x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 44 - SU WAYE SU

  • 129001 words
  • 132000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 168

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
haƙuri shima saida ya samu nasa rabon, saida tayi musu tas da yi musu warning cikin masifa sannan ta juya tabar wajen....

Da sauri Hajja Mama tace; "I'm very sorry ni najamaka,

Da yaren shima yayi yaƙe yana kuma bata haƙuri itama dan shi inda sabo ya saba wannan ba komai bane indai mutanen cikin gidanne duk haka suke, saida ya gama sannan ya sanar da ita cewar tana zuwa.

Suna daɗe agun Hajja mama na ta ɗanyi masa tambayoyi a dabarance, kuma na fahimtar wasu abubuwan, shidai baisan me ya kawota ba, amma tunda yaji gurin ƴar aiki tazo to yasan bata dangantaka da ƴan gidan dan haka ya saki baki yake ta hira da ita, sunɗau wajen awa biyu kafin wata mata ta ƙaraso wajen cikin sauri, da farko bata gane taba, saida Hajja Mama ta tashi tsaye tana dariya tare da yin magana sannan ta gane ta duk da tasan da zuwan nata amma shigar ta sai yasa taga kamar ba ita ba, itama murmushin tayi mata tana mata sannu da zuwa, sai kuma suka juya wani yaren da nakasa fahimtar ma wane yare ne suke.

Sallama sukayiwa me gadin sannan suka juya da niyar shiga cikin gidan...

Suna shiga ƙofar da taga kowa na shiga, sai taga babba falo ne sosai me girman gaske, faɗar yanda cikin gidan yake ɓata loƙaci ne,
Benen guda uku ko wanne da inda ya dosa alamun dai sauran part part ɗinne da kake ganowa ta waje, guri matar ta nuna mata tace; "Yaya Fatma ki zauna daga nan ta nuna mata ƙasa tace bari inje in sanar da Madam kinsandai yanda na baki labarin ta dan haka sai kinyi haƙuri da duk kalar tarbar da kika samu, dan wallahi har yanzu bansaba da cin mutuncin nan ba, kin cuce ni wallahi da kika turo ni gidannan, duk cikin yaren da suka sauya take mata magana incase koda wani zaiji su bazaiji komai ba.

Murmushi kawai Hajja Mama tayi mata tace Malama ki wuce ni ina ruwana ai wajen neman biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, abunda kin kusa gamawa ma, komai yazo ƙarshe.

"Hmmm daman kullum ma ai haka kike cewa kuma naganki ke kaɗai ina yarinyar da kike cewa zaki kawota.

"Kin Maha bana son surutu wannan long story ne inajin ma na fasa kawo ta amma dai zanyi tunanin ba lalle ta juri wannan wulaƙancin nasu ba, dan naga shaida tun daga bakin gate..✍️



*Ayi da wannan page ɗin Please 🥺 wlh yau sai a hankali*


*Wallahi nayi missing ɗin masu comment da yawa, akwai waɗanda bazanma manta da suba, domin sunban haɗin kai sosai a baya amma yanzu kam sai a hankali*




*Duk meson na saka shi a group ɗin Su waye su yayi min magana, ta wannan number 08124226526 iya littafin su waye su, dan Allah kar wanda ya min magana akan meman wani littafin, ko yace min in saka sa a group ɗin littattafai, to wallahi duk wanda yayi min magana bazanyi reply ba, sbd an saba yi min irin haka Ni ga abun da nace amma sai wasu si ta tambayata in tura musu littattafai dan Allah ku daina bana so ba littattafai nake turawa ba nawa kawai nake turawa*


_Ƴan facebook kuma kuyi searching ɗin su waye su hausa novel group kuyi join akwai a ciki tundaga farko har inda aka tsaya, dan ba kullum zanna posting a kowane group ba_
[4/19, 10:24 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*



(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)

_______*08124226526*_______


*_episode 39💧_*



💧💦محمد لرسول الله...!💦💧


*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*


Bismillah..✍️



"Kin Maha bana son surutu wannan long story ne inajin ma na fasa kawo ta amma dai zanyi tunanin ba lalle ta juri wannan wulaƙancin nasu ba, dan naga shaida tun daga bakin gate...

"Kaɗanma kika gani, baredai inje in sanar da ita, kar hakanma yazama laifi, wani benan dake tsakiya ta hau.

Hajja Mama kam falon ta shiga bi da idonta sai ta zama ƴar ƙauye acikin sai kalle-kalle take baki sake tana mai mamakin yanda ya gina gida irin wannan.

Budurwar da ta mareta ɗazu itace ta fito tana ta faman dariya ita da wani namij wanda shima dariyar yake.

"This old women from whare? naganta tun a bakin gate.

