Sauran sojojin ne suka shiga shigowa duk suka zagaye su kowa ya tsaya akan kowacce yanda babu damar su tashi.
Kallon su ya shiga yi, idon sa ya sauka akan wani soja da yaga idon sa ta kalli waje ɗaya bin idon nasa yayi yaga inda yake kalla, taku ɗaya yayi yaje gaban sa, yana zuwa kuwa ga kwashe shi da wani lafiyayyen mari, gaba ɗaya gurin saida suka tsorata, su kansu su Ameela duk saida suka dafe kumatun su dan ji sukayi kamar su aka mara,
"Get out from here..!
Sum Sum Sum ya fice hannun sa dafe da fuskar sa, yana cewa "Sorry Sir" a haka ya fice daga falon...
Sauran kuwa gudun suma kar hakan ta faru dasu duk suka shiga hankalin su tare da sunkuyar da kawunan su babu wanda ya kuma kallon wata ma bare su kallowa kansu wani abun....
Juyawa yayi ya kalle ta ya kuma maida kallon sa kan cinyoyin nata a karo na biyu da yaga har yanzu bata rufe ba...
Ganin inda ya kalla yasa ta saurin jan rigar ta batasan loƙacin da ta miƙe tsaye ba, bakin ta ne ya fara motsi alamar gunguni, tana ɗagowa taga kallon da yake binta da shi, kamar zai kamo ta, kawai sai ta saki tsaki, tana aika masa da harara, saboda duk ji tayi haushi ya kamata wayasan tunloƙacin ma da rigar ta yaye amma bazai ce ta gyara ba saboda iskan ci zai tsaya yana kallon ta, hakan yasa ta kuma sakin tsaki batare da tasan tayi ba,
A fusace yayi kanta zai kamo ta ganin hakan tsoro ya kamata bata san loƙacin da ta kwasa a guje ba tayi wani ɗaki dake gefen ta, saidai kafin ta rufe yayi saurin saka ƙafar sa a bakin ƙofar, idon sa ya watsa mata da yasa ta fara jin tsoron sa, ganin yanda ya haɗe fuska yana binta da mugun kallo yasa taji jikin ta na ɓari, da baya da baya ta fara ja tana girgiza kai cikin tsoro tace nifa badakai nake ba, da wancen shegen nake wanda naga yana kallon kaga kai kuma baka kalle ni ba shiyasa nace badai nake ba Allah ka yarda dani....
Duk abun da take bai motsa daga inda yake ba sai kallon up and down da yake binta da shi, cikin ɓacin, me take nufi da shegen da yake kallon ta to waye ya kalle ta in bashi ba, shine shege kenan....
Takawa ya fara yi yana shiga cikin ɗakin, ganin ya fara shiga yasa su Aunty Babba duk suka miƙe suna shirin zuwa wajen, sojojin duk sukayi saurin tare su, suka hanasu damar motsawa ma bare su kai da zuwa can,
Tana ganin ya fara takowa ta kuma tsorata jikin ta har karkarwa yake ita kanta mamaki take yanda ta tsorata haka duk irin damben da suke da mutane to ya akai shi zai gagare su kuma har take jin tsoron sa harda rawar jiki,
nufar ta kawai yake ita kuma tana kuma ja da baya, tana yayyarfa hannu, haka suka shiga taku tana ɗaga ƙafar ta zai ɗora tasa akai jira yake yaga iya gudun ruwan ta, aikwa dai tana zuwa jikin bango ta tsaya, tana kuma tunanin yanda zatayi, a gaban ta ya tsaya tare da zaro wata ƴar ƙaramar bindiga, Beenish na gani jikin ta ya kuma ɗaukan ɓari,
Ɗora bindigar yayi akan goshin ta, da sauri ta rufe ido abun mamaki sai kawai hawaye suka shiga gangaro mata bata san sanda suka taru ba har suka kai ga saukowa...
