nake gari ya ɗan fara duhu, dan bazan iya barin su, saidai zan miki wani mutun ci ɗaya iya wuya jikar ki za'ayi mata sassauci amma sauran babu wanda zan ƙyale fa karma ki kuma cemin wani abun magana ɗaya nake. Yana faɗa mata haka ya kuma kashe wayar...
Ji tayi kamar tayi tsuntsu ta ganta a unguwar shiyasa ma bata gaya masa tana garin ba, dan kar ya rigata zuwa, duk yanda taso ta isa gurin kafin magriba tayi amma saida aka kira sallah tana hanya, bata isa unguwar ba kuwa saida aka idar da salla motar su na shan kwana saiga mashin ɗin magana ɗaya nan ya shawo kai tare da wata adaidaita a bayan sa, saidai kuma tun kan su ƙaraso suka hango motocin su bulama agun burkin mashin ɗin sa yana cire glass ɗin dake idon sa, suma masu daidaitar tsayawa sukayi ganin uban gidan nasu ya tsaya suma suka tsaya..
Da sauri hajiya Rabi ta buɗe motar ta fito dan ita bata hango motar su bulama bama, saida ta fito tana shirin zuwa wajen magana ɗaya hakan yasa ta ja da baya, ganin har ya rigata zuwa kenan,
Bulama da suke shirin shiga cikin gida sukaji ƙarar mashin ɗin magana ɗaya hakan yasa duk suka juya suna binsu da kallo, suma su magana ɗaya kallon nasu suke,
Hajiya Rabi da tuni jikin ta ya ɗauki ɓari, ta fara yin gaba zataje wajen magana ɗaya, saiga wata motar nan ta shigo da wani irin mahaukacin gudu saura kaɗan ta kwashe Hajiya Rabi tayi saurin matsawa gefe,
Saida Barazana dake wannan mahaukacin gudun saida suka shawo kwana taga motocin dake gurin hakan yasa tayi saurin taka burki da saura kaɗan su buge mashin ɗin magana ɗaya shima kansa saida yayi hanzarin matsawa tare da wawuro wata uwar ashar yana makawa na motar duk da besan waye a ciki ba,
"Me kuma yake faruwa? Sukayi wa kansu da kansu tambayar da basu da amsar ta,
Beenish ce tace "mu fita mu gani mana, naga motoci harda mashin da napep ko me suke anan kode kunci bashin wani ne iya tafiya ta..
Barazana ce ta ɓuɗe motar tana cewa ko bashi mukaci ai baza ayi mana wanann layin a ƙofar gida ba, bare ma bashin uban wa zamu ci, ta faɗa tana shirin saka ƙafar ta waje, Ameela dake gefen ta tace Zee tsaya mana bafa musan su waye ba, kar muyi gaggawar fit...
Kan ta ƙarasa maganar ma taji Aunty Babba ta buɗe murfin gefen ta, tana buɗewa ta fice daga ciki, ai sauran ma ba wanda ya tsaya bata amsa suka fice haka itama dole ta fito,
Fitowa sukayi duk suka jeru a gaban motar sannan suka fara nufar inda suka ga motoci waɗanda ke daf da ƙofar gidan su, tun kan su ƙarasa ma Bulama shima ya shiga takawa yana nufo su,
Maryam dake laɓe taga abun yafi ƙarfin ta tuni ta kira Dannar ta sanar da ita duk abun dake faruwa, tana kashe wayar kuma itama ta fito saidai daga gurin duhu ta tsaya bata tsaya inda zasu ganta ba,
A tsakiyar wajen suka tsaya, shima ya tsaya tare da zare glass ɗin sa tare da sakin wani ƙayatace murmushi wanda saida haƙoran sa suka bayyana gaba ɗaya,
Cikin ɗan zaro ido Aunty Babba tace "Uncle!!!
Maida duban sa yayi gare ta, shima fuskar sa ɗauke da mamakin ganin ta anan....✍️
Kuyi haƙuri da wannan da Allah wallahi yau nayi busy da yawa da ƙyar na samu ma nayi wannan ɗin da babu gwanda ba daɗi, zakuji sa sai a hankali gashi nan gashi nan dai....
My WhatsApp number 08124226526
[3/5, 12:22 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
Maida duban sa yayi gare ta, shima fuskar sa ɗauke da mamakin ganin ta anan,
Da gudu ta faɗa jikin sa ta rungume sa cike da farin ciki, tana cewa "Uncle daman kana nan ina ka shiga ina ta neman ka har na gaji da neman ka tunda ka barni kullum nake tunanin ka,
Runtse idon sa yayi yana cije baki, da ƙyar ya ɗaga hannun sa shima yayi hugging ɗin ta back, tare da ware idon sa akan Barazana duk da suka zuba ido suna kallon su cike da mamakin inda suka san juna.
