faru dasu suka tausaya mata suka ɗauke ta agaban motar ita da namijin dake gurin ya matsa mata ta zauna, a yanda take jin ta ai ko akan cinyar sa ne zama zatayi ita dai burin ta kawai ta ganta a gida jikin ta gaba ɗaya rawa yake...
A daidai ƙofar gidan su tace a sauke ta suka sauke ta su kuma sukayi gaba, daman ta hanyar suka biyo, suna sauke ta ta faɗa gida da gudu tana kuka..
Duk saida ta tsorata ƴan gidan waɗanda suka fara bacci duk saida ta tashe su tana kuka yake labarta musu abun da ya faru amma masu jajanta mata kaɗanne sauran duk tsaki suka buga suka koma makwancin su,
Ita da uwar ta kawai aka bari tana faman rarrashi itama kuma hankalin ta ata she musamman ma da taji an ɗauke Salma hakan bai mata daɗi ba, gani take shikenan kuma sun daina samun ɗan taɓa ka lashe ɗin da suke samu tunda babu wacce suke samu ta sanadin ta...
*Hajiya Rabi ikon Allah*
Ba ita ta dawo gida ba sai wajen ƙarfe 12:40am tana dawowa part ɗin ta kawai ta wuce ta kwanta daman indai tayi tafiya irin haka tasan kafin ta dawo kowa yayi bacci dan haka bata haɗuwa da kowa saidai da safe su farka su ganta, to yanzu ma hakan ce ta kasan ce babu wanda ta ne ma.....
Washe gari tunda tayi sallar asuba ta kuma komawa bacci ba ita ta farka ba, sai ƙarfe sha ɗaya da wani abun kafin tayi wanka kuma ta fito, sai 12:00pm, tana saukowa me aikin ta shiga yi mata sannun da zuwa tana ƙara gyara mata kan dining ɗin zata fara zuba mata abinci tace "a'a Saude miƙo min nan gurin ma, anan zanci, ta faɗa yana ƙarasa zama akan kujerar,
Zubo mata tayi tare da miƙo mata inda take, har zata juya tace kinbawa baƙuwar nan abinci jiya da yau,
Dafe kanta tayi "tace kashh wallahi na sha'afa gaba ɗaya dan Allah kuyi haƙuri bari inje inkai mata dake jiya, Khalifa ya ake ni da na dawo kuma gaba ɗaya na manta, bari yanzu inje inkai mata....
"Ayya babu komai, ki hanzar ta, naga ma bangan sa ba, ko har ya fita aiki ne,
"Wallahi ban sani ba, bamu haɗu bama tunjiyan, amma bari idan na kai mata sai in duba part ɗin sa,
"Ai naga 12 ma tayi nasan ya fita, ina Auta banji motsin ta ba nasan dai yau bata da lecture ko tagaya miki take wani wajen?
Dakatawa tayi daga niyar tafiyar da take tare da juyowa sai tace "gaskiya Hajiya bana tunanin ta kwana a gidan ma dan na leƙa ɗazu da asuba in tashe ta sallah naga bata nan, ɗazuma saida na kuma leƙawa da ban ganta ba naje na tambayi me gadi ko bata dawo ba, bata shigo ba tun jiya da ta fita da yamma bata dawo ba.
Cike da mamaki Rabi tace "bata dawo ba? Kar de a wajen suka kwana, kuma shine har yanzu bata dawo gida ba, jeki bari in kirata inji inda ta tsaya...
Tana ƙoƙarin kiran nata ne ma saiga Fauziyya nan ta shigo fuskar cike da rashin walwala hasali ma yau hijabi ne ajikin ta, Hajiya Rabi bata lura da yanayin ta ba, kawai tace "yauwa daman ku nake shirin kira yanzu sai kuma gaki ina salmar take?
Shiru tayi tana ƙarasa zama a gaban ta cike da faɗuwa gaba murayar ta kamar zatayi kuka ta fara bawa Hajiya Rabi labarin abun da ya faru ta ƙarashe bata tare da fashe wa da kuka, ga mamakin ta sai ma ce mata da tayi ta dena kuka taje gida zata sa ayi bincike in sha Allah babu abun da zai same ta..
Tayi manakin jin haka ta ɗauka zata lulluɓe ta da faɗa amma sai taga ko kaɗan ma hankalin ta bai tashi ba ita take bawa haƙuri ma, duk da haka jikin ta babu ƙwari ta tashi ta fita daga falon,
Saude dake gefe tana jiran ta ƙarasa maganar tata, saida taga fitar yarinyar sannan ta ƙaraso cikin sauri tace "Hajiya banga kowa a cikin store ɗin ba naga an buge kwaɗon ma ankara yasa..
