x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 26 - SU WAYE SU

  • 75001 words
  • 78000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 169

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads


Saida ya kaita wani ɗaki sannan ya shiga banɗaki ya haɗa mata ruwa yace tazo ta shiga tayi wanka, kamar wacce ake controling ta kasa magana kuma duk abun da yace mata yi take, saboda duk abun da take buƙata yake cewa tayi,

Tana shiga ya fita bai daɗe ba ya dawo ɗakin da wata riga da hijabi a hannun sa, harda bra da pant ko a ina ya samu su oho, fita ya kumayi,

Bayan fitar ta ta fito, tana fitowa taci karo da kayan tasaka kuwa abun ta, akan capet ɗin ɗakin ta tayar da sallah ta fara jero waɗanda tasan batayi ba.

Tana cikin sallar ya shigo da leda a hannun sa, ajiye mata yayi a gefe ya jira har ta idar sannan ya buɗe mata take away ɗin da ya siyo mata abunci, fried rice ce sai ɗan soyayyen nama da kuma soyayyen dankali a gefe,

hijab ɗin ta cire ta hau ci saida taci ta ƙoshi ta kora da lemo da ruwan duk da ya siyo mata,

Saida ya tabbatar da ta gama sannan ya zauna a gaban ta, ya kuma gaida ita, ta amsa masa kuwa sai yanzu yaji maganar ta,

"Nasan baki sanni ba nima kuma bansan ki ba saidai kuma wacce take miki wannan abun ƙanwar mahaifiya tace kamar ɗa nake agun ta, tun bankai haka ba nake wajen ta, to ɗazu ɗazunnan nayi mugun gani ko ince ji a wayar ta duk da daman wasu loƙatan nakan zargin ta da rashin gaskiya saidai bansan me take aikatawa ba sai yau, nazo zan shiga falo ɗazu naji wasu zantukan ta...nan ya kwashe duk abun da ya gani da kuma ji yagaya mata komai da komai.....

Jinjina kai matar tayi dan batayi mamaki ba saboda tasan komai tasan halin su...

Ci gaba yayi da cewa dan Allah yanzu ina so inji me yake faruwa wace ce ke me take aikatawa, me su ke so ki basu dan Allah duk ki gaya min dole sai naji wani abu kafin inyi ƙoƙarin taimakon ki saboda ni yanzu nasan wasu abubuwan kuma ina da nombobin wasu jndai akai bincike za'a agano komai cikin sauƙi tunda ina sa shaida.....

"Hmmm to yaro nima dai bansan komai ba amma nasan wani abun kamar yanda aka ban labari.....

*Waiwaye adon tafiya inji masu iya magana kin*

___Kwance take akan gado tayi rigingine tana kallon sama, yayin da hannunwan ta kuma ke dafe da tsohon cikin dake jikin ta, Kafin daga bisani tayi saurin saukowa daga kan gadon da take, Sakamakon wani matsanan cin ciwon ciki da taji tare da ɗaurewar mara, ƴar ƙaramar ƙara tasaki tana durƙushewa agun tare da fashewa da wani irin kuka na fitar hayyaci, Cikin fitar hayyaci ta fara kiran, "Rabi...Rabi..Rabi...!!!,

Shiru shiru bataji ta amsa ba, hakan yasa tayi shiru ta ci gaba da murƙusu sun ta aƙasa tana juyi, takai wajen 15 minutes agun babu wanda ya shigo ɗakin,
Jin ciwon ya ɗan lafa mata ne yasa ta tashi da ƙyar tana layi, wayar ta ta ɗauka da mayafin ta da jaka ko yafa mayafin batayi ba ta kwashe su duka ta riƙe a hannu ɗaya, a haka tafara takawa ta nufi hanyar fita,tana ɗan ɗingisawa hannu ɗaya wanda ta riƙe kaya da shi yasa ta dafo cikin ta ɗayan hannun kuma tana dafa jikin bango.

