yan taho masa, tunda suka taho bai kuma magana ba, har suka shigo.
"Faheema ce tace "gaskiya wanda ya kawo shawarar fitar nan ya cuce mu yanzu ga abun da kuka jawo mana, kawai rabon musha wahala ne, yanzu da mahaukatan karnukan nan sun cije mu ai saidai a haifi wasu, wai gaskiya munji jiki,
Ɗan murmushi Zaid yayi duk da agajiye yake amma hakan ba zai hanasa yin halin da ya saba ba, kallon Bilal yayi da ya warware ƙafa sai kace ƙaramin yaro, "jin jiki ai sai rago nidai ras nake jina, saboda jarumine ni ba mata maza ba, kalli dan Allah yanda yayi wata irin kwanciya sai kace ya kwana yana tafiya.
Dariya Faheema tayi tace "tun ɗazu nake kallon sa nima, naga ma kamar goge hawaye yake.
Da sauri Zaid ya leƙa fuskar sa ta ɗayan gefen, ya ɗago yana cewa wallahi kuka yake, wallahi ancuci yaron nan gata yayi masa yawa, gaskiya ka haɗu da aiki kayi ka gama dan ba mai rarrashin ka anan kowa ta kansa yake ko mata ma basuyi ba sai kai, anya kwa yaron nan ba mata maza bane, kai tashi induba ka inga Allah wataƙil ka ɓoye mana kai mata maza ne, ta sama dai nagani babu nono amma bansan ƙasan ba, yana maganar yana shirin taɓa masa ƙugu wai zai cire wandon ya duba.
Dariya su Faheema sukayi har Faheema najin kunyar maganar tasa, Salma kam tashi tayi tsaye tana cewa "wallahi baka isa ba ka takurawa yaron nan fa da yawa.
Da sauri Bilal ya tashi zaune yana ture hannun sa kamar zai fashe da kuka haka yake ji cikin muryar kuka yace "dalla malam kar rabu dani wai kai wane irin banza ne wallahi baka da hankali ko kaɗan mtssw a gaban yara kake wannan zancen, yana faɗar haka ya kuma kalli Salma yace "ke kuma waye yaron naki?
Dariya Salma tayi tana ƙarasowa kusa dashi ta zauna gefe tare da cewa "baka ji bane babban mutum, amma ni ba haka nace ba jarumi, wai yanzu ƙafar ta daina ciwon ne?
Ya tsina fuska yayi kamar bashi yayi magana yanzu ba, har ya koma kalar tausayi, ɗan danna ƙafar yayi, da sauri yace "ashh wayyo Allah na ƙafata wallahi inajin ma ta ruɓe zafi take.
"Dariya ce ta kama su gaba ɗayan su jin yanda yake faɗar maganar yanzu ya gama masifa amma ana tambayar sa ji yanda ya sauya loƙaci guda.
Salma ce tayi saurin danne dariyar ta tace "babu abun da ya same ta gajiya ce kawai yanzu haka ma zaka iya tashi tsami tayi shiyasa kake jin zafi da ka taɓa, tashi in taimaka maka muje saima in gasa maka da ruwan ɗumi sai kayi wanka ka kwanta zakaji kana tashi zakaji daidai.
Ƙara ɓata fuska yayi yana ya tsina fuskar yana kallon ƙafar tasa, ganin yayi ta kumbura, take ga shiga girgiza kai yana taɓe fuska kamar yaga kashi a jikin ƙafar tasa,
"Wallahi bazan iya ba kalli fa yanda ta kuma kumbura akan ɗazu, taya zan iya takawa, ko motsata nayi sai tayi naji zafi,
Ɗan taɓa ƙafar Salama tayi, aikwa da sauri ya riƙe hannun ta yana sakin ƴar ƙaramar ƙara, tare da cewa "dan Allah ki bari kar ki taɓa min ƙafa in kuma so kike ki kashe ni to, na gaya miki yanda take zafi kodan ba ajikin ki take ba.
