x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 13 - SU WAYE SU

  • 36001 words
  • 39000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 160

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
kai, ta dage, shi kama mahaifin sa zuwa loƙacin babu ruwan sa dan har sun ƙulla alaƙa ma me ƙarfi tsakanin shi da Yunusa Sarkin noma.

Shima kuma saurayin nata ɗan gidan me gari, ya gama shirya duk abun da zai faru loƙacin auren sai ya tayar da hankalin kowa dake cikin garin, ya shirya gaba ɗaya ƴan daban yankin akan yanda za'a yankawa mutane mutunci kuma kan me uwa jawabi za'ayi duk wanda ya hallaci ɗauren auren saidai a zo a ɗau gawar sa, da me gari yaji labari shima a wannan karan hankalin sa a tashi ba shiri yasa aka kirawo masa shi, yaja masa kunne amma tun agaban sa yace indai yaga hakan bai faru ba to saidai idan auren nan aka fasa aka aura masa ita, me gari yaga tashin hankali, yasa aka kirawo su Yunusa da Malam Rabo akan su haƙura da maganar auren su bawa ƴaƴan su haƙuri saboda ga abun da ɗan sa yake shiryawa, tun kan Malam Yunusa yayi magana, Malam Rabo yace ai aure babu fashi, yayi duk abun da zaiyi suka zasuyi nasu, shi akan me bazai jawa ɗan sa kunne ba, kenan saidai duk abun da yaga dama shi zaiyi a garin babu wanda ya isa ya taka masa burki to wallahi a wannan karon bai isaba, sun gaji da wannan son kan da yake nunawa mutane akan ɗan sa, duk abun da yake so a garin shi za'ayi,

Me gari baiji daɗin maganar sa ba, amma yana tsoron me zasuyiwa ɗansa shine kaɗai matsalar sa, dan yasan Malam Rabo cike da bai, baifiya nuna ko waye shi ba amma idan ka kaisa ƙarshe zaka gane waye shi, kuma baya shiga abun da ba ruwan s.....✍️

*Ayi haƙuri da wannan ba'anan naso tsayawa ba wlh fitace ta kamani ta gaggawa, banson yazamana kuma ranar ta wuce banyi ba gwanda ko yaya yake inyi muku, in sha Allah gobe zamu ɗora da labarin da muka fara*
[3/5, 11:48 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________


*_episode 14💧_*


💧💦محمدالرسوالله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

Me gari baiji daɗin maganar sa ba, amma yana tsoron me zasuyiwa ɗansa shine kaɗai matsalar sa, dan yasan Malam Rabo cike da bai, baifiya nuna ko waye shi ba amma idan ka kaisa ƙarshe zaka gane waye shi, kuma baya shiga abun da ba ruwan sa, shiyasa ba kowa yasan halin sa ba,

Babu abun da aka fasa da maganar biki,

Ranar wata juma'a Yunusa da Malam Rabo suka kira yaran nasu, tare da sanar dasu abun dake faruwa duk da sunji labarin haka, dan haka a loƙacin duk suka dan shiga damuwa gudun abun da kanje ya dawo, Amma sai Alhaji Rabo ya kwantar musu da hankali tare da basu wasu ƙulle ƙullen magani ya nuna musu yanda zasuyi amfani dashi, sunkwa ji dadin hakan da da ƙwarin gwiwar su suka bar wajen,

Da sati ya zagayo aka fara shirye shiryen ɗaurin auren, shima kuma Jambo(ɗan me gari) yana nan yana nasa shirin dan shiru ma yayi musu kamar baya shirya komai kuma bai kuma zuwa wajen mahaifiyar ta ba, itama taji daɗin da ya daina zuwa yi mata kashede akan ta dakatar da bikin, hakan yasa itama ta ɗan saki jiki.