Tana gama saukowa ƙasa ga mamakin ta sai taga babu kowa a falon, har kitchen ta leƙa taga babu kowa, tana ta mamakin ina Rabi ta shiga, juyawa tayi da niyar ta koma sai tajiyo kamar magana ta wajen window, da sauri ta ƙarasa gurin window ɗin tare da yaye labulen, saura kaɗan zuciyar ta ta bugu agun, mijin ta da yayi tafiya baya gari, amma kuma tagansa tare da Rabin da take kira, sai kuma wasu mutum biyar da bata san ko SU WAYE SU ba. Muryar Rabi ta jiyo tana dariya tace kar ka damu nasa mata maganin bacci bazata taɓa tasowa ba shiyasa nace maka ko acikin falon zamu iya zama, tashi sukayi gaba ɗayan su, suka nufo cikin falon, saurin sakin labulen tayi, duk da halin da take ciki haka ta daure tayi saurin komawa wani wajen ta ɓuya, tana ɓuya suka shigo, maganganu da suka farayi ne yasa cikin tashin hankali hannun ta har yana karkarwa ta danna recording a wayar ta, kaf maganganun da sukayi ta gama kwashe su acikin wayar ta, Rabi ce ta hau sama tace bari ina zuwa, bayan hawan ta, sai kuma tayi saurin saukowa tace, mamaki da tsoro ɗauke a fuskar ta tace "Bata saman fa na duba ko ina banganta,dukan su miƙewa sukayi sai suka haura saman.

Tana ganin sun tafi tayi saurin fitowa daga maɓoyar ta, ta fice daga gidan, gudu gudu tafara yi ga cikin ta kuma da yaƙara murɗa mata ta zube awajen, me gadi ya hangota ya taho da gudun sa yana tambayar ta, cikin tashin hankali ta shiga labarta masa abun dake faruwa tare da basa wayar da jakar hannun ta, tace yayi saurin barin gidan gaba ɗaya, yaje ya saurari komai, zai fahimta...

Shima gaba ɗaya hankalin sa ya tashi, yana ta tambayar ta ko su waye su amma bata gaya masa ba tace su tafi kawai kar su fito su tadda su agun zasu kashe ta, yaso yashiga amma ba dama dole ya haƙu da ƙyar da taimakon sa ta miƙe ta cigaba da tafiya suka fito daga gidan,

Suna fitowa daga saman windown gidan sukajiyo muryar wani yana cewa gata can, ɗaga kai tayi tagansu, sai tacewa me gadin ya gudu ita kuma zata tafi asibiti, Nan suka raba hanya da me gadin, a bayanda zaiyi ya tafi yabarta, itama wata hanayar ta nufa ga tsohon ciki, da zata iya haihuwa yanzu ko anjima, saidai bataje ko ina ba, suka fito a motocin su, juyowar da zatayi tagan sa daf da ita, ido huɗu sukayi da mijin ta, kafin tayi wani yunƙurin barin wajen yayi sama da ita ƙara kawai tasaki daga nan bata ƙara shurawa ba, me gadin na laɓe daman beyi nisa ba yana ganin sun tafi yayi saurin fitowa daga gurin, cikin kuka yafara jijjigata yana cewa SU WAYE SU..!????✍️✍️✍️

*Sai kuma Monday idan Allah ya kaimu gobe zanyi bacci harda munshari😅😅😅*

More comments more typing 🤗

Please share, likes, vote and comment 🥰
[3/5, 12:01 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*

💧💪Jajirtattu writers association 💪💧

______________________________


*_episode 25💧_*


💧💦محمد لرسول الله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

"Rasa inda zai saka ransa yayi gashi gurin duk ba motocin da suke wucewa, gashi tayi masa nauyi amma da haka ya daure ya arowa kan sa jarum ta, ya ɗuke ta da ƙyar, ya nufi titi da ita sauƙin ta basu da nisa da bakin titin.

