x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 51 - SU WAYE SU

  • 150001 words
  • 153000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 157

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ɗaga singilet ɗin sa itama ya cireta yana daf da shiga ɗaki ya shiga cire belt ɗin sa ya fara cire wandon ƙasa, yana shiga ɗakin ya ƙarasa cire sa, ya doshi banɗaki, ya daɗe yana wanka kafin ya fito daga banɗakin ɗaure da towel, idon sa ne ya sauka kan gadon sa, a ɗan firgice ya kuma waro idon sa dan ganin sa da kyau, kamar mutum yake gani a kan gadon akwance, matsawa yayi kusa da gadon.

Da ƙarfi yace "what...!!!!

Cike da mamaki yake binta da kallo ganin yanda ta kwanta ɗaiɗai tana sauke numfashi, hannun ta kuma naɗe da farin abu ta miƙar dashi gefe...✍️✍️


_Ba yawa sorry 😔 amma da babu gwanda ba daɗi ko inji masu iya magana._



*Duk meson na saka shi a group ɗin Su waye su yayi min magana, ta wannan number 08124226526 iya littafin su waye su, dan Allah kar wanda ya min magana akan meman wani littafin, ko yace min in saka sa a group ɗin littattafai, to wallahi duk wanda yayi min magana bazanyi reply ba, sbd an saba yi min irin haka Ni ga abun da nace amma sai wasu si ta tambayata in tura musu littattafai dan Allah ku daina bana so ba littattafai nake turawa ba nawa kawai nake turawa*

_Ƴan facebook kuma kuyi searching ɗin su waye su hausa novel group kuyi join akwai a ciki tundaga farko har inda aka tsaya, dan ba kullum zanna posting a kowane group ba_



[4/25, 12:52 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*



(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)


________* 08124226526*_______


*_episode 45💧_*



💧💦محمد لرسول الله...!💦💧


*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*


_Bismillah..✍️_


_____Cike da mamaki yake binta da kallo ganin yanda ta kwanta ɗaiɗai tana sauke numfashi, hannun ta kuma naɗe da farin abu ta miƙar dashi gefe.

Kamar wanda mayan ƙarfe ya zuƙo haka ya ƙarasa gaban gadon yana kuma zaro ido yana kallon ta da kyau, jinjina kai yayi cike da ƙara tabbatar wa kansa ita ɗin ce.

Cikin zafin ya ware tafin hannun sa, ya ɗalla mata duka a gadon baya, a firgice Beenish ta buɗu idon, amma tama kasa tantance me taki kuma daga kuma a ina take, bata gama tunanin me ya faru da ita ba, RK ya damƙo ƙafarta ya shiga jawo ta daga kan gadon, da sauri ta tashi zaune tana ƙoƙarin ƙwacewa amma ya hanata, ɗayan hannun me lafiya ta miƙa tayi sauri ta riƙe zanin gadon nan ya tattare ya biyo hannun ta sai tayi sauri ta riƙo wani guri a jikin fuskar gadon, yana janta amma ta riƙe fuskar gadon ƙam, saida ya kuma tattaro ƙarfin sa, yayi mata wata irin fusga, bata san loƙacin da ta saki jikin gadon, gaba ɗayan ta ta taho zata sillo ƙasa, ganin dai da gaske so yake ya faɗo da ita ƙasa ahaka yasa tayi saurin riƙe towel jikin sa ƙam, hakan yasa shi dole ya dakata da jan da take masa.

Cikin mamaki ya ɗago yana kallon cikin idon ta, itama kallon nasa tayi, kowa kagani fuskarsa kamar tsohon kunun da ya kwana, kowa ya haɗe rai tamau kamar babu wanda ya taɓa yin dariya acikin su kowa zuciyar sa ta farfasa take ji suke kamar su cinye junan su a haka.