Zaid ne ya miƙe tsaye ya cewa "Allah sarki Boy shikenan zai zama gurgu tunda ƙafa ta ruɓe a yanke ta za'ayi tunda bazata taku ba, Allah yasa Hajja Mama ta dawo da wuri tayi saurin kaika asibiti a yanke ta kar ka fara yi mana wari, dan kamar naga tama ɗuri ruwa ta ciki, shiyasa ta kumbura.
Zaro ido Bilal yayi jin abun da Zaid ɗin dan har ga Allah ya ɗauka da gaske yake musamman da yaji yace shi yasa ta kumbura gashi dama da ya danna yaga ta lotsa kuma shi bai taɓa ganin tayi hakan ba daman sai yau,
Idon sa har sun kawo ƙwalla yace "Dan Allah da gaske yanke min ƙafa za'ayi?
Salama na ɓoye dariyar ta tace "idan ka zauna ba, kana kai wasu loƙutan anan gurin baka tashi ba, shikenan yanke ƙafa babu fashi dan akwai wata ma da na sani hakan ta taɓa faruwa da ita sai yanke ƙafar akai yanzu haka tana nan a unguwar mu ta zama gurguwa, indai kaima kazama irin ta zan kaika taga ɗan uwanta irinta.
Ai Bilal baisan loƙacin da ga miƙe tsaye ba yaji zafi amma haka ya daure ya shiga tafiya yana cewa gashi nayi, nidai bazan koma irin ta ba, ki daina min wannan mummunan fatan ban ajiye ƴaƴa ba, idan na zama gurgu taya zan iya samun ƴaƴa nasan ma, nasan ma babu wacce zata aure ni, yana maganar yana ci gaba da tafiyar.
Sosai suka shiga yi masa dariya gashi dai a ido da girman sa amma kwata kwata bashi da wayo, yana abu kamar ƙaramin yaro.
Faheema ce ta ce "ba yanzu angaya maka akwai irinka ba ai sai kuyi auren kawai kunga kunyi anko.
Salama "tace "ai da gudu ma zata amince, kaga shikenan daman har yanzu batayi aure ba itama.
Shima Zaid dariyar yake masa yana jinjinawa shirmen Bilal, wai shi yanzu ya yarda, gashi kuma ya tashi.
Da gasken dai yake duk dauriyar da yake sai yaji dai ƙafar taƙi ɗaukan sa da sauri ya zauna akan kujera yana ɗagata, yace "innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wallahi ta ci gaba da zafin, dan Allah ku kira Hajja Mama ta kaini asibiti dan Allah ku taimake ni kar a yanke min ƙafa.
Tun suna masa dariya harde sukaga abun nasa da gaske ne, dole suka taimaka masa Zaid ya ɗauke sa da ƙyar ya shiga dashi ɗakin su, ban akan gado ya sauke sa, Salma kuma ta shiga neman banɗakin ɗakin saboda bata gaɓa shigowa ba, ganin ƙofa yasa ta shiga, Allah ya taimaka yanda take tunani banɗakin akwai heeta ta ɗebo ruwan zafi ta sirka a robar da ta gani a banɗakin, da sauri ta fito, towel ɗin da ta gani gefen gadon ta ɗauka, ta tsugunna a gaban ƙafar tasa, Zaid ne ya riƙesa dan ya hana ta taɓa ƙafar,
Da ƙyar suka haɗu ita da Faheema suka gasa masa ƙafar sosai yanda zaiji daɗi, tun yana shure shure har ya fara daina jin zafin kafin ma su gama har bacci yayi awan gaba dashi, saida suka gama sannan suka duba ko zasu sami man zafi amma babu normal vaseline suka shafa masa a ƙafar, Zaida ya gyara masa kwanciya kan gadon, ƙara miƙar da kafar yayi cikin bacci.
Salama ce ta kalle sa ta sakin murmushi ta ce "Oh ni ƴar gidan Rabi shi kuma haka yake tab amma da matsala yana namiji yana irin wannan rakin?