Yau ta kama ranar Asabar ranar ɗaurin auren tunda aka tashi agarin da safe gari yayi wani irin kalla kamar za'ayi ruwa, sai wajen yamma aka fara taruwa a ƙofar gidan su Malam Rabo mutan gari na ta zuwa da ƴan uwa amma ba kowa ba ne yazo domin wasu sunji labarin abun da Jambo zaiyi ranar ɗaurin auren shiyasa wasu suka ƙi halartar wannan taron,

Ƙofar gida ta cika taf da mutane sai aure kawai za'a ɗaura dan har anfara gabatar da ɗaurin aurin,

Basu kai ga ɗaurawa ba, saiga tawagar Jambo sun danno kai tare da makaman su a hannu ko wane sai cije baki yake, suna ganin haka mutane suka fara shirin miƙewa daga gurin, Malam Rabo yayi saurin dakatar da su yace kar kuke ko ina, kuyi zaman ku, babu abun da zai faru ku tsaya, nan wasu sukayi saurin tsayawa dan koda sun tafi ma, ba tsira zasuyi ba,

Malam Rabo ne ya miƙe tare da zare malin-malim ɗin sa, ya nufi wajen su, tare da ɗauko wani abu baƙi me gari, daga inda ya fara tsiyayar dashi har ya kusa ƙarasawa kusa da su sannan ya ɗan ja da baya ya tsaya,

Duk da sun ganshi amma basu dakata da tahowar da suke ba, saida suka zo daf dashi sannan suka ɗan tsaya, Jambo ne a gaba, kafin suyi magana Malam Rabo yace; ko ku dakata da abun da kuke in ba hakaba zaku gane shayi ruwa ne,

Wata mahaukaciyar dariya suka kwashe da ita, Jambo yana nuna sa da yatsa, bayan sun gama dariyar Jambo yace; "Me ka is kayi ne zaka matsa mana mu wuce ko mu fara takan ka,

Da wani irin kallo Malam Rabo yake kallon sa kafin ya ɗaga hannun sa ya wanke sa da mari ya kuma kwashe shi da wani marin ta ɗayan side ɗin, yaran na ganin haka suka yunƙuro makaman su zasu saukewa Malam Rabo, saidai suna ɗagawa sai suka ji kamar anfisge mu su makaman duk suka ƙwace daga hannun su suka zube ƙasa, da mamaki suka kalli hannu su suka kalli ƙasa,

Daga nan kuma sai kawai suka gansu cikin daji dukan su hankalin su ya tashi har shi kansa Jambon dan tunda ya mare sa ya dafe fuska ɗaowar da zaiyi yaga babu kowa a gaban sa, gurin da suke duk ya zama daji waige waige suka shiga suna son gano me ya kawo su nan..

Malam Rabo dake gaban su yana ganin abun da suke ya watsa musu mugun kallo ya juya gurin masu ɗaurin aure yace aci gaba daga inda aka tsaya, wasu a gurin sunyi mamaki waɗanda basu san waye shi ba, ƴan uwa kuwa da nakusa dasu babu wanda yayi mamaki dan sun san halin sa zaiyi abun da yafi haka ma,

Nandai aka ɗaura aure sannan aka fito da abinci a kaci aka sha, sannan aka sallami kowa da kowa ya kama gaban sa, daddare aka kai amarya ɗakin mijin ta,

Bayan Malam Rabo ya kunce rufa idon da yayi wa su Jambo suka dawo cikin hayyacin su, amma kuma sai ya kasa taɓuka komai dole ya bar maganar a loƙacin, amma bayan kwana biyu ya dawo cikin hankalinsa yaci gaba da ɗaukan mugun ƙudurin sa a akan su, dan ya ɗau alƙawarin bazai taɓa barin su suyi rayuwa cikin farin ciki sai ya ƙuntata musu har ƙarshen rayuwarsa, amma a duk loƙacin da yaje gidan dan ya cutar da su, to sai yaga gidan ya shafe ko ya zama ruwa, tun abun na basa mamaki har dai yayi tambaya ga wani boka yagaya masa dalili kuma yace muddun yana so burin sa ya cika to sai ya fara gamawa da shi kansa Malam Rabo ɗin in ba haka ba, bazai taɓa cin nasara akan ahalin da ya shafi yarinyar sa duk abun da ta haɗa alaƙa da shi to bazaiyi nasara ba cikwa harda mijin da kuma duk wani abu da zasu haifa, dan haka a kullum burin sa yanda zai cinma burin sa ya kashe Malam Rabo,

