x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 53 - SU WAYE SU

  • 156001 words
  • 159000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 184

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
*🌬️Yaya Azeema😎*



(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)


________* 08124226526*_______


*_episode 46💧_*



💧💦محمد لرسول الله...!💦💧

*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*

_Bismillah..✍️_



*GHAMBURJ*

___Shiru shiru tun suna jiran dawowar Hajja Mama har sukayi bacci gaba ɗayan su, a ɗaki ɗaya suka kwanta, washe gari tun kafin su tashi, wanda Hajja Mama tasa ya kula dasu, ya kawo musu abinci, bai tashesu ba, ya ajiye kawai ya fita.

Salama ce ta fara farkawa duk ta tashe su loƙacin har rana ta fito saboda gajiyar da su kayi ne yasa suka kasa tashi da, da ƙyar duk suka iya miƙewa Faheema ce ta fara shiga bata fito ba saida ta haɗo da wanka rasa yanda zatayi tayi saboda bata da kaya ɗan leƙowa tayi ko zata samu wata dabarar taga dai babu wata dabara, sai kawai ta mayar da nata, sannan ta fito, daga ita sai Salama ta shiga, tayo alwala ta fito, sai Zaid shima saida ya haɗo da wanka sannan ya fito da towel saboda su suna da kaya shi da Bilal, Saida sukayi da gaske sannan Bilal ya tashi shima buɗe ido kawai yayi saida ya daɗe a kwance sannan ya zuro ƙafafun nasa yana yatsina fuska dan a tunanin sa zaiji zafi, sai kuma yaji ba zafin amma duk da haka saida ya ɗan ranƙwafa, babu zafin amma ji yaka kamar da akwai, sude kallon sa kawai suke har ya shige toilet ɗin babu wanda yace masa uffan, shima da wankan ya haɗo sannan ya fito, sai wani haɗf rai yake yaƙi ya kula kowa, duk da Salama na tayi masa magana amma bai kula ta ba, sai ya koma bakin gadon sa yaɗan jingina, wai so yake su gama abun da zasu yi su fita ya shirya sannan yayi sallahr.

Ganin kowa yayi wanka yasa Salama itama bayan ta idar da sallahr ta tashi taja wani towel dake gefen gadon Bilal bai ganta ba da bazai bari ta ɗaukar masa ba, tana shiga bata daɗe ba ta fito ɗaure da towel abun ta babu ruwanta, kayan ciki kuma bra da pant kuma ta wanke su kafin ta fito.

Duk da kallon suka shiga binta da kallo, Zaid kam tundaga kan ƙafarta yake kallon ta har kan ƙirjinta ko ƙiftawa bayayi, Faheema ce tace ke kam bakya jin kunya kika fito a haka gaban maza, kallon Zaid tayi suka haɗa ido yayi saurin janyewa daman loƙacin ya saka kayan sa sai kawai ya ɗan sosa ƙeya yana dariya yace "bari na baku guri ku shirya, shi wannan har ya fara bacci saidai idan kun gama sai ku tashe shi, dan shima mu yake jira mu fita ya shirya shi yasa ku ka ga ya zauna gashi nan kuma har bacci ha kuma ɗaukar sa.

Taɓe baki Salama tayi tace "waɗannan yaran ina ruwana da su, abun da ba tsirara na fito ba, kuma duk wanda ma ya kalle shi yaga zai iya gani ba taɓawa ba asarar ido.

"Hmmm lalle yarinya mune yaran naki, to ko Bilal mafarki yake bare ni da nake gansameman saurayi dande kin kawai ina tsoron Allah ne shiyasa zan fita, amma da hmmm... Yana faɗar haka ya fice daga ɗakin.

Hararar bayan shi Salama tayi tare da cewa "kaji dashi, can ta matse maka.

Faheema tace "to Allah ya shirye ki dan ni wallahi bazan taɓa iya fitowa a haka ba, shiyasa ma na mayar da kayana.