Tsayawa yayi kallon ta ganin yanda tayi sai kawai ya kuma mayar da kan bindigar kan wuyan ta yana ɗan motsi da ita kamar irin saita ta yake zai harbe ta, da sauri ta buɗe idon ta tana buɗewa suka haɗa ido, sai ta tsaya bata janye ba, ta gefen ido take kallon sa, cikin aro jarumta da dauriya, ta faki idon sa ta gefe tayi saurin ƙwace bindigar tare da ɗaga ƙafarta ta kaiwa ƙasan wandon sa duka, tare sa tura sa da ƙarfi, nan kwa yayi baya amma ba sosai ba, da sauri tayi gefe tana nuna sa da bindigar tace idan ka kuma yin wani yunƙuri sai na harbe ka anan gurin, bil haƙi da gaske yake, sai wani zazzaro ido take, tana jujjuya bindigar tana saita ta, saki kawai ya rage tayi dan har dannawa tayi tana saki bullet zai fita.
Naɗe hannun rigar sa ya shigayi dan shi kaɗai yasan irin hukuncin da zai yi mata saboda tunda yake ko namiji babu wanda ya taɓa yi masa abun da tayi masa, duk da yanajin zafin dukar masa alulu da tayi amma yayi jarumta ya dake kamar baiji dukan ba, nufar ta ya kuma yi, yaga me zatayi ɗin,
Ja da baya ta kumayi duk da ga bindigar a hannun ta amma saida ta kuma tsorata saboda yanda taga yanayin sa ya kuma sauyawa, kamar ba mutum ba,
Ganin da gaske dai kamata zaiyi batasan loƙacin da ta saki harbin ba, saidai kuma iska ce kawai ta fito saboda ba bullet ko ɗaya a ciki,
Zaro ido tayi cikin sauri kuwa ta jefa masa bindigar zata gudu taku biyu yayi ta cafko ta, gashin kanta ya damƙo sannan ya jefata gefe ta faɗi nan kwa ta saki ƙara ƙarfin hali ta kumayi ta miƙe ya kuma mayar da ita da ƙafa, zata tashi yasa ƙasan takalmin sa ya danne mata hannu, take ta kuma sakin ihun azaba, "wayyo Allah hannuna...
Daga waje su Ameela suka jiyo ihun ta ai duk yanda sojojin nan su so hana su saida suka yi yanda sukayi suka ƙwace daga gurin su duk suka nufin cikin ɗakin, suma sojojin binsu sukayi cikin sauri duk a kusan tare suka shiga ɗakin, loƙacin da suka shiga shi kuma RK ya caƙumo wuyan rigar ta ya ɗago ta tsaye, naushin ya kaima ta tayi saurin tsugunnawa ya daki iska, sai kawai yasa ƙafa ya kuma jefata gefe, a dadai wajen suka ƙarasa gaban sa, saidai basuyi yunƙurin yin komai ba sojojin suka yi ram da su duk suka kame su, suka fara jansu zasu fita dasu amma sunƙi basu haɗin kan fitar...
Duk da haka bai haƙura ya kuma tunkarar ta ya kuma yin ball da ita daga inda take sai da ta kusan shigewa ƙarƙashin gado, sosai ya jigata ta, saida ta dawo tayi laushi ko motsi me kyau batayi sannan yajawo gashin kanta da haka ya ringa janta har ya fito da ita wajen falon nasu, inda sauran ma suke, sun tsaya ne kawai saboda bindigar da aka nuna musu ance duk wanda ya motsa daga gurin sai sun harbe sa, hakan yasa suka kasa komai,
Karɓar bindigar hannun wani sojan yayi ya samu waje kan kujera ya zauna, duk da haka Beenish na riƙe a hannun sa, saida ya zauna sannan ya sake ta tare da nuna mata inda zata tsugunna ba musu kuwa ta tsugunna san jikin ta gaba ɗaya ciwo yake mata..
"Ku bincike mana ko ina!
