x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 18 - SU WAYE SU

  • 51001 words
  • 54000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 159

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
juya gefe ta goge saboda bata so kowa ya fahimce ta.

Da sauri Ameela ta jawo ta ta rungume ta tana bubbuga bayan ta tace; "Haba Babyn baby meye hakan kuma, duk me ya kawo wannan maganar da har zaki sa kanki cikin damuwa haka, duk dan saboda naƙi zuwa zaki na wannan maganar....

Ƙoƙarin janye jikin ta tayi cikin kukan tana cewa; "dole inyi me yasa za'ace kike kina cewa bazaki ba, ki sake ni kawai mun rabu dake amma kema sai ki rabu damu... tana maganar tana ci gaba da ƙoƙarin janye jikin ta daga riƙon da take mata.

Ƙara riƙe ta Ameela tayi, cikin sanyi murya tace; "shikenan naji zanje ki daina kuka Auta Please.!

Ɗan janye ta tayi daga jikin ta, ta shiga share mata hawayen tana ɗan ƙaƙaro murmushin yaƙi tace; "komai ya wuce kar ki ƙara yin tunanin komai, kuje kuyi test ɗin kar ki bar komai a ranki da zaisa ki faɗi a test ɗin ki maida hankalin ki kai, me kike son ci idan munje gida in dafa miki?

Jikin ta a sanyaye tace; "komai ma ki dafa zan ci.

"Tom shikenan zan miki favourite food ɗin ki, kiyi ƙoƙari sosai kinji?

Kai ta kaɗa mata kawai amma duk da haka hankalin ta ba'a gun yake ba.

Sakin ta tayi tana juyawa tace "Zee muje...
tana faɗar haka tayi gaba bata kalli kowa ba.

Bayan ta Ammu tabi da kallo tana ɗan girgiza kai a hankali ta ce; "She is never change!

Ɗan murmushi Barazana tayi tana kuma jinjina wannan lamarin nasu, kallon ta tayi ta ce; "Kiyi haƙuri zata canza watarana"

"Hmm Ameela kenan halin ta sai ita, Allah ya shirye ki. cewar Aunty Babba.

"Aikam dai, Ammu mu tafi kar ta fusata ta canza hanya, ba kamuwa take ba.

"Hmmm muje to, naga har ta shiga mota, gaba tayi barazana tabi bayan ta, har sun ɗanyi gaba tayi saurin juyowa ta ce; "oh Faheema koh? Ga su Beenish nan sai kiyi musu bayanin abun da yake tafe dake, Beenish ga Faheema nan.... Tana faɗar haka ta juya cikin sauri tabi bayan Hajiya Dannar.

Beenish ce ta kalli Faheema ta ce; "muna sauraron ki, zamu shiga test.

Murmushi ta ɗan yi sannan ta ce; "ah ba wani abu bane naga kawai kuna burge ni nazo mu gaisa, gashi kuma kuna sauri ma haɗu gobe bari inje nima,

Ita ma mmurmushin tayi mata "ayya to shikenan Allah ya kaimu, mun gode sai anjima... Daga nan ta riƙo hannun Babyn baby sukayi gaba, a gun suka barta tsaye tana ta faman bin su da kallo, daga ƙarshe ma sai ta koma gurin ta zauna kawai ta rafka ta gumi tana tunanin a bun da ya faru yanzu a tsakanin su, duk maganganun da suke kawai bin kowa take da kallo ta rasa wane irin tunani ma zatayi a kansu, yanda suke gudanar da rayuwar su, sai taji sun bata tausayi kuma sun ƙara shiga ranta.... Ta daɗe a gun tana tunani kafin daga bisani ta tashi ta nufi office ɗin Dr. Aveed...

Ameela ce ta shiga driver seat a motar su, Hajiya Dannar tana ƙarasawa ta buɗe motar da kanta ta shiga gefen ta, Barazana kuma ta shiga baya, sannan taja motar suka bar cikin makarantar.....

