x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 45 - SU WAYE SU

  • 132001 words
  • 135000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 180

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ɗaya da Amarya dan batayi mata yanda take so shiyasa ta basa jituwa kowa ji da kaine dashi, ita take sakawa kuma take hanawa saboda Jabir baya zama kwata-kwata yau yana nan gobe yana can bashi da wata shaƙuwa sosai da iyalan sa, a fuska yana da fara'a da kirki saidai a zuciyarsa bashi da wannan mugun mutum ne na bugawa a jarida saidai ba kowa yasan hakan ba, hatta mahaifiyar sa Moha bata san wani halin sa ba marar kyau kawai ita dai yaje ƙasashe ya dawo ya zube musu duk abun da suke buƙata da kayan more rayuwa, to ita bata da matsalar komai tana cewa yi zaiyi indai matsalar kuɗi ce, mijin ta ya daɗe da mutuwa sakamakon heart attack da ya same shi saidai anyi binciken gano abun da ya haddasa masa hakan saboda anyi mamakin jin yanda loƙaci ɗaya ya kamu da wannan abun kuma ya mutu ta farar ɗaya amma ba'a gano ba har yanzu, tom kinji ɗan takaitaccen labarin gidan sauran kuma idon ki ya gane miki kya gano da kanki.

Jinjina kai Hajja Mama ta yi tana gyara zama ta ce "duk naji bayanin ki saidai ina da tambayoyi, wace mata ya fi so acikin su?sannan waye aminin sa, wanda suka fiye mu'amala dashi? Yana da nasa part ɗinne shima ko kuma a nasu part ɗin yake?

"Uhmm gaskiya bansan wacce yafi so ba, tunda banfiya shiga part ɗin su ba, nafi aiki a part ɗin Moha, aminin sa kuma akwai wani saidai bansan a ina yake ba, suna dai yawan zuwa tare, sannan yana da nasa part ɗin saidai babu wanda yake shiga, sai matan sa suma sai yana nan idan baya nan ƙullewa yake, saboda bashi da yarda yana da zargi, kuma ko ya yaga rashin gaskiya a tattare da kai zai koreka daga gidan, shiyasa har yanzu nakasa sakewa inyi abun da ya dace saboda ina tsoro wallahi, dan na taɓa jin sa a waya yana magana akan akashe wani saboda yana bibbiyar rayuwar sa, shiyasa nace kizo da kanki dan ɗakin nan masa bazai shigu ba duk yabi yasa Camera aciki saboda ba mazauni bane yasa yayi haka yaga masu shige da fice da cikin gidan sa...

"Bashida kusanci da ɗaya daga cikin ƴaƴan sa da yake iya sakar masa wani abun...

"Me yaran suka iya, ai babu abun da yake nuna musu na rayuwa kawai dai suci su sha suyi facaka da kuɗe shine kawai a gaban su...

"Amma ai naji ance yanzu ya dawo da zama baya ɗaya ya daina yawace yawacen da yakeyi?

"Gaskiya ban sani ba, amma dai nima naga ya daɗe a gida da ko wata cikakke bayayi amma yanzu yayi kusan wata huɗu bai tafi wata ƙasar ba, inajin to ya daina ɗin banda masaniya iya dai abun da nasani kenan na faɗa miki.

Nan dai suka ci gaba da tattaunawa ta tambaye ta ta bata amsa har suka gama suka kwanta, Hajja Mama kwanciya dai tayi kawai amma sai ta kasa bacci, Maha kwa tuni baccin gajiya yayi gaba da ita.

Miƙewa Hajja Mama tayi ta fito daga ɗakin wayar ta ta zaro cikin dabara ta daddana ta ta kira wanda suka zo ɗazu yana ɗagawa tace "Gee kana ina ne? bansan me yace mata ba, ta kuma cewa "matar nan da ƙarya a lamarin ta yanzu tagama min bayani amma nasan ta ɓoye min wasu abubuwan ina ganin kamar muyi musu kutse basai na tsaya wannan wahalar ba a cikin gidan dan bazan ɗauka ba, yanzu kawai babban abun da zanyi shine nan da kwana uku zanyi ƙoƙari in samu number sa, in kuma shiga ɗakin da zarar na gane wani abun kawai mayi binciken ta yanar gizo, amma dai zan gayawa Boss kawai yagaya min direct inda yake tunanin ina akwatin take dan har yanzu fa bangama yarda da shiɗinne ko bashi bane dole sai mun gano gaskiya kafin muyi wani abun, suna gama magana ta kashe wayar, wata number ta kuma kira.

Nan ma ana ɗagawa bayanin da tayiwa Gee shi ta kuma yiwa uban gadan nasu, sannann ya kuma gaya mata wasu sirrikan cikin gidan tunda abokin sane, godiya tayi masa, tana kashe wayar ta saki murmushi tace "Boss kun kusa zuwa hannu.