Irin kallon da yake wa Barazana ne yasa ta ɗan fara tsarguwa tare da kawar da kanta daga gare shi,
Wani irin murmushi ya kuma saki irin nasu na ƴan duniya, shima janye idon sa yayi daga kan ta sai loƙacin ya samu damar ɗago Aunty Babba tare da sumbatar goshin ta sannan yace; "nima har nagaji da neman ki sai da ƙyar na samu wani bawan Allahn yagaya min kina garin Kano yau satina ɗaya a garin nan ina nemanki sai da ƙyar na samu ina nuna hoton ki duk inda naje sannan wani yace min ai school ɗin ku ɗaya amma baisan gidan ku ba, da ƙyar dai na samu wanda yasani shine aka rako yanzu ma wanda ya rakoni ya tafi da kun gaisa wataƙil ma kun san shi..
Wani farin ciki taji ya kuma zo mata jin yanda ya sha wahalar neman ta, cike da farin cikin ta kuma rungume sa tana cewa, "Allah sarki ashe haka kasha wahalar nema na kaima, sakin sa tayi sai faman murmushi take, ta juya ɓangaren su tana kallon tace "kunga Uncle ishaƙ da nake baku labari,
Duk murmushin yaƙe sukayi mata suna ɗan russinawa suka gaida shi, dan babu wanda yayi farin ciki kawai dai sun nuna mata kara ne, dan yanda suka ganshi dai suka ga duk ba yanda take basu labari, mussaman ma Zee da taga kallon da yake mata duk ta tsargu hakan yasa tayi wani sak dan ji tayi kawai bai mata ba.
Bakin Aunty Babba kamar gonar auduga, bakin ta yaƙi rufuwa cikin murna ta ce Uncle mu shiga daga ciki, Ameela ku muje mana, kawai ɗan jinjina mata kai sukayi suna kuma kallon ko ina na gurin, aransu suna ayyana to dan zuwan sa ne kawai kuma sai ya lodo mutane haka, dan su a tunanin su duk mutanen sa ne..
Aunty Babba ce taja hannun sa suka fara yin gaba, sai Beenish da Barazana da suka bi bayan ta Ameela kuma hannun Babyn baby ta kama suka koma motar dai ta tayar da ita, suka bi bayan su da motar a hankali suke tafiyar har suka ƙarasa bakin gate ɗin.
Ganin suna shirin yin gaba taja hannun sa, yasa Rabi saurin ƙarasowa, kusa da su magana ɗaya, basu san da ita agurin ba sai maganar ta kawai da sukaji...
"Naseeru!
Da sauri Magana ɗaya ya juya jin ankira sa da sunan sa na asali, Saida yayi mamakin ganin ta,
Cikin sauri tace "kuyi sauri wancen da suke shirin shiga dashi mugune kuyi sauri ku dakatar da shi, zan baku ko nawa kuke so, kar ka bari ya shiga gidan kaji Naseeru?
"Yaushe kika zo daman kina cikin garin loƙacin da mukayi waya shine kuma baki gaya min ba.
"Dalla kabar wannan maganar kaga shiga fa zasuyi, duk wata magana mayi daga baya.
Waye wancen ɗin to naga ai sun san juna da waccen me yasa kika ce a dakatar dashi kada ya shiga?
Cike da gajiyawa da maganganun da yake mata dan bata so su shiga kuma bata son su haɗu da Bulama agaban yaran dan zai nuna yasan ta kuma batason yaran su san sun san juna, shiyasa ta kasa ƙarasawa tun ɗazu,
Kallon ta yayi sai ta kuma juyawa ya kalli can inda yaga Aunty Babba ta ƙwafe tana fam zuge gate ɗin,
Fito yayi tare da cewa "kice dai kawai akwai wani dill ɗin tsakanin ku, to kawai kije kiyi gaba da gaba da shi mana mu zamu take miki baya.
Cikin ɗan zaro ido Rabi tace "kai amma baka da tunani sai kace wata ƴar daba zanyi gaba kuna bina a baya, haba Allah ya kiyaye, agaban su so kake sunamin kallon ƴar daba, jika ta fa yazo ɗauka mugu ne kuma cutar min da ita zaiyi, kuma akan abun da bai shafe ta ba, wata matsala ce a tsakanin mu, bana son kuma saka su a ciki dan haka kawai koda sun shiga ku rufarwa yaran sa, daga nan sai ku shiga, shi kuma sai ku fito dashi daga cikin gidan, kuyi masa talala bashi da wani ƙarfi inya so anan zaku samu damar ɗauko min yarinyar da na nuna maka hoton ta, ka gane?