Batare da ta kalle ta b, tace "nikwa ai kinga nama yi bawai zan iya ba, ni banga wani abuba aciki ba, tana faɗar haka ta matsa kusa da Bilal tace "ɗan Boy tashi kaban kayan ka na saka kafin nawa su bushe kaji?

Ko motsawa baiyi ba yana jinginan da yake alamar bacci yayi nisa, duddaba ɗakin tayi taga inda kayan su yake taje kawai ta duba wanda taga ya mata kama da nasa ta ɗau wata riga me dogon hannu ta saka sai dogon wando tasaka abin ta, kana ganin kasan kayan maza ne, amma sai suka yi mata kyau.

Zaid ne ya ɗan leƙo batare da ya gama kallon cikin ɗakin ba, yace "kuyi sauri kuzo muci abinci in kuka daɗe kuma zakuzo ku tarar da kwano, yana faɗa ya koma, Faheema da taƙaicin Salama ya cika ta yasa ta tashi tabi bayan Zaid saboda ita ta gama daman.

Bayan Salama ta gama shirya wa sai tazo ta tashi Bilal da ƙyar ya iya buɗe idon sa, ganin kamar kayan sa yasa ya ɗan zaro ido yace "wa yace ki saka min kaya? Wallahi sai kin cire min.

Dariya taya tace haba "big boy ka taimaka min wallahi bazan iya maida nawa ba, sunyi dauɗa gashi matar nan bata dawo ba bare ta bamu kayan musaka.

"Ni ina ruwana sai kin cire su na gaya miki, ya faɗa yana miƙewa tsaye fuskar sa a haɗe kamar zaiyi kuka, dan shi ya tsani sharing a rayuwarsa ko wannan ɗinma da tasaka masa bazai kuma sakawa ba amma dai sai ta cire masa abun sa.

Zuwa yayi ya ɗauki wasu kayan sai ya shiga bathroom ɗin ya saka ya kuma yo wata alwallar ya fito sai loƙacin yayi sallah, yana idarwa ya kuma kallon ta yanda ta kwanta masa akan gado, ji yayi ta kuma ɓata masa rai, miƙewa yayi "ki tasar min daga kan gado malama kuma nagaya miki ki cire min kayana koh.

Dariya ta kwashe da ita tana tashi zaune, wai shi nan bai yarda ba masifa yake mata, "wai nan dan Allah masifa kake harda wani haɗe rai angaya maka zanji tsoron ka ne, ko me? Wallahi ɗan Boy bazan cire kayan nan ba, in kuma zaka iya kazo ka cire min.

Cikin haushi tace masa ɗan yaro, yayi kanta ya kamo rigarta wai zai nuna mata ya fita iskanci, da sauri ta riƙe rigar tana dariya tace "kaji min yaro da lalata salla sakar ni, ta faɗa tana riƙo duka hannuwan sa biyu, sai kuma tayi ƙasa da murya tace haba mutumina dan Allah kayi haƙuri ka barmin, ko dan kulawar da nake baka, ka manta abun da nayi maka jiya, kuka fa kazo kana yi mana ni kaɗai naji tausayin ka amma shine yanzu zaka zo kamin rashin mutunci akan kayanka, hana nawan haba kyakkyawana son kowa ƙin wanda ya rasa fine boy wallahi kana da kyau ka dena haɗe ran nan baka kyau, tana maganar tana ɗan murza hannun sa cike da solon ƙwarewa da daɗin baki, kuma ta kafe shi da ido hakan yasa shi dole jikin sa yayi sanyi baisan ma loƙacin da ya shiga lumshe ido ba.

Murmushi ne ya kusa ƙwace mata tayi saurin tsayar da shi tare da miƙewa tsaye tana kuma kama hannun sa, baisan loƙacin da ya rungume ta ba jikin sa duk a mace, dariya ta ɗanyi itama tana rungume sa, tare da cewa ko kaifa amma kana tayin abu kamar ƙaramin yaro, yanzu dai muje in baka abinci da kaina, tunda tsohuwar can bata nan sai in karɓeta koh?