Bayan aure suna zaman su lafiya yau da gobe sai Allah ayi faɗa ayi daɗi, har sukai wajen shekara biyu bata samu ciki ba, Saida shekara ta uku ta zagayo Allah ya azurtata da ciki,

Da Jambo yaji labari saida yayi duk yanda yayi ta hanayar wajen noman sa a ka zubar da cikin, ba daɗewa Allah ya kuma bata wani, shikam wannan karon baiyi nasara ba dan Malam Rabo ya tsaya akai basu isa su kuma yin wani abu ba, a haka har ta haifi ƴar ta kyakkyawar wacce taci sunan mahaifiyar ta ZAINAB, sai ake ce mata Abu,

A wata rana Jambo yayi nasara akan Malam Rabo tare da haɗin bakin matar sa, duk wani dube duben sa da yake yi baikai ga nan wajen, ba, ranar suna cikin ɗaki ta kawo masa abin batare da yayi zargin komai ba, ya hau ci, yana ci kuwa bayan wasu loƙata sai ya fara jin murɗawar ciki, nan ya hau riƙe ciki, tunda ya fara jin haka jikin sa ya basa da ƙyar inba ƙarahen shi ne yazo, dan haka tun kan yayi nisa ya mutun, ya ɗauki alƙalami da takarda loƙacin ba ta ɗakin, yayi sauri yayi rubutu me ɗan tsayi cikin dauriya, sai ya buɗe wata jaka yasaka ta aciki tare da rufe jakar sai ya shiga banɗaki ta nan, ya jefa jakar ta katanga, sannan ya fito yana fitowa, kuwa ba jimawa kumfa ta fara cika masa baki nan ya zame a gun, ya fara kyar ma,

Yana faɗuwa matar na shigowa nan ta fara watsa masa mugun kallo tana cewa alahamdulillah yau ƙuduri biyu ya cika, na cika masa burin sa kuma nima na cikawa kaina nawa burin yanzu ina da damar da zan auri wanda nake so,

Waya ta ɗaukata kira Jambo ta sanar dashi yabar duniyar, nan shi ma ya fara murna, sannan yace kar ta bari kowa ya shiga gidan yanzu zaije can gidan nasu,

Loƙacin Labaran(Ɗahiru, mahaifin Zee) suna zaune shi da Khadijah, sai Abu dake hannun mahaifin ta, tana ta ɗan kalle kalle, ita kuma ta haɗe rai ta juya masa baya, akan tace zataje gida yaƙi barin ta, saboda sun ɗan samu saɓani ta dena yi masa magana, shine ta daure tace zata gida shi kuma yace bazataje, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba, tana son haɗuwa da mahainta amma ya hanata, baisan dalilin ta na zuwan ba, shiyasa take ta cika tana batsewa,

Tashi tayi ta shiga ɗaki tana ɗauko mayafi tazo ta tsaya a kansa tana girgiza jiki tace kaban takaddar sakina sai in barmaka gidan gaba ɗaya, gwanda inyi rayuwa da mahaifina da in zauna dakai, ban taɓa neman abu na rasa ba, amma yanzu kai sai faman juya ni kake kamar waina a tanda to wallahi kayi kaɗan dan banƙi in baka auren ka ba,

