da yafaru gaba ɗayan su ransu sai ya ɓaci bare kuma ace ba'agan saba gaba ɗaya ba tabbbb.....!
Drivern ne ya shiga nuna musu hanyar da yaga sunbi nan suka bi suma, amma tafiya me nisa sukayi basu gansu ba basu me kama dasu ba,
Sun kai wajen awa ɗaya suna abu ɗaya tun suna ɗaukar abun da wasa har yazo yafi ƙarfin su gashi sun kasa tunkarar gida bare su sanar,
A taƙaice dai sai da suka gaji dan kansu suka haƙura da neman su, suka nufi gidan zociyoyin kowannen su na dukan tara tara,
Wata unguwa suka shigo wacce kallo ɗaya zakayi mata ka gane bata ƙananun mutane bane, Ta masu hannu da maiƙo ce, tunda suka shawo kwana suka tunakari wani tamfatsetsen gida da girmansa yafara tundaga farkon layin har zuwa karshen sa,
Bakin tanƙameman gate ɗin suka dosa inda tundaga waje daga saman gate ɗin aka rubuta*WELCOME TO THE ƊAN IJJE'S HOUSE*
Horn suka doka abakin gate ɗin take aka shiga sutale musu santalelan gate ɗin ya tafi sululu kamar an shafawa miciji ɗanyar kuɓewa, haka gate ɗin ya tafi,
Ana gama buɗe musu nagaba yafara danna tasa hancin motar ya afka ciki sannan sauran ma duk suka bi bayan sa, building ne babba me girma gaske wanda ya gaji da haɗuwa tundaga wajen ma zaka gane ba ƙaramin kuɗi aka kashe masa ba, duk yanda zan fasalta muku baza ku gane irin sa domin zama gaya muku yanda shi kansa wajen yake ɓata loƙaci ne ba kaɗan ba, dan haka kawai kuyi imagine,
Parking lot suka nufa tare da jere motocin a inda suke saidai kuma ko gama tsayawa basuyi ba kamar daga sama suka ga mutanen cikin gidan na nufo inda suke har sauri sauri suke, alama ma de kamar ƴar rige rigen zuwa wajen nasu suke,
Ai babu wanda yayi yunƙurin buɗe motar bare suyi gigin fitowa daga cikin motar, Suna ciki har suka ƙaraso kusa da motar amma duk sai suka ja burki suka tsaya... Sakamakon rashin a wacce motar yake, dan su basu san ma a motar da ya fita ba,
Da ƙarfi Wani yaro yace... "UNCLE BILAL a wacce motar kake ni zan fara ganin ka, kafaɗa min ni kaɗai, kar ka bari suji, Ni zan fara baka kyauta ta....
Dariya wasu daga cikin su suka saka masa,
Tsayawa sukayi a gaban motar da take a farko a cewar su ai dole shine ma agaba, flowers ɗin da suka zo da ita wasu jajjaye su suka shiga watsawa motar kowa ya fito da abun dake hannun sa, wasu kuma suna kunna wuta wasu kuma abunnan me ƙyalli ne ah hannun su suma suna watsawa sama, Sannan nan suka shiga cewa "HAPPY BIRTHDAY TO YOU... HAPPY BIRTHDAY TO YOU, HAPPY BIRTHDAY HAPPY BIRTHDAY, HAPPY BIRTHDAY TO YOU.....!
Ɗaya ce ta wakilce su da cewa "P P P..!
