x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 41 - SU WAYE SU

  • 120001 words
  • 123000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 194

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ɗaya rayuwar sa yayi tunanin abun ya riga ya wuce me yasa sai yanzu zasu dawo da hannun agogo baya, shi bama duk wannan ba me yasa Boss zaiyi masa haka me yasa zai bada damar a ɗauke sa, badan da haɗin bakin sa ba yasan ba ta yanda za'ayi hakan ta faru ace duk girman muƙamin sa amma a shiga har cikin gidan mutane a ɗauko sa, tabbas yasan abubuwan da akayi amfani da su a gurinnan babu wanda zai bada damar yin hakan in bashi ba, to amma me yasa abun da ƴar aikin nan ta faɗa kenan da gaske ne, ba da zuciya ɗaya yake zaune dashi ba why hakan zata kasance.

Da ƙarfi ya furta "Impossible ƙarya kake indai na gano gaskiya dole in ɗau ƙwaƙƙwaran mataki akan ka, saina nuna maka Ni soja ne, duk wanda yaci amanata bazan taɓa barin sa da rai ba, ina haƙuri akan komai banda yaudara da cin amana, yana maganar yana muzurai kamar shi da wanine a ɗakin.



Hajja Mama na fita daga wajen sa ta nufi inda suke ajiye kayayya ki, tana shiga daman tayi shirin fita wata jaka ta ɗauka kawai ta rataya ta a baya, tare da rufe fuskarta rabi, ta zaro wata ƙaramar gun ta ɗaga doguwar rigarta ta totseta ajikin wandonta, sannan ta ɗauki wani ƙaton glass ta kuma ƙwamawa a fuskar ta, a haka ta fito cikin sauri babu kowa a gurin harta fita tana fita tabi ta hanyar da ta saba bi, saida tayi nisa sannan wani namiji yazo da mashin yana zuwa yaja burki a gabanta, ɗaga ƙafa tayi kawai ta ɗani ya tayar da mashin ɗin suka ci gaba da tafiya, daida suka fito wani babban titi sannan ya tsaya sai ga wata motar nan kuma ta tsaya, buɗewa kawai tayi ta shiga gaba, aka kuma jan motar.


"Sai fa kayi gudu dan saura minti talatin flight ɗin mu ya ɗaga idan mukayi missing wannan karan zamu rasa abubuwa da dama.


"Kai Hajja Mama duk wannan gudun da muke ai ina tunanin zamu isa kafin jirgi ya ɗaga, yauwa bakuyi magana SMA ɗin ba ko har yanzu bai farka ba?

"Eh" kawai tace dashi dan shima baisan me take shiryawa ba.

"Okay sai mun dawo kenan?

"Eh" ta kuma cewa dashi a karo na biyu.

Shiru motar ta ɗauka sai gudu da yake kwararawa,

Sun ɗanyi nisa kenan ya kuma cewa; "amma wai kina da tabbacin mutuminnan yana ƙasar kuwa ance fa baya zama a ƙasa ɗaya kullum cikin yawo yake.

"Haba Gee wace maganar kake haka saida aka tabbatar min tare ma da iyalen sa suka shigo kuma anbani information ɗin komai ai duk inda ma yaje nan yake sauka domin duka familyn sa suna ƙasar, kuma zaiyi wajen wata ma a cikin ƙasar ai yanzu hankalin sa ya kwanta baya tunanin akwai waɗanda zasu iya bibbiyar rayuwar sa, ya ɗauka komai yazo ƙarshe yaci bilis zaiyi rayuwa yanda yake so.

"Hmm to Hajja Mama bazanyi musu dake ba tunda kinfini sanin dawan garin, Allah yasadai adace shiɗinne, kinsan binciken da muka taɓa yi, kamar yana acting ɗin mutum biyu kuma alamu sun nuna kamar yana da twin brother a yanda Hajiya ta taɓa sanar dani kenan.