Cikin ɓacin batare da ya ɗauke ido daga kallon da sukewa junan su ba, yace "Are You mad? Kina haukan ne, sakar ni!

Itama cikin haɗe ran tace "kafara sakina tukunna in bahaka wallahi kana kuma jan ƙafata zan ja abunnan, tayi maganar tana ɗauke idon ta daga kansa ta mayar dashi kan hannun dake kan towel ɗin.

Da ɗayan hannun sa ya ɗora kan hannun nata zai murɗe amma yanda ta riƙe towel yasa dole ya sake ta dan yasan koya ya motsa mata hannun zata iya kunce masa towel ɗin dan yajisa ma sako sako kamar ya kusan kuncewa, amma taurin kai ya hanasa sakin ta dan bayaso yayi abin da take so.

Wata tsawar ya kuma daka mata yace "ki sake kafin inkashe ki a ɗakin nan kuma wallahi na kashe banza, ke wace irin mahaukaciya ce, uban me ya kawo ki ɗakina, idan ma iskancin kine ya motsa to ki fita waje ki nemi irinki, banza mahaukaciya ƴar iska, ki sake ni nace!

Tunda ya fara wannan maganar ta kafe shi da ido tana aika masa da kallon tsana, ji tayi zuciyar ta kamar ta ɓula waje ta fito, tunda take babu wanda ya taɓa yi mata kalar wannan zagin shiyasa ranta yayi ƙololowar ɓaci.

Itama cikin tsawar da taso ma tafi tashi tace "kai dalla Malam dakata! Kaine babban mahaukacin wanda baisan darajar mata ba, kuma wallahi wallahi idan baka sakeni ba kana kuma wani motsi anan sai naja towel ɗinnan sai kafi jin daɗin kirana da ƴar iskar da kyau, mugu kawai azzalumi ga babban haukanan kanayi, in ba hauka ba mezaisa ka yin wannan daƙiƙancin bakaga halin da nake ciki ba amma dake ba Allah a ranka kake shirin ka jawo Ni ƙasan gurin ba ruwan ka da me zai faru idan na faɗo ɗin, to wallahi ka sani baka isa kayi min duk abun da kaga dama ba, dan ba jakar ka bace ni.

Idon sa har ƙanƙancewa yake saboda tsabar ɓacin rai, bakin sa ya shiga taunewa kamar zai fasa su, hannun sa kuma dunƙule su, har karkarwa suke, ita kanta taji hakan a hannun sa da ya riƙe ƙafar ta, daman a tsorace take jin hakan yasa ta kuma tsorata saidai bata bari ya bayyana ba, saima ƙara wurga masa kallon banza me cike da tsana da take watsa masa, itama kuma tana ƙara riƙe towel ɗin da kyau yanda de tasan bazai kunce ba, dan barazana ce kawai itama bazata so taga ƙato gaban ta hakaba.

Gashin kanta ya damƙa da mugun ƙarfi wanda hakan yasa tayi saurin sakin sa tana dafe kan zata cire hannun nasa, amma ina takasa, take hawaye ya shiga sauko mata, tayi saurin gogewa dan bata so ya gani ya kuma raina ta, a haka ya miƙar da ita tsaye, bata daddara ba ta kuma saurin ɗora hannun ta kan towel ɗin da tasan nan ne kawai mafitar ta, ta daidai inda ya ƙulle ta ɗora, cikin ɗaga murya tace "mugu ka sake ni kaina ciwo yake, kuma wallahi saina ja abunnan, tana faɗa ta shiga alamun kamar zata kunce ɗin, da ƙarfi ya sake ta yana turata baya, yana turata towel ɗin ya fara kunce cikin sauri ya riƙo sa yana maida shi maɗaurin sa, juyawa kawai yayi cikin sauri ya nufi wajen wardrobe ɗin sa, Allah Allah yake ya shirya shi kaɗai yasan me zaiyi mata yau, dan saina lahira yafita jin daɗin, sai ya koya mata hankali ta shiga taitayin ta sai ya sanya mata tsoron sa tunda yaga kamar bata tsoron sa.