Sauran kuma suce hureee......ta kuma cewa P P P....! Suka ƙara cewa hure....!Suka faɗa da ƙarfi suna ƙarasa watsawa motar abubuwan dake hannuwan su.....✍️
*Ga duk wanda me buƙatar asaka shi a group ga number ta(08124226526) yayi min magana in saka shi dan bazan ringa share ɗinsa tare da link ba gwanda duk wanda yake so yayi min mgn sai in basa link saboda tsaro badan tsoro ba*
*Tafiyar ta dabance komai na cikin littafin na dabanne nima ɗin kuma ta dabance, shiyasa zan sambaɗo muku wannan labarin na daban, domin ku karanta kuma ku zama na daban.....🤗*
*Idan kinsan ke bata daban bace to bazaki iya karanta littafin nan ba, domin iya mutane na dabanne na musamman zasu iya karantawa*
This book contains many different things, If you have small brain. So don't start reading this book, Dan littafin na dabanne sai ka nutsu zaka gane sa dan akwai cukurkuɗu a cikin sa, sannan ya haɗa komai, Siyasa, Kasuwanci, malamta, Yaudara, Sonkai, Tausayi, mugunta, Son zuciya, Son abun duniya, Son kai, mutuwar zuciya, barkwanci, nishaɗantarwa, ilimantarwa, tare da darasin rayuwa kala kala...da dai sauransu akwai abubuwan ƙaruwa da yawa a littafin ba wai iya labari bane, shiyasa nace muku shiɗin na dabanne amma nasan duk da haka wasu baza su yarda da na daban ɗin bane sai sun karanta, ɗaya tamkar da dubu.....
Abun dai sai wanda yazo kusa dani na basa sirrin yaji sannan zaisan abun da nake son yasani, kar ayi bakai ko abaka labari kawai kudai ku zo kuji in faɗa muku.....💃💃💃
*Me ƙaunar mijin ta ko saurayin ta tayi min share ɗin sa zuwa groups*
*Share saboda Manzon Allah*
My WhatsApp no 08124226526
[3/5, 11:27 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________
*_episode 2💧_*
💧💦محمدالرسوالله..!💦💧
Bissmillah.....✍️
"Duk wannan budurin da suke babu wanda yasan meke faruwa da ƴan cikin motar domin zufa tagama wanke musu jiki gaba ɗayan su, duk da sanyin AC dake cikin motar hakan bai hana gumi fita daga jikin su ba, kowanne su yayi ƙuru da ido yayin da gaban su ke dukan dari ɗari, sun tsorata matuƙa kowa acikin tashin hankali yake, dan basu san ma ta ina zasu fara yi musu bayani ba.
'Wata ce tace; "JANNAT...! "wai jiran me muke tunda bazai buɗe ba mu ai sai mu buɗe sa tunda jan ajin nasa yaƙi ƙarewa, nasan yana kallon mu yayi mana shiru, tayi maganar tana kallon glass ɗin motar da take tunanin yana gurin wataƙil ma ita yake kallo.
"Hmmm kema aikin san halin BILAL yanzu hakama wannan abun da muke duk a banza baisan muna yiba, ya nan yana baccin da yasab...
Tun kan takai ƙarshen maganar tata, yarinyar da tayi magana ɗazu tace; "Ni nasan ma UNCLE baya cikin motar nan dan jikina yabani wataƙil ma yana waccen motar. ta nuna motar bayan ta, duk bin gun sukayi da kallo, Amma babu wanda yabar wajen.
Wacce aka kira da Jannat tace "Bari kuga tana faɗar haka tasa hannu ta buɗe motar, wayam suka gani babu kowa abayan motar,
A kusan tare wasu suka ce Kashhh...!! Suna me dafe goshin su cike da rashin jin daɗin rashin ganin sa, ashe duk wannan abun da sukayi daman baya ciki,
Yarinyar ce ta kuma cewa "You see what I'm saying... Tayi maganar cike da ɗan iyaye harda taɓe baki tana yi musu nuni da hannu ta.
Ta gefen tace ta ɗan dungurar mata kai tare da cewa "MUBEENA iyayi ai ba faɗar kice tasa hakan ba,
Bata kulataba tayi ga ta nufi wajen wata motar, tunkan ta ƙarasa ma aka buɗe motar, tsayawa tayi tana jiran taga me fitowar...
Sauran ma duk maida hankalin su sukayi ga wajen motar.
Ɗaya daga cikin Bodyguard ɗin sane ya fito daga motar ciki da ƙarfin hali, dan yadade zaman bazai musu ba shiyasa suka yanke shawarar gwanda kawai sugaya musu ayita ta ƙare,
Yanzu ma de ba haka suka so ba, dan ba wanda suke son gani ba suka gani.