"Shiru Hajja Mama tayi tana nazarin maganar sa tabbas kamar ta taɓa ji itama ance twins ne to amma ya akai ko da yaushe mutum ɗaya ne yake bayyana ina ya kai ɗayan kenan dan ba halayyar su ɗaya ba, amma koma menene dai zasu gano gaskiyar...

Suna tattaunawa har suka ƙaraso airport ɗin ajiye motar sukayi a wani gareji sannan suka doshi jirgin suka ɗai, saboda akwai wata a ƙasa ansan su a gun ba ayi wani yi checking ɗin suba suka wuce cikin jirgin direct, suna shiga ba'a daɗe ba jirgin su ya ɗaga zuwa ƙasar Algeria...


$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$

*BARACK*

_____Suna ƙarasawa suka shiga ciki a daidai part ɗin sa sukayi parking ɗin motar, firfitowa sukayi tare da su, abakin ƙofar suka tsaya sannan ɗaya ya shiga ciki dan ya sanar dashi isowar su, yana shiga ya tarar da Moohad a falon yana zaune kan kujera da wani file a gaban sa yana duddubawa, sallamar da sojan yayi ne yasa shi ɗagowa yana amsawa,

Yana ƙarasowa ya sanar dashi ƙarasowar tasu dan yagayawa RK ɗin,

Jinjina kai Moohad yayi dan shi sam baiso haka ba, yafi so RK ya rabu da su akan me zai tsaya wani bi takan ƴan mata, bayan ga muhimman abun dake gaban su.

Tashi yayi gudun ɓacin ranshi amma da cewa zaiyi ya maida su wallahi shi hakannan lamarin ke bashi haushi baisan me yasaba, kodan baisan me ya haɗa su ba oho.

Bai daɗe da shiga ba ya fito tare da sanar dashi cewar ya shigo dasu falon kawai dan bacci yake saidai idan ya farka yayi musu abun da zai musu.

Yanda Moohad yace haka sojan ya fita ya shigo dasu sannan ya kuma juyawa yabar falon.

Tunda suka shigo suke faman bin falon da kallo suna ganin yanda ya cika falon da hotunan sa, falon suka shiga bi da kallo basu ganshi ba sai Moohad, shi kuma tunda yayi musu kallo ɗaya bai kuma kallon su ba, suma kuma babu wanda yace dashi wani abu.

Da sauri Beenish ta dafe bango jin zata faɗi sai kawai ta zame ta zauna a ƙasa zaman ma ji tayi bazata iya ba sai kawai ta kwanta tana ƙudundune jikin ta saboda zazzaɓin da taji yana neman rufe ta ga falon da sanyi.

Da sauri Barazana da Ameela suka tsugunna suna taɓa jikin ta tare da yi mata sannu, bata samu damar amsa musu ba sai ƙara nannaɗe jikin ta da takeyi,

Zaki sha ruwa Barazana ta tambaye ta, da ƙyar ta iya ɗan girgiza mata kai alamun "a'a,

Sosai hankalin su ya fara tashi ganin yanda jikin nata yafara kyarmar sanyi.

Ameela ce ta ɗago da sauri tace "dan Allah ko zaka ɗan kashe Ac nan bata da lafiya tana jin sanyi,

Ɗan ɗagowa yayi ya kalle ta tare da kawar da kansa baice komai ba ya ɗau remote ya kashe Ac yana kashewa kuma ya tashi daga gurin ya kuma shiga ɗakin RK ɗin, dan ya ƙarasa aikin sa, yana shiga ma yaga ya tashi yana zaune akan gadon sai ruwa a hannun sa yana sha,

"Kaje baƙin ƙa sun ƙaraso ɗaya ma bata da lafiya tana karkarwa.


