x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 54 - SU WAYE SU

  • 159001 words
  • 162000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 163

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
suna tafiya ba suka ƙaraso garin, wajen wata bishiya suka yada zango, kowa agajiya, su o'o kam ba'a magana, dan jinsa yake ma kamar mutuwa zaiyi,

"Faheema ce tace "yunwa fa nake ji ya kamata mushiga cikin garin mu samu wani abun mu siya muci ko,

Bilal da idon sa ke rufe ya kwanta a ƙasa yace "Ni kuma dan Allah ku kaini asibiti kar na mutu banga Abbanaba kusiyo mana waya mu kirashi yazo ya ɗauke mu kunji dan Allah?

Duk kallon sa sukayi jin yadda yake maganar amma Salama ce kawai ta kula shi, Zaid kuma miƙewa yayi yace bai kamata mu shiga garin a haka ba da waɗannan jakunkunan kar wasu su zarge mu tunda ba'asan mu ba.

Faheema tace "idan muka barsu kuma akazo aka kwashe fa, da kuɗaɗe fa da yawa.

Zaid yace "A'a ba barin su zamuyi ba daman ga Bilal nan sai mu barshi muje mu dawo.

Salama ta ce "Gaskiya duk da haka kar mutafi gaba ɗayan mu, Bilal da zai iya bacci ma agun ya barsu azo a kwashe, kawai ku barmu ku kuje ku biyu mana ku siyo mana mu sai mu zauna anan ɗin ni dashi.

Faheema ta ce "to ai shikenan ma kawai bari muje ku sai ku kula, ko ince ki kula dan nasan mutumin naki yanzu zai yi abun.

Ɗan murmushi Salama tayi tace ba komai idan ma yayi kude kuje kuyi sauri kada ayi rashin rai ku taho mana da tea, daga nan su Zaid suka nufi cikin garin.

Bilal na ta numfashi da ƙyar ya miƙe zaune, ya kalli Salama yace "fitsari nake ji wallahi"

Hararar sa Salama tayi tace "to abakina zakayi kajini da yaro sai kai tayin wani abu kamar ɗan goye harda wani taɓe baki wai fitsari kake ji, to zo kayi ga bakin na buɗe maka, ta faɗa tana wala bakin ta.

Haushi ne ya kamasa jin abun da tace hakan yasa ya miƙe tsaye yana ta faman turo baki shi a dole ta bashi haushi, waiwaye ya shiga yi yana neman ina zai ɗan iya ɓuya yayi fitsarin.

Can ɗan nesa da su ya hango wani kango da ɗan sauri yana ɗingisa ƙafa saboda zugin da take masa, shi kaɗai yasan me yake ji amma gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa, da ƙyar ya ƙarasa jikin kangon sai kuma yaji tsoron shiga gurin laɓewa yayi ya ɗan leƙa yaga ba komai aciki sai ya shiga ya matsa can wajen wasu ci yayi da suka ɗan rufa gurin ya tsugunna ya fara calla fitsarin sa har lumshe ido yake saboda ya matse sa, motsi yaji daga gurin batare da yagama fitsarin ba ya fasa ihu yana miƙewa tsaye, ko wandon baigama sakawa ba yayi baya yana kuma sakin ihu maimakon ya fita amma sai kawai ya tsaya guri ɗaya yana kallon gurin yana ihu, da sauri yaga wata mata ta miƙe daga gurin tana ɗan karkaɗe jikin ta, wani irin ihu Bilal ya kurma yana nufo hanyar waje harda su faɗuwa, yana faɗuwa ya kuma miƙewa tsaye, yana gudu yana jan wandon sa sama, Allah ya taimake sa ma bamai zip bane me roba ne.

Da gudu matar da ta fito daga cikin ƴan ciyayin,itama ta fito daga gurin tana biyo bayan sa,

Juyawar da zaiyi ya ganta tana biyo shi, kuma haukacewa yayi yana ƙara gudu, cikin ihun ya fara cewa "wallahi bansan kuna gurin ba dan Allah kuyi haƙuri kuyi haƙuri, Abba Abba! Har ya fito daga gurin baidaina ihu da kwakwazon ba.