Nan sauran sojojin suka fara shishshiga ɗaki ɗaki suna bincike gidan, shi kuma yana zaune dasu a falon yasaka musu bindiga duk wanda yayi ƙwaƙƙwaran motsi sai ya harbe sa, hakan kwa yasa duk suka kasa motsi....
Saida suka gama caje gidan tsaf sannan suka fito suka ce basu samu komai ba, da ya danganci kayen maye, saidai kuma kuɗaden da suka gani waɗanda Dannar ta bawa Ameela,
Karɓa yayi ya ajiye su a gefen sa, batare da ya kalli inda take ba yace; "Get up and put on your clothes,
Ƙin motsawa tayi, hasali ma yi tayi kamar batasan da iya yake ba,
"Don't let me repeat it again"
Cikin rashin jin daɗin jikin ta ta miƙe da kyar take iya takawa zuwa ɗakin su, tana shiga taga yanda suka hargitsa musu ɗaki tsaki taja a ranta tana mamakin yanda sojoji suke da mugun ta gaba ɗayan su mugaye ne, guri ta samu ta zauna da niyar babu inda zata ta shigo kenan, kwanciya kawai tayi akan gadon tana ƙara tunanin yanda ya ringa ball da ita, dan haka ta barwa ranta abun da zatayi masa dan sai ta rama cin mutun cin da yayi mata, sai yayi da nasanin dukan da yayi mata dan wallahi bai daki banza ba sai ta rama....
Tana kwance agun tana ta saƙe saƙen abun da zatayi masa, sai kawai ji tayi ambanko ƙofar da ƙarfi, a tsorace ta tashi tana kallon gurin kuwa suka haɗa ido da shi batasan loƙacin da ga diro daga kan gadon ba, tsayawa yayi a bakin ƙofar yana aika mata kallo me cike da gargaɗi,
Turo baki tayi tana sake yin gunguni magana ciki ciki ta nufi wajen wardrobe ɗin su, buɗe tata tayi sai ta zaro riga me haɗe da hijabi ganin yana gurin kuma bazata ta taɓa ce masa ya matsa ya bata guri ba kar taje ya kuma kammala ta, kawai sai ta ɗora ta akan rigar jikin ta ta saka hijabin, ko ɗaure sa batayi ba, tana juyowa taga baya gurin ma, wata zuciyar ce tace kiyi zaman ki wallahi kar ki fita ko ina, wata kuma tace kin manta waye shi kenan, ai da sauri ta fito daga ɗakin, ashe gwanda da Allah ya taimake ta ta fito saboda yana bakin ƙofar fita yayi daman dan gabata guri ta saka kayan, tana fitowa ya daki kanta yana turata, gadan gadan ta tafi zata faɗa kan wani glass da sauri ya jawo hannun ta ya tsayar da ita, tana tsaya kuma ya ci gaba da tura ta, tayi tunanin a falo zasu tsaya, sai taga yaci gaba da tura kanta hanyar waje, sunaji suna gani ya fita da ita daga falon, saida suka fita sannan sojojin suka sake su, suka bi bayan su, suma da sauri duk sukayi wajen...
Babyn baby sai kuma take tana "cewa ina zasu kai ta, kunga fa zai tafi da ita muyi wani abun, kar mu bari ya tafi da ita kashe ta zasuyi, dan Allah kar ku kashe ta ita kaɗai ta rage min a duniyar na kar ku tafi da ita, itace uwata itace ubana, itace komai nawa, Aunty Babba kunga fa ya saka ta a mota dan Allah ku tayani roƙon sa gwanda su ajiye ta ni su kashe ni, gaba ɗaya ta fita hayyacin ta daman tunda taga yana dukan ta take kuka, amma ganin za'a tafi da ita ne yasa kukan yanzu yafi na farko....
Da gudu taje wajen motar tana ƙara roƙon sa, amma ko inda take bai kalla ba, sai ma sawa da yayi aka janye ta daga gurin motar sannan yasa drivern yaja motar suka nufi hanyar fita,
Dukan su babu wanda bai zubar da ƙwalla ba da suka fita daga gurin ga kukan da Babyn baby take yafi ɗaga musu hankali, sun haɗu sai rarrashin ta suke duk da suma hawayen suke.....