Take yarintar ta daina dariyar tana yatsina fuska tare da watsawa Hajja Mama wani mugun banzan kallo a wulaƙance.

Wani abu Hajja Mama taji ya tsaya mata a rai ita fa batajin zata iya jurar abun yarinyar nan amma dai zata koya mata hankali ta cikin ruwan sanyi zata dafa ta har sai ta yi lugub da dahuwa.

Yarinyar tana sane ta biyo ta gaban Hajja Mama tare da janye hular kanta da ƙarfi ta jefar gefe, ganin furfura akanta ga kan wani iri kawai ta kwashe da dariya tana nuna ta da yatsa ta ce "dan Allah ji kanta ƙazama kawai wayasan uban abun da ta zo yi wannan ba ƴar garinnan bace saidai daga can wani ƙauyen garin tazo, shima saurayin dariyar ya taya ta ya ce "Hosna kinmin daidai fa da kika mare ta ai kinyi mata da sauƙi ma da nine wallahi sai namata fiye da haka naga ke iya ɗaya kika tsaya, tana ji ana horn amma saima ta leƙo taga waye sannan zata buɗe.

"Ke! yarinyar ta kira Hajja Mama tana dungure mata kai tare da jan gashin ta da ƙarfi, "sannan ta kuma cewa "tashi kije ki wanke min motar da na shigo da ita cikin 10 minutes nake so zan fita kada ki wuce haka kuma ta wanku in ba haka ba, yau sai kin kwana a zaune kina min tausa.

"Hajja Mama batasan loƙacin da ta saki zagi a ranta ba, tana me mamakin wannan ƙarfin halin irin na yarinyar nan, wai ita basan ma wace ita ba, aiki aka kawo ta ba aiki zatayi ba, itadai kawai tunda ta shigo cikin gidan su kuma taganta kalar talakawa shikenan saita takata yanda take so, daga zuwanta, a fili kuma sai tayi ƙasa da murya "ta ce "kiyi haƙuri ƴan mata amma ni ban iya wankin mota ba bakiga ni tsohuwa bace bazan iya ba kidai ban wani aikin yarinya.

Wani irin kallo tayi mata jin ta kira ta da yarinya abun da tafi tsana kace mata yarinya.

Namijin ne yace "baki isaba sai ki koya yau nima zan baki tawa ki wanke ki tashi ki fita loƙacinki ya fara, guri ya samu ya zauna kan kujera ita kuma yarinyar ta riƙe ƙugu tana girgizar kai tana jiran tashin ta, amma fa Hajja Mama bata da niyar tashi saima gyara zama da tayi dan ko uwar su bata isa tasa tayi wankin mota ba, saboda sun raina mata hankali zasu saka ta wankin mota uwar wankin mota zatayi musu ba wankin mota ba, ta ƙaici yasa ta sakin tsaki a fili batare da tasan tayi ba.

Hosna na shirin yin magana kenan taji ance "Hosna go back your part bance Kar na sake ganin ƙafar ki a cikin falon nan ba, kada na sake ganin ki, me baƙin hali irin na uwarta fice min daga nan.

Wani irin haushi taji ya kamata ta tsani matar nan tana mata abun da take so wani loƙacin yanzu a gaban tsohuwar nan za ta yi mata haka.

Cike da marairaicewa da shagwaɓa tace "Moha wai bana baki haƙuri ba, ki haƙura mana kuma ni laifin tayi min, shine nace taje ta wanke min mota fa kawai.

Da matar da ta shigo da Hajja Mama ita da wannan matar dakewa yarinyar magana suka ƙarasa shigowa cikin falon.

Cikin wani irin taku take takawa kamar bata son tafiyar da take, bata bawa yarinyar amsa ba saida ta samu wata kujera da ta babban ta da sauran kuma tana tsakiyar su kamar irin ta sarakai, cikin isa ta zauna akan kujerar tana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, taci manyan kaya irin nasu, bata da wani jiki kayanne ma suka ƙara mata kumari tsohuwa ce itama sosai dan zata iya girman Hajja Mama ma, saidai hutu yasa tsufan Hajja Mama ma yafi fitowa.

Cikin isa ta ta ɗago ta kalli yarinyar tana aika mata da wani kallo me cike da gargaɗi, hakan yasa yarinyar ta fahimce ta tasan sauran tunda tagaya mata haka to bazata kuma maimaita mata ba.

Cikin jin haushin Hajja Mama fiye da na da ta juya tabi ta gefen benen dake ɓarin dama, ta tafi fuuuu cikin fushi.

Shi kuma namijin gaban tsohuwar ya ƙarasa tare da ɗan rungumar ta ta gefe yana sumbatar ta a kumatu, baice komai ba kuma shima yabar falon amma shi waje ya fita.