Salama na zaune tajiyo ihun sa da gudu ta taso tayo wajen sa, a hanya suka haɗu yana ganin ta yayi bayanta ya rungume ta yana ɓoye fuskar sa bayan ta, cikin kuka, yace dan Allah ki ɓoye ni aljana ce ta biyo ni, ki basu haƙuri dan Allah kar su kamani.

Ita kuma ganin matar na binsa yasa ta tsaya tana kallon matar, a hankali tace kai mutum ce fa ba aljana ba, kaga tayi maka kama da aljana,

"Girgiza kai ya shiga yi yana cewa "wallahi aljana ce bakiga daga inda ta fito ba, kizo muta fi dan Allah, kizo mutafi! Mutafi! Sai cewa yake su tafi amma ya ƙanƙameta ko ta ina zasu fara tafiyar.

Matar ce da ta ƙaraso ta fara murmushi tace "haba ɗan sauriyi ni ba aljana bace mutumce kamar kai, bansan kowa ba agarin shiyasa nazo nan na kwanta, kalle ni ka gani wallahi mutum ce.

Shiru yayi da kukan da yake saida ya gama sauraron ta sannan ta ƙasan hammatar Salama ya ɗan buɗe ido ɗaya yana leƙen ta, yana ganin ta ya kuma rufe ido tare da cewa "naji nidai kizo mu bar gurin nan, dan shi bai yarda ba aljana bace, in ba aljani ba waye zai kwanta anan gurin da hankalin ka,

Murmushi Salama tayi wa matar tace "Allah sarki kuma sai kizo ki kwanta anan gurin, ai da kin nemi ko gidan mutanene, muma kuma kinga baƙine ɗazu muka sauka mu da ƴan tafiyar mu, in ba damuwa ki ɗauko kayan ki sai mu nemi masauki tare.

"Amma baƙi da hankali daga ganin ta sai ki kama ki yarda da ita loƙaci guda idan kuma aljana ce fa, ko kin manta mutumin nan yace kar mu yarda da kowa a hanya, dan Allah kizo mutafi, duk wannan uban jawabin da yake fuskar sa na bayan ta, saboda har yanzu bai yarda da ita ba, saidai kawai ya dena mata kallon aljana saboda ya kalli ƙafar ta yaga ba ƙofato.

"Dan Allah rabu da wannan zabon kije ki ɗauko kayan ki in kuma a haka kika zo kizo mu tafi tare.

Daɗi ne ta rufe ta ta saki murmushi dan itama hakannan taji ta yarda dasu, dan haka ta juya ta ɗebo kayan ta da ta yi shimfiɗa da wasu wasu kuma tayi filo, ta rufa, da wasu, duka tattara su tayi ta saka a ledar ta ta fito da saurin ta.

Bilal na ganin ta kuma fitowa ya ɓuya a bayan ta, yace wallahi saidai ki zauna da ita, yana faɗar haka ya juya da gudu ya nufi inda suka sauka.

Sallama kam ita ko ajikin ta dan ita ba ruwanta da ƙyamar talaka ko rashin yarda da mutum ita kowa ma nata ne, babu ruwanta, tare suka jero da ita tana ta faman zubar tana bata labarin yanda Bilal yake da tsoro kamar mace, shiyasa taga yana yi mata wannan abun amma da ya fahimta zai daina, yanzu ma dan ya riga da ya tsorata ne, matar sai dariya take itama tana gaya mata yanda ya nuna tsoron sa loƙacin da yaganta, Allah ya sama baiyi mata fitsarin a kanta ba, a gefen ta yayi.

Suna tayiwa Bilal dariya har suka ƙaraso inda yake, yana zaune yana ganin ta ya kuma haɗe jikin sa yana ɗora kansa akan gwiwar sa, yana damƙe hannun sa.

Salama ce ta zauna a gaban sa tana cewa "dalla rago kawai, wai kama gama fitsarinne ko in rakaka ka ƙarasa, tana maganar tana masa dariya.