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
*RABI*
___Su uku ne a zaune a wani falo, ita da wasu maza guda biyu,
Kallon wani mutum tayi da ƙasumba ta cika masa fuska rabin ta kuma duk fara ce, girar sa ma ta kusa haɗewa saboda yawan ta, kana ganin sa kaga kallar mugaye, ya harɗe hannu wansa akan ƙirjin sa, yana binta da kallo saida yaji tayi shiru da maganar ta sannan yace; "wannan matsalar kice tsakanin ki da ita sauran ya kamata kije ki nemo ni banda dill akan ta, loƙacin da kukayi baki sanar dani ba munafurtata ma kika yi baki sanar dani kina aiki a ƙarƙashin su ba, dan haka babu wani abu da zan iya yi miki akan ta, matsala ta guda ɗaya ce da kika ce Maryam na raye har yanzu itace dole zanyi wani abu akai amma Dannar babu matsala ta da ita, Maryam kuma indai a duniyar nan take bazata min wuyar gano inda take ba, bare ma kince zata kawo miki ziya a karo na biyu to yanda akabi aka kawar da ita wancen loƙacin to yanzu zamu sake shiri sosai ta yanda in ta tafi ta tafi kenan bazata sake dawowa ba,
"Amma Bulama kasan da wani shirin namu ko yakamata ka ajiye wannan muje mu fara gamawa da wancen idan tazo hannun ka sai kayi duk wani abu da zaka yi daga baya, wani ƙayatacen murmushi ya saki yana shafa gemun sa yana kallon mutumin da yayi magana, cikin wani kalar murmushi yace Merah ka gaya mata kuwa wannan sabon albashir ɗin...
"A'a ka faɗa mata waƙa abakin me ita ai tafi daɗi..
Rabi kallon su kawai take cikin rashin fahimtar inda maganar su ta dosa.
Bulama ne ya lalle ta yace "yanzu duk a ajiye maganar Maryam zamuji da ita daga baya yanzu sabon shiri ne yazo na musamman bansani ba ko zamu kuma samun haɗin kanki a wannan gaɓar kamar yanda kika saba...
Duk da batasan meye ba amma a yanayin maganar da suke sai taga kamar da rainin hankali a ciki sai kawai ta sha jinin jikin ta.
Hajiya Rabi babban albashir ɗin da zan miki shine na cewar na gano inda jikar ki take muradin raina dan haka ki fara shirin gagarumin biki da ba'a taɓa yin irin sa ba, domin na musammanne wannan bikin yayin da santalelen saurayi da bai taɓa aure ba zai tare da santaleliyar budurwar sa me jini ajika, da ya daɗe yana jira....
Cike da tsoro da ɗan firgita tace "ban fahimci me kake nufi ba kamin magana yanda zan gane mana..
Dariya yayi sosai haƙoran sa na fitowa ya kuma shafa gemun sa yana ɗaga mata gira ɗaya yace; "zaki gane ne Idan kin hanani auren uwa ai yanzu baki isa kin hanani auren jikar ki ba, na gano inda Abu take kuma nan da wani satin ina me farin cikin gayyatar ki ɗaurin auren jikar ki tare da ni abokin aikin ki..
Miƙewa tayi tsaye cikin tsananin ɓacin rai tace; "JAMBO..!!
Juyowa yayi yana kuma kashe mata ido yace kin tuna da tsohon sunana kenan da kika ji an ambaci jikar ki, ke kanki baki san idan suke ba daga ita har ƴar taki, to ni ina bibbiye dasu kuma nasan inda suke dan haka baki isa kin dakatar dani ba, ta sanadin ki na shiga gidan yari dan haka ki jira ramuwar da zanyi akan ki, dan Jambon da kika sani har yanzu ina Jambo na ban sauya ba saima abun da yayi gaba, ina ɗaga miki ƙafa ne saboda wasu abubuwa, amma a kullum idan muka haɗu ji nake kamar na na shaƙeki ki mutu fito dake da nayi daga prison badan in taimake ki bane saidan in ɗau fansa da kaina bana son kowa ya ɗauka, bayan kuma yaudarata da kikayi kika je kina aiki da maƙiya na dole ki karɓi abun da kika shuka....