Maimakon ta doshi gidan su sai kawai tayi doshi wani waje dasu, saida sukaje wajen ma sannan Barazana da hankalin ta ke waya ta ɗago taga gurin sannan tace; "Ameela meye hakan ba gida zaki kaita ba naga munzo nan wajen?

Eh ai ba daɗewa zatayi ba, yanzu zamu rabu zansiyiwa baby abu ne a waccen plaza ɗin ta faɗa tana nuna ɗan nesa dasu,

"Hmm kawai tace mata bata ce komai ba, tasa kai ta fita daga motar tare da rufo musu ƙofar,

"Ina jin ki... Ameela ta faɗa idon ta na gefen window tana kallon waje.

Kallon ta kawai take amma ta kasa magana, saida taja loƙaci me tsawo tana ta faman thinking....

"Mama na wai har yaushe wannan ƙiyayye zata ƙare ne, me yasa baza ki haƙura ki dawo wajena ba, ko ki yafe min, har yanzu kina min kallon me laifi, amma ina so ki ƙara ban loƙaci zan gaya miki duk abun da kike so, ko ban faɗa miki da kaina ba loƙaci zai gaya miki, ki ƙara ban loƙaci kinji...

"Eh naji zaki iya tafiya idan shi kaɗai ne ya kawo ki"

Dafe goshin ta tayi tana jin wani iri aran ta, amma da haka ta ƙara daurewa, ta ci gaba da cewa; "babu abun da ya kawo ni da ya wuce inzo ingan ki, saboda nayi missing ɗin ki
[3/5, 11:53 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*

(THE WRITER OF 💅SARKI SAMEER 💅)

______________________________


*_episode 19💧_*


💧💦محمد لرسول الله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

__Tana fita Ameela ta fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya, jingina kanta tayi ajikin mota ta ce; "Ammu..! Ammu..! Ammu..!!!! Sai kiran ta take tana kuka.....

Saosai take kuka tana dafe zuciyar ta, "Ammu me yasa? Me yasa?

Ɗaukar sarƙar da kuɗin tayi ta damƙe su ƙam a hannuwan ta duka biyu sannan ta kaisu gurin bakin ta, ta ɗora bakin ta akan su tana sumbatar su, a haka ta barsu hawaye sai zubowa suke daga idanun ta kamar famfo fuskar ta tayi jaa saboda tsabar kuka.

A haka Barazana tazo ta tarar da ita, buɗe motar tayi ta shiga tare da rungumo ta, tana bubbuga bayan ta, batace mata komai ba suka ci gaba da zama a haka har saida taji tayi shiru dan kanta sannan, ta rabu da ita tare da cewa ta fito daga wajen ta jasu su tafi gida, haka sukayi exchanging gurin Barazana ta jasu, tunda suka hau hanya kuwa babu wanda yayi magana har suka je gida,

Ko da suka shiga gidan kuwa, Su Beenish sun dawo gida suna falo suna ta jiran zuwan su, suna shigowa kuwa suka bisu da kallo.

Cikin fushi Beenish tace; Ina Ammun?

"Ta tafi" Barazana ta bata amsa.

Ameela kam bata kula kowa ba kuma bata kalli inda suke ba duk da tasan su ɗin kallon ta suke amma sai kawai ta wuce ɗaki ta bar su awaje.

Da sauri Babyn baby ta yunƙura zata bita Beenish ta dakatar da ita, ta hanyar ruƙo hannun ta,

Guri Barazana ta samu ta zauna tana sauke ajiyar zuciya tare da cewa; "ku barta ta fara samun nutsuwa ni bansan me suka tattauna ba dan fita nayi na basu guri, naga itama Ammun idon ta fal da ƙwalla ta wuce mota dan ko haɗa ido dani barayi ba.