Banza yayi mata bai kulata ba bai kuma ɗago ba yanzu dai ya yarda ba aljana bace, abun da ya hanasa ɗagowa kuma kunya ce dan tunanin sa ko ta gansa ba wando yana fitsari, shiyasa yaƙi ɗagowa, gashi kuma Salama ma zata kuma raina sa tunda har ta fara tsokanar sa, duk yanda taso ta kulata ƙin kulata yayi, gashi bayaso ya tashi yaje wani gurin ya kuma gamo da wani abun da bar mata gurin zai yi gaba ɗaya.

Suna zaune agun Salama tana tsokanar sa su Zaid suka dawo gurin tundaga nesa suke zancen macen da suka hango agurin, ko da suka ƙaraso da ido Faheema ta tambayi Salama tana nuna matar.

"Gulma ajali in ba'ayi ba a mutu, ki zauna mana amma daga zuwa har kin fara min signer da wace, bakyau dai zuɓɓe.

Kunya Faheema taji ta kamata jin tonon siririn da Salama tayi mata, sai kawai ta maze tace "to ai gaskiya ne kinsan duniya ba abun yarda bace, mu barku ku kaɗai muzo mutarar da ku da wata kinsan ai dole mu tambaya.

Zaid ma yace "nima daman yanzu nake shirin tambaya tundaga can muke tambayar kanmu da wace ce?

"Uhm da gaskiyar ku to wannan dai da kuke ganin ta, aljanar big boy ce, yanzu ya samo ta yake fitsari, shine ta biyosa har nan.

"Kumar ya aljana? Ban fahimce ki ba, Faheema ta tambaya tana ɗan zaro ido.

Salama ce tace "malame kunga ku bamu abinci muci bansan gulma, idan mun gama kwaji komai, duk yanda suka so ta basu labari ƙin basu tayi, matar ma zata yi magana ta hanata, tace ta rabu da su wallah sai taci abinci zasuji komai, kamar suyi mata dukan tsiya haka su ka ji, amma dole suka rabu da ita suka zauna suna buɗe abubuwan da suka siyo.

Anyi anyi Bilal ya ɗago kansa yaci abinci yace wallahi indai matar nan tana gurin bazai ɗago ba, cikin sanyin jiki matar ta miƙe tsaye tace "yaro kayi haƙuri bari in tafi, amma ni bazan taɓa zutar da ku ba, kuma ba aljana bace wallahi.

Shi kansa Bilal bai san loƙacin da bakin sa ya suɓuce ba yace "cuta nawa kuma tunda kin riga da kin ganeni, me yasa tun kan na tsugunna baki motsaba, saida na kusan gama fitsarin bayan kin gama kalle ni zaki motsa, yanzu kuma zaki wani ce bazaki cutar damu ba, ai ni kingama cuta ta wallahi.

Ita kanta matar saida da dariya ta kamata, suma su Zaid da basu san labarin ba saida suka shiga yi masa dariya, matar ta danne dariyar ta ce "dan Allah kayi haƙuri wallahi wallahi banganka ba, kaji dai na rantse, da gaske nake nima bacci nake kuma a lulluɓe nake saida naji motsin ka, sannan na shiga cire mayafin da ma rufa, ina ƙoƙarin buɗewa naji kana ihu shiyasa na yi saurin miƙewa amma dan Allah kayi haƙuri ka yarda da abun da nace maka.

Yana daga kwancen ya kuma cewa "ki ƙara rantsewa bakiga komai ba.

"Wallahi banga komai ba.

Zaid ne yace kaji min ɗan iskan yaro to in ta ganka ma meye aciki, wannan bata haife ka ba, ba uwarka bace, ke ma kuma kika tsaya biye masa, to babu inda zata saidai ka dawwama anan kuma muna gama ci zamu bar gurin sai muga yanda zakayi.

Ɗagowa Bilal yayi yana aika masa da harara yana tutturo baki, kuma duk da haka bai ɗago ya kalli matar ba,

Salama ce ta ce "kinga Mama ki yi zaman ki muci abinci ki rabu da wannan yaron.