A hankali ya ɗaga mata kai saidai bashida niyar sakin ta, tayi tayi ya sake ta sai ya maƙe kafaɗa yana kuma rungume ta da kyau, yau taga abun mamaki yaro dashi ji abun da yake, ganin yana shirin ya kashe mata jiki yasa ta ciresa daga jinta da ƙyar da ya haƙura, sannan ta kamo hannun sa suka fito wajen hannun su cikin na juna.

Zaid ne baki sake yace 'to ke kuma meye hakan kayan sa ne sukayi miki kika saka?

"Eh ina ruwan ka tundade ba kayan ka bane, Bilal ne me bada wannan amsar.

murmushi kawai Salama tayi suna ƙarasa zama a inda suka ga abincin tsakiyar falo sun zuzzuba amma babu wanda ya ci suna jiran su ne daman.

Na gaban Zaid Salama ta ɗauka tace "yauwa bari in fawa bawa auta idan yaci ya ƙoshi sai muci.

Da sauri Zaid ya ƙwace yace wallahi baku isa ba idan zaku zauna muci gaba ɗaya ku zauna kuma yasaka hannun sa yaci, shi yaro ne da kusan kullum sai an bashi abinci a baki, itama waccen tsohuwar duk ta lalata sa da hakan, shine kema zaki zo ki ɗora daga inda ta tsaya to baki isaba saidai kar yaci abincin yau.

Haɗe rai Bilal yayi, ya tsani abun da Zaid yake masa ko ina ruwan sa da rayuwar sa, baisan me yasa yake masa irin waɗannan abubuwan.

Salama kuwa rabuwa tayi da shi ta jawo kwanan ta kuma zuba wani tare da cewa me baƙin ciki saidai ya mutu kada Allah ya kaisa gobe ehhh yaraye me baƙin ciki saidai ya mutu, yo in banda baƙin ciki ina ruwan mutum damu, kaima ga wata nan ka lallaɓata ta baka abakin idan so kake, mude babu fashi babu wanda ya isa ya hana mu ah to, dan ko a gaban uban waye sai na basa, kai nifa bana tsoron ta mutu ko tai rai, ta mutu kowa ya huta, tayi rai kuma muci ubanta hankali kwance (hmm in baki magana ba ai ba ƴar gidan Rabi bace, babar Abulele dan kun tsotsa keda Zee)

Zaid yaji haushi maganar ta hakan yasa ya kasa tanka mata, saima abincin shi da yaja ya fara ci, Faheema kam dariya ta shiga yi tana cewa Allah ya shirye ki Salama kude da zaku iya sai kuyi, mukam mun barwa yara.

"Gwanda da kuka barmana ai, dan ko baku bari ba sai munyi abun da muke so, yo Allah ya baka hannu ya baka komai rai da lafiya sai muƙi morar abubuwan mu, bawa fine boy kulawa yanzu na fara saidai idan ko zamu wayi gari muga wani yayi boom shi kaɗai ya fashe saboda baƙin ciki, kuma a ranar ma cigaba zamuyi babu abun da ya sha mana kai ko babban yaro ya kace?

Murmushi yayi tare da ɗaga mata gira, cike da daɗi jin yanda ta tsare masa har Zaid ya kasa magana hakan ba ƙaramin faranta masa rai yayi ba.