Yana ƙarasawa ya tari wata napep da sauri yasaka ta a ciki saida suka fara tafiya ma ya faɗa masa inda zai kaisu a bakin wani asibiti ya sauke su tare da taimakon me napep ɗin suka fito da ita a haka suka shiga cikin asibitin, suna shiga kuwa likitoci suka yi saurin tarar su aka shiga da ita ciki....

Ya kasa tsaye yakasa zaune, sai zarya yake a bakin ɗakin da aka ajiye ta addu'a yake tayi Allah yasa kar ta mutu.

Sosai likitoci suka duƙufa akan ta suna bata taimakon gaggawa amma ina har yanzu babu alamun zata farfaɗo, yanke shawara sukayi kawai suyi mata operation su ciro ɗan dan sunji alamun da ransa.

Babu ɓata loƙaci cikin gaggawa suka shirya komai aka fito da ita aka nufi ɗakin CS ɗin, nan aka nemi saka hannun sa ba wani ɓata loƙaci ya karɓa yayi signing yana ci gaba da addu'a sukuma aka fara gudanar da aikin.

Sun ɗau loƙaci kafin suka samu suka ciro ɗan, ana ɗauko ta yarinya ta callara kuka, nan suka fahimci macece yarinyar, duk yanda suka so suka matar ta farfaɗo bata farfaɗo kuma abun da yasa basu barta ba, saboda bugun zuciyar ta na bugawa shiyasa suka san bata mutu ba,

Shirya Babyn akayi tsafa aka saka mata kaya, sannan aka fito dasu daga ɗakin CS ɗin loƙacin da suka fito baya nan yaje masallacin cikin asibitin..

Sai bata kulawa ake anan har yanzu shiru, wani likitan zuciya suka kira azo a gwada yi mata aiki ko za'a gano inda matsalar take, saidai kuma yana zuwa da ya bincika ta bugun zuciyar ya tsaya har ana shirin rufeta za'a sanar dashi ta rasu sai kawai aka ga, hannun ta ya ɗan motsa, hakan yasa sukayi saurin dakatawa suka ƙara haɗuwa akanta, bugun zuciyar ya kuma dubawa sai yaji yaci gaba da bugawa, tun yanayi a hankali har yadawo yi sa sauri da sauri, duk hamdallah sukayi suna sauke ajiyar zuciya dan sunji daɗi.....

Duba tasu ka ci gaba dayi kafin suka samu numfashin ya fara dawowa sosai sukayi farin ciki da haka, ganin zata farka yasa su kuma yi mata allurar bacci sannan suka daidai ta mata oxging ɗin dak kan hancin ta yanda zai ci gaba da taimaka mata wajen shaƙar numfashin.

Fita sukayi sannan suka sanar da mutumin da ya kawo ta zuwa loƙacin ya dawo, sosai yayi farin ciki da jin anfito da baby lafiya itama kuma ta farfaɗo bata mutu ba, har sujjadar farin ciki yayi sannan ya shiga ciki, ɗaukar yarinyar yayi da suka ajiye ta a gefen gadon.....

Bacci kawai take yarinyar tasaka hannu a baki, ƙura mata ido yayi tana ta kallon ta jin son yarinyar yayi yana ta shiga zuciyar sa, ta hannun sa ko babban motsi bayayi saboda kar ta tashi, da ƙyar ya iya ajiye ta sannan ya fita daga ɗakin zuwa yayi akayi masa lissafin duk kuɗin da zai bada miƙa musu ATM yayi suka ciri adadin kuɗin su sannan ya karɓa ya koma ɗakin yana zuwa kuma ya sake ɗauke yarinyar ya riƙe ta yaci gaba da kallon ta......

Ba ita ta farfaɗo ba sai can cikin dare wajen ƙarfe biyu sannan ta farfaɗo tana farfaɗowa kuwa idon ta ya sauka akan su shida yarinyar da suke kan kujera yana bacci a zaune, sai yarinyar a hannun sa a haka bacci ya ɗauke sa shida yarinyar..