"Hmmm Ameela bansan wace irin zuciya gare ta ba, duk da itama Ammun na da laifi amma yakamata zuwa yanzu su san me sukeyi gaba ɗaya, wallahi bana son wannan abun da sukeyi duk da kowa na da laifi,

"Ai kam dai amma koma meye ina tunanin wannan zuwan ba kamar sauran zuwan da take yi ba, kamar ta canza, tunda kikaga daga ita sai drivern ta take yawo, kuma naga kuɗi a hannun Ameela tunda ta karɓa wataƙil da kwai wani abun a ƙasa, saidai mu jira idan ta sauko ta gaya mana yanda sukayi da ita.

"Hmm to ai shikenan, mu bar maganar yanzu, ki zubo abincin dan mu har munci, Baby ke kuma ki zuba ki kaiwa Ameela ki tabbatar taci.

"To ta amsa dashi tana miƙewa ta nufi hanyar kitchen ɗin har taje daf da shiga, Barazana tace, "Baby! Ni ma ki zubo min.

Itama da to ta amsa sannan ta ƙarasa shiga kitchen ɗin nasu......,

*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*


*GHAMBURJ*

___Wata ƴar tsohuwa ce take ta sambaɗa gudu a tsakiyar wani ƙaton fili da baka ganin gida a guraren sai bishiyu kawai suma tsalli tsalli,

Kai baka ce ta tsufa ba, ganin yanda take gudu, dan a ƙalla zata kai wajen shekara sittin da wani abun, jinkin ta ɗan tsamurmiri amma a dake take, kuma tana da ɗan tsawo, jikin ta sanye take da riga da zani sai wani yalolon mayafi da ta yafa akai, ga wata jaka ƙatuwa dake saƙale a jikin ta, yayin da wasu ƙartin maza guda uku suke rufa mata baya suna binta.

Gudu take felfalawa kamar ba gobe, suma kuma basu fasa bin ta ba, ganin tayi musu nisa kuma tazo inda zata zo yasa ta tsaya kafin su ƙaraso daf da ita tayi sauri ta cire mayafin ta tare da wurga musu shi, cire jakar tayi tare da wurga ta wani ƙaton ruwa dake ɗan nesa da ita kaɗan tana dai iya hango sa, sannan ta cire rigar jikin ta ta tsige zanin dake jikin ta, sai gata daga ita sai riga da wando wandon ma iya gwaiwar ta, ɗan kwalin kanta ta zare tare da ƙara gyara parking ɗin gashin ta da furfura ta gama cinye sa, ɗan kwalin da baida girma ta ɗauka ta rufe rabin fuskar ta dashi sannan ta ɗaga rigar ta saiga wasu ƙananun wuƙaƙe guda biyu, zaro su tayi ta riƙe su a hannuwan ta dama da hagu sai kawai ta tsugunna agun ta sunkuyar da kanta zuwan su kawai take jira,

Gudu suke suma ɗaya daga cikin su yana gudun yana waya, suna zuwa daf da ita sakawai suka ka burki a gun suka kasa ƙarasowa ganin yanda ta ɗago tana kallon su idanun ta kawai suke gani gata da manyan idon yanayin yanda take kallon su yasa suka ga kamar ba mutum ba,

"Ku taho! Ku taho!! Ku taho mana...! ta faɗa tana daka musu tsawa tare da miƙewa tsaye,

"Ki sauke wannan wuƙar kar ki kuma tunanin guduwa ki tsaya anan gurin, ɗaya daga cikin su yake gaya mata haka.

Dariya tayi da ƴar murayar ta da bata fita sosai tace "gani kuzo ku kama ni mana tana faɗar haka kuma tayi cilli da wuƙaƙen tana dunƙille hannun ta alamun su taho ta shirya da hannun ta.

Matsawa suka fara yi kusa da ita, tare da rarrabewa zasuyi mata tara tara, nan kwa ta fara wahalar da su tana zille musu, suna cikin haka kawai sai taga yuyar ƴan sanda suna tunkaro su,

Da baya da baya ta fara ja tana tunkarar wajen makeken ruwan nan, da ta wurga jakar,

Da sauri ƴan sandan duk suka ƙaraso wajen suma suka shiga bin ta, wasu daga cikin sune suka zaro bindugu.