Zaid yace kaɗan ma kika gani, amma bacci yafi yawa a rayuwar sa dan baya gajiya da bacci, yanzu nan sai ya kai gobe bai tashi ba, kuma ko ya tashi yana gama abun da zaiyi zai kuma komawa bacci, abun har mamaki yake ban.
Cike da mamaki "Faheema tace to kode yana da cutar bacci?
"Nima abun da nake tunani kenan, wataƙil dai yana da ita, dan baccin masa yayi yawa, cewar Zaid.
(Idan masu karatu baku manta ba, a baya munyi bayani akan Bilal duk da ban gama bada labarin rayuwar sa ba, amma yana da cutar bacci, ragwantar sa kuma da shagwaɓa ta samo asali ne shi yasa zaku gansa haka, zakuji labarin nan gaba zaku kuma fahimtar waye Bilal)
$$$$$$$$$$$$$$$$$$
*RK*
___Ji yayi gaba ɗaya zaman Barack ɗin ya ishe shi, tashi yayi kawai yaje ya kuma shiryawa, yabar Barack ɗin tare da sojojin dake yi masa tsaro, gidan su yace su kaishi, suna zuwa ƙofar gidan yace su sauke shi daga waje, shiga cikin gidan yayi shi kaɗai, tundaga me gadi har sauran sojojin dake tsaron cikin gidan saidai sukayi mamakin ganin sa a ƙafa ya shigo kuma shi kaɗai, saidai babu wanda ya iya tambayar dalili sai dai kawai salute da suke ta faman yi masa, har ya wuce.
Bai doshi cikin gidan ba ya nufi hanyar part ɗin sa kawai, shiga yayi, babu kowa a ciki a gyare yake tsaf sai ƙamshi da yake, cikin ɗakin sa ya wuce yana zuwa kawai yayi ruf da ciki, tare da rufe idon sa, amma daga ya rufe sai marin yarinyar nan ya dawo masa a kunne tare da mugayen maganganun da ta jefe sa dasu, tsaki yaja ya tashi zaune yana cije baki ji yake abun yana dawo masa sabo, duk yanda yaso ya manta da ita kasawa yayi, badan gobe zaiyi tafiya ba kuma tafiyar ta zama dole da ba abun da zai hanasa komawa gidan yarannan ya koya mata hankali.
Yana zaune yana tunane tunane wani abu ya faɗo masa a rai da sauri ya ɗauko wayar sa a aljihu ya shiga laluben wata number da naga ansaka Bro 2 danna kira yayi, ana ɗagawa ya ce "in kana gida ka sameni a part ɗina, yana faɗar haka ya kashe wayar, ya kuma komawa ya kwanta yana kallon sama.
Bai daɗe ba, yaji anyi nocking ɗin ƙofar,
"Come in yace yana kuma gyara kwanciyar sa yayi, saida yaga shigowar sa sannan ya tashi zaune.
Da sallama ya shigo, saidai bai samu dama ya amsa masa ba, cikin nutsuwa ya ƙarasa shigowa, yana zama akan bedside drawer, tare da gaida shi, sannan yace gani.
"Juyowa yayi yana fuskantar tarsa, tare da cewa ya "wani abun ya kuma faruwa ne naga mood ɗin ka haka?
"Da sauri ya girgiza kai tare da cewa "babu komai kawai ina tunanin halin da Faheema take ciki ne, dan Allah yaya kuyi wani abun mana, har yanzu wai ba'a gano inda suke ba?
Ɗan numfasawa RK yayi, tare da cewa ana bincike har yanzu dai ba'a gano ba amma in Sha Allah za'a gano nan bada jimawa ba, ka kwantar da hankalin ka,
Cikin sanyin jiki Dr Aveed yace "to Allah yasa, wallahi banajin daɗin rashin ta agidan nan.