Maha na gefen ta ta sunkuyar da kai ƙasa kamar tana gaban sarki, tana jiran tabi me zata ce,

Wani irin kallo ƙurilla da takeyiwa Hajja Mama yasa gaban Hajja Mama faɗuwa dan saida ta fara tsarguwa itama duk abun ta saida tayi ƙasa da kai, dan kallon da matar take mata yasa duk tajita uncomfortable take ta kuma nutsuwa.

Saida ta gama ƙare mata kallo wajen minti goma bata ce komai ba, kafin daga bisani cikin magana ɗaiɗai ta ce "har tsawon kwana nawa zaku kasance tare?

Da sauri Maha ta ce "two weeks kawai zatayi kafin ta samu wajen aiki, ina neman alfarma ma da zata samu anan gidan shikenan sai mu zauna tare ta ita aiki sosai kuma zakuji daɗin zama da ita bata da matsalar komai.

Duk wannan maganar da take mata amma idon ta nakan Hajja Mama, saida taji tayi shiru sannan ta ce "zanyi tunani tukunna yanzu dai zata iya zama zuwa satin biyun sannan kuma itama aiki zatayi ba zama ba, kigaya mata duk wasu dokokin gidan yanzu ta kiyaye idan na same ta da laifi ɗaya zata fuskanci hukunci, sannan kar ta kuma jayayya da ƴaƴan gidan nan duk abun da suka sakata tayi shi muddun tana son zaman lafiya acikin gidan nan,

"Tom in sha Allah zata kiyaye, nagide nagode da wannan taimakon Allah saka da alkhairi Allah ƙara tsawon kwana me albarka.

Sosai matar taji daɗi amma bata nuna ba kuma bata amsa a fili ba, saidai a zuciyar ta, a fili kuma saita ɗaga mata hannu, tare da miƙewa tsaye, ta shiga takunta ɗaiɗai tana kamo babbar rigarta, tayi tafiyar ta ko uffan bai haɗa ta da Hajja Mama ba dan bada kowa take magana ba.

A kusan tare suka sauke ajiyar zuciya dan duk ta cika musu falon da tana ciki.

Maha ce ta ƙaraso gurin Hajja Mama ta ce "yi sauri taso muje kar yarinyar nan ta dawo dan idan ta dawo sai kinyi wankin motar nan yau.

Hararar ta Hajja Mama tayi tana miƙewa tsaye ta ce "Allah fa bazan ba, muje inda zaki kaini dan na gaji da zaman ƙasan nan, ƙafafuna har sun fara ciwo.

Dariya Maha tayi ta ce "ɗan wannan zaman tab anya kwa zaki iya kwana biyu ma bare sati biyu?

"Ba lalle ba daidai idan bangama abun da ya kawo ni ba ina sa ran ko sati bazanyi ba zan gama, sai mu tafi dake.

"Kinga muje dai, in kai ki ki huta zan dawo in ɗora abinci,

"Abinci tun yanzu?

"Eh yanzu idan na farama sai zuwa dare kafin in samu in huta, a hakan ma kuma bani kaɗai bace mu uku ne, amma duk da haka bama gamawa da wuri dan kina zama wani zaice miki ga abun da yake son ci, kuma dole ki tashi a rana sai muyi girki sama da kala goma.

"Jinjina kai Hajja Mama tayi tana girmama abun ita fa ko tunkunya yanzu tama manta yanda ake ɗora ta duk da ta iya girki a baya amma yanzu rabonta da girki bazata iya tunawa bama.

Wata ƙofa suka bi sai ta sadasu da kitchen daga nan kuma suka kuma buɗe wata ƙofa ta fita dasu ɓangaren da masu aikin gidan suke, ɗakunane a jere kawai sannan kowa da nasa ɗakin, babu wanda aka haɗa da wani.

Suna shiga ta nuna mata komai sannan ta fita, saboda baccin dake idon Hajja Mama batasan loƙacin da bacci ya ɗauke ta ba, bata farka ba sai wajen ƙarfe huɗu tana tashi taga kayan abinci a gefen ta saidai kuma ita kaɗace Maha bata ciki, tashi tayi ta shiga banɗakin ciki tayi wanka tazo tayi sallah sannan taci abincin, wayar ta ta ɗauko tayi kira ita sai yanzu ma ta tuna tabar ƙofar yaran nan a buɗe duk da bata tunanin zasu fito, gashi ta barsu waje ɗaya kuma batayi musu bayanin zata daɗe ba, duk da su suka ɓata mata rai yasa batayi sallama da su.

Me kula dasu ne idan bata nan ta kira danjin yanda suke amma yake shaida mata abun da ya faru ƙoƙarin fitar da sukayi, amma babu inda suka je, yasa aka sako musu karnun ka ya razana su yanda basu kuma ba.

