Basu dai na hirar ba har saida suka ga sunzo gida me gadi ya wangale musu ƙaton gate ɗin sun shiga.
Gidan fal yake da ma'aikata kamar yanda aka saba a koda yaushe saidai na yau sun ɗan banbanta saboda gyararraki da akeyi, ga yawan sojojin da suka ƙaru a cikin gida ko ina cike yake da matakan tsaro ciki da waje....,
Ko da suka shiga cikin falon ma nan ma aiki akeyi ƴar fitar da sukayi har ancanza kujerun falon ga masu decoration na ta aiki saka flowers da prime ajikin bango, ko ina dai aiki akeyi babu inda ba a gyarawa, sakamakon aikin da akeyi yasa suka rabu shi Aveed ya nufi part ɗin sa ita kuma ta nufi wani ɗaki tana cewa Washh nagaji wallahi Mom ki fito ki goya ni, tayi maganar daidai loƙacin da take tura ƙofar wani ɗaki.....
Tana shiga taga wayam babu kowa a ciki maimakon ta fito sai kawai ta ƙarasa shiga ciki ta faɗa kan makeken gadon tana warwara hannu sai kace wacce tayi wani aikin ko tayi tafiyar ƙasa......
*COMMISSIONANA*
A ranar dai ba samu daddaɗan labari ba daga mai magana ɗaya ko da ya kira sa sai ce masa yayi ai wata tafiya ce ta kama sa ta gaggawa amma ya bada ayi masa binciken su gobe yana dira akan su zai fara aiki....,
Da har zai fara yi masa masifa ma, sai mai magana ɗaya yace ƴallaɓai harma na fara aikin yau kawai kasan bana magana biyu ɗaya nake, a iya jiya da na fara har na samu labarin su kuma nasan inda suke kuma ankawo min cewar sun haɗu da ƴar gidan tsohon governor harma ta gayyace su shagalin gidan su na dawowar yayan ta da zasu gudanar da yamma dan haka zaisan yanda zai tada husuma a ɗauke su agurin taron..,
Yaji daɗin jin labarin, anan shima yake sanar dashi ai harda su a manyan baƙi kuma suna tasu tawagar zasu je gurin dan haka ko a motar ƴan sanda ne za'a iya ɗauke su ai babu wanda zaiyi zargin wani abun, sune masu bada kariya dan haka suna da hanyoyi da yawa da zasu tada husuma batare da ansan su bane..... Nan sukai ta shirya yanda zasuyi da yanda zasu tsara komai ya gudana ba tare da ansamu matsala ba.
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
*HAJJA MAMA*
Me mashin ɗin da ya ɗauke ta yana kawo ta wani waje ya tsaya ta sauka, yana sauke ta kuma ya juya, ya koma bakin ruwa ta ƙarasa, tana zuwa ta shiga cikin jirgin ruwa suma bakin wata hanya suka sauke ta daga nan ta tsallaka wata hanya saiga wata jeep nan ƙatuwa ta shawo kwana a gaban ta ta tsaya suna tsayawa ta shiga cikin sauri,
"Saifa kunyi sauri so nake mu shiga garin gobe da safe da wuri yanda zamu tsara komai kunsan zasu sa matakan tsaro sosai to so nake kafin su ankare muyi mu shige....,
Yanda tace kuwa haka sukeyi gudu kawai sauke shararawa tun sunayi akan hanyar ƙasa har suka hau titi, suna hawa titi tace ku tsaya, tsaya wa me tuƙin yayi daman su biyu ne a gaban motar, batare da ta fita daga motar ba, ta cire rigar jikin ta da komai sannan tace bani guri.....
Yasan me take nufi dan haka ya buɗe motar ya fita ita kuma ta tsallako gaban motar yana fita ya rufe sannan yayi saurin zagayowa ya koma inda take ko rufewa bai gama yi ba, ta figi motar a guje, gudu take sosai kamar zasu tashi sama......