Bata san loƙacin da ta miƙe ba a zabure tace "kamar ya bata ciki, me kike yi waye ya shigo har cikin gidanan ya fita da ita me kike nufi ki ce min kamar zata rufe ta da duka haka tayi can kuma sai tayi ɗif tunawa da tayi da sa'insar da sukayi tsakanin su da Bulama, da hannu tayi mata alamun ta bar wajen...
Zama tayi tana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, da farko ɗaukan Salma da akayi tunanin ta wajen Maryam ya tafi amma yanzu kuma da taji an ɗauke matar nan hankalin ta ya karkata da Bulama ya shirya komai daga ɗaukar matar har kuma ƴar ta sallama, aikwa ya ɗaukar wa kansa bala'i,
Tashi tayi ta koma ɗakin ta tare da wawuro wayar ta ta danna kira ana ɗagawa tace; "Saleem Merah kaga abun da Bulama yayi min daga jiya zuwa yau, ya ɗauke min yarinya sannan kuma ya ɗauke matar dake cikin gidana, to wallahi ni bazan kira sa ba da kaina ka kirasa kagaya masa ya dawo min dasu in da ya ɗauke su, in ba haka ba wallahi sai nayi masa abun da bazai ƙara moruwa ba ka gaya masa haka, sannan kuma duk wani abu da yake so yaji daga bakin ta bazaiji komai ba zan rufe mata baki duk yanda zaiyi bazata taɓa ce masa komai ba, dan wallahi idan bai dawo da su ba ko yatsan sa sai ya gagare sa ɗagawa daga inda yake bazai ƙara motsawa ba, idan kuma yana ganin ƙarya ne ya gwada ya gani, zai san wacece Rabi sai na nuna masa alsalin kalata da jabuna yake tare baisan wace asalin ba, tana gamawa ta kashe wayar bata jira cewar sa,
Cilli tayi da wayar tana samun waje ta zauna har ta zauna ta kuma miƙewa wayar ta kuma ɗauka ta shiga daddanawa nan wayar ta fara ringing bugu uku aka ɗaga, ana ɗagawa tace "magana ɗaya anan garin naku akwai wata yarinya zan turo maka da hoton ta ina so ka kawo min ita nan kuma bance ko yatsan ta ka taɓa ba, ka ɗauko min ita cikin kwanciyar hankali ka lallaɓata, zan turo maka da address ɗin inda zaka same ta sai kasa ka ido akan ta sannan sai kabi a hankali dan ba ita kaɗai bace tana tare da ƙawayen ta...
Daga cikin wayar yace "Angama baura uwar kuɗi babu abun da zai same ta ai umarnin ki kawai nake jira a koda yaushe dan ma wasu ƴan wahala sun jiƙa min aiki garin yiwa wani mutum aiki akan su suka min ɓalli ɓalli yanzu haka jinya nake amma dai naji sauƙi sannan sai na ɗau fansa dan wallahi basu daki banza ba mata basu iya su taka ni ba in barsu kuma ko su waye su ko ƴaƴan waye wallahi sai sun bambance aya da tsakuwa,
"Kaga wannan matsalar kace ka cikani da surutu koma meye ka fara gama min da nawa aikin sannan kayi naka daga baya.
"Yanda kika ce haka za'ayi hajjaju angama yanzu ke kaɗai nake jira....
Kashe wayar tayi tare da ɗauko wani hoto na Barazana da ta ɗauke sa a facebook tayi saving ɗin sa, tana tura masa ta tura masa sunan unguwar har number gidan saida ta tura masa, tana tura masa tana shirin ajiye wayar kawai kiran sa ya shigo wayar ta, ɗauka tayi da sauri tana cewa "yauwa kagani ko gashi nan na turo mak...
Bata kai ƙarshe bama yace "hajiya wannan ɗin wacece to ita agunki, ai harda ita a labarin da nake baki yanzu kuma address ɗin gidan su ne kika turo min meye haɗin ki da wannan yarinyar?
Saida ta ɗan tsorata da jin abun da yace tasan shi baya yafiya musamman ma da taji abun da yake cewa ko ƴaƴan uban waye ko su waye su tasan kuma zai iya yin komai tunda ya faɗa.
Cike da ɗan tsoron tace "Magana ɗaya kar kayi musu komai dan Allah gaba ɗayan su, ita kuma yarinyar da zaka ɗauko min jika tace ƴar gidan Kubra ce dan haka ina mai ƙara gargaɗin ka da kada ka cutar min da jika har ragowar ma kajini....