Tura tana da yayi yasa Beenish ta faɗa kan karyayyen hannun ta, azaba ta sakata sakin ihu, amma tuna abun da zai mata idan yagama yasa tayi arowa kanta jarumta cikin hanzari ta miƙe tana saukowa daga kan gadon ga hawaye duk yagama wanke mata fuska, ɗayan hannun tasa ta riƙo hannun me karaya, da sauri ta nufi ƙofa tana satar kallon sa, ganin ya juya, yana ɗauko kaya.

Buɗe ƙofar tayi a hankali, ta fito daga ɗakin, bata san loƙackin da ta sauke ajiyar zuciya ba, cikin sauri ta kuma nufar ƙofar falon zata fita tajiyo Muryar sa yana cewa "idan kika sake ki fita daga falon nan sai nayi gunduwa gunduwa da namanki, yana maganar yana dosota.

Da sauri ta buɗe ƙofar tana cewa "ashema na cika mahaukaciyar idan na tsaya, tana faɗar haka ta fita shi kuma yana ƙarasowa tana fita, tsayawa ya saka ya ƙarasa saka rigar da ya riƙo a hannun sa, dan wando kawai ya saka, yaga bata ɗakin hakan yasa ta ɗauko rigar ya biyo ta.

Yana gama saka rigar ya fito waje saidai harta ɓace baigan taba, haushi yaji ya kuma cikashi, sojojin gurin ya shiga balbalewa da masifa yana tambayar su ina tayi kuma waye ya kawota nan part ɗin, cikin sauri ɗaya yace "Sir babu wanda ya fito yanzu, tun ɗazu dai da Moohad ya kawota ta fita bai kuma dawowa ba kawai dai yace mu kula da gurin da kyau idan munji kukan ta ko ta fito tana buƙatar wani abun mu bata kafin ka dawo, ai sojan nan na rufe bakin sa yasakar mar wawan naushi a baki sai kace shi yayi masa laifin, yana naushin sa ya caƙumo wuyan sa yace "how dare you uban wa yace kubar wasu ƴan iska su shigar min part, baka da hankali ne kake min wannan bayanin da bakin ka, yanzu jakar nan ta fito amma kace bakuga kowa ba, ni zaku munafurta ta ina tabi inba tanan ba?

Da sauri sojan ya shiga basa haƙuri yana kakarin amai dan ya shaƙeshi da yawa, sakin sa yayi yana yin kan sauran ragowar biyun dake gurin suma duk saida suka samu rabon su, sannan kamar zarrare ya doshi inda aka sauki su Beenish, yana tafiya yana ayyana irin abun da zaiwa mata da ita da Moohad, dan jin Moohad ne yasa yaji ransa ya kuma ɓaci dan me yasa zai kaita part ɗin shi, meyasa baikaita nasa part ɗina, me yasa yake masa shishshigi a rayuwar sa, zaiyi maganin sa amma, yana tafiya yana zayyana abubuwa a cikin ransa, kana kallon fuskar sa kasan ba lafiya.

Beenish na ganin ya tafi tayi saurin fitowa daga bayan ƙofar ashe tana fitowa taga wasu sojojin sai ta koma da baya tana leƙawa taga yana saka riga sai tayi sauri maƙale abayan jikin labule har yagama ya fita bai san da ita ba,

Tana fitowa wani soja yayi saurin tarar ta yana cewa yanzu Sir RK yazo nemanki, Abdul je ka kirasa gatanan mukuma mu tsare ta kayi sauri kar yayi nisa.