Juyawa tayi zata gudu, ɗaya yace kina ɗaga ƙafar ki daga nan gurin zan harbe ki, ki tsaya anan wajen.

Tsayawa tayi tana ɗaga hannunwan ta sama, takowa suka ci gaba dayi suna tunkarar ta ganin sun kusa yasa ta kuma yin taku uku ta matsa daga kusa dasu,

"Kar ki kuma motsawa daga nan gurin ki tsaya anan, amma bataji ba da wayo da wayo suna mata barazan tana kuma matsayawa har saida taji ta a inda take son jin ta,

Suna daf da ita tazarar su bata fi taku huɗu ba, kawai sai ta ɗaga hannunwan ta sama tana juya musu baya, duk basu san me ta tsara ba dan basu san da ruwa ba agun dan ya ɗanyi zurfi idan baka san da shi ba bazakace da ruwa ba agun.

Tana kallon su ta gefen ido tsiran su baifi taku ɗaya ba, kawai ta daka uban tsalle ta faɗa cikin ruwan nan jikake fumm... Har ta ɓace, dan duk a tsorace sukayo gurin ruwan suna ta faman leƙe amma basu ga ko motsin ta ba.

Turus duk suka tsaya kowa mamaki ya gama kashe su,

Ɗaya daga cikin su ne yace; "To ku ya kai kuka bari har ta ɗauki jakar ta gudu baku kamata ba ku da angama tsara komai daku akan kar ku bari kowa yagan ku sannan duk wanda yazo ɗauka kuyi sauri ku kamasa kar ku bari ya gudu, kuma ina bindigar hannun ku meye amfanin baku ita da baku harbe ta ba ko a ƙafane haka akai daku? Sai faman magana yake musu me tafe da faɗa dan ransa ya ɓaci rashin kamata.

"Sorry Sir wallahi bamuyi tunanin ita ce me ɗaukar kuɗin ba, bayan munyi waya munce munzo sai aka ce mu ajiye ta agun sannan mu ajiye bundugun da muka zo dasu in ba haka ba kuma to mu koma hakan yasa muka a jiye a ƙasa tunanin mu idan sunzo ɗauka sai muyi saurin ɗauka mu harbesu, amma sai kawai mukaji ihun wannan matar muka juya da sauri muka ga ta tsugunna tana ruƙe ƙafar ta hakan yasa muka bar bundugun a wajen muka tafi wajen ta, muna daf da zamuje gurin kawai ta miƙe cikin sauri da bamu ankara ba tazo ta ɗauke bundugun sannan ta saita mu tace duk wanda ya kuma motsawa daga inda yake sai ta harbe mu, dole muka tsaya, ta saita mu da ɗaya sauran kuma duk zare musu bullet ɗin ta zubar tare da jefar da bundugun saida take saitin jakar sannan ta ɗauka ta fara gudu sai loƙacin muka bi bayan ta muma, bamu san na loƙacin da ta jefar da ɗayar bindigar ba kawai gani mukayi bata hannun ta, muna gudun har muka zo nan kaji yanda mukayi..

Iska ya shaƙa tare da furzar da me zafi daga bakin sa, yana dafe kansa yana yarfa hannu tare da cije baki, ji yake kamar ya harharbe su....

"Amma baku da hankali ku zaku je gurin ta, yanzu gashi nan kun jawo mana asara, yanzu me kuke so muyi idan mun koma, Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un kuna so mu koma gida yanzu babu yaran babu kuɗin kuma babu wanda muka kama sunyi ci riba biyu kenan wannan uban maƙudan kuɗi da aka basu, sun ƙwace kuɗin kuma basu bada yaran ba wannan wane irin abu ne....

Su tsuru-tsuru sukayi gaba ɗayan su kowa na tunanin mafita, ɗaya ne ya kuma cewa;

"Ogah kuma daman kasan yace shi kuɗi ba damuwar sa bace dan haka kar ayi wani yuƙurin kaiwa waɗancan farmakin kama su kawai mu basu kuɗin su bada yaran kar ayi wani abun da zaisa su hana yaron gashi kuma abun da yake gudu ya farun ya faru..