"Jambo!! Kasan bana tsoron ka kuma bazan ji ba, dan haka kayi duk abun da kaga zakayi nima zanyi nawa sharri na yafi naka wallahi hattara yaro, nagaya maka bansan inda suke ba, to na san inda ko wannen su yake da kabiyo ta wajena ma da tuni da daɗe da baka address ɗin ko wanne su babu wanda bansan inda yake ba kuma komai suke akan ido na ne, ko angaya maka nima bacci nake zuwa inyi to da ido ɗaya nake bacci, mu zuba mugani ni da kai shege ka fasa, in baka fasa auren Abu ba uwar ka shegiya ta haife ka, nima ai ina nan da niyar ɗaukar fansar kaga kuwa saidai fansa ta ɗauki fansa ko angaya maka na manta da kashe min miji da kayi a gaba na kuma kasa na karɓi laifin kisan sannan kasa nayi rayuwar gidan yari to nima babu abun da na manta, Abu na haɗa ta da mutanen da baka isa ka tunkare su ba ƙaryar ka kayi nasara akan ta, Abu ba kalar ka bace yarinya ƴar ƙwalisa ga kyau ga wanka ga kuma gata kuma da tsari ajikin ta ko angaya maka zama da Alhaji Rabo a banza mukayi sa duk wani abu da kaga ya yi babu abun da ban iya ba, dan haka kabini a hankali kafin in maida kai kwaɗo anan gurin banza sha sha yanzu wasan ya fara in ka isa ka auri Abu kaga in zaka iya, har ni zakayi wa barazanar kashewa to ɗan shege ka fasa mu zuba mugani mu ko ku....
"Dariya ya kuma yi maganganun da tayi ko ajikin sa, "yana dariyar yace, haka kika ce ko?
"Eh na haka nace, sannan nima bari inyi maka wani albashir uban ka me gari yana hannuna kana wani yunƙuri zaka rasa shi badai shi kafin ji dashi ba kaf duniyar nan wasa da rayuwakan jinina daidai yake da wasa da ran mahaifin ka, sai ka duba ka gani auren Abu ko ran mahaifin ka, ka rabu da ahalina nima zan rabu da naka, ka fita a harka ta salin alin in ba haka ba wannnan dukiyar da kake taƙama da ita sai nasa ka kasa taɓa ko tsinke daga cikin ta sannan duk mutanen dake kusa dasu kai kake ji da su duk sai na kwashe su in ka isa ka ƙwaci kanka kai kaɗai, daga nan kuma zan sa ka sake komawa gidan yarin zama na har abada inka ga ka fito to gawar ka za'a fito da ita.. tana gaɗar haka ta buga table ɗin dake gaban sa tace loƙacin ka ya fara daga yanzu tana faɗa ta juya, har takai ƙofa ta tsaya tare da cewa; "kai kana nan har yanzu?
Da sauri Alhaji Merah dake gefen Bulama ya jinjina kai yana ɗaukar muƙullin motar sa yace "ai ƙafar ƙafata ranki ya daɗe sawun giwa ai ɓadda na raƙumi yake...
Murmushi tasaki tare da cewa Jambo fatan nasara a wasan mu na ƙarshe, tana faɗar haka ta fice Merah na bin ta a baya.....
Kofin glass ɗin dake gaban Bulama yakama sa ya damƙe a hannun sa baisaki ba saida ya fashe kwalba ta shiga hannun sa take ta fasa masa hannu jini ya fara zuba, miƙewa yayi cikin tsananin ɓacin rai ya fara facali da kayan falon komai ball yake dashi abun fasawa kuma