'Yana fitowa sauran ma duk suka shiga fiffitowa har suka gama fitowa gaba ɗayan su.
Cike da ƙaguwa Mubeena tace "UNCLE BILAL...! ta kira sunan sa tana jiran taji ta inda zai amsa.
Gaba ɗayan su suka haɗu a waje ɗaya kallo ɗaya zakayi musu ka fahimci ba ƙalau suke ba.
Wata mata ce ta ƙaraso gurin su cikin tsuke fuska take binsu da kallo kafin daga bisani tace "Where is Bilal...!? Tayi maganar tare da ƙara canza yanayin ta, dan jikin ta yabata Bilal baya cikin ko wacce mota musamman da taga yanayin fuskokin su ya sauya tasan something is wrong,
Gaba ɗayan su shiru suka yi tare da sinnar da kansu ƙasa, babu wanda ya iya furta komai saboda sunfi kowa sanin wacece ita.
Cikin ɗaga musu murya sama tana me daka musu tsawa tace; "Ku bani amsa. Nace ina Bilal? Me yasa kukayi shiru Answer me. I said where is Bilal? Why are you silent? Ina yake..!?? maganar take ko tsayawa batayi cikin fara hassala tana tsare su da manyan idanunwan ta dara dara tubarkallah.,
Babu wanda bai razana ba da yanayin yanda tayi maganar, take cikin su ya ɗuru ruwa,
Cikin rawar murya ɗaya yayi ƙarfin halin cewa "Ma'am we so sorry, Bilal is not here, the some people have gone with hi...
Hannu ta ɗaga masa tana binsa da wani irin mugun kallo, kafin ma tayi magana mutanen gurin suka shiga cewa "What...., Wasu mutanen sun tafi dashi, What does that mean, what do you want to say..!?
Matar da tayi magana ce ta kuma katse musu tambayoyin su tare da maida duban ta ga sauran tana me harɗe hannunwan ta akan chest ɗin ta, tana kallon su alamun suci gaba da maganar da suke...
Cikin rawar murya cike da tsoro wannan tsohon ya shiga labarta musu duk abun da ya faru tundaga A har Z.
Cikin zazzaro ido take kallon sa jijiyar goshin ta har sunfito, ɗaga murya tayi tace "SU WAYE SU..!? a cikin garin nan dake ku kuma lusaraye ne har kuka tsaya mata sukayi muku haka, wallahi! wallahi! wallahi! gaba ɗayan ku sai ranku ya ɓaci muddun wani abu ya samu Bilal ko na rashin jin daɗi ne sai na lahira ya fiku jin daɗi, shine har kuka iya tako ƙafar ku kuka shigo cikin gidan nan, kuma kuka iya kallon ƙwayar idona kuke gaya min kun tsaya mata sun tafi dashi...
Nan mutanen wajen ma kowa ya shiga tofa albarkacin bakinsa tsayawa faɗar na kowa ɓata loƙaci ne, amma dai sun ɗau zafi da yawa saura kaɗan su fara hayaƙi...
Hajjaju kiyi haƙuri ki kwantar da hankalin ki mubi komai a sannu yanzu bai kamata mutsaya ana maida yanda akai ba, loƙaci is going abun da yakamata muyi shine muje asan yanda za'ayi a fara bincike, tun kan ƴallaɓai yaji wannan maganar muyi mu gama in ba haka ba kuwa basu kaɗai ba kowa na gidan nan sai ya fuskanci fushin sa dan haka muyi abun da ya kama ta.