Ƙittt taji ya kashe wayar da sauri ta miƙi tana ƙara gwada kiran sa amma sai taji a kashe, hankalin ta ne ya kuma tashi, nan take ta fara zufa, tunani ta shigayi dole ta tafi Kano yanzu in ba haka ba tasan komai ma zai iya faruwa idan shi baiyi nasara ba Bulama zai iya yi akan ta, bata da wata kariya a tattare da ita tasan dai bai isa yayiwa Salma komai ba amma ita Abu idan ya ɗauke ta zai cutar da ita kafin tayi wani yunƙurin dan tasan duk inda ma yake yanzu haka shirin shi na gaba kanta ne kuma ya fara da sune dan ya raba mata hankali ta tada hankalin ta akan waɗannan ta tsaya yin wani abun shi kuma ya zagaye ya tafi Kano gurin Abu dole kwa tayi gaggawar da katar da shi, dole taje ta taho da jikar ta a yau ɗinnan tunda da miyagu biyu akan ta, ga Jambo ga kuma magana ɗaya...✍️✍️✍️
*Duk me son littafin sarki sameer complete, da kuma littafin Su waye su da nake yi yanzu tundaga farko har zuwa inda na tsaya yayi min magana ta wannan number 08124226526*
[3/5, 12:21 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)
______________________________
*_episode 30💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
Bismillah..✍️
*PAID BOOK💸*
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
*Fateema*
__Sun daɗe suna kuka saida suka yi me isar su sannan suka daka ta.
Khalifa ne yace "Duk naji labarin ki kuma in sha Allah zan taimaka miki, amma fa nima sai na fara sanin inda jakar take, saboda ita nima zan samu hujja, ko a gidan kuka barta?
Cikin muryar kuka tace "A'a ba acen muka barta ba tana hannun mahaifinsa saidai bansan garin da yake ba yanzu, yadai taɓa gaya min yaje gurin mahaifinsa sunyi maganar ya karɓe ta, yayi masa alƙawarin zai ajiye masa ita, to yanzu dai bansani ba mutumin yasan da mutuwar sa ko kuma shi ya mutu ko yana raye shine bansani ba, kuma koda yana raye bansan garin da yake ba,
"Ko sunan da baki sani ba?
"Eh bansa..... Katse zancen tayi tana tunanin kamar ta sani, sai can ta kuma cewa "nadai san yana amfani Shu'aibu Ali Bashir, kuma shide da asalin su ƴan wani ƙauye ne Lautai to amma yanzu bansan inda yake ba, saidai ko a gwada zuwa can ɗin ayi bincike ko za'a samu wanda yasan inda ya koma.
Ɗan numfasawa yayi kaɗan kafin yace "to shikenan zan bincika in sha Allah ke yanzu anan zaki ringa zama ko da wasa kaki fito, zan kawo miki komai na buƙata, kafin zuwa wani loƙaci, ni yanzu a yau zan tafi lautan in bincika nasan ko ba ya nan nasan za'a samu wanda yasan inda ya koma..
"Me zai hana mu tafi tare?
"A'a mama gwanda de ke ki zauna ɗin kibari inje in dawo saboda tsaro yanzu nasan sun baza ido suna neman ki, ko ya kika fita sai sun iya gano ki kinga kuma gaba ɗayan mu zasu kuma kamawa, dan haka gwanda kiyi haƙuri ki zauna ɗin.
"To Allah ya bada sa'a yasa kayi nasara..
"Ameen ya masa mata, dashi sun daɗe agun suna tattaunawa kafin daga bisani ya tashi ya fita, zuwa yayi duk wani abu da yasan zata buƙata saida ya siyo mata ya kawo mata sannan yayi mata sallama ya kuma fita...
Zaune tayi ita kaɗai agun tana ci gaba da tunanin rayuwa, saboda labarin da ta bayar sai yasa komai ta tuna sai ta zubar da ƙwalla, tuna loƙacin da ta tafi tabar su Beenish har yanzu abun da yake kuma yi mata ciwo kenan tafiyar da tayi ta barsu batasan halin da suka faɗa ba daga gurin da ta barsu, hawaye ne yaci gaba da gangaro mata agunn ta zame ta kwanta tun tana yi idon ta a buɗe har ta fara rufe su a haka bacci yayi gaba da ita.
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
*Five star ⭐*
____har yanzu Babyn baby taƙi yin shiru suna falo duk suna bata haƙuri duk da suma dauriya kawai suke, suna cikin wannan halin wayar Ameela tayi ringing burus tayi da ita taƙi ɗauka, nan ya katse aka ƙara kira daga ƙarshe ma batare da ta duba ba kawai ta kashe wayar ma gaba ɗaya..
