x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 42 - SU WAYE SU

  • 123001 words
  • 126000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 191

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
zuciya tare da maida dubansu ga Beenish dake ta bacci, gefe suka samu suka zauna suka zabga tagumi duk sun zama wasu iri dasu sai kace basu ba.

"Ɗayan ya fishi kirki" cewar Ameela.

Barazana ta ɗan ɗago ta kalle ta tana sake sauke numfashi, tace "daman wannan inda kirki yake ai bai doshi hanyar ba, wallahi bai more hali ba ga baƙin hali ga mugun ta gashi baida kunya kalli fa a yanda ya fito babu kaya ajikin sa ko kyan gani ma babu jiki duk a bubbuɗe kamar tsofaffin birayen nan masu kama da mutane, ga tsayi kamar tsohon ginin da aka tsayar babu rufi, murya kamar ta tsohon kwaɗo, yana wani haɗe rai kamar kumurci, sai wani ciccije baki yake kamar wanda sukayi ƙaurin suna gurin farauta, wannan asalin sa ma takarin saudiya ne, wai "ku uban waya baku izinin hawar min kujera? Mtsw ko uban me zamuyi da ƙazamar kujerar sa falon ma fa warin karti yake, da munci gaba da zama ma sai nayi am...


Damƙar da taji anyiwa kanta ne yasa ta dakatawa da maganar da take, cikin tsoro da furgici yanda tagansa yasa taji fitsari na shirin zubo mata,

"How dare you!? Who are you, who is your father in this town, and repeat what you said! Yana maganar yana fitar da huce me zafi jijjiyoyin goshin sa har sun bayyana...

Baijira komai ba daga yanda ya riƙeta yayi jifa da ita gefe, wata wayar wuta ce manne ajikin bango haka yasa ƙarfi ya fincikota daga jiki, yayi kanta, kafin tayi wani yunƙurin tashi daga gurin tuni ya rufe ta da duka.

Innalillahi kawai Ameela take maimaitawa ta miƙe tsaye ta ɗora hannu aka tuni hawaye ya fara zubo mata ganin yanda yake dukan ta, ganin bazata jura ba yasa tayi kansa ta baya ta fara dukan sa tana jan rigar sa, amma ko gezo beyi ba dan hankalin sa baya gurin,(to nidai nace Allah sa ba allurar ce ta motsa ba)

Ihun Barazana ne ya tashi Beenish dake baccin wahala, ganin yanda yake dukan Barazana ta manta ma bata da lafiya,

Cikin sauri taje gurin tana zuwa ta gaban sa ta fusge bulalar tare da sauke masa marin da ita kanta batasan tayi ba.

Cak ya tsayar da idon sa akan ta tabbas duk da matsayin sa na soja da juriya amma yaji marin, saidai mamaki da al'ajabi ya hanasa koda motsi, kawai ya zuba mata ido.

Cikin ƙuncin rai tace "wai kai wane irin mutum ne eh wane irin halittane kai me yasa baka da tausayi baka da imani me muka tsare maka me muka yi maka kake shirin azabtar damu shin kai baka da tausayin mata ne me ka maida mata, me ka ɗauki mata, ka rasa a inda zaka gwada ƙarfin ka sai kan mace! Matan ma waɗanda basuyi maka komai ba, idan mugun ta kake son yi kaje kayi da ƴan uwanka maza abun kunya ne ka tsaya kana waɗannan abubuwan da mu, mugu azzalumi marar imani da tausayi.

Itama marin yazo zai kai mata yaji an riƙe hannun sa, saura kaɗan yakaiwa wanda ya riƙe hannun nasa mari da ɗayan hannun saidai yana sauke idonsa akanta yayi saurin dawowa hayyacin sa, cike da mamaki yake binta da kallo,

"Haba namiji duniya haba sa maza gudu, bansanka da irin wannan ɗabi'ar ba, yaushe ka zama haka, yaushe ka fara ɗora hannun ka akan mace, ka manta alƙawarin da kayi min ya akai hakan ta faru yaushe ka fara karyan alƙawarin bansani ba?

"Ammi...

Da sauri ta ɗora hannun ta akan bakin sa ta girgiza masa kai alamar kar yace komai, hakan kuwa yayi kamar yanda take so,

Jan hannun sa kawai tayi suka nufi hanyar ƙofa abakin ƙofa suka haɗu da Moohad yayi saurin matsa musu.

Wani mugun kallo RK ya watsawa Moohad tare da kai masa wani mugun naushi a dantsen hannun sa yana jijjiga kai irin zamu haɗu ne.