Dawowa tayi ta zauna idon ta nakan Bilal yanda taga yana ta wani ɗauɗɗauke kai gefe, ita sai ys bata dariya ma, shi nan ashe kunya ce ta hana sa ɗagow, nan dai su Zaid suka ɓuɓɓuɗe abubuwan da suka siyo, kowa ɗaukan abun da yake so yayi suka hau ci abubuwa suka siyo da yawa ga ruwana sanyi da lemuka, nan dai kowa yaci ya ƙoshi dan Bilal ma baisan loƙacin da ya saki jiki ya ringa tura abincin ba...

$$$$$$$$$$$$$$$$

*MARYAM*

_____Drivern na mayar dasu gida, Babyn baby ta kwanta zazzaɓi ya rufe ta, saboda kukan da tasha, har dare zazzaɓin ba sake taba, saida Maryam ta lallaɓa ta fita a daren taje ta samo mata magani sannan ta dawo, ta ɗan soya mata ƙwai amma ta kasa ci, ta tambaye me zataci kafin ta sha maganin tace babu komai, da ƙyar dai ta lallaɓata tasha lemo, sannan ta bata maganin tasha ta kuma kwanciya, saida Maryam taga ta kwanta sannan hankalin ta ya ɗan kwanta a gefen ta ta zauna tana kallon ta, nan take ta shiga tunanin mahaifiyar ta dan har yanzu bata mance fuskar taba, saboda suna yanayi da Babyn baby.

Anan falon ta rabu da ita kan kujerar dan bata so ta tashe ta, itama sai ta ɗauko bargo a ɗaki ta shimfiɗa a ƙasa, ƴar ƙaramar wayar ta ta ɗauko ta kunna radio nan take jin sanarwar abun da ya faru da Bulama asibiti ya ƙone da wani gidan sa gobara ta kamasu, da sauri ta tashi zaune tana mamakin ya akai hakan ta faru ko shiyasa jiya ya fita ba tare da ya ɗauki Zee ba,indai kwa hakane ya zama dole gobe su bar gidan nan, dan dama bazata iya zama ba ita kaɗai saboda Bulama ya san tana gidan ko badan kanta bama, idan yazo zai iya cutar da Babyn baby idan ya rasa sauran,kusan kwana tayi tana tunanin mafita, saida safe ta kira Hajiya Dannar ta sanar da ita abun dake faruwa, nan Amma tace mata ta bari zata zo gidan anjima sai su tattauna.

Babyn baby ta tashi jikin da sauƙi saidai bazata iya zuwa makaranta ba, hakan yasa dole ta zauna a gida dan ta ƙarasa warwarewa, tunda ta tashi take kiran layi kan su Beenish amma babu wanda ya ɗauka daga cikin su, ta kira ko wannen su yafi sau ashirin, bata da aikin yi daga takira layin wannan idan ba a ɗaga ba, sai ta kuma kiran na wannan haka tai tayi, rashin ɗaga wayar tasu shi ya kuma ɗaga mata hankali, tayi jigum ta zanbga uban tagumi idon ta duk ya cika da ƙwalla kana ganin ta zata baka tausayi.

Maryam na ganin ta haka ta zauna ta riga janta da hira tana kwantar mata da hankali, amma duk da haka ta kasa sakin jikin ta.

Suna cikin wannan halin Ammu ta ƙaraso gidan, saida ta kira Maryam tazo ta buɗe mata ƙofa, tashi tayi taje ta buɗe mata, tare suka shigo cikin gidan.

Ammu na ganin ta saida taji tausayin ta da sauri ta ƙarasa ta zauna a gefen ta tana rungume ta tace "haba my little baby me yasa zaki saka kanki cikin damuwa, jifa kwana ɗaya yanda kika koma, dan Allah ki kwantar da hankalin ki, bafa daɗewa zakyi ba, ko bakya so agano inda mahaifiyar ki take, duk fa anayin wannan abunne duk domin ke, yanzu da kema fa nake shirin turaki wani gidan yau kiyi min naki aikin yanda mamanki idan ta dawo zataji daɗin abun da ƴarta tayi akanta.

Da sauri Babyn baby ta goge hawayen ta tace ina so!

"Yauwa mu daughter ko kefa, idan kina shiga wannan damuwar kuma ai bazaki iya komai ba, ke da ya kamata ki zage ki zama jaruma, amma sai kina kuka saboda wasu sun tafi, sai kace baza su dawo ba.

Cikin muryar kuka "Babyn baby tace da gaske Mamana tana raye bata mutu ba?