Kuka Beenish ta sakar musu tace "dan Allah kuyi min rai kar ku kirashi na roƙeku wallahi zai iya kashe ni idan ya ganni baida imani kuma ni bani na kawo kaina ba nan gurin hasalima bansan gurin sa bane wallahi da zangayawa wanda ya kawo ni bazan zauna, amma dan Allah ku rufamin asiri kada ku kirashi, ku kira wannan ɗin da mukazo tare yazo ya taimaka min ya fitar dani daga gurin nan in ba haka ba, wannan azzalumin sai yaga ya nakasani zai rabu dani gwanda in bar nan gaba ɗaya.

"Babu inda zaki kina nan damu sai kin zama cikakkiyar soja me dauriya ba me tsoro ba, ki rage wannan tsoron nasa da kike ki barni dashi yanzu zo muje nakaiki part ɗina idan kin warke kya fito.

Juyawa tayi tana kallon Moohad da yana zuwa yaji tana wannan maganar, ƙarasowa yayi tare da kamo hannun ta, yace "muje"

Binsa ta shiga yi batare da ta kuma cewa ko uffan ba, har sun ɗanyi gaba, ya tsaya ya juyo ya kalli sojojin yace "kada wanda ya sanar dashi komai kubar shi a baku gantan ba, ko da wasa kar ku kuskura ku faɗa masa, nagaya muku, duk jinjina kai sukayi suna sara masa, sannan yaja ta suka ci gaba da tafiya, suna tafiya tana zubar da hawaye, sosai take jin zuciyar ta na mata zafi.

Babu wanda yacewa kowa komai har suka ƙarasa part ɗin nasa, wani ɗaki ya kaita sannan yace tayi wanka ta kwanta ta huta, me gyaran karayar zaizo ya kuma dubata, godiya tayi masa sosai, sannan ya fita daga ɗakin har yaje tsakiyar falo ya kuma tsayawa ya dawo yayi nocking ɗin ƙofar sannan ya tura kai ya shiga, tana inda ya barta bakin gado bata zauna ba, jin ya shigo yasa ta juyo ta ɗan kalle sa.

"Kisakawa ƙofar nan muƙulli dan nasan yana zuwa can idan bai ganki ba zai iya zuwa nan, jinjina masa kai kawai tayi, sannan ya fita, yana fita kuwa yazo tasaka muƙullin kamar yanda yace mata dan dama anan ɗinma a tsorace take, amma tunda ta rufe ta ɗanji dama dama.

Moohad na fitowa ya shiga wani ɗaki dake jikin inda take, shiga yayi daga nan yayi wanka, sannan ya fito, yana fitowa ta shiga shiryawa bai gama shirin ba yaji an banko masa ƙofar falo ci gaba yayi da shiryawar sa dan yasan ko waye, yana gama shiryawa shi kuma ya turo ƙofar ɗakin, Moohad bai juya ya kalle sa ba, saida ya gama abun da yake sannan ya juyo yana kallon sa kamar yanda shima yake kallon sa.

Takowa ya shiga yi zuwa gaban Moohad rai a murtuke yace "f**ck you Mooha, tana ina? Ina ka kaita yanzu kuma? Why zakana min shishshigi, me yasa zaka kai min wancen abun part ɗina, me yasa eh?

"Shima Moohad ɗin haɗe ran yayi yace "ni bansan akan wane abuba kake magana.

"Moohad! Kar ka bari ka kaini ƙarshe zanyi ƙasa ƙasa dakai anan gurin wallahi ina ɗaga maka ƙafa ne saboda da darajar Ammi da kake ci, amma badan haka ba, kasan baka isa kamin abubuwan da kake min ba.

Murmushin taƙaici Moohad yayi yana kallon sa still, "daga tambaya kace min wancen abun ni kuma nasan bankai wani things ɗin part ɗin ka ba, ko nima zaka karyanin ne? Kabi duniya a hankali, ka ɗagawa yarinyar nan ƙafa.