"Juyawa tayi tana kallon ta, tana me marairaicewa kamar zatayi kuka, tace "KHATUME taya kikeso in kwantar da hankalina kinsan Bilal shine rayuwata bana son duk wani abu da zai taɓa sa bare kuma ace min baya nan, sunfa tafi dashi bansan me zasuyi masa ba, zasu iya cutar dashi, ko SU WAYE SU bazan taɓa barin su ba, duk sai nasa anƙulle su domin hukuncin kidnapping sai sunyi zaman gidan yari zasu san sun shiga wasan da bana su ba,
Juyawa tayi gurin Bodyguard ɗin cikin nuna su da yatsa ta kuma cewa "Wallahi idan wani abu ya sameshi bazan ƙyaleku ba, kuje duk inda zaku nemo sa sannan ina son ganin su ku haɗo da su nabaku nan da ƙarfe biyar ɗin yamma tana kaiwa nan ta juya fuuu tabar wajen, tare da sakin wani irin shu'umin murmushin gefen baki a hankali ta furta Allah raka taki gona umma ta gaida ayssha, mugun iri kawai, tana tafiya tana wannan maganar a hankali tana jinjina kai alamun akwai maganganu da yawa a ranta.
Wacce aka kira da Khatume ta kalli sauran saboda ita tana da sauƙin kai cikin sanyin murya tace "dan Allah kuje ku tsanan ta bincike ku gano inda yake kafin ƴallaɓai ya dawo kar kubari kowa yaji labarin nan, gudun tada wata maganar yanzu bari in shiga ciki zan sanar da Abbakar sai yasa Police su bibiyi hanya suma.
Godiya sukayi mata dan sunji daɗin yanda ta karɓi abun sun ɗauka ma abun zaifi haka zafi dan haka ba ɓata loƙaci suka shiga motocin su cike da samun ƙwarin gwiwa suka fita daga gidan ita kuma ta tarkata sauran suka bar gurin suma kowa ciki da mamaki da al'ajabi........
**************************
"Zaune suke a cikin wani ɗaki me faɗi babu komai a cikin sa, yana tsakiyar su hannunwan sa a ƙulle da igiya sai ƙafafun sa suma a ƙulle ko riga babu ajikin sa daga shi sai ɗan boxer bakin sa a ƙulle da salatif, kafin nan kuma saida suka fara ɗan sassamashi da duka saboda taurin kai da yaso yayi musu suka nuna masa nasu taurin kan yafi nasa,
Fari ne sosai irin har fatar nan, baida jiki sosai amma yana da ɗan tsaho kaɗan yana da kyau sosai akwai idanu ga hanci ga gashin kansa kamar na ƴan India a kwance,
Wayar sace a hannun su ɗaya tana ɗaukan sa videon jikin sa,
Me ɗaukar hotonce tace "BABYN BABY cire masa abun bakin sa muyi masa tambayoyi idan yabamu amsa ya tafi idan kuma bai bamu ba yaci gaba da zama anan, nifa yaron ma yaɗan burgeni aradu gashidai a ido babu ruwan sa amma sai ɗan iskan jiji da kai da wulaƙan ta mutane, kinsan saida mukazo ma nagane sa ranar da muka je restaurant ɗinnan,
Ɗaya tace "To yanzu ina jiji dakan gashi tunɓur agaban mu, yayi mana wani gigin mu saki videon ɗan iska, a social media muga ta tsiya,
Bayan ta cire masa, suka sakashi a gaba suna tayi masa sheƙiyanci da tambayar rainin hankali saboda ɗaukar sa suke yi, idan yaƙi bada amsa kuma sai su zabga masa mari a haka saida suka sa fuskar sa tayi ruɗu ruɗu ta kunbura saboda yaron ajebo ne ɗan madara jikan madara...
"Kai dan ubanka waye baban ka mun manta ma bamu san ko ɗan gidan uban waye ba muke wannan abun yakamata ya gaya mana full address ɗin sa ko ya kukace,
"Hhhhhh Barazana baki da mutunci wallahi to uban me zamuyi da sunan ubansa, ba damuwar bace tunda de burin mu yaci ka kuma mun samu abun da muke so ai ɗan koli yaci riba kamata yayi ma yanzu mumaida shi inda yafi kauri,
Wacce aka kira da Barazana tace "nima haka nake tunanin kar afara neman sa dan da alama anaji dashi.
