*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*
Bismillah..✍️
____*BULAMA*
Ba ƙaramar razana yayi ba da ganin wannan sabon lamarin, waya ya ɗauka ya shiga kiran mutanen sa amma, duk wanda ya kira sai yaji wayar a kashe, hauka ya kusan yi, ana bada hannu kuwa yaja motar da wani irin mahaukacin gudu, ko kallon gaban sa ba yayi, wani gidan sa ya nufa memakon ya koma wancen sai yayi wani wajen, yana shiga falon gidan ya shiga fashe tashen abubuwa, tare da buɗe wani fridge ya ɗauko kwalbar wine, ɓalle murfn kawai yayi ya kafa baki saida ya shanye tass yaji batai masa daidai ba, sai ya kuma ɗauko wata itama shanye ta, saida ya sha uku sannan ya farfasa kwalaban, ya shiga tangaɗi a falon yana sun batu shi kaɗai, a wannan yanayin nasa ya kuma lalubo wayar sa, cikin yanayin maye ya dannawa Rabi kira yaci sa'a kuwa yana kira ta ɗaga,
Tana ɗagawa ta fashe mishi da wata iriryar dariya, kafin ma yayi, magana tace "kaɗan na ka gani nasan yanzu duk inda kake zuciyar ka bata maka daɗi, to idan baka dawo dasu ba, haka zan tasaka asarar abubuwa ko ban tona maka asiri ba amma sai nasa ka rasa komai daka mallaka, kuma batare da kowa yasan ina aikata hakan ba, sai ka dawo kana roƙona, dan haka kayi gaggawar yin abun da nace maka, dan wannan abun domin taɓi ne, nagaya maka daman nafi ƙarfin kayi jayayya dani, ka jira next plan ɗina, tana kaiwa nan bata bari yace komai ba ta kashe wayar.
Shi kam kamar soko duk da baya cikin hayya cin sa sosai amma tsaf ya fahimci me tace, ɗaga wayar yayi kawai yayi jifa da ita take ta tarwatse, riƙe kansa yayi da hannu biyu yana zazzaro idanu tare da ƙwala wata uwar ƙara, gaba ɗaya jikin sa rawa, yake can kuma sai ya zauna kawai ta fashe da dariya ta hauka, sak kana ganin sa zaka ce ya zare kamar sabon mahaukaci, cikin dariyar yace "ƙarya kike Rabi baki isa kinga ƙarshen dukiya ta, ina da kuɗin da ni kaina bansan inda da su ba, wallahi ina da wallahi ina da kuɗi, kuɗi ba eh su ina da kuɗi ina da dukiya dukiya dukiya sosai,
Miƙewa tsaye yayi yana tangaɗi ya nuna ya tsansa kamar yana da magana da mutum yace "Wallahi kuɗi gare ni babu wanda ya kaini kuɗi, ku gaya mata yawan kuɗi na, sunfi cikin kofin nan, ya nuna wani kofi dake kan kujera, kuɗina idan na ɗauko su sai sun cika kofinnan taf harma su zuba, kugaya mata ƙarya take bazata ga ƙarshena ba, ni ko mutuwa bazanyi ba, saboda ina da kuɗi ko anzo ance na mutu zan bada kuɗin da zan ta rayuwa a duniya babu wanda ya isa yaga baya na, eh haka na ce haka na ce kowa ma yasani kuɗi na sun kusa ɗari uku da hamsin hhhhhhh ehhh muje muje mujee, wawwara ƙafa yayi kamar ya hau abu yana tura hannu sa wai suje, (ko ina zasu oho) shi kaɗai sai faman hauka yake kala kala daga ƙarshedai bacci ne ya dakatar da wannan haukan, da bamu san iya ina zaije ba dashi ba....