Ya tsina fuska yayi yasan sarai su waye tunda yace ɗaya bata da lafiya yagane, amma sai ya taɓe baki tare da cewa "ni banyi da wasu zasu zo min dan haka kaje kace musu bana nan,

Shima dake iya yasan halin sa rainin wayonne kawai, sai yace "Wallahi zanje nace su tafi kuma bazaka kuma sawa a ɗauko maka su ba, in ba haka ba kasan sauran,

Tsaki kawai yaja yana miƙewa ya shiga bathroom.

Ganin hakan yasa Moohad ficewa daga ɗakin yana ƴar mitar sa arai.

yafi minti talatin aciki kafin ya fito da ya fito ma memakon ya shirya sai kawai ya kuma kwanciya akan gadon yana kallon pop ɗakin saida ya daɗe sannan ya tashi ya nufi hanyar waje daga shi towel a ƙugu ya fita daga ɗakin.


Loƙacin da suka da ya fito sai ya tsaya yana kallon ikon Allah, ganin su akan kujerun sa, waya basu wannan damar take mood ɗinsa ya sauya yana haɗe girar sama da ƙasa.

Su Ameela ne ganin ba kowa a falon ga sanyi ƙasa yasa suka ɗake ta suka ɗora ta akan kujera sannan suka zazzauna a gefenta suna ta faman yi mata sannu, sosai take basu tasauyi yanda take faman ƙanƙame jiki tana damƙe idon ta saboda azabar sa kanta ke mata, gashi daman ita bata iya cuta ba, tana daɗewa batayi ba amma idan tayi tana shan wahala sosai.

Basu san da fitowar sa ba sai jin tsawar sa da sukayi,

"Uban waya baku izinin hawar min kuje ra da ƙazamin jikin ku!

Zaro ido sukayi jin abun da yace musu basu san loƙacin da suka miƙe tsaye ba suna kallon sa, sai kuma sukaji kunya sukayi saurin sunkuyar da kansu ganin sa ba kaya sai towel.

Ita dai Beenish bata samu damar ko motsawa ba bare ta tashi duk da tana jin sa amma bazata iya tashi ɗin ba.

Ganin wata akwance bata da niyar tashi yasa shi ƙarasowa kusa da ita yadaka mata wata uwar tsawar da tafi ta farko, kamar zai rufe ta da duka,

Jin hakan yasa ta tashi zaune da ƙyar tana dafe kai har ƙwalla ta fara cika mata ido.

Da sauri su Ameela suma suka koma gefe suna kamewa guri ɗaya dan harga Allah ya tsorata su suma.

"Get up!

ya kuma daka mata tsawa, kasa motsawa tayi sai kawai hawaye da suka shiga zaryo mata,

Su Ameela kasa jura sukayi da ganin yanayin da take ciki hakan yasa duk suka juya baya suna runtse ido gashi ba damar da zasu taimake ta da suka fahimci hankalin sa baya kansu sai kawai Ameela tace "mu fita ko zamu samu wannan ɗinnan yazo ya taimaka mana, har suka fita kuwa bai sani ba.

Duk yanda Beenish taso tayi masa magana ta roƙesa amma daga ta buɗe baki sai kuka, ganin yana shirin dukanta yasa tayi ƙarfin hali da ƙyar ta miƙe tsaye, amma tana tashi gaba ɗaya tayi luu zata faɗi tayi saurin dawowa daidai saidai tana kuma tsayawa ta kuma tafiya luu zata faɗi zaro ido ganin zata faɗa kan Center table ɗin dake gefe cike da tsoron abun da zai faru idan ta faɗa kai, baisan loƙacin da yayi sauri ya cafko hannun ta na, amma duk da haka saida ta faɗa shi kuma ya bita batare da yasan ya akai hakan ta faru ba, saidai baikai ga danne ta ba yasaka hannu ya tokare kansa,

Sai loƙacin ta ɗan buɗe idon ta tare da kuma lumshe su a hankali,

Ƙoƙarin tashi ya shiga yi yana tashi kuma towel na kuncwa daga ƙugu, a haukace yayi ƙasa ya tsugunna yana zaro ido tare da kallon ta daidai loƙacin itama ta ɗan buɗe ta kuma rufewa saboda nauyin da taji sunayi mata, taji zafin faɗuwar da tayi amma ko ƙara ta kasayi muryar ta dashe.