Lumshe ido tayi sai kawai hawaye ya shiga fitowa daga cikin idon ta tunawa da abun da akayi mata da kuma wanda yayi mata, kuka ta farayi sosai duk da bata bari ya fito sosai ba, amma da haka saida yaji kukan kamar a mafarki haka yayi saurin buɗe idon sa cikin sauri ya miƙe tsaye ya ƙarasa daf da ita ya shiga bata haƙuri yana danna wannan abun da idan andanna sa likitoci suke zuwa zaiyi ƙara acan wajen su, (na manta sunan sa)

A cikin mintinan da basu fi biyu ba zuwa uku sai ga wani likitan ya shigo cikin gaggawa yana zuwa ga shiga tambayar ta farfaɗo, Eh yace mata yana kuma cewa ta duba ta.

Dubata likitan ya kumayi amma sai yace lafiya ƙalau babu wata matsalar amma ta rage samuwar dake ranta ta daina wanann kukan zai iya taɓata...

Godiya yayi masa, ya fita daga ciki, shi kuma mutumin yaci gaba da yi mata sannu yana bata haƙuri, cikin kuka tace "Me yasa zasuyi haka me yayi musu da suke son ganin bayan sa, dan Allah kar ka bari a kashe shi kaje kayi saving ɗin life ɗin sa, sannan ka tafi da yarinyar ka riƙeta a gun ka na baka ita kasaka mata duk sunan sa kake so, sannan kar ka taɓa sanar da kowa yarinyar nan na raye daga ciki kuwa har ƴan uwa na, ka sanar dasu abun da na haifa ya rasu, idan ta girma taje gurin su ta neme su da kanta, domin zama cikin su a yanzu itama rayuwar tana cikin hatsari muddun suka san tana raye itama baza su bar ta da ranta ba da hali ma kabar ƙasar saboda kaima baza su barka ba mugaye ne basu da imani a zuƙatan su munafukai ne gaba ɗayan su...

Sannan ga kuɗaɗe nan kayi duk abun da kaga ya dace da su, kaje ofishin ƴan sanda ka shigar da ƙara sannan ka basu wannan recording shi kaɗai ne zaisa a kamasu shikaɗai ne hujja, idan kayi haka kayi tafiyar ka in yaso su zasu iya ci gaba da binciken amma dai komai yabar hannun ka baza su ƙara bibiyar ka b.......

Tari ya taso mata babu ƙaƙƙautawa ta dafe bakin ta ita kaɗai tasan halin da take ciki saboda zuciyar ta wani irin zafi take mata,

Tana tarin tace "ka kula min da yarinya sosai na baka amanar ta, sunan kaka ta, ka bata ilimi, kamin alƙawari matuƙar kana raye zaka kula da ita kamar yanda zaka haifi ƴar cikin ka....

Da sauri yace na miki alƙawari, amma dan Allah ki gaya min su waye su in sha Allah sai na ɗaukar miki fansa akan duk wanda ke da sa hannu sai inda ƙarfina ya ƙare kuma bazan kai ofishin ƴan sanda ba domin duk munafukai ne ana basu kuɗi zasu rufe komai ko su maida laifin ma kaina, nayi aiki a wajen su naga yanda suke gudanar da aikin su cikin cin hanci basa yin adalci akan duk wani case da akazo musu dashi, idan baka da kuɗi ma wani loƙacin korar ka suke, dan haka ki faɗa min kawai ni zanyi maganin su nayi miki wannan alƙawarin....

Tarin ya ɗan lafa mata kaɗan amma tana jin ƙaikayin sa a ƙasan maƙogaron ta, cike da dauriya tace; "Nima ban san su waye su ba, idan ka cire Rabi da Haisam sauran bansan su, amma dai duk ƙungiyar su ɗaya kuma kamar akwai wasu da basu halacci gurin ba naji suna maganar su tare da komai dai yana ciki ka saurara da kyau naji suna ta ambatar RED GANGSTER bansan me hakan ke nufi ba.... Shiru tayi tana ƙara jinjina girman abun abun da bata taɓa kawowa aran ba mafi kusan ci da ita wai su suka yaudare ta suka ci amanar ta, daman duk soyayyar da suke nuna mata ta ƙarya ce.....

