x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 47 - SU WAYE SU

  • 138001 words
  • 141000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 173

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
shi ɗin bazan yafe muku ba,

"Kada ki yafe ɗin ko kinji na roƙi yafiyar ki, zuwa dole yarinya ta shirya, idan so kike ya dawo ya tarar dake a cikin gidan yayi miki maimaici to ki zauna ke kaɗai, nasan next time da katako zai miki, dan haka ya faɗa bayan fitowar ki, mantawa mukayi bamu gaya miki ba, dan shi yace ya fi so yaga ya sauya miki kamannin ki gaba ɗaya sannan zai rabu dake, dan baiyi miki komai ba.

Da sauri Barazana tace "dan Allah da gaske kike haka yace?

"Hmmm ki tambayi Ameel kiji, ko zan miki ƙarya ne, tana gama faɗa mata haka ta ƙara gaba, tabar Barazana da wasi wasin da gaske ne ko ƙarya Beenish tayi mata.


Beenish na shiga ɗaki ta tarar da Ameela ta kifa kai a katifa tana kuka ƙasa ƙasa, da sauri ta ƙarasa kusa da ita tana tambayar ta me ya faru duk akan tafiyar ne, amma sai ta girgiza mata kai alamun a'a.

Haƙuri ta shiga bata kawai dan tasan bazai wuce zuwan Ammu bane ya sata kuka.

"Beenish wai me Ammu take nufi dani ne, na gaji da wannan rayuwar ta faɗa min ko ni wacece amma taƙi, me yasa take min taurin kai akan rayuwa ta, saidai ta juya Ni yanda take so, amma ni bazatayi min abun da nake so ba, me yasa Beenish, tayi maganar tana kuma ci gaba da goge hawayen da yaƙi ya tsaya.

"Ameela ki nutsu ki ban hankalin ki nan, ina so daga yau ki cire wannan tunanin a ranki dan Allah kibi komai a hankali tunda kikaga haka kinsan dole da dalili ni bana tunanin Ammu da wani abun, ya kamata kiyi mata uzuri, ki kuma bata loƙaci kamar yanda ta gaya miki ɗin nan gaba da kanta batare da kin tambaye ta ba, zata gaya miki komai, yanzu kiyi mata wannan buƙatar taki, in sha Allah ita ce ta ƙarshe na miki alƙawari daga mun dawo zan tsaya tsayin daka har sai ta gaya miki, ko bata faɗa miki ni zan binciko komeye gaskiyar lamarin, daman kinga ke aikin kike so to tunda yanzu yazo cikin sauƙi ba shikenan ba dama ta samu, dan Allah ki daina bujire mata, uwa uwa ce koma ta wacce hanyar ta haife ki ai ta riga ta kawo ki duniya, kinji dan Allah kiyi haƙuri komai ga wuce ki fara shiri mu tafi kawai.

Da ƙyar dai ta samu ta shawo kan Ameela ta amince zata je ɗin, taji daɗi da taga ta shawo kanta yanzu matsalar ta kawai Babyn baby bata san wane hali zata shiga ba, tasan dole bazataji daɗi ba amma ya zatayi dole ce ta saka ta hakan, ta hanyar ne kawai zata samu damar ɗaukar fansa biyu akan su, shi da kuma mahaifinsa.

Daga wajenta ta kuma fitowa falon ganin Babyn baby zaune agun da ta barta sai taji ta kuma bata mugun tausayi, zuwa tayi gabanta tare da kamo hannun ta, bata ce mata komai ba, ta kamata ta fita waje da ita, can bayan gidan su tayi da ita wajen wata bishiya da wataran suke fitowa su zauna awajen, akwai kujeru agun, zaunar da ita tayi akan kujera ɗaya, ita ma ta zauna akan ɗaya, shiru tayi tana ƙare mata kallo, ɗagowa tayi itama ta kalle ta, yanayin kallon da tayi mata yasa taji wani yumm kawai sai taga loƙaci guda ta koma mata Umman su, da sauri ta girgiza kai tana damƙe ido, tare da jan dogon numfashi, sannan a hankali tace "Allah ya bayyana mana ke Umma idan kuma kin mutu Allah ya jiƙanki, Allah yasaki a aljannar fiddausi, mu kuma Allah ya bamu ikon rama muku abun da sukayi mana,

A hankali Babyn baby tace "Ameen"