Dake soja ne sai ya dake duk da yaji zafi saima murmushin gefen baki da yayi yana ɗan shafa gurin, sannan ya ƙarasa shiga cikin gurin, yana bin ƴan matan da kallo, cikin ɗan sakin fuska yace "ku ɗauke ta muje akai ku gida.

Da ƙyar Barazana ta iya tashi da taimakon Ameela ta miƙe tsaye jikin ta duk yayi shatin bulala, da ƙyar take takawa, ganin kamar bazata iya ba yasa Moohad ya riƙo ta ta ɗayan gefen ya riƙeta sosai yanda zata iya takawa da kyau, bata da choice da ya wuce haka dole ta saki baki, yau ba bakin tsiwa jikin ta ƙwara yai la'asar dan ta daku ba ƙarya.

Beenish kam bakin gadon ta koma tana dafe kanta da taji yana shirin dawowa, sosai wannan mutumin yake shirin shiga rayuwar su, yasan meye agaban su meyasa yake abun da yayi yau ɗinne ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba, taji haushin sa da tsanar sa fiye da da, amma wallahi sai ta rama yanda yasaka suka zubar da hawaye sai tasa ya zubar da nasa hawayen sai tasa yayi da nasanin irin wannan dukan da yayi musu, ko bata rama ta hanyar duka ba sai ta rama ta ƙuntata masa zuciya yanda ta tsane sa itama sai tasa yaji kaf duniya babu wacce ya tsana irin, in ma ya tsane ta yanzu ta nan gaba sai tafi ta yanzu.

Har su Ameela suka fita da Barazana suka fita suka saka ta a mota, tana zaune tana tunanin,

Ameela ce ta kuma dawowa ta ganta a haka, saida tayi mata magana amma bataji ta ba har saida ta taɓota, sannan ta ɗago jajayen idanun ta ta sauke su akan ta batare da tace komai ba.

Ameela tace "ki taso muje mana"


"Ameela me mutuminnan yake so damu ne me ya maida mu mai muka tsare masa, ki kalli fa irin wulaƙancin da yake mana kala-kala yanzu ya dace ya saka mace a gaba ya ringayi mata irin wannan dukan kamar ya sami jaka ko shi ya haife ta, namiji ce ita da zai dinga dukanta, kiga fa abun da yayi min ɗazu bani da lafiya amma saboda da bashi da ko ɗigon imani haka ya ringa yi min ihun kare akai saboda jahilci na rantse da Allah bai daki banza ba, wallahi sai na nuna masa ƴar halak ce ni, tana kaiwa nan kuma ta fashe da kukan baƙin ciki dan tana maganar tana kuma jin yanda zuciyar ta take mata zafi, ji take idan ta samu dama sai ta iya raba ransa da duniya...

Rungume ta Ameela tayi tana cewa "kiyi haƙuri dan Allah kibar wannan maganar tundade yanzu ance mu tafi kinga ai anyi mana iyaka da shi, In sha Allah ko hanya bazamu ƙara haɗawa dashi ba, mun rabu kenan, ki taso mutafi.

Shiru tayi tana share hawayen ta amma bawai dan taji haƙurin da take bata ba, dan ƙudurinta na nan bai sauya ba kuma bazai sauya ba bazata taɓa jin sanyi aranta ba in bataga ta ƙuntata masa ba kamar yanda take ji.

Miƙewa tayi tsaye, Ameela ta kamo hannun ta suka fito har yanzu jikin ta a sanyaye yake batajin ƙwari sosai,

Jin zasu fito yasa Moohad saurin juyawa ya bar bakin ƙofar, dan duk yaji me suke cewa.

Suna fitowa daga ɗakin a kan kujera suka ga, su RK shida Ammin sa, tunda suka fito Beenish ta ƙura masa ido tana kallon sa, shima itan yake kallo yanda take aika masa da kallon tsana shima haka yake aika mata dashi har bazan iya tantance waya fi tsanar wani ba acikin kallon da sukewa juna,

Kawai saka ƙafarta take Ameela nayi mata jagora tana janta, shi kuma hannun sa na cikin na Ammi yanda taji yana damƙe hannun ta tasan lalle ranshi a ɓace yake, kuma idan ta bashi dama komai ma zai iya aikatawa, ƴar kallo kawai ta zama ta kalli idon sa ta kalli Beenish abun ya mugun tsaya mata a rai yaushe suka haɗu da har sukayiwa kansu irin wannan tsanar haka kana kallon idon su zaka gane hakan.

Beenish bata janye idonta akan sa ba har saida suka fita daga falon, shi kasa janye nasa ma yayi saboda yanda yake jin sa har yanzu kalamanta basu daina yi masa yawo akai ba, ji yake kamar yaje ya shaƙeta ko ta daina numfashi bazai barta ba, baisan loƙacin da ya shiga ƙoƙarin miƙewa tsaye ba, Ammi tayi saurin dakatar dashi, ita tama rasa me zata ce masa dan abun ya gama sha mata, kai loƙacin da Moohad ya faɗa mata bata yarda ba amma yanzu sai taga abun ma yafi wanda aka gaya mata.