Kuka ta kuma fashewa da shi tana cewa "me yasa? Rabi mai yasa me na tsare miki da kike son ganin bayana da na ɗan dake ciki na tunkan yazo duniya ma wane irin laifi na aikata miki, wanda na ɗauki son duniya ma na ɗorawa ya cuce ni da shi za'ahaɗa baki aga baya na, saboda son zuciya irin nasu, kuɗi kuɗi kuɗi me acikin dukiya idan banda bala'i dukiyar ma da ka haɗata da gumin ka wata masifa take zamar maka bare kuma wacce zaka gina ta da haramun kaciyar da kanka da haram ka gina ƴaƴan ka da haram bayan ka zalun ci mutum wannan wace irin rayuwa ce shin mutane basa mantawa da zasu mutu ne ko tunanin su mutuwa bazata zo kansu ba, wannan rayuwa rashin gaskiya da son kai yayi yawa acikin ta ga maci amana ace makusan cin ka dashi za'a haɗa kai a cuce ka aga bayan ka duk dan saboda son zuciya da ba Allah a zuƙatan su......kuka take sosai tana wannan furucin wani irin baƙin ciki na kuma taso mata ji take ma gwanda tabar duniyar ma ta huta gaba ɗaya dan ta tsana aci amanar ta babu abun da ta tsana fiye da munafurci akan muna furci tasha rabuwa da mutane da yawa kuma ko waye kai duk yanda kuke da ita idan kayi mata zata iya raba hanya dakai...

Haƙuri kawai yake bata yana cewa tayi shiru saboda yanayin da take ciki kana ji kasan maganar take cike da ɓacin rai da ƙunar zuciya...

Sun daɗe suna hira tana ƙara faɗa masa wasu abubuwan anan da duk wani abu da tasan zai buƙata, sannan kuma koda wasa tace koda ta mutu kada ya sake ya yaje gurin dangin ta bare ya basu ƴarta...

Kiran sallar asuba ne ya katse musu hirar su, tashi yayi yace bari yaje yayi sallah, jinjina masa kai tayi kawai tana ƙara lumshe idon ta dan bacci bacci taji yana shirin ɗiban ta, yarinyar nakan ƙirjin ta ta rungumo ta da hannu ɗaya suna saurarar bugun zuciyoyin su, a haka bacci yayi gaba ita......

Bayan ta idar da salla ya haura upstairs ɗin dake cikin asibitin inda ake saida magunguna nan ya nufa zai siyo mata magungunan da kuma madara da akace abawa yarinyar tunda uwar bata cikin hayyacin ta kafin zuwa ta dawo daidai...

Yana gama siya yabiya kuɗaɗen sannan ya juyo saidai juyawar da zaiyi ya hango wata mota daga nesa tana nufo asibitin, kallo ɗaya kuma ya fahimci wace motar ce.

A mugun guje ya ya sauko daga saman dan kayan ma sakin su yayi agun,yana saukowa ya nufi hanyar ɗakin da aka kwantar da ita yana shiga yaga tana bacci ƙarasawa yayi ya zare yarinyar a hankali sannan ya kuma fita da ita daga ɗakin wani ɗakin ya shiga inda ya samu wata mata ta haihu shi da niyar ya basu ajiyar ƴar yayi amma da yayi musu bayani ma cikin ɗan ƙanƙanan loƙaci yanda dai zasu fahimci abun da yake nufi, sai kawai suka tausaya masa tare da sanar dashi cewar ai suma yarinyar da suka haida ta rasu ma, nan wata mata me karsashi
End Ads