"Ƙwarai kuwa kuma anan ne nima zan rama abun da sukayi min, kai muyi jafa ya faɗa yana kallon sauran mutanen nasa, tuni sukayi gaba kowa na faman jan ƙafa yana nuna yafi kowa shegantakar sa tafi ta kowa kowa ƙwaran kansa ne, duk bakunan su kamar guntun baƙin man mashin....
Da sauri Rabi tace "kai! Kai! Kar ku taɓa ƴan matan dan Allah ko nawa kake so zan biyaka ka rabu da su akan wannan ramuwar taka, nasan hakannan baza suyi maka haka ba, duk yanda akai kaine la shiga hurumin su, yanzun ma wallahi in kun shiga Allah sa ku fito ƙalau amma duk da haka kar ku taɓa kowaccen su ɗauko min ita kawai zakayi sannan ku fito da mutumin da suka shiga dashi, shikenan abun da zakuyi min ina jiran ku a cikin mota,
"To ai kin gama magana indai zaki biya ni lahanin da sukayi min to angama magana.
Nan sukayi gaba ita kuma ta koma cikin motar ta,
Maryam jikin ta sai ɓari yake gashi bata son duk su ganta itama musamman Bulama bata so su haɗu itama a fannin ta a cewar ta idan ta fita duk suka ganta batasan wane mataki zasu ɗauka ba, gashi kuma yaran baza su yarda da ita ba, indai har suka ga sun juna a tsakanin su, gashi daman basu san taba, babu me yarda da ita, shiyasa ta kasa ƙarasawa gurin da suke, da ta kwa sun shiga cikin gidan ji tayi kamar tayi tsuntsu taje ta dakatar dasu, gashi sai kiran Hajiya Dannar take amma bata ɗaga ba, gaba ɗaya hankalin ta ya tashi, tana lungu kuma gurin duhu ne dashi babu haske agurin, daga inda take duk tana hango komai da suke, abun da yafi ɗaga mata hankali ma da kuma mamaki ganin yana magana da ɗaya daga cikin su alamun ma sun san juna tunda har da su runguma da kuma sumbatar goshi abun ya matuƙar ɗaure mata, kai tunda take bata taɓa sanin suna da alaƙa ba kuma Hajiya Dannar ma bata taɓa bata labari ba...
Ga shi kuma ganin Rabi na magana da ƴan daba shima ya kuma ɗaga mata hankali dan a tunanin ta duk tare suke da Bulama duk shirin sune bakin su ɗaya....
Su Magana ɗaya na zuwa wajen mutanen nan suka shiga kai musu duka nan suma suka shiga mayar musu, dan basu san hawa ba basu san sauka ba kawai sukaji suna dukan su dan haka suma ba shiri suka shiga ramawa, suna cikin wannan damben sai ga jiniya nan ta karaɗe wajen, su Magana ɗaya kallo ɗaya sukayi gurin suka gane su waye nan kwa suka fara sakin waɗancen suna neman hanyar guduwa, sauran da basu sani ba suka tsaya agun, har sojojin suka shiga dirowa daga motar suka nufo su da bindigun su a hannu, sai loƙacin duka fara ƙoƙarin guduwa amma babu inda sukaje duk akayi ram dasu,
Hajiya Rabi kam da suka wuce ta gaban su ai tuni tasa drivern ta ya yanka juyi da ita suka bar gurin tun kafin a ankare dasu suka bar unguwar ma gabaki ɗaya.
"Magana ɗaya ma da yaransa duk sunyi nasarar tserewa saidai kuma duk sunbatu abun hawan su agun da saiyadojin su suka gudu"
Nan suka kwashi yaran Bulama suka saka su a cikin motar su, su kansu basu san me ya faru ba suke faɗan, sude sun biyo sahun ƴan matanne da RK ya turo su, ashe loƙacin da suka tafi ɗauko Beenish gidan sukaje sai aka hana su shiga, har suna shirin komawa saiga mahaifiyar Faheema nan zasu fita kallo ɗaya ta gane su dan haka bata kawo komai a ranta ba tace a bar su su shiga yanzu zata dawo su jirata..
