai,
A washe garin ranar da daddare mutanen Bulama suka kuma dawowa wannan gida, saidai da suka dawo kamar haɗin baki duk yanda suka so su samu wani abu amma babu abun da suka samu sannan kuma suka kuma tabbatar musu da cewa duk sun mutu sunje sun bunne su tunda safe, Kabeerat ma taci sa'a bata nan, amma part ɗin ta saida sukayi masa filla filla suna bincike amma babu komai dole suka haƙura babu yanda suka iya haka suka bar gidan da zulumin abun da zasu cewa Bulama dan yace in basu nemo sa ba duk sai ya kashe su gwanda su lalubo sa kar su sake wani ya mallake sa, su tabbatar da sun nemosa sun kawo masa shi.....
Sai da sukayi kwana biyu a asibitin sannan aka sallame su daga asibitin, koda suka koma gidan babu wanda yayi maganar abun da ya faru tsakanin Mama da Kabeer, a daren ma haka suka ci gaba da basu kulawa ta ko wane ɓangaer taimaka musu ake hasali ma ba'a part ɗin Khabeerat suka zauna ba, washe gari ne ma suke sanar dasu cewar mutanen sun kuma dawowa, suka kuma gaya musu abun da sukace, suma su Kabeer sun basu labarin duk abun dake faruwa, nan sukai ta ƙara jinjina lamarin, daga taimako ga abun da suka kuma jefa rayuwar su ciki, hakade suka ƙaraci maganar su har aka watse duk da ba kowa ne ya hallaci gurin iya mazan gidanne sai ƴan manya manyan matan gidan, da kuma Kabeerat..
Suna zaune a falo loƙacin su kaɗai ne a ciki Mama ta kalli Kabeer tace "Kabeer sai da nace kar ka basu yanzu gashi nan Allah yayi kwanan mu bai ƙare ba sun ƙwace abun kuma sun so kashe mu ɗin, daman nasan ko anbasun ma baza su taɓa barin mu ba, yanzu da wane ido zamu kalli yarinyar nan idan ta dawo ta gama gaya mana komai ta nemi mu taimaka ta sauke nauyin ta ga abun kuma da kayi mana...
"Mama ai da ban basu ba da abun da zasuyi mana sai yafi haka kuma dole suyi mana dukan da sai sun kashe mu ɗin kuma zasu caje mu daga ƙarshe sugani su ɗauka bayan kuma sun kashe mu, amma yanzu da na basu kinga komai ya zo da sauƙi gashi basu kashe mu ba da ranmu, kuma aiki dole muyi sa ba fashi sai inda ƙarfin mu ya ƙare, duk fa maganar da tayi mana nayi recording hakan ma kaɗai ya isa hujja ga kuma wanda Fateema ta yi musu, ga kuma na memoryn kinga kuwa duk wata hujja ta bayya na..
Cike da rashin fahimtar maganar da yayi ta ƙarshe tace kamar ya ga memory, memoryn me kuma muke dashi, bai bata amsa sai murmushi da yayi mata yana miƙewa tsaye yace "zo muje ki gansa, tashi tayi kamar wata sokuwa ta shiga binsa har suka fita daga falon suna fita kowa ya shiga tambayar su lafiya me ya faru ina kuma zasu, nan Kabeer yace part ɗin Kabeerat zasu, haka suka tafi har suka ƙarasa part ɗin, da sallama suka shiga, tana kitchen ta jiyo sallamar su fitowa tayi da sauri tana amsa musu, fuskar ta ɗauke da fara'a...
Ƙarasa shiga suka yi suka samu guri suka zauna, Ita dai Mana kallon Kabeer kawai take jira take taga me zaiyi kuma taga kamar baida niyar faɗa mata, ƙosawa tayi tace "kai wai me ka maida ni kace na biyo ka munzo kuma kayi shiru ka barmu muna ta hira ka nuna min mana...
Tashi yayi tsaye sai ga kalli Khabeerat sai yace "kin cire abun da nace miki, kar kaɗa masa kai tayi tare da cewa ban cira ba naga da mutane da yawa tunda kuka suma ake zarya kanku kaga babu dama cira, daman so nake in shigo nan ɗin nayi maka maganar sai kuma gashi kunzo..
Juyawa yayi ya kalli Mama da ta zubawa sarautar Allah ido, kanta yaje ya tsaya ga manakin ta sai kawai taga ya cire mata mayafi tare da ɗan kwalin dake kanta, kamo kan yayi ya shiga zura hannu yana ƙwaƙwalo cikin manyan kitson dake kanta na zanen hausa.
"Kai wai meye hakanne ne me kake nema?
"Shiru yayi mata sai yace "Kabeerat ɗan ban kibiya sai an tsefe shi naga yaƙi fitowa...