Da ƙyar ta samu damar cewa "calm down please kar ka bar hakan ya dameka wannan ba komai bane ka manta da ita yarinta ce ke damunta.

"Ammi" bata da kunya bakiji irin maganganun da take gaya min am not her mate, amma zata tsaya gaya min magana how u can imagine ta ɗaga hannu ta mareni amma duk da haka Ammi kike cewa ba komai bane in rabu da ita why Ammi? Taya zan iya yin hakan, how Ammi? How how? I swear I will never leave her Ammi without punishment..!!!

"Ya Allah, Allah na gode maka da kaban ɗa me jin magana da haƙuri irin wannan, yanzu ɗan albarka a gabana kake irin wannan furucin yaushe wai ka canza hali ko daɗewar da mukayi bama tare wasu suka gurɓata min tarbiyyar ka, yau ni nake faɗa kake faɗa, nace ka rabu da ita kana gaya bazaka taɓa barinta ba, Tom shikenan ai yanzu ka isa da kanka sai kayi abun da kake so, bazan kuma saka ba ko in hanaka ba, kayi duk abun da kake so, tana faɗar haka ta cire hannun ta daga nasa tana shirin tashi tsaye, da sauri ya riƙota yace "Ammi no ki daina faɗin haka, ya kamata ki fahimce ni, ki gane tunda kikaji na faɗi haka abun is too touch me it's painful, I'm very shocke da ta min wannan abun babu wanda ya taɓa yi min irin a duniyar nan Ammi yarinya ce fa ko sa'ar Faheema bata kai ba, amma kike cewa in rabu da ita, Ammi Please try to understand me.

Haɗe rai tayi tace "kayi abun da nace kada kasake kabari naji ance ka kuma shiga harkar su in ba haka ba kuwa zamu ɓata da kai kuma saima sanar da mahaifin ka, tana gama faɗin haka ta ɗau jakar ta ta fice daga falon, be kuma yin magana ba bare ya hanata fita harta fita gaba ɗaya.....

Yadai jita amma baya jin wannan karan zai yi abun da take so dan yanda yake ji bazai iya barin yaran nan su ci gaba da walwala ba batare da ya koya musu hankali ba musanman wannan yarinyar da ta mare sa...



$$$$$$$$$$$$$$$$$$


*GHAMBURJ*


___Sosai Bilal yake kuka da jin wannan mummunan labarin, Zaid ne shima kamar yayi kukan ya zauna yake basa haƙuri amma ina yaƙi yayi shiru su kam ƴan matan ma mamaki ne ya kamasu ganin ƙato da shi namiji ya zauna yana kuka, alhalin ko su da suke mata basuyi ba, sai shi shafaffe da mai.

Da ƙyar dai suka samu yayi shiru, nan dai suka kuma tattaunawa a tsakanin su, suna zage hajja mama tass, saboda da suna da yawa yasa kowa ya saki jiki har suka ɗan ci abinci duk da ba daɗinsa suke ji ba, yanzu duk hankalin su yayi gida musamman Bilal da Zaid,

Bayan sun gama ne Salma ta tashi tare da zuwa wajen wani window tana leƙen waje sai taga ai kamar ma dajine wajen, tana shirin barin wajen ta hango Hajja Mama tana ta sauri daga nan kuma taga tayi wata kwana tanayin kwanar kuma ta daina ganin ta, da sauri tace "kuzo ku gani kunga matar nan har tayi kwana.

Da sauri duk suka tashi suna rige rigen zuwa, saidai ko da suka leƙa ɗin daji kawai suka gani.

Faheema ce tace "ai daji ne ma, yanzu bazamu iya fita ta windown nan ba, duk window suka shiga bi da kallo Salma tace "ke yanzu taya zaki iya fita daga fara gwada sai muma muyi.

"Bilal yace "wai bata ce ƙofa a buɗe take ba saidai karnuka ta gashi wajen kuma babu karnukan kawai dai daman tsoratar da mu take.

Zaid ne yace "daɗi na dakai baka da tunani kawai sai ta kama barin ƙofa a buɗe ashema ba sato mu tayi ba.

Ɓata rai Bilal yayi jin yace masa marar tunani a gaban ƴan matan salon su raina sa.