Hannun ta miƙasa tace bani biyar in baka goma, miƙo mata tafin hannun sa yayi ta ɗora nata suka ɗan tafa kaɗan, sannan ta juya ta juyo da plate ɗin abincin, tana ɗebowa da cokali, tace "yauwa oya open your mouth mutumina, nan ya wangale baki ta zuba masa a baki ya shiga taunawa, haka ta ringa bashi tana bashi tana uban surutu tare da yiwa Zaid habaici kala kala, tun Zaid na jurewa har ya fara mayar mata da martani, ganin kamar ya ɗau abun da zafi yasa ta ringa yi masa dariya tana bashi haƙuri tace shi wai baisan wasa ba tsokana ce fa kawai daga ƙarshe dai sai tashi yayi daga falon ya koma ɗaki, ita kuma saida Bilal ya ci ya ƙoshi sannan ta ci nata, Faheema itadai na zaune tana kallon ikon Allah abun dariya tayi sauran ta zuba ido har suka gama suka tashi daga gurin suka kuma komawa ɗakin, nan suka buɗe sabuwar hira duk yanda Bilal yaso yayi bacci amma Salama ta hanasa dole ya zauna ya haƙura....

Haka sukayi ta rayuwar su su kaɗai suyi faɗa su shirya daddare ma a ɗaki ɗaya suka kwana, Bilal kam da Salama gado ɗaya suka kwanta saida Zaid ya takura musu akan wallahi baza su kwanta tare ba, dan ba agarin mahaulata suke ba, sannan dai Salama ta rabu da Bilal daman ita bada niyar kwana ta kwanta ba, tayi haka ne kawai saboda Bilal da yayi bacci zata tashi ta koma kusa da Faheema, Bilal kam ba haka yaso ba, yaji haushi Zaid da ya hanata kwantawa kusa dashi.

Cikin dare wajen ƙarfe uku wani tashin hankalin da basu san dashi ba, suka fara jin harbi ta ko ina, gaba ɗayan su cikin tashin hankali suka farka, kowa na dirowa daga kan gadon, har rige rigen leƙawa suke ta window su gani, basa ganin komai saboda da duhu sai harbin da sukaji ya yawaita, buɗe ƙofar ɗakin sukaji anyi duk a tsorace suka juyo suna kallon me shigowar, shima cikin tashin hankali yace kuyi sauri ku fito, duk rikicewar sukayi suka ma rasa ta inda zasu bi, Bilal ne ya riga ƙarasowa gurin mutumin, duk akusan tare suka fito daga ɗakin, wani ɗaki ya buɗe musu yace suyi sauri fa, suna zuwa ya basu wasu jakunkuna ko wannen su tasu a cike take, tsoro ma yasa suka kasa riƙe jakunkunan, saida yayi musu da gaske sannan kowa ya rataya a baya, tafiya suka ɗanyi sannan suka ƙaraso wajen wani ɗaki me matattakala cikin sauri mutumin yake tafiya shi yafara hawa matattakalar sannan ya buɗe wata ƴar ƙaramar ƙofa, sai ya dawo ciki yace duk su kawo jakunkunan miƙamasa sukayi sannan suma suka fara fita daga ciki saida suka gama fita shima ya fito, nan ɗin ma dajine saidai kwata kwata ba aganin wancen gidan.

Cikin sauri ya shiga cewa kunga wannan hanyar ita zaku tabi kada ku tsaya sannan kar ku hau ko wace mota karma kubi hanyar da zata kaiku titi sai kunyi tafiya sosai, sannan waɗannan jakunkunan, akwai mahimman abubuwa aciki Hajja Mama zata bi diddigin inda kuke akwai waya acikiz duk inda ma kuke zata neme ku, sannan akwai kuɗi kuma aciki zaku iya taɓa koma nawa kuke so aciki kuyi buƙatar ku, akwai ATM aciki a nannaɗe ajikin wata takadda akwai pin ɗin ajikin takaddar, dan Allah kar kuyi wasa da ita, nan idan kun fita akwai wani ƙauye zaku iya tsayawa acikin sa ko gida ne ku siya sannan ku adana jakunkunan aciki, ku ɓoye su, sai ku kwashi kuɗin da kuke so kuyi amfani dasu koda baza ku zauna a ƙauyan ba, dan Allah na roƙe ku ku kaɗaine ya rage mana da zaku yi mana wannan taimakon, Hajja Mama ba muguwa bace, kuma bata kawo ku nan dan ta cutar da ku ba, yanzu babu loƙacin da zanyi muku bayani amma dai nasan daga ta dawo daga tafiyar da tayi zata nemeku kuma zatayi muku bayani kunji.