Taƙaici da baƙin cike ne ya ishehi jin furucin da take, da sauri ya miƙe yana kwantar da yarinyar, binta yayi da kallo yace; "Ni kike gayawa haka, mahaifin naki yanada iko dake ne a yanzu bakida wanda ya wuce ni a yanzu zaki zaɓi mahaifin ki akaina ko to shikenan tunda haka kike so indai saki ne kin samu, bantaɓa tunanin haka daga gare ki ba, tsaki yaja yana shirin barmata gidan dan zuciyar sa a kusa take baya so zuciya ta kaisa ga aikata abun da zaizo yana danasani dan yana sonta baya son rabuwa da ita koda ta buƙaci hakan bayajin zai iya,

Ganin yana shirin fita yasa tayi saurin shiga gaban sa ta caƙumi kwalar rigar sa, tace idan kana ƙaunar uwar da ta haife ka ka sake ni inje inga mahaifina so nake in gansa me yasa bazaka fahimta bane, taja tsaki tana ci gaba da shaƙe shi.

Haushi ne ya ishe shi rufe idon sa yayi kawai yana ƙara buɗe su yace ki sake ni na riga na rantse bazan barki kije ba ko so kike inyi azumi baza ki sani kaffara ba, dan haka ki sake ni, in bahaka ba kuma zanyi miki abun da bazaki taɓa mantawa ba, banda buru insaki ki zubar da hawayen ki ko inga kinyi kuka ta sanadi na, amma yanzu in baki shiga hankalin ki ba, zaki ga me zai biyo baya,

Tsalle tayi ta dire tace bazan ma zauna da kaiba bare kayi min abun da bazan manta dashi ba baka isa kayi min komai ba, wallahi kaji na rantse in kaga nasake ka to ka sake ni, idan ka sake ni ai bana ƙarƙashin ka koh? Zan koma hannun mahaifana yaci gaba da kula dani ni banma san auren haka yake ba, da banyi ba, arasun Allah, duk abu a takurawa mutum baida ikon kansa, to wallahi baza ta saɓu ba bindiga a ruwa, kasake ni kawai dannagaji da zama dakai,

"Na sake ki saki biyu, in kin samu miji kiyi aure in sha Allahu nima bazan ƙara jin sha'awar zama dake ba, tunda har kika iya min wannan maganar, to kije shikenan ba, yana kaiwa nan ya fisge rigar sa ya ture ta gefe ya fita zuciyar sa na tafarfasa kamar zai tashi sama, dan shi kaɗai yasan bala'in da yake ciki.

Yana fita ta fashe da kuka, ta fara sunbatu akan meyasa dan ta nemi saki zai sake ta ɗin daman ba son ta yake ba tun farko kuka take sosai dan guri ma ta samu tayi zaman dirshen ta fara rero sa dan batajin zata iya auren wani bayan yasan shi kaɗai take so amma zaice taje tayi auren (hmmm mata mata! Mata iyayen mu, wai ka nemi abu da kanka amma idan anyi kazo kana kururuwa, mata da yawa haka suke, Allah ya shirya mu yaban zaman lafiya da mazajen mu )

Fitowar sa kenan yayi karo da Jambo, sun kakkafa mashi nan su, ganin yanda suke kallon sa ga makamai a hannun su yasa yaɗanji faɗiwar gaba, amma duk da haka bai dakata ba, yaci gaba da tafiya yana tunkarar su,

Yana ƙarasawa kuwa bai ankara ba suka raɗe sa da gora nan yafara ganin bibbiyu ya faɗi suka ɗauke sa daga gurin, wani daji suka kaisa zuwa loƙacin ya farfaɗo, a gaban Jambo suka tsugunnar dashi, saida ya gama yi masa dariyar mugunta, sannan yace; "Na kashe Malam Rabo tare da taimakon sirikar ka mahaifiyar matar ka, da sauri ya ɗago yana kallon sa, cike da mamaki da kuma tsoro, bakin sa sai motsi yake yana so yayi magana amma tsoro ya hanasa, saboda ba ƙaramar razana yayi ba da wannan maganar tasa,