Da dabara ya jawo towel ɗin ya mayar jikin sa da sauri ya tashi yana gyara ɗaurin tashin hankalin sa kawai Allah yasadai bata gansa b....

Bai gama tunanin nata ganin ba, sai yayi saranda zuciyarsa na bugawa tunawa da yayi da sauran ƴan matan dake falon, da sauri ya runtse idon sa yana kiran innalillahi shikenan yanzu sun gansa ko motsi yakasa bare ya juyo....✍️✍️





*_Barkan mu da dawowa bayan hutu me yawa da ɗauka sbd ɓatan waya ta, ina me bawa kowa haƙuri da zaman jira, kana taka Allah na tasa Allah beyi zanyi wayar ba tun a loƙacin, sai cikin azumi dai Allah ya nufa nayi, saboda Azumi kuma yasa banci gaba da posting ba sai yanzu, ina mai ƙara baku haƙuri🙏🏿_*


ZBazan manta da abun da wasu readers ɗin sukayi min loƙacin da aka sace min wayata, wasu sunyi ƙoƙari sun nuna min ƙauna, a junan su suka haɗa min kuɗi masu yawa suka turan sukace in rage asara, gaskiya naji matukar daɗi sosai da Wannan gudunmawar tasu, bazan taɓa mantawa ba, Ina godiya sosai da sosai ga duk wanda da tasa gudummawar aciki, Nagode Nagode Allah ya saka muku da mafificin alkhairi ya biyaku da gidan aljanna, yanda kuka faranta min Allah Ubangiji ya faranta muku kuma*

*Saboda tsawon loƙacin da na ɗauka bandawo online ba yasa akayi missing ɗin sunayen waɗanda suka haɗa gudunmawar da na jero sunayen, amma ina fatan saƙon godiyata yaje gare ku*
[4/19, 10:24 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*



(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)

_______*08124226526*_______


*_episode 37💧_*



💧💦محمد لرسول الله...!💦💧


*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*


Bismillah..✍️

___Bai gama tunanin nata ganin ba, sai yayi saranda zuciyarsa na bugawa tunawa da yayi da sauran ƴan matan dake falon, da sauri ya runtse idon sa yana kiran innalillahi shikenan yanzu sun gansa ko motsi yakasa bare ya juyo...

Sosai gaban sa yake faɗuwa da abun da ya faru da shi, itadai yana tunanin kamar bata gansa ba to su kuma da suke bayan sa ba, sun gama kalle sa yanzu da wane idon zai kalle su, yana cikin wannan tunanin yaji anturo ƙofar, Moohad nayin sallama, kasa amsawa yayi bare ya juyo,

Moohad ne ya shiga yi masa magana; "Haba my man ka ɗaga mata ƙafa mana taji sauƙi baka yanayin da take ciki ba, ka ringa tausayin mutane mana.

Duk da haka RK bai motsa ba bai kuma basa amsa ba bare yasa ran zai juyo,

Can kuma ya tsinkayi muryar Moohad ɗin yana cewa kun wani tsaya a waje ku shigo mana, kuzo ku ɗauke ta gashinan ma kamar faɗuwa tayi, kuma da ba sai ku bashi haƙuri ba ku kuma gaya masa halin da take ciki, ai bawai ku fita nemana ba da baku same ni ba fa, yazo ya cutar muku da ƴar uwa.

Wani irin sanyi RK yaji ya ziyarce shi tunda kan yatsar sa har tsakiyar kansa, take ya saki wata nauyayyiyar ajiyar zuciya batare da ya sani ya furta alahamdulillah a fili.

Moohad ne ya matso kusa dashi yace "alahamdulillah da me, ina maka magana ka shere ni,

Murtuke fuska yayi yana kawar da kai gefe irin shifa baya son raini, a ransa kuwa wani mugun daɗi yake ji da babu wanda ya gane masa jiki.