Still dai sai naga ta kuma dialing ɗin wata number, anan ɗagawa ta saki wani murmushi tare da cewa "ranki ya daɗe Allah ƙara nisan kwana, aiki fa na kyau yanzu haka ina cikin gidan sirikinki, zamu fara bincike, kuma ina jin ƙamshin nasara da yardar Allah wannan karon zamuyi nasara komai zaizo ƙarshe, saidai ina so ki kuma yiwa Hajiya Dannar magana akan wannan matar fa, dake hannun Rabi dan barinta a hannun su akwai matsala, kuma dole saida ita wasu abubuwan zasu bayyana, dan ba komai muka sani ba.

Shiru tayi tana sauraron ta, kafin ta ce "to shikenan sai najiki mu kwana lafiya, sannan ta kashe wayar, juyawar da zatayi taga kamar inuwar mutum ta bayanta, fasa juyowar tayi tana satar kallon gurin ta gefen ido, sosai tayi mamakin ganin Maha ce, tana shirin juyowa tayi saurin komawa ɗaki ta kwanta tare da rufe idon ta alamun bacci take batasan kuma ta riga da ta kamata ba......

$$$$$$$$$$$$$$$$$$$

___Sai wajen biyun dare aka sauke su Beenish a gida, da ƙyar duk suka iya shiga gidan jikin su duk a mace tunda suka taho kowa da abun da yake tunani, daman Zee ce uwar surutu to kuma yau ansamu akasi babu bakin maganar, RK ya kashe shi da bulala.

Ko da suka shiga saida sukai ta bugu kafin Maryam tazo ta buɗe musu, tayi mamakin ganin su, bata taɓa tunanin zasu dawo ba, dan har ta koma gurin Babyn baby gudun karta tashi taganta ita kaɗai, Allah ya sama bata farka ba har yanzu.

Shigowa duk sukayi amma babu wanda ya samu damar yin magana dan basu da wanan ƙarfin, Zee kam har yanzu sharar hawaye take tana ta shafa duk inda taji ya tashi.

Ganin su haka yasa Maryam shiga tashin hankali ta shiga tambayar su amma duk shiru sukayi mata saidaga baya ne ma, Ameela tayi ƙarfin halin ce mata ta bari da safe sayi mata bayani, dole ta rabu dasu suka wuce ɗakin su itama ta wuce nata ɗakin, tana ta jinjina lamarin nan nasu.

A ranar dai bacci ɓarawo ne kawai ya ɗauki Zee dan da ta rufe ido sai taji kamar ya ɗaga bulalar zai sauke mata sai tayi sauri ta buɗe ido, haka tai tayi da ƙyar ta samu bacci ya sace ta, Beenish ma dai da ƙyar ta iya yin bacci da ƙudirin aranta na ɗaukarwa kansu fansa akan banzancan...

$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$

*Hajiya Rabi*

____Har yanzu hankalin ta yaƙi kwanciya da Bulama gani take kamar zai koma ya ɗauke mata jika kuma tasan zai iya ɗin tunda ya faɗi hakan, ga kuma ɗauke Fateema da yayi, yanzu taya zata fara gayawa mutanen nan anɗauke ta, ga ƴarta da aka ɗauke kuma, abun ya haɗar mata goma da ashirin, dole gobe tayiwa Bulama dirar mikiya tasan yana garin, sai ta fito masa a mutum zai fito mata da su.

Da safe kuwa kamar yanda ta ce "tana tashi daga hotel ɗin ta shirya ta fito tare da drivern ta suka ɗauki hanya, ƙarfe takwas da ƴan mintuna ta dira a gidan me gadi buɗe musu kawai yayi batare da wani bincike ba, tunda shi ba wani sanin halin me gidan yayi ba, bare yasan ba kowa ne zaizo ba,

Suna shiga sukayi parking a gaban gurin, sannan ta fito cikin sauri ta ƙarasa gaban ƙofar tare da yi masa bugun hauka, bam bam bam kawai take bugawa ba ƙaƙƙautawa irin bugun nan me cin rai inkaji anayi ma irinsa.