"Moohad kawai kagaya min inda take kasan me tayi minne, kuma me yasa zaka kaita har cikin ɗakina kuma kan gado na, what kind of this nonsense, me yasa zaka kaimin waccen jakar ɗakina, kasan da ka kaita kasan irin munanan zagin da ta ringa yimin kuma yanzu shine zaka ɗauke ta.

Sauke ajiyar zuciya Moohad yayi cikin sauko da muryar sa tayi low ya dafa kafaɗar sa yace "RK bana son irin waɗannan abubuwan su ringa shiga tsakanin mu, kodan saboda Ammin da kace, ni ya kamata nayiwa wannan tambayar tunda ni already na riga da na kaita can kuma loƙacin naga bata cikin hayyacin ta ne ga karaya a hannun ta duk naga me ya haɗaku tundaga farko har ƙarshe, loƙacin da nakaita part ɗinka saboda yafi kusa ina tsoron kar ta rasa ranta shiyasa na kaita can na kira akazo aka ɗorata, kuma a ɗakin ma barta daman yanzu nake shirin in shirya inje in gano yanda jikin nata yake, sai gashi kuma kai kazo min da wata irin magana ya akai ta fita daga ɗakin ba tare da sanin ka, Allah yasa dai ba guduwa gida tayi ba.

Tunda ya fara maganar kallon sa kawai yake kamar me shirin gano wani abu akan fuskar sa, saida ya dire maganar tasa ba tare kuma da ya ce masa komai ba kawai ya juya ya fita jin yace Allah yasa ba guduwa gida tayi ba, cikin sauri yake tafiya, har yazo wajen wasu sojoji nan ya ce musu a cikin yaran da aka kawo, akwai wata da ta gudu dan haka su bincika cikin gurin da waje da duk inda suka san mutun zai iya ɓuya suje su lalubo masa ita yanzu nan.

Nan ya tashi hankalin mutane da yawa akan sai an nemo masa ita duk inda ta shiga, sannan daga nan ya sa akaje aka kirawo masa Ameela da Fashion, suma tsatstsare su yayi sai sun faɗi inda take, duk rantsuwa suka shiga yi masa basu san inda take ba, suma neman ta suke, amma bai yarda dasu ba, yace ya basu nan da awa ɗaya suke su fito da ita a inda suka ɓoye ta, haka suka fito kowa hankalin sa a tashe suna tunanin ina ta shiga kuma ta ina zasu fara neman ta...?



$$$$$$$$$$$$$$$$$$



_______BULAMA_


Bai farka ba sai wajen huɗu na rana yana farkawa ya gansa kwance aƙasan falon tashi yayi cike da taƙaicin kwanciyar tasa anan, take kuma abun duk da ya faru dashi ya shiga dawo masa cikin kwanyar sa, tashi yayi yaje ya ɗauki wayar sa yaga bazata kuma amfani ba, hakan yasa ya cire sim ɗin sa, ya jefar da ita agun maimakon yafara yin wanka amma a haka ya fito daga gidan jikin shi duk warin giya, gidan da ta ajiye Aunty Babba ya nufa, yana zuwa parking kawai yayi ya fito, ma'aikatan sa duk namasa sannu da zuwa amma babu wanda ya kula cikin gidan kawai ya dosa, saida yaje zai buɗe ya tuna muƙullin na mota tunanin me yasa ya rufe ƙofar ma oho masa, wani yasa yaje ya ɗauko masa muƙallin, yana kawo masa ya buɗe ya shiga, yana shiga Aunty Babba kwance tana ta muƙursusu tana yarfa hannun ɗaya ɗayan kuma ta riƙe cikin ta, da sauri ya ƙarasa gurin ta shi yama manta da ita wallahi ashe fa ya ƙulle ta a gidan.

"Kash sannu me ya same ki? Me yake damun ki.

Sai yanzu ta ɗago da jajayen idon ta ta kalle sa, yana tsugunnawa a gabanta ta rungume sa tana kuma fashewa da kuka.

Ya
End Ads