"Matsa muga a wane kitsonne, nuna mata yayi, hannun ta saka itama tana ɗan jan jan kitson tana sako sako dashi, ita dai Mama zama tayi kamar ƙaramar yarinya tana jira taga ikon Allah,
"Yauwa kaji shi na taɓo sa, ta faɗa tana ƙara cusa hannu saita turo sa ta gaba, saiga Memory tsudum ya fito, kafin ma ta ɗauka tuni yayi saurin ɗauka yana cewa "Alahamdulillah wallahi nayi tunanin ya faɗi, Mama ga memoryn cikin flash ɗin ya faɗa yana miƙa mata..
Zaro ido tayi cike da mamaki da kuma neman ƙarin bayani dan har yanzu bata gama fahimtar inda maganar sa ta dosa ba,
"Kinyi mamaki koh?
"To ya bazanyi mamaki ba ni kamin bayani yanda zan gane taya wannan abun ya shiga tsakiyar kaina bansani ba,
"Mama ai tun loƙacin da na karɓa kafin mu fita na canza memoryn da nawa nasaka musu nawa na saka nacikin flash ɗin daman nayi haka in case saboda gudun matsala, daman yana aljihuna a cikin leda loƙacin da muka fita muka gansu nan har muka dawo ciki da gudu, kafin su shigo da naga kin tsorata sosai hankalin ki duk baya jikin ki, bana rungume ki ba in zaki tuna, saidai har na ɗaga ɗan kwalinki nasaka banjin kina cikin hayyacin ki, a loƙacin nasaka, ita kuma ta gani, bayan na sake ki na tura ki, ciki kafin mu shigo nayi sauri nace mata koda mun mutu ta cire abun da nasaka miki, takai sa kotun da ta sani ta bawa alƙali, nayi hakane dan muma mu sauke nauyin koda shi alƙalin baiyi hukuncin da ya dace ba, shida Allah kuma banajin ma indai alƙali aka samu direct ba abi ta hanyar lauyoyi ba, za'a iya samun shari'a me kyau indai har ya kalla kuma ba mugun ta yasa gaban sa ba to dole yayi hukuncin da ya dace....
Sosai Mama tayi al'ajabi da mamaki tare da jinjina masa wannan dabarar da yayi tana kallon sa tace "Ikon Allah gaskiya to bansan wace irin tsorata nayi ba, dan wallahi ko kaɗan banji komai ba, banma san yaushe ka rungume ni ɗin ba..
Ɗan murmushi yayi yace "ai naga alama tun a loƙacin, yana maganar ya koma ya zauna yana sake jin ransa fari ƙal.
"Mama ya kamata fa mu fara shirin tafiya tundade komai daidai muje muji kuma ya jikin wancen bawan Allah duk da nasan babu abun da zai same sa zasu basa kulawa, kuma bazasu bari ya tafi tunda nayiwa likitan baya ni.
"Eh nima daman zuwa gobe da sassafe nake so mutafi, yanzu kaga yamma tayi idan muka tafi zamuyi dare sosai.
"Mama ai darenne ma loƙacin tafiyar tamu shine babu wanda zai fitar mu zai ga shigar mu gwanda mu tafi kawai saboda tsaro,
Da farko a'a tace masa saida ya nace tare da kawo mata advantage ɗin tafiyar daren nasu, sannan ta amince, haka suka fara shiri babu wanda yaso tafiyar tasu amma haka suka basu haƙuri, suka tafi, da motar gidan aka ɗauke su aka kaisu har tasha, sannan suka tsaya saida mota tashi sannan suka koma gida kowa na kuma jinjina ma wannan lamarin da suke jin sa kamar almara.
Ƙarfe takwas na dare suka sauka a garin, suna sauka kuma babu inda suka wuce sai asibitin, koda suka je kam suka samu yanda suke so, har ya warke saboda su ma ya zauna jiran su saboda ƴar sa, amma da tuni ya tafi, nan ma basu daɗe suka karɓi sallama, sannan suka tafi can gidan gaba ɗayan su, suma lafiya lau suka samu su fateema saidai tashin hankalin su da suka ringa kiran warya su bata shiga sai sukayi tunanin ko wani abunne ya same su amma duk da haka basu ɗaga hankalin su sosai ba, sai suka dangan ta hakan kawai da ko rashin lafiyar tasa ce batayi sauƙi ba.
Tun a daren ranar Kabeer yabawa Shu'aibu (me gadi labarin) labarin duk wani abun da ya faru, shima ya basa abun da yafaru har suka zo asibitin, wannan abun ya faru, tun a washe gari suka fara shirye shiryen yanda zasu ɓullowa lamarin..
A kwana a tashi yau har sunci wata guda babu wanda ya ankara dasu kuma suna ci gaba da binciken su, inda suka kuma samun wasu hujjojin dangane da asibitin, a ɓoye suke komai, kuma Allah ya taimake su har yanzu dai Bulama bai cinma su ba,
A watanne ina Shu'aibu ya gano duk abun dake faruwa da kwai saka hannun mijin nata amma shi baima san da shi ba, yadai san da Rabi tunda daman Kabeer yabayar har da ita cikin labarin da ya basa, dan haka yaci gaba da haɗa ƙwararon hujjoji ta hanyar sabon me gadin da sukayi a gidan, anan ya gano duk ƴan ƙungiyar da suka haɗa, kuma suka ci gaba da bibbiyar su ɗaya bayan ɗaya kuma sun gano kamar ba ƙungiya ɗaya suke ba da Bulama, saidai kowa yasan abun da kowa ke aikatawa.