Kallon ta tayi tana ƙara gyara zama, sannan tace "Haneefa kiyi haƙuri ki kwantar da hankalin ki inje indawo wannan zuwan zanyi shine badan kowa saidan farin cikin ki, da banyi niyar gaya miki amma yanzu zan gaya miki, ta wannan hanyar ce kawai zata sa mu samu abun da muke so shekaru da shekaru, idan na zama soja ta hakane zan iya samun damar da zamu kamasa da hujja sosai, ta sanadin wannan sojan zamu samu damar ɗaukar fansanmu akan mahaifin sa, idan bata haka ba banga ta inda zamu samu power ɗin da zamu iya ɗaukar mataki akansa a matsayin sa na tsohon gwamna kinsan bamu isa kai tsaye muce gashi gashi ba, babu wanda zai yarda damu, wataƙil ma saidai musa kanmu a matsala amma idan ya zamana muna da kusanci da shi zamu samu babbar hujjar da kowa ma zai ganewa idon sa bawai yaji daga bakin mu ba, kin gane abun da nake nufi, to dan Allah ki kwantar da hankalin ki masan matar nan zata baki kulawa duk da bansan ta ba, amma ma yarda da ita, kuma itama Ammu nasan bazata cutar damu ba, akwai shirin da suke duk dan ganin komai ya tafi daidai.

"Ajiyar zuciya Babyn baby ta sauke tana jinjina kai "tace haka ne kuma, shikenan ba damuwa kije ɗin zan zauna, amma dai bazaku daɗe ba ko?

"Eh in sha Allah, kuma indai naga da dama ana iya yin hakan, to duk sati zamu ringa zuwa muna ganin ki.

Ɗan murmushin yaƙe Babyn baby tayi kawai dan a cikin ranta duk da haka bata so, amma kawai zata barta ne, tunda taga tanaso, kuma dan akanta zatayi hakan, bata da zaɓi da ya wuce ta haƙura ɗin koda ita hakan bazai mata daɗi ba.

Haka Beenish ta ɗan ringa janta da hira harta saki jikin ta sannan suka tashi suka koma cikin gidan...

Suna daf da zasu shiga cikin falon sukaji anayin horn tsayawa sukayi, Beenish tace "to suwa kuma muka samu, mtsw mantawa ma nake wallahi ya kamata mu samo me gadi, shiga ciki bari in duba ko waye.

Shiga ciki Babyn baby tayi, ita kuma ta nufi wajen gate ɗin nata batare da ta kawo tunanin komai ba a ranta.

Karamar ƙofar ta fara buɗewa zata leƙa, kawai taji an banko ƙofar da ƙarfi, har saida aka buge mata hannu, tsayawa tayi tana kallon mutumin shima kallon ta yake tare da ƙarasa shigowa ciki, yana shigowa wasu ma mutum biyu suka shigo, harɗe hannun ta tayi a ƙirji tana kuma ƙare musu kallo.

Ɗaya ne yace "Oga ita ce?

Karkaɗa musu kai Bulama yayi yana ƙoƙarin shiga cikin gidan, Beenish tayi saurin tare gabansa, tace "Malam lafiya, wa kake nema.

"Matata! Ya faɗa ransa a haɗe yana shirin tureta ya wuce, tayi saurin matsawa, baki sake tana tunanin wannan kuwa kansa ƙalau, tana ta tunanin kamar tasan fuskar amma ta manta a inda ta sansa, tunani ta shigayi, bata ja loƙaci ba, da ta kuma kallon bayansa take ta gane waye.

Kafin tayi yunƙurin dakatar da shi tuni yayi gaba, mutanen sa na mara masa baya, da sauri tabi su, dataga dai zasu rigata shiga kawai tasaka gudu, ta wuce su tana shiga, saidai bata rufe ƙofar ba ya saka ƙafar sa tare da turo ta ya ƙarasa shigowa,

Juyawar da zatayi taga duk ba kowa a falon, sai TV dake ta faman aiki ita kaɗai tsayawa tayi taga iya gudun ruwansa kuma taji me ya kawo sa gidan kuma bayan ya ɗauki wacce yazo ya ke nema,

Zainab! Zajnab! Zainab!! Matata kina ina ki fito mu tafi yau zaki zama amarya, sai zagaye falon yake yana maganar ƙatuwar muryar sa duk ta cika gidan, Beenish har saida ta saka hannu ta toshe kunnen ta.

Murɗa wani ɗaki yayi ya buɗe sai yaga ba kowa a ciki. Yana wannan dube duben yana ƙwala mata kira.

Beenish ce ta nufi ɗakin su kafin ta shiga ma duk suka fito cikin sauri suka ƙarasa shigowa falon,

Bulama kamar zarrare haka yayi kanta da sauri yana washe baki, yana zuwa kawai bata ankaraba saijin hannun ta tayi anasa.

Ai bata jira wata wata ba, ko tambayar keke faruwa, kawai ƙwace hannun ta tare da ɗauke sa da mari tana matsawa gefe dan tana ganin sa ta gane sa, kuma angaya mata waye shi, tun laƙacin da Babyn baby ta shigo ta sanar dasu, sai Maryam ta leƙa ta window tana ganin shine kuwa tace duk su wuce ɗaki dan ba mutumin arziƙi bane, su shirya ba alkhairi ne ya kawo sa ba, saidai bata basu labarin komai akan sa ba.