Bulama dake kwance gefen Ameca ta wani rirriƙe sa tana ta bacci abun ta, shikam daddana wayar sa yake cikin kwanciyar hankali yana cigaba da harƙallarsa, yaji ana yi masa wanna mahaukacin bugun, da sauri ya ƙwace jikin sa daga gurin Aunty babba, hakan da yayi yasa ta farka har zata kuma caƙumosa ya ture ta yayi sauri ya tashi,

Jallabiya ya ɗauka ya zura ya fita itama cikin sauri ta tashi zaune tana mamakin jin irin bugun da ake, tashi tayi ta shiga banɗaki.
Yana zuwa ya buɗe cike da son saukewa duk me wannan bugun masifa, yana buɗewa yayi tozali da ita ciki da mamakin abun da ya kawo ta ya tsaya tana kallon ta,

Haɗe rai tayi tana bi ta gefensa kawai ta shiga cikin falon, juyowa yayi a fusace ya ce "uban me kika zo yi min gida da wannan safiyar sai kaci kin bini bashi, waike yaushe Saliyo hankali ne, jifa bugun da kike ɓalla min ƙofa zakiyi kina da kuɗin da zaki biyan....

"Kaga Malam dakata ba shirme ne ya kawo ni ba, batare da ɓata loƙaci ba kagaya min inda ka kai matar nan da kuma ƴata sannan ka fita harkar jikata idan ba haka ba, wallahi wallahi wallahi sai kayi da nasanin sanina cikin rayuwar ka saina nuna maka wayon ka na banza ne, wallahi sai na tona maka asiri idan kana san zaman lafiya kagaya min!

Kamar gunki haka ya tsaya kallon ta, cike da mamakin akan abun da take magana, yadai san maganar jikar ta baya ga haka kuma baisan sauran zancen da take ba.

"Jamboo! ta kuma kiran sa cikin tsawa da ta karaɗe duka falon,

Shima cikin tsawar ya mayar mata da martani tare da jan hannun ta, tana ƙoƙarin ƙwacewa tana ya sake ta amma taka sa saboda ƙarfin su ba ɗaya ba, fita yayi da ita daga cikin falon ya rufo ƙofar tunawa da yayi Ameca na cikin gidan,

Ke Rabi wai maganar me kike haka, ni ina ruwana da wannan maganar taku, meye haɗina da matar nan, wannan matsalar ku ce ba tawa ba kinsan bana shiga harkar da batawa ba, ƴar ki kuma meye haɗina da ita ko, me tayi yi min kinsan dai bana jinkiri akan ɗaukar fansa kawar da mutun yafiye min komai sauƙi, dan haka kiyi saurin dawowa hankalin ki, jayayya da Bulama ba abun wasa ba ne, bakin rijiya ba gurin wasan yaro bane, ni zakiwa barazanar tonawa asiri kinfi kowa sanin wanene ni..✍️



*Duk meson na saka shi a group ɗin Su waye su yayi min magana, ta wannan number 08124226526 iya littafin su waye su, dan Allah kar wanda ya min magana akan meman wani littafin, ko yace min in saka sa a group ɗin littattafai, to wallahi duk wanda yayi min magana bazanyi reply ba, sbd an saba yi min irin haka Ni ga abun da nace amma sai wasu si ta tambayata in tura musu littattafai dan Allah ku daina bana so ba littattafai nake turawa ba nawa kawai nake turawa*

_Ƴan facebook kuma kuyi searching ɗin su waye su hausa novel group kuyi join akwai a ciki tundaga farko har inda aka tsaya, dan ba kullum zanna posting a kowane group ba_
[4/19, 10:24 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*



(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)

_______*08124226526*_______


*_episode 40💧_*



💧💦محمد لرسول الله...!💦💧



*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*

Bismillah..✍️


______Ke Rabi wai maganar me kike haka, ni ina ruwana da wannan maganar taku, meye haɗina da matar nan, wannan matsalar ku ce ba tawa ba kinsan bana shiga harkar da batawa ba, ƴar ki kuma meye haɗina da ita ko, me tayi yi min kinsan dai bana jinkiri akan ɗaukar fansa kawar da mutun yafiye min komai sauƙi, dan haka kiyi saurin dawowa hankalin ki, jayayya da Bulama ba abun wasa ba ne, bakin rijiya ba gurin wasan yaro bane, ni zakiwa barazanar tonawa asiri kinfi kowa sanin wanene ni.


"Jambo duk abun da zaka yi ka yi amma muddun baka dawo mini dasu ba, zaka gane kurenka, kasan ko dame dame murna tafi magarya daɗi, kasan ko da kwana ɗaya na girme ka, dan haka kabinin a hankali yanda kake tunanin kanka to ni na wuce tunanin ka, kar nake kallon ka, a yau ɗinnan idan baka dawo min da su ba zaka ga me zai faru ka jira!