"Hmm yanzu dai duk ba wannan ba abun da yasa na kiraka, shine inason inji ƴan matan da kake gaya min na cikin school, sune waɗanda suka zo cikin gidan nan, ranar da abun ya faru.
Da sauri Dr Aveed yace "Eh suma ankama su ne? Dan tun ranar ban kuma ganin su ba.
Daman abun da yake kokwanto kenan shin sune ko basu bane, kuma ya kasa tambayar sa, yaji daɗin jin hakan tanan zai fara ko ya musu hankali gaba ɗayan su, sannan sai ya kore su daga makarantar yana dawowa daga tafiyar da zaiyi sai sunbar makarantar kuma su da wata makarantar har abada.
A fili kuma sai ya jinjina kai kawai yace "okay, ban sani ba kawai dai na tambaye ka ne, dan naga yanda kake ban labarin su haka na gansu ranar shiyasa na tambaye ka, zaka iya tafiya, sannan ka cire damuwar rashin Faheema, zata dawo nan bada jimawa ba.
Daga nan yayi masa sallama ya fita, yana fita ya tashi ya shiga wanka ya fito ya kuma sauya wasu kayan, zuciyar sa har ta rage raɗaɗin da take masa, jin sune a cikin makarantar sa.
Fita yayi daga part ɗin shima ya shiga cikin gidan, wajen Dadyn sa ya nufa yaje suka gaisa, bayan sun gaisa yake kuma tuntuɓar sa shima akan batun ɓatan su Faheema, amsar da ya bawa Dr Aveed ita ya bashi shima sannan ya fito daga nan ya kuma komawa part ɗin sa dan har fushi yake da Ammin sa, data hanasa yin komai tun a loƙacin, da tunanin yanda zai yi ya kwanta, washe gari yana tashi wajen ƙarfe goma ya shiga shiryawa, saida ya shirya, sannan ya shiga part ɗin gidan, yana ganin mahaifiyar tasa a falo yaji wani sanyi a ransa dan bazai iya dogon fushi da ita ba, amma duk da haka sai ya ɗan ɗaure fuska, yana wucewa wajen dinning da yaga Dadyn su awajen shi da Dr Aveed,yana zuwa ya gaida Dadyn sa, shi kuma Aveed ya gaida shi, lafiya ya amsa masa kawai yana jan kujera ya zauna.
Binsa da kallo Ammi tayi tana jinjina kai itama taje wajen dinning ɗin, baki riƙe tace "Eh gaskiya na yarda wallahi ancanza min kai a inda kaje, girman abun da nayi maka har yakai ga kaganni ka ɗauke kai ko gashe dani baza kayi ba, me kake zo ka zama ne wai...
Dady ne yayi murmushi irin nasu na manya, yace "me kuma ya haɗa ku da ɗan naki yau muka jiku a rana?
"Haɗe rai RK yayi batare da ya kalle ta ba yace "nifa ban kula dake bane that's why na wuce, good morning, hope you are fine?
Ƙin amsawa tayi saima kallon sa da ta tsaya yi cike da mamaki, daga nan batare da tace komai ba kuma kawai sai ta juya tabar wajen.
Dady ne ya kalle sa yace "me kayi mata, me yasa zaka ganta kaƙi gaishe ta, koma me ya faru ai bai kamata kayi mata haka ba, ko sa'ar kace da zaka yi fushi da ita, ka tashi kaje ka bata haƙuri dan nasan fushi tayi.
Shima ji yayi ba daɗi, sai yaji duk bai kyauta ba, tashi yayi da sauri yabi bayan ta, har takai ɗaki, ɗakin ya danna kai kawai ya shiga batare da ya ƙwanƙwasa ba, a tsaye ya ganta dan shigar ta kenan taji ƙarar buɗe ƙofar hakan yasa ta tsaya,
Da sauri ya zagayo ta gaban ta, yana kafeta da ido, haɗe rai tayi itama, tace "get out of my room!