Shine fa da suka shiga sukayi karo da Beenshi a falon gidan hannun ta ɗaure da aunka a bayan wata kujera, falon ba kowa sai wata ne aiki itama jikin ta da kayan sojoji, suna zama kuwa saiga RK ya fito duk tsurewa sukayi dan basuyi tunanin ganin sa ba, cikin wata riga yake fara me ɗan gajeren hannu sai wandon sojoji gajere da ya saka, sai wani takalmi baƙi da gaban sa ya ɗan kwanto ya rufe masa yatsun ƙarfa yayi, kansa babu hula sai gashin sa da ya sha gyara yayi baya dashi sai gefe da yake a ɗan lanƙwashe lanƙwashe na gaba kuma duk yama kusa rufe goshin sa amma shima anan naɗe yake a jere kuma, daga gani ma daga wanka ya fito saboda yanda fuskar sa tayi wani fayau da ita gwanin burgewa kyan sa ya ƙara bayyana saidai muce masha Allah domin Allah yayi halitta akan bawan Allahn nan,(tunda na ɗora idona akan sa har yanzu duk wanda na kalla a kusa dani sai inga kamar a gidan zoo nake ina kallon wasu halittun hhhh)
Suma ai duk saranda sukayi suna kallon sa saboda duk haɗuwar da sukayi dashi basu taɓa kallon sa irin na yanzu ba ko a ɗazu da facemask a fuskar kuma da hula ko ganin kalar gashin sa basu yi ba, yanzu kam sosai suka saki ido da hanci suna kallon sa, sunga halittar da basu saba ganin irin taba, saida na rufewa su Abulele ido gudun kar ta bari ya kamata tana kallon sa ta bamu kunya...
Haɗe rai yayi yana ƙarasa shigowa cikin falon wayar sa ya zaro ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yayi kamar ma baisan da su a falon ba, duk da yana sane dasu da duk irin kallon da suke masa.
Saida ya daɗe yana aikin dannan waya su kuma tsoro da yanda yayi da fuska yasa duk suka rasa me zasu ce masa gaba ɗaya.
"Stop looking at me witch.
Ba shiri duk sukayi ƙasa da kansu cike da mamakin abun da yace ko wacce sai ta shiga tsarguwa kode ita kaɗai take kallon sa shiyasa yace mata mayya, saboda da su duka suke kallon sa zai ce musu mayu, dan haka ko wacce sai ta fara tunanin ai da ita yake.
Tunda yayi maganar kuma bai kuma ce musu komai ba.
Beenish da taƙaici ya gama isar ta ta miƙe tsaye, ta matso kusa dasu tace dan Allah ku roƙe sa ko zai saurare sa nagaji da zaman nan tunda ya ɗauko ni ya barni a mota fa kamar wata akuya kuma yasa anfito dani ya kuma bari na anan duk magiyar da nake mishi yaƙi ya saurare ni kamar ba musulmi ba ko inda nake ma bai kalla ba,
Duk shiru sukayi suna sauraron ta amma suna tunanin abun da zaije ya dawo, dan sai yanzu da suka gansa suka ƙara jin shakkar sa saboda kwarjinin da yayi musu, sai yanzu ma suka ga gaskiya abun da tayi masa bata kyauta ba ita tajawa kanta a yanda yake da matsayi ga ƙarfi gashi soja sojoji kam ba imanine da su ba, tsaf zai iya yi mata abun da yafi ma abun da yayi mata ɗin, duk sai suka nemi wani ƙarfin su da suke ji dashi suka rasa dan dama su kaɗai ne basu zo da wani shiri ba da zasu iya yin faɗa da kowa ma bare kuma dashi..
Babyn baby ce ta ta rungume ta kamar zatayi kuka tace "Zai haƙura Yaya ki kuma basa haƙuri muma daman haƙurin muka zo mu bashi, in sha Allah zai haƙura da abun da kikayi masa ki kwantar da hankalin ki babu me raba mu dake muna tare mutuwa ce kawai zata iya rabamu,
"Ok fine"
Duk juyawa sukayi suna kallon sa da yayi maganar amma duk da haka bai ɗago ba idon sa nakan wayar sa, saima gani da sukayi ya miƙe tsaye, bai kuma kalli inda suke ba kawai yayi hanyar fita, nan suka shiga basa haƙuri amma ko tsayawa baiyi ba bare ya juyo saima ficewa da yayi daga falon duk bin bayan sa sukayi da kallo baki sake.
Kuka Beenish ta saka "cikin kuka tace wai me yake nufi da mune kunga irin rashin mutuncin nasa duk maganar da zakuyi masa bazai saurare ku ba bare yabaku amsa ni wallahi tafiya ta zanyi inyaso ya kashe ni wannan ai wulaƙanci ne daga yin ɗan ƙaramin abun da bai taka kara ya yakar ya ba, sai ka hau mutum da duka kuma ka ɗauko sa ka rabasa da ƴan uwansa ambaka haƙuri ambasa haƙuri amma yaƙi kula mutane ma bari ya faɗi wani abun...
Ameela ce ta shiga bata haƙuri, tana cewa zai haƙura ne, agun sukai