Bataji daɗi ba faɗa ta hau yi masa tana cewa akan me zai yi haka yanzu da karen ya ciji wani fa yace me kenan, wannan ai gangancin ne, ta inda take fita bata nan take shiga ba, ita batama ga laifin su ba sai laifin sa, shidai haƙuri ya dinga bata Allah ya soshi ma bai bata labarin abun da ga faru da Bilal ba dan duk yana kallon su abun da suke, har suka shiga gidan.

Nan ta kuma gargaɗin sa da cewa ya basu kulawa sosai tunda zata daɗe kar ta kuma jin wani abun ya faru, saida ta kuma tambayar sa lafiyar Bilal gudun ɓacin rai yace mata yana lafiya tana sake a cikin su, suna gama tattaunawar ta kashe wayar nan dai ta ringa kiraye kiraye tana bada umarnin yanda za ayi wasu abubuwan.

Maha bata dawo ba sai wajen ƙarfe goma loƙacin Hajja Mama har gaji da jiranta ta ɗan fara gyangyaɗi, saida ta dawo ta tashi sannan ta bata abincin da ta tawo mata dashi, tare suka ci sukayi sallah sannan sukayi shirin kwanciya, sai loƙacin suka samu dama zasu tattauna.

"Amma Maha kina ƙoƙari fa ai bazan iya ba, duk dade nima ba wani zaman nake ba, amma bazan iya irin naki ba.

"Ba tun farko nace muku bazan iya ba kika ƙi yarda da haka har na saba.

Jinjina kai hajja Mama tayi tana kuma yi mata sannu, sannan ta ce "to ina jinki ance kigaya min dokoki faɗan inji zan iya ko bazan iya ba in haɗa kayana insan inda dare yayi min.

Dariya Maha tayi sannan ta gyara zaman ta ta fara magana.

"Kamar yanda nagaya miki alhaji Jabir yana da mata biyu, amaryar tana da yara huɗu, twins maza sai wani namijin sannan mace aɗaya autar su, ita ce wannan da kika fara haɗuwa da ita, uwar gidan kuma tana da yara bakwai, maza huɗu mata uku, matar ɗazu kuma itace mahaifiyar Jabir kakar sauran yaran kenan, ta ko wanne fanni ba sauƙi a cikin gidan nan, har dama dama uwar gidan itama kuma abun da yasa take da sauƙi tana da siyasa, saidai tana da masifa sosai amma bata kai sauran wulaƙancin ba, kuma tana da son kai da son ƴaƴa indai kun samu matsala da ita to akan yaranta ne, in kikayi mata duk abun da take so zaku zauna lafiya, ba kamar amaryar ba da tana da wulaƙancin da ɗaurewa yaro gindi da rashin ganin laifin su kome zasu aikata bazata taɓa tsawatar musu ba...

Tsohuwar kuma Sanan ta Habiba, saidai kowa na kiran ta da Moha, bata son raini duk ƙanƙantar sa tana so kabi ta sau da ƙafa tana son kaji tsoron, bata da sakin fuska kuma bata da mutunci fiye da tunanin ki, kuma duk wanda ke gidan nan juya shi take dole kayi mata biyayya, duk abun da tace ayi shi akeyi kamar de ita ce da gidan komai a hannun ta yake, duka yaran gidan babu wanda yake wani abu da kansa in ya wuce uzurin banɗaki da kuma cin abinci komai zasuyi a nan zasu barsa sannan kowa ɗakin sa shika ɗai me har ƙaramin su da yake shekara tara, sannan ko wacce rana kowa da kalar abincin da yake ci, zamuyi girki kala kala, sannan idan munjere sun fito cin abinci zamu bubbuɗe tare da tambayar ko wannensu abun da ke so kowa zai zaɓa wasu zasu ce duk babu abun da suke so saidai a dafa musu wani abun, dole muyi sauri muyi musu duk abun da suke so, idan kika kuskura kikayi musu kuskure to zasu watsa miji abincin sannan duk girman ki zasuyi zasu yi miki tsawa zasu saka ki aiki kai tsaye hatta yaron ɗan shakara tara zakiji yana daka maka tsawa shi ba haka shi ba wancen ma, ɗan ƙaramin abu zakiyi zasu balbale ki da masifa, duk haka ɗabi'un su basu da tarbiyya ko kaɗan sannan basu da kunya masu kunyar cikin su ƙalilan ne,

Moha tana son kan familyn ta ya haɗu dan haka tasa yayi zubin ginin sa a haka kowa da kowa sannan a falo suke haɗuwa suci abin da ko wane loƙaci, saidai duk da haka basa inuwa
End Ads