Jinda gaske dai take tunanin ta shi ya ɗauke su, ya sauya kalar fuskar sa, yace "Rabi idan ma wasa kike kidaina kinsan bana son abun da banyi ba ace nayi, ni ban ɗauki kowa ba, amma kin zo sai faman ihu kike min da sanyin safiyar nan, dan Allah ki barmin gida kike ki zargi wani amma banda ni. Yayi mata maganar cikin lallami da lamana, amma ita ina tayi nisa saima ƙara rufe sa da masifa da tayi ta inda take fita bata nan take fita ba, abun shima ransa yayi mugun ɓaci ya shiga zazzaga mata masifar saura kaɗan ma ya rufe ta da duk yayi saurin saita kansa yana nuna mata ƙofa da ta fice ta basa guri ko ya zane ta wallahi yayi mata dukan tsiya, jin hakan yasa itama taci gaba da hayyayaƙo masa, tun yana haƙuri har saida tasa ya wanke ta da mari rikici sosai ya ɓalle a tsakanin su, suna wannan abun Aunty babba ta fito saidai bataji komai ba, suna ganin ta Bulama yayi shiru ya juya ya haɗe rai yace ta koma ciki idan tayi magana kuma sai tabar masa gida, tasan cikin fushi yake hakan yasa kawai ta koma saboda daman bata san abun da ya haɗa su ba.

Rabi dai bata bar gidan ba saida sukayi kaca kaca sukayi rabuwar baran baran, ta tafi zuciyar ta kamar ta fashe, shima a gurin nasa hakan ce ta faru a ƙufule ya shiga cikin falon, yana shiga, Ameca ta fito daga ɗaki, cikin sauri ta taho gurin sa tana cewa "my dear I'm filling hungry, tana maganar tana ƙarasowa inda take zata rungume sa, da sauri cikin fushi ya turata gefe saura kaɗan ta faɗi amma ko inda take bai kalla ba, ya nufi ɗaki, tayi mamakin abun da yayi mata amma duk da haka bata ɗauke sa matsayin laifi ba, ta kuma bin bayan sa dan tana tunanin baya cikin hayyacin sa, gwanda taje ta rarrashe shi ko zuciyar sa zatai sanyi,

Yana daf da shiga ɗaki ta cimmasa, a kusan tare suka ƙarasa shiga ɗakin, ta baya tayi saurin rungumo sa, tana shirin ta fara yin magana yayi wani irin juyowa zai cire ta amma sai yaji ta riƙe sa gam ƙara yunƙuri yayi a karo na biyu, amma still sai yaji ya kasa, cikin tsawa yace "dalla malama sakar ni ki fice min daga ɗaki,

Maƙe kafaɗa tayi cikin alamar shagwaɓa tace "haba dear please mana kayi haƙuri koma me ya faru ka nutsu sai kaban labari, kar ka bari abun da ta gaya maka ya ɓata maka rai, ni bazanso ganin ka cikin wannan yanayin ba, ka dawo yanda kake,

Bata ankara ba yasa duka ƙarfin sa ya wani kalar janye jikin sa sannan ya haɗa hannun duka biyu ya tura ta waje da ƙarfi, yana turata ya rufe ƙofar ji yayi gaba ɗaya haushin ta yake ji ya tsaneta sai kace ita tayi masa laifin, kawai ji yake kamar yayi tsalle ya gansa agaban abar sonsa, da yayi niyar yabita a hankali amma abun da rabi tayi masa sai ya nuna mata isar sa, ayau sai ya ɗauke yarinyar nan in ta isa ta dakatar da hakan.

Cak Aunty babba ta tsaya takasa motsawa daga zaunen da take saboda turowar da yayi mata bata wasa bace, har saida ta faɗi daɓar, ba ƙaramin mamaki tayi ba ganin yanda ya sauya loƙaci ɗaya, amma duk da haka tasan ba laifin sa bane laifin matar da ta zo ne kuma ko wace ita sai ta gane kuren ta dalilin ɓatawa masoyin ta rai da tayi, ta ɓata mata yanayin sa, da tuni yanzu suna zaune lafiya yana bata kulawa suna shan soyayyar su, amma tazo da Safe nan ta ɓata musu loƙaci, da ƙyar ta iya miƙewa zuciyar ta ciki da jin haushin matar nan da bata san ko wace ce ba, falo ta koma ta zauna, ta daɗe a agun, da taji dai takasa jurewa ta kuma tashi tazo bakin ƙofar ta ci gaba da bubbuga masa tana basa haƙuri cike da rarrashi, amma yin duniya ko motsinsa bata ji ba, komawa falon tayi gashi wata baƙar yunwa take ji me kaɗa hantar ciki, ta dudduba taga ko da kitchen amma ta rasa inda yake, haka ta haƙura ta dawo falon ta kuma zama, tafi awa huɗu tana zaman jiran sa, sannan ya fito daga ɗakin, da sauri ta kuma miƙewa zata kuma tunkarar sa yace "don't ever touch me,

Tsayawa tayi tana binsa da kallo tare da marairaicewa kamar zata yi kuka, tace "Uncle kar ka min haka, bafa
End Ads