"Yanzu waɗanda ya rage saura naka mahaifin daga shi sai taka uwar sai kuma matar ka sannan ƴar ka idan nayi maka haka na gama fanshe soyayyar da ka ƙwace min, na rasa wacce nafi so kaima kuma zaka rasa waɗanda kake so, amma kuma wani dalili ya shigo ya ruguzan wannan tsarin duk zan barsu su rayu babu wanda zan taɓa a cikin gaba ɗayan su a bisa sharaɗi ɗaya, kalma ɗaya tak zaka faɗa ka kare waɗannan rayukan, idan kuma kaƙi to zaka karɓi gaba ɗayan su,

Da sauri bakin sa yana rawa yace "eh na yarda wane sharaɗi ne indai zaka barsu da ransu nayi maka alƙari zanyi.

Ba Jambo kaɗai ba dukan su saida suka sanya mishi dariya yanda yake maganar cikin tsoro da karkarwar jiki,

"Idan ance kai ka kashe Malam Rabo kace "Eh....!

Cikin razanin da yafi wanda yake ciki ya fara jinjina kai hawaye na zubo masa daga idonsa,

"Oh baza kayi ba, to shikenan jeka, zaka samu gawar ko wannen su nan da kwana huɗu zakayi jana'izar su bayan kwana ɗaiɗai kullum zamu kashe mutum ɗaya, daga nan kuma za'a kamaka a bisa sharrin da zamu ƙulla maka, kai kayi gaba ɗaya kisan tare da kuma da wannan da baka amince ba, dan haka sai ka zauna cikin shiri, suna faɗar haka suka bar wajen yana tayi musu magana ma amma sunƙi su saurare sa,

Ya daɗe a wajen yana nazari da tunanin amma yakasa samun mafita, yakai wajen awa huɗu a wajen, da ƙyar ya iya tashi gwiwayin sa babu ƙwari, dan yana cikin tashin hankalin da baitaɓa shiga ba, wannan wace irin baƙar ranace a gare sa,

Yana shiga cikin garin ya fara jin surutun mutane akan mutuwar Malam Rabo a tsince ta ƙofar gidan sa, mutane har tarar sa suke suna gaya masa magana,

Shikam in banda hawaye dake ta faman zubo masa da shi kansa baisan loƙacin da suke zubowa ba, baisan inda yake tafiya ba kawai jefa ƙafa yake dan har ma ya fara dena jin abun da mutane suke cewa ba, gurin taron mutane yazo, ashe ƙofar gidan malam Rabo ne, loƙacin har ankai sa a dawo, nan aka fara taruwa akan sa wasu nayi masa tambayar anga gawa a ƙofar gidan sa shi ya kashe shi ko bashi bane wasu kuma nayi masa ta'aziyya ganin halin da yake ciki, dan wasu basa zargin sa sunfi zargin Jambo saboda ansan ƴar tsamar dake tsakanin su, shiyasa zargin ya hau kan mutum biyu ko Jambo ko Labaran.

Kamar tsohuwar mahaukaciya da ta ruƙa haka ta fito ko ɗan kwali babu akan ta ji tayi kawai ana cewa ga Labaran nan yazo yana kuka tazo ta kuma caƙumar wuyan sa tana jijjigasa tana kuka, tana cewa, "me yasa zaka kashe min mahaifi daman wannan ne abun da kake cewa sai kayi min abun da bazan taɓa mantawa da shi ba, duk ƙarfin abun da nayi maka yakamata ka ɗau fansa akan mahaifina nifa nayi maka bashi ba, meye nasa aciki, tsanar da kamin har takai ga ka kashe min mahaifi duk dan ka ƙumtata min, ta nan zaka rama abun da nayi maka,

Shaƙeshi ta kumayi sosai tana cewa "yanda ka kashe shi kaima sai ka bisa dan saina kashe ka, kuka take kawai duk tazama mahaukaciya tubaran, mutane sai janta suke suna ƙoƙarin rabasu,

Shi kam gaba ɗaya ya zama kamar mutum mutumi
End Ads