Salama ce "wane irin bayani bama son komai kuma duk bayanin da kayi mana wallahi bazamuyi ba, matar ta sato mu daga gaban iyayen mu amma ka wani ce ba muguwa bace, zadai mu ɗauki kuɗin ciki mu koma gurin iyayen mu amma duk wasu sauran abubuwan ku ku tashafa, ƙone su ma zamuyi, Faheema ma ta ɗora da ta ta maganar akan bazasuyi yanda yace ba, dukan su ma haka suka ce babu wanda yace zaiyi.

Mutumin nan kamar yayi musu haka ya shiga roƙon su yana ƙara yi musu bayani, yace da cutar dasu za'ayi da tuni an cutar dasu, basuga kuma abun da yake faruwa ba, amma ya fito dasu dan ya kuɓutar dasu, amma duk da haka ƙin amince masa sukayi, tun a loƙacin ya ta gwada kiran layin Hajja Mama dan ya sanar dasu amma layin akashe, gaba ɗaya ya rasa inda zai saka ransa gashi an riga da ansanshi duk inda ma yaje zasu lalubo sa, idan kwa yana hannun yaran babu me kawowa yana gurin su, gashi su kuma sunƙi amincewa,

Abun tausayi yace "to shikenan kuje Allah ya tsare hanya indai ku kun rayu ai da sauƙi, zaku iya tafiya, yana faɗar haka ya juya idon sa yayi ja, baisan me zaicewa Hajja Mama ba idan suka haɗu kuma shi wallahi bayan haka baisan me zai yi ba, ba ciki ya koma ba, shima wata hanyar ya nufa daban.

Suna ganin ya tafi duk suka kalli junan su, tare da kallon dajin har sun fara tausayin kansu yanzu cikin daren nan zasu fara tafiya agun, ji sukayi kamar ƙarar harbin na ƙaruwa ga mutumin har yayi musu nisa yasa suma dole suka shiga tafiya cikin sauri, Zaid ne ya riƙo hannun Bilal dan sun san shine abun tausayi zai fara yi musu raki, Salama kuma jakar tasa ta karɓa, sai suka rasa me zasuyi farin ciki ko baƙin ciki gashi dai sun fito abun da suke taso kenan saidai kuma wuyar da zasu sha a hanya ta hana su farin ciki, haka sukai ta tafiya tun suna hira har kowa yayi liƙis babu wanda yake iya magana, da sukaga dai sun gaji dan sunyi wajen tafiyar awa biyu dan gari har ya fara hasken asuba sai kawai suka samu wajen wata ƙasan bishiya suka zauna, suna zama Bilal ya zame ya kwanta kan cinyar Salama sai bacci, duk da agajiye take itama amma haka ta barshi ya kwanta.

Saida gari yayi haske sosai sannan suka tashi Bilal duk sun zama abun tausayi gashi ko kaɗan basa hango ɗigon gari, gashi ba ruwa bare suyi salla, har sun fara tafiya, Zaid yace "ya kamata fa ko taimamace muyi kafin muci gaba da tafiya tundade kunga babu garin a kusa, duk na'am sukayi da maganar sa, saidai kuma su matan babu me hijabi ajikin su, sai mayafi da Salama ta ɗara ne akanta shima ba babbane sai suka haɗa da ɗankwalin Faheema sukayi sallar a haka, daga nan suka kuma ɗaukar hanya, nan ma saida sukayi tafiyar kusan awa uku sannan suka fara hango wasu gine gine, murna suka shiga yi sosai dan su koma inane kawai suna so su gansu agurin mutane sai su hau mota ta kaisu garin su, kowa ya tafi gida shine kawai burin su.

Basu fi 30 minutes
End Ads