"Ai ba laifin mu bane danni wannan abun nafi ganin laifin commissionana tunda duk shi ya tsara mana hakan gashi kuma ba'ayi nasarar komai ba...... Nan dai sukai ta kace nace ɗin su su kaɗai sun kasa samun mafita dole suka kaɗa bujen su suka koma gurin motocin su suka tafi gida kowa da zulumin abun da zai faru idan sun koma......

Iyo kawai take acikin ruwan nan saboda tsabar ƙwarewar ta ko motsin ruwa ta sama baka gani, kamar kifin ruwa haka take yawo cikin ruwan, ba ƙaramar tafiya tayi ba a cikin ruwan, sannan ta kawo bakin gaɓa, tana fitowa ta tarar da su a tsatstsaye suna jiran ƙarasowar ta....

Ɗaya daga cikin su ne ya ɗanyi murmushi yace; "Hajja Mama ai mun ɗauka sunyi gaba dake ne da mukaji shiru yayi yawa,

Hannu tasa ta share ruwan fuskar tana girgiza kanta tana girgizar da ruwan dake kanta.

"Me yin hakan kuwa ba ƙaramin shiri zai yi ba, "bani kaya tana miƙa wa na gefen sa hannu. Bata yayi sannan suka juya baya.

Suɓalle wandon tayi sannan tasaka wani sket ɗan ƙarmin shima baikai mata har ƙasa ba, sannan ta cire rigar ta sauya wata, tana gama sakawa ta ɗanyi musu gyaran murya sai loƙacin su juyo.

Wata ƙatuwar jacket ya kuma rufa mata ta zura a jikin ta, sannan ya bata wata hula me hat (hula me faɗi, irin ta ƴan chaina kun gane ta) sannan ta karɓi glass ta ƙwama a idon ta, sannan ta karɓe jakar da ta cillo musu ɗazu tayi gaba, binta suka yi a baya.

Tafiya kaɗan sukayi suka kuma zuwa wajen wani ƙaton ruwan, jirgin ruwa suka shiga me shegen kyau, sannan matuƙin sa yaja sukayi gaba.

Nan ma saida sukayi tafiya me ɗan tsayi sannan suka kuma zuwa bakin gaɓar, sauka tayi daga cikin jirgin ita kaɗai, ta kuma nufar wata hanyar, su kuma daga nan suka juya basu bita ba.

Daidai wani waje ta tsaya tare da tsugunnawa ta kwashe ƙasar dake gurin saiga ƴar ƙaramar ƙofar ƙasa, ɗaga ta tayi ta buɗe matattakalar ta farawa takawa tai tashiga har saida ta sauka ƙasa sannan ta kuma yin gaba can kuma sai ga wani gida daga nesa, haka ta taka taje har bakin gidan sannan ta buɗe ƙofar tana buɗewa tayi karo da wata kyakkyawar mage me shegen tana ganin ta ta tsugunna tana murmushi ta shafa kanta sannan ya ɗauke ta ta rungume ta, tana jikin ta ta miƙe ta nufi wani ɗaki tana shiga ta sauke ta, ɗaki ne madaidaici babu komai a cikin sa sai kujera guda ɗaya da ɗan table a gaban kujerar, sai jikin bangon da yake taf da hotunan mutane wani bangon hotuna ne an saka musu jar maka wasu kuma an kansile su, wani bangon kuma an saka musu good da green, wasu kuma anja layi akan fuskokin su.

Bayan ta ajiye jakar ta ƙarasa jikin wani bango ta ɗau kama tayiwa wani good amma me lanƙwasa, sannan ta kuma matsawa jikin wani kallon hoton take tare da saka hannu ta shafa fuskokin su tana sakin wani ƙayataccen murmushi wanda kana ganin sa kasan daga ƙasan zuciyar ta yake fitowa, hannun ta ne ya tsaya akan wani hoto tama murmushi tace; "sarkin rigima, gaba ta ƙarayi da
End Ads