Ko motsawa baiyi ba, saima ɗage mata gira ɗaya da yayi yana kamo duk hannuwan ta, "Ammi na ni kaɗai, I'm very sorry please, ni da zanbar gidanma yanzu, bana so in tafi ranki a ɓace, kiyi min addu'a kawai, kar naje naga ba daidai ba.
Batasan loƙacin da tace "ina zaka kuma?
"Ammi kindai san aikin mu ai, kullum tafiya tana iya tasowa mana, zanje Lagos ne.
Cikin rashin jin daɗin hakan tace "Haba haba shikenan mutum bazai hutaba nifa bason aikin nan nake ba, ace kullum mutum baya gida, dududu kwanan ka nawa da dawowa zaka kuma tafiya, gaskiya ni nagaji da yawon nan wallahi, gashi yanzu sanadin aikin nan naka anzo an ɗauke min yarinya kuma kunƙi kuyi wani abun akai, daga kai har mahaifinka kamar ma baku damu da ita ba, kullum sai na zubar da hawayen rashin ta amma har yanzu shiru, dan Allah ka nemomin ƴata kar wani abun yasame ta, ta ƙarasa maganar cikin raunin murya.
Kallon ta kawai yake tama manta fushi take da shi daga jin zai tafi duk tabi ta gigice, saida ya bari ta gama tayi shiru sannan yace "Ammi ya kamata ace kin saba da wannan amma kullum na tashi tafiya sai kinyi wannan maganar, aiki na riga da na fara kinga ai ba damar ajiyewa, nima bansan da tafiyar ba sai shekaran jiya ake gaya min, an riga da ansaka sunana ni zan horar da sababbin sojojin da zan a ɗauka a wannan loƙaci, kuma gobe ne, amma ni yau zan tafi da yamma, kiyi min addu'a kawai amma wannan aikin ai saidai in mutuwa nayi kinsan abune da nake so tun ina yaro so sai kinyi haƙuri, Faheema kuma zata dawo kece kike ganin kamar anyi shiru ne amma ana kan aiki har yanzu, ta sirri ake binciken ne, dan dole sanayyar wasu akayi hakan, saboda ɗauke SMA kawai yasa muka gane baza mu iya ganowa ta irin binciken da muka fara ba, shiyasa muka canza salon binciken, kuma in sha Allah zamu gano ko su waye su.
Badan taso ba dole ta haƙura, suka ɗan tattauna sannan yayi mata sallama dan daman yagama shiryawa, yana fitowa yayi Dadyn sama bayanin tafiyar tasa, shidai ba wani ƙorafi addu'a kawai yayi masa, sannan ya fice, yana fita tarin sojojin da suka san da tafiyar suka shirya suma suka zo ɗaukar sa, yana fitowa duk suka shiga sara masa, aka buɗe masa ƙofa ya shiga, suka fita daga gidan, Barack suka fara zuwa, saida yayi wasu ayyukan sannan wajen ƙarfe huɗu ya fito, nan suka kaisa airport shi da wasu sojoji uku suka shiga jirgin sauran kuma suka koma, nan jirgin su ta ɗaga zuwa Lagos...✍️
_Zakuga kwana biyu bana samun damar yin me yawa, wallahi ayyuka ne sukayi min yawa wannan satin, amma in Sha Allah zuwa wani satin sai kunji da karatu._
*Duk meson na saka shi a group ɗin Su waye su yayi min magana, ta wannan number 08124226526 iya littafin su waye su, dan Allah kar wanda ya min magana akan meman wani littafin, ko yace min in saka sa a group ɗin littattafai, to wallahi duk wanda yayi min magana bazanyi reply ba, sbd an saba yi min irin haka Ni ga abun da nace amma sai wasu si ta tambayata in tura musu littattafai dan Allah ku daina bana so ba littattafai nake turawa ba nawa kawai nake turawa*
_Ƴan facebook kuma kuyi searching ɗin su waye su hausa novel group kuyi join akwai a ciki tundaga farko har inda aka tsaya, dan ba kullum zanna posting a kowane group ba_
[4/19, 10:29 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*