Faheema ce me irin tunanin Bilal ɗin tace "kuma fa hakane, bari muga, tana zuwa ta murɗa ƙofar ga mamakinsu kuwa sai suka ga ƙofa ta buɗu, farinki ciki ne ya kamasu gaba ɗayan su, suka nufi ƙofar basuyi tunanin komai ba kawai duk suka saka kai suka fita suna fita ƙofa ta rufe, tafiya suka fara yi sai suka gansu kawai a ƙaton waje ga kuma ƙofofi sude inda suke saka ran itace hanya suka bi dan basu tsaya bi takan kofofin ba, sude burin su kawai su gansu a wajen dajinnan, murna kawai suke yau zasu fita, musamman su da suka daɗe a cikin gidan,

Tafiya sukai sosai amma har yanzu sun kasa gano inda zasu bi su fita daga gurin, daga sunyi inda suke tunanin hanya ce, sai suga ba haka bane, ga gurin shiru kamar babu kowa a ciki, sun sha wahala sosai kafin suka zo wajen wani window me glass da har zasu wuce, Bilal yace musu, tundade muna hango wajen kawai mu fasa glass ɗin tunda babu ƙofar fita.

Nan sukabi shawarar Bilal saidai kuma abun da zasu fasa ɗin suke tunani laluben makami suka shigayi amma basu samu ba, nan Faheema ta cire takalmin ƙafar ta da yake da ɗan tudu, ta bawa Zaid tunda shine babba acikin su kuma zai fisu ƙarfi, a hankali ya shiga dukan gurin bugu ɗaya kuwa ya tsage, yana kuma bugawa da ƙarfi ya tarwatse ya saura kaɗan ya shiga masa ido su kuma duk tsugunnawa sukayi.

A hankali suka shiga fita cikin da bara kar su yanke har suka gama fita gaba ɗayan su, nan ɗinma de da suka fita sai suka ga zagaye yake da katanga, tafiya sukaci gaba dayi, suna tafiya suna hira hankalin su kwance, sun kusa tsakiyar wajen sukaji haushin karnuka da suka rasa ta inda suke, nan fa ido ya raina fata musamman da suka tuna da maganar Hajja Mama, tsayawa sukayi wannan ya kalli wannan ya kalli wannan sun kasa motsawa, basu ankara ba saida sukaji haushin ya kusantosu.

Ihu suka saka gaba ɗayan su suna juyawa da gudu kowa takansa yake babu wanda yasan yana da gudu sai yau, amma fa gudun kare da mutum ba ɗaya ba, tuni mahaukatan karnukan suka kusan kamasu, suna zuwa daidai wani waje kawai sukaji ansaƙalo ƙafafun su duk zubewa sukayi suka faɗa da gaba, babu wanda baiji zafi ba haka suka kuma miƙewa zasu gudu duk sukaji ƙafafun su a saƙale ga karnukan sun kusan cinmasu gashi basuga kowa agurin ba, daga su sai filin Allah sai igiyar da ta riƙe su, sai kuma karnukan da suka zo dab dasu kowanne su ma zaro harshe...✍️



*Comment ɗinku shi zaisa inji ƙwarin gwiwa in ringayi musamman yanzu da na daɗe banyi typing ba, inbakwa ƙarfafamin gwiwa, taya zan iya, jiya na fara amma masu comments kaɗanne, to gashinan kunga alama tun anan dan wannan baifi rabin najiya ba, shima da ƙyara nayi, gsky ba kamar da ba duk kunyi shiru hmmm*


*Duk meson na saka shi a group ɗin Su waye su yayi min magana, iya littafin su waye su, dan Allah kar wanda ya min magana akan meman wani littafin, ko yace min in saka sa a group ɗin littattafai, to wallahi duk wanda yayi min magana bazanyi reply ba, sbd an saba yi min irin haka Ni ga abun da nace amma sai wasu si ta tambayata in tura musu littattafai dan Allah ku daina bana so ba littattafai nake turawa ba nawa kawai nake turawa*
[4/19, 10:24 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*



(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)

_______*08124226526*_______


*_episode 38💧_*



💧💦محمد لرسول الله...!💦💧

*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*

Bismillah..✍️


_____Gaba ɗaya karnukan sukayi kansu saura kaɗan su cije su, da sauri me tsaron su ya ƙaraso wajen tare da yiwa karnukan magana, suka dakata daga abun da suke shirin yi.

Duk korasu yayi gefe ya tsaya yana kallon yaran da duk sun gama ficewa daga ahayyacin su, ihun wannan na wuce na wannan ba ga mazan ba baga matan ba kowa ihun yake, ashe duk matsorsta aka tara, su malam Bilal kam harda kuka shida su Faheema Zaid ne dai ihun kawai yake amma babu ƙwalla.

"Abun da zaifi muku sauƙi shine ku koma inda kuka fito in bahaka ba kuma bazan ƙara taimaka muku, dan
End Ads