Memakon Bulama yaji zafin marin da tayi masa saima shafa gurin da yayi da hannu sannan ya sumbaci hannun nasa yana sakin murmushi dan tunda yasakata a idon sa yaji ya manta da duk wani ɓacin ran da ya taho dashi.

Da sauri sauran biyun sukayi kanta zasu kamata, su Ameela suka yi saurin shiga gaban su ita da Beenish,

Ɗaya ne ya ɗaga hannunsa zai make Ameela tayi saurin damƙe hannun sa, ɗayan hannun ta kuma ta ɗaga rigar ta tare da zaro kwalbar spray ɗin su da suka saba amfani da ita, tana zarowa ta fesa mishi saitin idonsa take yayi baya yana saka hannun sa ya shiga murza idon.

Barazana ma zaro nata tayi ta fesawa ɗayan, Bulama da glass a idon sa shiyasa basuyi gaggawar fesa masa,

Cikin murmushin sa da ya saba, yace "da kyau amaryar kada kiyi min taurin kai kizo mutafi zan baki farin cikin da baki taɓa samu ba, wallahi muguwar ƙaunar ki nake, ƙauna ce danƙararriya a cikin raina da na ɗau tsawon loƙaci ina dakonta, nagama jinyar ta mamanki sai kuma ke kika kuma maye gurbin ta, fatan dai ta taɓa baki labarin tsohon saurayin ta, wanda zai iya yin komai akanta, koma ince wanda yayi abubuwa da dama akan ta, yanzu kuma ya dawo kan ƴar itama kuma zai iyayin komai akanta, dan haka matata ki taho mutafi na baki farin ciki, kece matata kece rayuwa ta komai mana naki ne duk wani abu da na mallaka mallakin kine matata.

Fashion ce ta kalle sa tana nuna sa da yatsa tace "uwar ka ce matar ka, ubanka ne ya haifa maka ni a matsayin mata, kaji mahaukaci taɓaɓɓe to saidai kaje a ɗaura maka auren da uwarka dan Abu tafi ƙarfin banzan tsoho kucaki irin ka, kai nayi maka kama da sa'arka, na rantse da Allah in baka ja waɗannan ƴan wahalar ba kun bar gidan nan ba, wallahi sai nayi maka sabuwar kaciya agidannan kaga sai kafi jin daɗin cin amarcin da uwarka, banza kwarto tsohon banza tsohon wofi ko kunya baka ji ba zaka zauna kana wannan maganar da ƴar cikin ka shashasha kawai kare bunsuru shine kawai me bin ƴaƴan cikin sa mtssww, taja tsaki tana shirin barin wajen, cikin fushi ya cafko hannun ta, Beenish da Ameela suka saka hannun biyu suka tura sa gefe, zasu ƙwace hannun Zee amma suka kasa dan ƙam ya riƙeta, yana haɗe rai, wayar sa ce ta shiga yin ringing da hannun ɗaya yasaka a aljinhu ya zaro ta ganin kirane daga waje me mahimmanci yasa shi ɗagawa yana saka wayar a speaker.

"Hello! Oga kayi sauri kazo babu lafiya an samu matsala wasu mutane sun shigo sun ƙwace kayan, sun fito da duk wanda yake cikin gurin sun kunna masa wuta yanzu haka gashi ci yake da wuta, kuma kayan shekaran jiya ma duk suna ciki,

Baisan loƙacin da ya saki hannun Zee ba, a mugun haukace ya juya ya fita daga falon ya manta ma yazo da wasu, dan gaba ɗaya hankalinsa baya kansa, yana tafiya yana lalubo number saidai idan ya kira sai a tagama ringing ba a ɗauka ba, har ya fita daga gidan ya shiga mota muƙulli daman na jiki hakan yasa kawai yaja motar ya fara gudu yana tafiya yana kuma kiran number daga ƙarshe ma sai yaji ankashe ta jefar da wayar yayi da ƙarfi yace "RABIII...! me yasa me yasa ni zakiyiwa haka me yasa sai ta wannan hanyar zaki rama, yana zuwa wani gurin goslow duk da saurin da yake dole ya tsaya, wayar sa ce tayi ƙara yayi saurin ɗaukowa dan a tunanin sa ita ce ta kira sa, yana dubawa yaga saƙon video ne ta Whatsapp da wata baƙuwar number, da sauri ya shiga, asibitin sa yaga yana ci da wuta, a ƙasa kuma aka rubuta masa ka duba labarai kaga meke faruwa, da sauri ya saki wayar a ƙasa bayan wancen gidan kuma yanzu asibitin sa me yake shirin faruwa ne?