Aunty Babba ce tace ya makata su tashi fa su gwada zuwa can gidan ko haƙuri ne su basa ya sake ta idan kuma da wani abun da yake so sai ya faɗa idan zasu iya sai suyi masa indai zai sake ta ta dawo cikin mu.
Duk na'am sukayi da maganar tata, batare kwa da ɓata loƙaci ba suka tashi sukayi suka shiga sauya kaya, ba ɓata loƙaci suka gama shiryawa, da sauri duk suka afka cikin motar, Aunty Babba ce me ƙarfin halin tuƙin.
Daman saida suka fara buɗe motar kafin suka shiga motar dan haka suna gama fita, sai Ameela ta fito zata rufe gate ɗin nasu, nan tayi karo da wata mata da tana ganin ta itama ta taso da sauri, har ta tsaya sai kuma ta ɗanyi gaba, ta fara rufe gate ɗin sannan ta juyo tana fuskantar ta zatayi mata magana kenan, matar tace, "Ameela koh?
Cike da ɗan mamakin jin sunanta a bakin ta, ɗan jinjina mata kai kawai tayi alamun eh"
"Sunan Maryam Hajiyar kice ta turo ni bakuyi magana da ita ba?
Sauya launin fuskar ta tayi tare da kawar da kanta gefe, sannan tace "to ina jinki me ta aiko ki?
"Jinjina kai Maryam tayi tana ɗan murmushin mamakin ta, ta kuma tabbatar da abun da mahaifiyar ta ta gaya mata.
"Uhmm ɗan gyaran murya tayi tana gyara tsayuwar ta tace "Ameela ki canza hali tare da ni zaku zauna duk da nagama kuna shirin fita ina zuwa?
Baki sake Ameela ke faman binta da kallon, cike da jin abun da take cewa, saida ta kai ƙarshen maganar ta ta, sannan tace "bama buƙatar wani a kusa damu muma mun ishi kanmu da kanmu, zaki iya komawa ki gaya mata haka, ko munyi da ita ta aiko mana wata ƴar aikinne...
Yanzu kam ba ƙaramin mamaki Maryam tayi ba batasan abun duk yakai haka ba, tana shirin yi mata magana kawai taga tayi gaba, tun kan tayi wani yunƙurin yi mata magana tuni ta buɗe motar ya shiga tana shiga kuma suka ja motar suka bar wajen..
Gurin da ta taso nan ta kuma komawa ta zauna cike da mamakin abun da tayi mata, ashe zata sha fama dasu, amma tayi musu uzuri tunda basu san ko ita wace ba, zata jira su dawo sai tayi musu bayani dalla dalla....
Shiru Shiru tana gurin har daf da magriba neman inda zatayi sallah ta farayi, ganin basu dawo ba, sai ta kira Dannar ɗin ta gaya mata duk yanda sukayi, nan ta kuma bata haƙuri sannan tace itama ta kikkira wayar ta a kashe amma zata gwada ta zauna tasan zuwa dare de dole su dawo....
Nan dai ta nemi wani gida ta shiga ta roƙe su zatayi sallah, ta samu tayi sallahr tayi musu sallama sannan ta fito, tana fitowa taci karo da wasu motoci guda biyu da sauri ta dakata, tana leƙen taga su waye saboda taga ba motar da yaran suka fita ba ce,
Fitowa mutanen suka fara yi, tana gurin duk suka fito, su su biyar ne kuma duk maza.
Na ƙarshen ne ya fito yana busa sigarin sa, tare da shafa sumar kansa yana ƙarewa gidan kallo tare da miƙa hannun sa sama yana miƙa, a hankali yace "masoya ta tare da sumbatar hannun sa ya miƙawa gidan..
Cike da tsoro Maryam ta zaro ido batasan loƙacin da tace "Bulama! Ko a mafarki ta gansa bazata taɓa kasa gane sa ba...
*HAJIYA RABI*
Tunda ta gama wayar ta fito a fusace, tana fitowa drivern ta yazo ya buɗe mata saida ta shiga, yaja motar suka fita daga gidan, saida suka fita tace "Ka ƙara gudu Kano mukayi...
Nan suka ɗauki hanyar kano, gudu yake sosai dan sai a zalzalar sa take ya ƙara gudun dan gani take kamar baya gudu, wajen ƙarfe biyar da wani abun suka sauka a garin kano, tana sauka ta kira, magana ɗaya taci kuwa sa'a tana kira ya ɗaga,
"Magana ɗaya kana ina? Tun ɗazu nake kiran ka wayar akashe ɗazu muna waya ka kashe min waya lafiya dai koh?
Daga cikin wayar yace "Hajjaju ai kiyi haƙuri rainane ya dugunzuma yanzu haka ma shirin zuwa nake na ƙaddamar musu, jira kawai