______*RABEE*
Tana zaune a falon ta ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana faman girgiza ta, fuskar ta ɗauke da murmushi, juyawa tayi ta kalli na gefen ta, tace "Saleem Mera, ka daina min wannan maganar babu me ɗaukar su, idan bashi ba, yanzu idan yaga da gaske nake zai fito da su, ya daɗe yana cin galaba akan mu, amma yanzu mu zamuyi nasara sai mun kawo ƙarshen sa,
"Gyara zama yayi shima yana kuma gyara glass ɗin fuskar sa, tare da ɗan sakin murmushi gefen baki, yace "amma kina ganin abubuwan da kike faɗa akansa zasu tabba ne, amma dai kin manta waye Bulama ko, bana tunanin akwai wanda zai kawo ƙarshen sa a duniyar saidai Allahn da ya halicce shi amma badai mutum irin sa ba, ni ina ganin kamar bashi ya ɗauke sun ba, tunda aranar ma da kika ce andauke su, har kika kirani, muna tare, kuma da ya ɗauka dole zai ban labari tunda kin san halin sa ba ya tsoron kowa yake ba, bazai ɓoye ba, zai faɗa miki amma tunda kika ga abun har ya kaiku ga haka to ki yarda dashi Bulama baya ƙarya koda kuwa ran wanda idan yagawa magana zai ɓaci to zai faɗe ta, amma zan iya rantsewa baida masaniya akan wannan lamarin.
Haɗe rai tayi ganin ya goyi bayan Bulama, "Ok yanzu bayan sa zaka goya kenan, bansani ba ko kun haɗa baki, nawa ya baka kuka ɗauke min yarinya?
Miƙewa Saleem Merah yayi yana gyara rigar sa yace "banda loƙacin wannan maganganun naki nidai gaskiya na faɗa miki, ki gaggauta dakatar da abunnan da kike, in kuma ba haka ba kin fini sanin halin sa, idan kuka saka ƙafar wando ɗaya dashi kece a ruwa ba shi ba, dan waɗannan abubuwan da kike masa kina ganin kamar zaiji wani abu to ko yaji na zuwa wani loƙaci ne, idan Bulama yace daga shi sai kayan jikin sa zaibar ƙasar nan batare da ya ɗauki tsinke a ƙasar nan, kuma ace bana sa bane to babu abun da zai ragu a kuɗin Bulama, duk yanda kike tunanin Bulama yafi ƙarfin nan, nidai ina mai ƙara baki shawara a karo na biyu da kiyi gaggawar dakatar da komai sannan ki nemesa ku sasanta tun kar loƙaci ya ƙure miki, na barki lafiya. Yana kaiwa nan ya juya ya fice daga falon.
Da sauri ta shiga ƙwala masa kira cikin ɓacin rai take kiran sa amma ko waiwayowa baiyi ba,
Miƙewa tayi ta bisa tana fita ya shiga mota, dawowa cikin gidan tayi ta shiga zagaye a cikin falon tabbas tassn waye Bulama, amma itama a wannan karon sai tayi fito na fito dashi, dan bazata rabu dashi yana cin galaba akanta ba, dole ta tsaya ta jajirce akansa, koda kuwa kuɗin ta gaba ɗaya zai ƙare to sai inda ƙarfinta ya ƙare....
*LAUTAI*
_____Khalifa ya daɗe yana jiran yarinyar ta dawo amma shiru shiru taƙi ta dawo ga dare da yake kuma yi, tashi yayi kawai ya fara tafiya duk da baisan inda zashi ba, zuciyar sa ce ta basa kawai ya koma gidan me garin, bashi da zaɓin da ya wuce na zuciyar sa, haka ya nufi gidan saidai kasa ganewa yayi saida ya tambaya sannan akayi masa iso ya ƙarasa gidan, da yaje yayi masa bayanin cewa yaje yaga ba wanda yake nema bane, shiyasa ya dawo a taimaka masa da ya kwana gobe sai ya tafi da safe, ba wani kokwanto ko bincike, me gari ya amince masa, aka bashi masauƙi ya kwana, da safe kwa ko karyawa baiyi ba, ana ta cewa ya tsaya akawo masa abinci yace "a'a ya gode sauri yake, haka ya tafi da yunwa, tasha kawai yaje ya hau mota ya tafi koma gida, ko da ya koma gidan da ta ajiye ta, ya koma jiki a sanyaye baiji daɗi ba da bai samu wani information da zai gaya mata ba, wanda zaisa taji daɗi.