Duk da Ammu bata da tabbass amma dan ta kwantar mata da hankali tace "eh tana raye mana, ai shiyasa duk muke wannan abubuwan dan mu gano inda take, amma sai kin zama jaruma kunji?

Cikin jin daɗi tace "zanyi ko ma meye indai zata dawo, inganta, banta taɓa ganin taba fa.

Ammu tace "ai nan bada jimawa ba zaki santa, harma kuyi rayuwa tare, kedai ki ta addu'a Allah yasa agano ta da wuri, duk wani shiri da muke ya tafi daidai.

"Ina yin addu'a kullum sai nayi mata addu'a, in sha Allah zanganta.

"Yauwa haka ake so, a koda yaushe mutum ya shiga wani hali yai ta gayawa Allah buƙatar sa, Allah zai biya masa, sosai Ammu taita janta da hira har tace da ita ta tashi taje ta shirya zasuyi magana da Maryam, sai su tafi anjima da yamma, ba musu Babyn baby ta tashi ta tafi batare ma da tunanin ina za'a kaita ba.


Saida ta shige ɗaki sannan Ammu ta sauke ajiyar zuciya tana maida dubanta ga Maryam da ta zuba musu ido kawai take kallon su, tana sauraron su.

Maryam ce ta rigata cewa da "har kin samu inda zamu zauna ne naji kince ta shirya da yamma zamu tafi.

"Eh mana, bana taɓa gaya miki daman inaso aje gidan Ɗan ijje ba, ina so ku gano waɗanda yake mu'amala dasu, da inda yake ajiyar kuɗaɗen sa, da shige da ficen sa, zaki je gidan ne a matsayin ƴar aiki Babyn baby kuma amatsayin ƴarki, nayi magana da wata ƙawata da take da alaƙa da matar gidan, tace zaku iya zuwa, daman suna neman masu aiki, saboda ɓatan ɗansa yasa duk ya zama kamar mahaukaci duk ya kori wasu daga gidan harda matar sa, ma'aikatan ma abu kaɗan zakayi masa ya kore ka, shiyasa yanzu gaba ɗaya suka rasa ma'aikata, kuma sai kunyi taka tsantsan dashi, zan tura miki dukan halayyar sa yanda zaku zauna lafiya dashi, sannan sai Babyn baby ta zama me biyayya sosai a gaban sa, sannan ku ringa jan ƴaƴan sa har ku saba dasu indai kuka saba dasu to shima zai saba daku, saidai bashi da yarda sai kunbi sa a hankali, ba kowa zai iya zama dashi ba har sai inka fahimci waye shi sannan zaku zauna lafiya, abun dai da muke buƙatar sani kin ringa da kin sani tun ba yanzu ba nayi miki bayani, loƙaci yayi da zamu gano gaskiyar lamari akan sa, shin da hannun sa ko babu hannun sa aciki.

"Jinjina kai Maryam tayi tace gaskiya ne wannan daman abun da ya kamata mu fara yi ma tun farko kenan, yanzu indai ansan da zuwan namu ai shikenan ba wata matsala ko yanzu zamu iya tafiya, danni wallahi Allah ina tsoron Allah ina tsoron Bulama dan mutumin nan ba a haifa sa da ɗigon imani ba, nasan yanzu duk wani shirin sa nice kan gaba, amma yanzu idan muka koma can nadan babu ta yanda zai taɓa kawowa ina can.

Dariya Ammu tayi tace "kai mutumin nan bashi kirki, kice har yanzu da tsoronsa bai sakeki ba.

Itama dariyar tayi tace "hmm ai baza ki gane waye shi ba, ba mutuwar ce abun tsoron ba, ta hanyar da zaibi ne abun tsoro kuma shi baya abu ɗaya yanzu dai ba ya ganni da yaran nan ba, to wallahi idan yazo har su zai haɗa dan shi bai ɗauki ran mutane a bakin komai ba, ko ita rabin sa'ar su ɗaya da abu ajinkin su, yana shakkar su da tsafe tsafen su amma badan haka ba da tuni ya daɗe da ganin bayan su, kuma da son da yakewa ƴar ta har takai ga ya
End Ads