Kuzo ku ɗauke ta ku ɗorata akan kujera, bari akawo mata magani, ya faɗa yana juyawa yana kallon su Ameela da shigowar su suka tsaya daga gefe, kasa motsawa sukayi bare suyi abun da yace da su, saida ya ƙara maimaita musu sannan suka fara takowa inda suke.

"F**ck you Moohad! How dare you zaka na min shishshigi ina ruwan ka da rashin lafiyar ta, wannan ba damuwar mu bace wanine yace suyi min laifin kasan me tayi minne da kake cewa in tausaya mata, ai ko mutuwa zatayi ba damuwa ta bace, dole tayi abun da nace mata, yana faɗa haka yasa ƙafa ya daki tata tare da cewa "get up! Before I shoot you anan gurin, dai ihu yake mata yana ta tashi saidai ko motsawa batayi ba,

Moohad ne ya zaro wayarsa yace kar ka fasa bari in kira Ammi ingaya mata kisan kan da zakayi.

Ƙwace wayar yayi tare da jifa da ita ta tarwatse a ƙasa, sannan ya kalle sa yace "Moohad ka fita daga harkata ka daina min irin wannan abu kaɗan kace zaka tayarwa da Ammi hankali wallahi zan maka abun da baka tunanin akan wannan halin, ka kaini ƙarshe wallahi duk abun da nayi maka kai kajawa kanka inga uban da ya isa yasani abun da banyi niya ba, kuma ka haɗa kayan ka kabar min gida bana son ganin ka I hate you!

Moohad yasan halinsa wannan ba sabon abune agun sa ba, shiru yayi masa kawai dan idan ya biye masa sai sun gwada ƙwanji agun, shiyasa kawai yaje ya ɗauki wayar sa da ta farfashe, ya fice daga falon batare da yace masa uffan ba,

Ganin ya fita yasa shi doka tsaki shima ya shige ɗaki, aka barsu su kaɗai, da sauri su Barazana suka ƙaraso gurin ta, sude yau sunga ta kansu, jijjigata suka shiga suka ga bata motsi da alamu ma suma tayi, cike da tashin hankali Ameela ta miƙe ta fara laluben inda fridge yake ko kitchen, can wajen dinning ta hango fridge ɗin, da gudu taje zata buɗe saidai a ƙulle yake, tana juyowa kuma ta samu ragowar ruwa kan dinning ɗin, ɗaukowa tayi tazo suka shiga yayyafa mata, amma bata motsa ba, suna cikin wannan tashin hankalin, aka turo ƙofar da sauri wata mata ta ƙaraso gurin hannun ta ɗauke da ƴar akwatin ta, alamu dai likita ce,

Cikin sauri tace ku kamo ta muje wancen ɗakin ta nuna wani ɗaki dake kusa da gurin.

Cikin sauri suka ciccibeta sukayi cikin ɗakin da ta ita tare da taimakon likitar,

Suna zuwa suka ga ɗakin kamar ɗakin asibiti harda gado a ciki, da sauri likitar ta shiga duba ta, saida ta daɗe a kanta kafin ta samu ta farfaɗo daga doguwar suman da tayi, tana farfaɗowa kuma tayi mata allurar bacci, saida ta tabbatar komai daidai sannan ta juyo tana kallon su Ameela da sukayi zuru suna kallon ta kowa jikin sa asake,

Murmushi ta ɗan sakar musu tare da cewa ku kwantar da hankalin ku tana farkawa zata tashi normal in sha Allah, idan da wata matsala zan dawo.

Suma murmushin yaƙe suka sakar mata, sannan ta fita daga ɗakin dan iya abun da aka umarce ta kenan kuma tagama shiyasa ta fita.

Tana fita suka bi bayan ta da kallo akusan tare suka sauke ajiyar
End Ads