Da sallama ya shiga cikin gidan, a zaune ya ganta a falon gidan ta zabga tagumi tana tunanin, dan harda yayi sallamar ma baiji ba, saida ya kuma yi da ɗan ƙarfi sannan ta juyo da sauri ta amsa masa tana sakar masa murmushin yaƙe.
Ji yayi jikin sa ya kuma yin sanyi gaba ɗaya tausayin ta ya kuma rufe shi, yana kallon ta yaji kamar yayi mata kuka, a kasalance ya ƙarasa shiga yana zama a kujerar dake kallon ta,
Tana ganin yanayin sa tasan ba'a dace ba, amma haka ta kuma yin ƙarfin hali dan ita ko a hakama ya barta taji daɗi, dan dama koda ta samo ɗin ai ba lalle a wani ɗau mataki ba akai ba, wataƙilma saidai ta kuma shiga wani halin.
Murmushin ta kuma yi masa, tace "kar ka wani damu kanka yaro, yanayin ka ya tabbatar min da komai, ni a hakanma tunda ka fito dani ai shikenan na godewa Allah, yanzu abun da zaka min kawai shine kayi min yanda zanbar garin na koma wani garin da bazasu san dani ba, ni ko aiki ne ma sai na samu nayi awani gidan bazan ringa fita ko ina ba, kaga zamana anan matsala ne wataran za'a iya bibiyar ka agano inda kake zuwa, yanzu wataƙil ma, suna can suna zargin ka, tunda baka kwana a gidan ba.
Baiji daɗin wannan maganar tata ba, amma duk da haka dole zai barta dan yasan dole za'a gano sa, ko da ga Camerar gidan ce tunda yasan da camera agidan shima kasada yayi kawai ya fito da ita, amma dai duk inda zai kaita ma, sai ya tabbatar da inda take babu matsala, sannan duk sati zai ringa zuwa yana ganin ta, sannan zaici gaba da bincike da kuma komawa wancen garin, dan in sha Allah sai ya taimaka mata gurin gano komai.
Jin yayi shiru yasa ta ɗan yi gyaran murya, tace "kar ka damu dan Allah kayi min wannan alfarmar ka ɗorani a hanya, ni yanzu babu wanda nasani babu inda nasani banda kowa, bansani ba ko ƴaƴana na raye ko sun mutu Allah masani, addu'a ta a kullum Allah ya bayyana min sa a duk inda suke a faɗin duniyar nan, in kuma sun mutu Allah ya jiƙansa ya kai haske ƙabarin su.
"Ameen ya rabbil izzati. In Sha Allah ma suna raye kuma zaku haɗu da yardar sa, zasu dawo gare ki, kema zaki ci gaba da rayuwa kamar kowa, komai yayi farko zaiyi ƙarshe, duk min tsanani akwai Allah, Allah baya bacci kici gaba da kai masa kukanki, zakiga sakamako me kyau wataran.
Kallon sa tayi tana jinjina masa kai tace "tabbas maganar gaskiya ce, nasan Allah baya bacci yana jin kukana, shiyasa har yanzu bai ɗauki raina ba, duk kuwa irin wahalar da suke gana min saidai wuya bata kisa sai loƙacin ka yayi, ko wannan fito da ni ɗin da kayi ma kaɗai ai ya isheni sakamako, tunda na fito yanzu aiki zanyi in samu kuɗi sai inta duba gurare da makarantu, sannan in koma can garin ko Allah zaisa inji labarin su, gurin me saida abincin zan fara zuwa inji daga inda na barsu ina sukayi ko suma mutanen sun ɗauke su wataƙil.