Ranar wata Laraba ya shirya bin uban gidan nasa, ta hanyar labarin da ya samu zaije wani gari kuma daga gani ba alkhairi ne zai kasa ba, sosai ya shirya dan zuwa yanzu har camera suka samu da recorder irin ta ƴan gidan radio harda abun zuƙo magana, a ranar ne yaje ya kashe wani dattijo da baisan waye ba kuma kafin ya kashe shi saida ya farfaɗa masa duk adadin mutanen da ya kashe dan haka shi bai isa yasa yaƙi kashe shi ba, indai akan muradin sane to saidai kowa ya mutu akan cikar burin sa, bayan yagama gaya masa maganar ya kashe shi, daman su kaɗai ne a cikin falon..
Yanayin yanda ya kashe shi ne yabawa Shu'aibu tausayi baisan loƙacin da hannun sa ya fara karkawa ba har ya saki camera ɗin, a ƙasa, karaf kuwa ƙarar faɗuwar ta akan kunnen mutumin nan, da sauri ya juyo kafin yayi wani yunƙuri tuni idon sa ya faɗa cikin idon sa sukayi ido biyu, aikawa da mugun gudu Shu'aibu ya tsugunna ya ɗauki abar sa, ya haura saman katangar da ya hawo ya shigo, yana hawa shima ya fito da gudu yazo zai jawo sa yana kai hannu zai riƙo sa shi kuma yayi saurin janye wa ya tsallaka, shima ƙoƙarin tsallakawar yayi yaji ina bazai iya ba, da gudu ya bar wajen ya shiga motar sa cikin mahaukacin gudu ya shawo kwanar inda yake sa ran zai gansa, saidai baiga kowa ba, ji yayi kamar ya kashe kansa saboda ta ƙaici shi za'aringa bibiya ana ɗauka kuma ma me gadin sane zai masa haka daman bai mutu ba kenan...
Hanyar gurin ya kuma bi cikin gudu ko zai gansa amma bai same sa ba, nan ya kafa masa matakan tsaro ta ko ina tare da hotunan sa duk wanda ya gansa zai masa kyauta yasaka nasa mutanen, gaba ɗaya garin a zagaye yake neman sa ake ta ko ina.
Hakan yasa Shu'aibu daina fitowa saboda ko ya ya fito za'a iya kamasa, kabeer ne kawai yake iya fita..
Amma saidai duk rashin fitowar sa saida ya gano gidan da yake, ranar suna zaune a falo gaba ɗayan su, sukaji wani irin mugun bugu, gaba ɗayan su tsorata sukayi, a hankali Shu'aibu ya tashi ya leƙa nan kwa yaga sune su wajen ashirin awajen, suna wannan bugun, dawo wa yayi a tsora ce yace sune suma duk miƙewa sukayi, cike da tsoro, nan suka fara tunanin meye mafita, Kabeer ne yace muje ta ɗakin Fateema akwai window babba kuma can daji ya ɓulla mu fita ta nan kawai dan ko ba mu buɗe zuwa wani loƙaci zasu iya ɓalla ƙofar su shigo,
Nan suka tashi cike da tashin hankali cikin sauri duk suka shiga ɗakin, saida Shu'aibu ya fara zuwa ya ɗauko kakar sa da duk wani abu da sukeyi yana ciki, jaririya na hannu Fateema sai Shu'aibu yace ta kawo yarinyar ita ta fara fita sai yabata yarinyar,
Da ƙyar kwa aka ɗaga ta ta iya fita sannan shi kuma ya taka abu ta buɗa hannun ta tunda da ƴar tazara tsakanin window da ƙasa, saida ya zura kan sa gaba ɗaya sannan ya rufe idon sa da ƙyar ya iya sakin ta, aikwa garin ta taro ta sai ta matsa daga gurin gaba ɗaya ta tafi zata faɗi ƙasa, da sauri ta kuma binta sai da kyar ta samu ta kamo ƙafar ta guda ɗaya sannan ta riƙeta, wani irin kuka ta fashe dashi saboda tsorata da tayi, nan duk hankalin su ya tashi suna tambayar lafiya..
Da sauri shima ya tsallaka baisan ma sanda ya dira ba, yana dira sukaji wata ƙatuwar muraya a falo ana cewa naji motsi anan ɗakin, Mama ce da Ruƙayya suka ce sun riga da sun kamamu kabeer kayi sauri ka fita bari inje ni inji dasu, in ɗauke musu hankali kafin su shigo nan kuyi sauri ku fita