Da sauri ya shiga facebook ɗin sa, nan yaga an watsa hoton sa da ana nemansa sai kuma rubuce rubuce a ƙasa da baida loƙacin karantawa, da ƙarfi ya jefar da wayar ƙasa.....



$$$$$$$$$$$$$$$$$$$


*Algeria*

____Da sauri Hajja Mama ta shiga ɗakin, tsayawa tayi akanta, tare da kiran sunan ta amma sai tayi mata shiru.

"Maha kiranki fa nake, nanma tayi mata banza ran Hajja Mama ya gama ɓaci dan dama bata yarda da ita ba gashi kuma abun da ta kuma yi mata, tayi mata laɓe, tsugunnawa tayi ta kaiwa wuyan ta damƙa cikin fushi Hajja Mama tace "me yasa zaki ci amana ta me yasa zaki juya min baya, me yasa Maha!?

Sai yanzu ta buɗe idonta tana shirin ƙwace wuyan ta, "kisakar min wuya mana meye hakan, ni bansan me kike cewa ba.

"Ƙarya kike Maha ƙarya kike kinyi min ƙarya, kina ɓoye min wani abun me yasa zaki min haka?

"Taya zan gaya miki bayan kin shaƙe ni.

Sakinta Hajja Mama tayi tana ɗagota zaune, tana tashi kuma sai ta fashe da kuka, cikin kuka "tace kiyi haƙuri Yaya wallahi bayin kaina bane ya daɗe da ganeni yasan duk wani shiri da kikeyi kuma yasan da zuwan ki, yanzu haka kalli can gurin, ta nuna mata wani guri, Hajja Mama na ɗaga kai taga Camera, sannan tace haka waje ma da akwai, duk maganganun da muka yi da wanda kika yi yanzu duk yaji komai, ya min barazana da ƴaƴana yanzu haka suna hannun sa, kawai zan gaya miki koyi gaggawar barin gidan amma ni nasan bazai taɓa barina ba ni da yarana, nagaya miki ne kawai dan na sauke nauyin dake kaina, nagaji da zaman ƙunci a gidan nan.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai Hajja Mama take maimaitawa a ranta bata taɓa jin tsoro ya shige taba irin nayau, ta razana da lamarin nan ba kaɗan ba, yanzu duk wayoyin da tayi ma acikin ɗakin duk ya ji kenan.

"Amma me yasa baki gaya min ba Maha, ko a wane basai ki faɗan ba tun kafin nazo ki ankarar dani, amma wallahi kin ruguza mana komai,

Miƙewa tayi ta shiga banɗaki saida ta shiga ta dudduba taga ba camera ɗin aciki sannan ta ɗau wayar ta ta shiga typing ta daɗe tanayi kafin ta turawa wata waya da bansan number waye ba, tana cikin banɗakin tajiyo ihun Maha da sauri ta fito daga banɗakin tana fitowa ta riske wasu maza agun sun ƙulle mata baki sannan sun shaƙe mata wuya, da sauri Hajja Mama taje zata taimaka mata wani ya jefa mata wani ƙyalle take ta zube agun, Maha ma ttun tana ihu har ta daina jikin ta ya saki sannan suka sake ta, ɗaya ne ya saɓi Hajja Mama a kafaɗa yayi waje da ita a cikin daren aka saka ta a mota aka fita da ita daga gidan...✍️


*Duk meson na saka shi a group ɗin Su waye su yayi min magana, ta wannan number 08124226526 iya littafin su waye su, dan Allah kar wanda ya min magana akan meman wani littafin, ko yace min in saka sa a group ɗin littattafai, to wallahi duk wanda yayi min magana bazanyi reply ba, sbd an saba yi min irin haka Ni ga abun da nace amma sai wasu si ta tambayata in tura musu littattafai dan Allah ku daina bana so ba littattafai nake turawa ba nawa kawai nake turawa*

_Ƴan facebook kuma kuyi searching ɗin su waye su hausa novel group kuyi join akwai a ciki tundaga farko har inda aka tsaya, dan ba kullum zanna posting a kowane group ba_
[4/19, 10:29 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*



(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)

08124226526*_______


*_episode 42💧_*



💧💦محمد لرسول الله...!💦💧



*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*



Bismillah..✍️



*GHAMBURJ*


____Su Bilal ba ƙaramar wuya suka sha ba kafin su gano hanya, dan har ɓata ma sukayi, suka rasa inda zasu dosa, saida wani mutum yazo ya nuna musu, inda zasu bi sannan suka koma inda suka fito.

Suna shiga falon gaba ɗayan su suka zube a ƙasa kowa na maida numfashi, Bilal kam zamawa kawai yayi rigingine yana kallo sama tare da wawwara ƙafar sa hannun kuma ya miƙar dashi, dan gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa, sai faman wash wash yake yana ɗan goge hawayen da yaji
End Ads