Cike da tausayawa jin abun da tace wai zata nemi kuɗi ta fara duba gurare, duniya da girma ta ina zaka iya fara neman mutum da baka san garin da yake ba, a ranshi yake wannan tunanin, a fili kuma sai yace "ai har gwanda ma dai gurin me abincin wane gari ne, ni sai in kaiki ai basai kin nemi kuɗi ba, ko nawa kike so zan baki,
Girgiza masa kai tayi tace "a'a wallahi baza ayi hakaba wannan ɗinma da kayi min ya isa nagode, zanje na nemo su da kaina indai sunan nan, nidai yanzu ka taimaka tun kan dare yayi inbar garin, shi kaɗaine taimakon da zakayi min, baiji daɗin maganar ta ba, haka yayi yayi da ita akan ta bari saida safe idan ma tafiyar zatayi tace a'a bazata kuma kwana a garin ba sai ta tafi, yace to ai so yake su tafi tare yaga inda zata nan ma taƙi yarda tace ya kaita tasha itadai kawai, sosai ta rikice masa tace bazata kwana ba, saida yaga dai da gaske take dan har ƙwalla ta fara tana gogewa, dan ita haka kawai take jin bata son zaman garin kuma bata so yabita gudun abun da kanje ya dawo, idan aka gano shine dole za'a saka a gaba ya fito, da ita, ita kuma batasan ta kuma komawa hannun su, shiyasa ma ta dage masa sai ta tafi yau tunda de bai samo wani bayani ba, daman ita ta haƙura da wannan abun, tunda duk akanta ta shiga halin da take ciki yanzu ta rasa kowa nata.
Badan yaso ba dole yace zai kaita ɗin, saida yaci abincin da ta dafa, sannan wajen ƙarfe biyar na yamma ya fito da ita daga cikin gidan a ɓoye suka bar unguwar yabi ta wata unguwar, saida suka fara tafiya ma sannan yake tambayar ta motar ina zata hau, tace masa koma motar ina ce yakaita zata hau, tasha ya kaita, inda motacin suke ta faɗan wasu garuruwan da zasu, tana jin an ambaci katsina, tace zata hau ta katsina, nan ta shiga motar ya bata kuɗaɗe masu yawan gaske bayan ya biya mata na motar sannan akwai ƙaramar waya a hannun sa, sai yabata dan baya so su rabu gaba ɗaya, idan ya koma garin akai nasara kuma ya rasa inda take shiyasa ya bata, daman akwai wani data sim aciki da babu wanda yasan shi da shi shima kuma babu wanda yake kira dashi amma dai yana da number, da farko ƙin karɓa tayi saidai taga idan tayi masa haka bata kyauta ba, karɓa tayi tana masa godiya, yana gurin har saida aka cika motar taf aka tayar sannan ya juya ya kuma yi mata sallama hakannan yaji jininshi ya haɗu da ita dande dole ta matsa masa ne yasa zai barta ta tafi, kuma shima yana tsoron kar agano sa, ta kuma shan wata wahalar shiyasa kawai ya haƙura ya barta ta tafi, har ya shiga mota ya tafi yana ta zullimin ta, da tunanin abubuwan da suka faru da waɗanda ta basa labari...
*LADIES STAR⭐*
____Ganin yanda Bulama ya fita yasa duk suka saki baki suna kallo, bayan fitar sa suka kalli yaran nasa da ya tafi ya bari duk sun tsugunna suna faman murza ido, a haka suka tisa ƙyarsu suka korasu waje basu damu da halin da suke ciki ba, suka rufo ƙofar su.
Komawa ciki sukayi cike da mamakin wannan mutumin, Ameela ce tace "wai wannan mutumin bashi ne ya ɗauke Aunty Babba?
Barazana ce tace "shine mana, shige ɗan iska, me zubin kwaratai, da wani bakin sa duk sauran duniya, wai amarya zan baki farin ciki zanyi miki yen yen yen sai wani hauka yake wa mutane, abun haushi wallahi duk ya ɓata min mood ɗina.