"Yo Allah na tuba munajin tsoron wani ƙaton banza ne ni bari ma kuga abun da zanyi wayar dake hannun ta ta katse videon sannan ta shiga daddanawa maida dubanta tayi ga saurayin da yake gabansu sannan tace; Nace ba munajin ka ya sunan ka full name kuma muke so...
Banza yayi dasu tare da kawar da kansa gefe shi kaɗai yasan hukuncin da zai musu saidai kuma matsalar itace duk baiga fuskokin su ba domin duk sunsaka ƙananun hijaban nan masu haɗe da rigunan su, kuma hijabin me niƙab ne iyaka idanun su kawai yake iya gani,
"Good boy yaro yanason lafiyar sa kenan kaga yanzu duk inda muka ji sunan munsan mun taɓa haɗuwa da ɗaya daga cikin ƴan gidan.
Wani irin kallo ya watsawa wacce tace masa yaro ita kuma sai ta ɗage masa gira tare da ƙifta masa ido tace "yadai bana son kallon banza fa yanzu jikin yaro zai gaya masa, ta ƙarasa maganar tana watsa masa harara.
Tana gama faɗar haka ta miƙe tsaye tare da cewa "Beenish kinyi shiru tun ɗazu bakice komai ba,
Ɗan murmushin ta saki tare da cewa "Babyn baby babu abun da zance kawaidai nima bansan me yasa naji nayi hakan ba, jikina duk yayi sanyi ina ganin mu sake sa ya tafi kawai mungama dashi ai,
Jinjina kai tayi tace "hmmm mutanen ne suka motsa ko to yayi, "AMEELA mu fita dashi ko akwai wani abu nidai duk binciken da zanyi a wayar nan nayi idan mun zauna zakuji komai,
Ameela tace " amma fa babu wanda zai tuƙasa saidai ya tuƙa kansa danni bazan zama direbar saba, ɗazu ma Sa'a yaci,
Barazana ce ta miƙe tsaye tare da cewa "Kunsan me nayi kuwa na turawa ubansa videon nan fa yanzu dan haka muhaɗa tarkacen muyi gaba,
"FASHION...! kinsan kwa me kikayi amma dai ba da number ki ba ko,
Babayn Baby tayi tambayar cike da ɗan zaro ido...
Dariya tayi tace sai kace yarinya irinki me tunanin ƴan yara,
Harara ta watsa mata tace "wallahi tunanin yafi naki,
"Hmmm da kamar wuya kam saidai zan yarda idan kikace naki yafi nawa a fannin soyayya amma bayan nan babu ta inda zaki fini,
Yanayin ta ne ya sauya loƙaci ɗaya take kuma ƙwalla ta cicciko mata ido dan haka sai kawai ta juya ma ta fita daga gurin da kallon suka bita, suna me jinjinawa wannan halin nata, da badama kayi zancen soyayya a gaban ta shikenan zaka fama mata ciwon ta.
Ɗaya daga cikin su tace "Haba ZEE me yasa zakiyi mata wannan zancen bayan kinsan dai halin ta, yanzu in bamuyi Sa'a ba sai takai gobe tana abu ɗaya,
Dariya Barazana tasaki tace "Rabu da ita zamu shirya wallahi hakan nan nake so inga tana kukan abun dariya yake ban, matar Baby a gidan Babyn ta Allah ya shirye ta....
Beenish tace "Daman ke ai haka kika iya inbanda kisa mutun a gaba babu abun da kika iya gaskiya ki rage kinsan dai abun yana hoting ɗinta bai kamata kiringayi mata haka ba,
"Allah sarki ƙawata bari inje in rarrashi abata kunsan dai ba'a shiga tsakanin mu ko inma mutum ya shiga shi zaiji kunya bari inje ku fito dashi, nasan ko Aunty Babba zata iya sunkuto mana shi da hannun ta me albarka ko babbar mu ta faɗa tana kallon ƙatuwar cikin su, itama harara ta watsa mata kawai dan tasan idan ta biye mata nan zata sata a gaba taita yi mata iya shege da tsokana,