Ƴar dariya Beenish tayi tace "ni daman tun ranar da muka fara haɗuwa naga yana miki ɗan iskan kallo ashedai ya yaba zai dawo,
Can zai yanka dan uwarsa ai nafi ƙarfin sa, wallahi ya dawo sai na kusan aikasa lahira.
Babyn tana ta dariya buɗar bakin ta sai tace "Fashion soja ne fa!
Haɗe rai tayi tana watsa mata harara dan tasan so take ta taso da abun da ya wuce, shiyasa taƙi tanka mata sai hararar dai kawai.
Maryam ce ta fito, daga ɗakin su, daman cewa tayi bazata fito ba sai ya tafi, dan tasan halinsa, tasan kuma sai ya dawo, tambayar su tayi ya sukayi dashi, nan Beenish ta bata labari, jinjina kai kawai tayi, aranta tace to canza gida ya kamamu kenan duk da tafiya ma zasuyi gobe amma ita da Babyn baby dole su sauya gida in ba haka ba kuwa Bulama ba imani ne da shi ba, yanzu ya tabbatar tana gidan bazai barta ta kuma kwana ba a duniya.
Gaba ɗayan su suka zauna harda Maryam suna ta hira dan rabon da suyi haka sun jima.....
Washe gari....
Kamar yanda Ammu tace musu haka suka shiga shiryawa duk da sunsha daru da Abu dan da ƙyar ta yarda zata bisu, da niyar kuma ko taje bazatayi abun da za'a ɗauke ta ba, tundade zaɓar mutane za'a yi to zata san yanda zatayi ta faɗi aƙi ɗaukar ta.
Wajen ƙarfe 9 Ammu ta ƙaraso gidan loƙacin duk sun shirya daman tun dare duk sun shirya kayan su, da safe wanka kawai sukayi suka saka kaya.
Bayan sun gama komai sannan suka fito gaba ɗayan su, Babyn baby tunda safe take kukan ta a ɓoye har airport suka rakosu Maryam da Babyn baby a motar drivern Ammu, saida suka zo tafiya sannan dai Babyn ta kasa jurewa saida ta fashe da kuka, amma haka suka rarrashe ta tana ta kukan suka tafi, duk da suma jurewa kawai sukai dan ta kusa tasa su kukan, Beenish kam saida ta goge ƙwalla batare da ta bari kowa ya ganta ba, haka suka shiga jirgi saida jirgin su ya tashi sannan su Maryam suka tafi gida.
jirgin su ya sauka lafiya daga nan kuma suka hau wata motar da Ammu tasa aka kawo musu, babban Barack ɗin sojoji aka kaisu, wanda yayi kusan biyun wanda suka je, sojoji kake gani ta ko ina ga bindugu da suka yawaita agun kamar kamar ba'a so, ga mutane damƙam acan nesa wajen wani babban fili, duk wani wanda za'a yi dashi ya halatta, sai tsakiyar filin gurin, manyan sune masu tantancewa, kowa da kayan gida ajikin sa, ƙarasawa su Beenish sukayi dan loƙacin da suka je har amfara gudanar da program ɗin, basu ji daga farko, amma na kawo su wajen ta juya, batare da sun san komawa zatayi ba.
Layi sukayi kamar assembly haka suke suna suraron bayanan da ake musu, gurin kwa tsit kake ji kamar babu mutane duk yawan mutanen dake gurin amma ko tari bakaji, sai muryar me sanarwa shima cike yake da kayan sojojin,
Suna gurin aka aka kawo wasu takaddu da yawa nan aka shiga raba musu jarrabawa ce, kuma a minti talatin ake so a gama duk wanda ya haura haka bai gama ba tun shin za'a yarda shi, raba musu aka shigayi ɗaya bayan ɗaya masu rabon suna da yawa anan ƙasa akace kowa ya zauna, sojoji na zagaye dasu wasu duk