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
*WASHE GARI....*
A cikin garin kafa babu inda labari baizagaya dawowar sa ba, hatta wasu ƙananun masana'antun rufe su akayi saboda gudan tada husuma, titina kam ba ko ina ake biba, tunda akace ƙarfe ɗaya na rana jirgin su zai sauka, tun kan loƙacin aka gama shirya komai cikin gidan su kam kamar biki fal yake da al'umma da ƴan uwa da manyan baƙi da aka gayya ta jiran sa kawai ake jira....
Jirgin su bai sauka ba sai daf da sallar la'asar, shi kansa airport ɗin cike yake da mutane, masu tsaro sai ƙara bawa gurin tsaro ake ga sojoji ta ko ina da bindugu a hannayen su(tab any mistake gam over yaseen hhhh)
Cikin shigar sa ta kakin sojoji ya zuro ƙafar sa da taci uban wani takalmin me tudu shima kalar kayan sojoji, kana ganin sa kasan Allah yayi halitta agun, dan a tsaye yake ƙira iya ƙira, sai babu inda ake iya gani ajikin sa, dan kansa ya saka p cap da aka rubuta RK da ƙaton tambarin fuskar sa cikin facemask ga glass da yasaka ya kuma rufe idon sa, babu me cewa yaga wani abu nasa saidai idan kasan shi daman zaka ce shine, hatta hannun sa safar hannu yasaka, sai wata zarmaƙeƙiyar bindiga da ya saƙala ta a gefen sa,
Yana saukowa aka shiga buɗa masa hanya ana ɗaga masa hannu, wajen wani mutum ya nufa shima da kakin sojoji yana zuwa ya ƙame yayi salute ɗin sa, ai yawancin gurin aka hau tafi dan kalar ƙamewar da yayi saida ta basu dariya kuma ta burge su dan wasu har ɗan kwaikwaya suke a gefe.....
Ɗan bubbuga kafaɗar sa yayi shima ya sara masa sannan suka ɗanyi hugging ɗin juna, kafin daga bisani ya basa waje ya wuce yana mara masa baya tare da wasu sojojin gefe da gefan sa da bayan sa duk sojoji ne banda na gaba masu share masa hanya motar da aka zo da ita domin shi suka nufa daman already an buɗe masa yana zuwa ya shiga kawai yayi akayi sauri aka rufe sa, daga nan aka tayar da motoci jiniya kawai kake ji ta ko ina wasu motocin agaba wacce yake ciki a tsakiya sai wasu a bayan su, haka suka jero reras suna tafiya a shimfiɗeɗen titi da aka dakatar da kowa sai ya wuce.
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
*Gidan tsohon governor*
A farfajiyar gidan akayi decoration ɗin komai hatta gurin da zai zauna duk an ware masa ga gurin manyan baƙi maza da mata gurin dai yayi kyau an ƙawata sa sosai cike da tsari, kujerun mata daban a gefe mazama haka duk da wani mugun gayyata akayi ba dan ba kowa ake bari bama ya shigo sai ka kai wani matsayi a cikin gari dan ko ƴan uwa ma ba kowa akabari ya halicci taron ba saida akayi selecting.
Su Beenish ma sun hallara amma da taimakon Faheema dan sai itace ta fito ta shiga dasu, wajen ƙarfe huɗu da rabi suka iso Faheema sai nan da nan take yi dasu, ta rasa inda zata tsoma ranta shi kam Aveed dake cikin mata suka shiga shima yana can wajen abokan sa bai samu damar ganin su ba,
Can na hango Commisiona a a layin manyan baƙi masu muƙami, duk inda su Beenish sukayi idon sa akan su ya kasa ya tsare, komai a tsare yake dan sun gama tsara komai, magana ɗaya ma yana wajen ya shigo a tawagar ƴan sanda sanye da kayan ƴan sanda ajikin sa, sauran yaran sa kuma suna waje suna jiran kira....
*Hajja Mama*
"Hajja Mama nifa ina tunanin ta yanda zamu shiga gidan nan kinga fa yanda sojoji suka zagaye ko ina mutumin dake gefen ta acikin baƙat motar su yake faɗa mata yana kallon ta cike da ƴar damuwa akan fuskar sa,
Wata ƴar ƙaramar dariya tayi tace abun me sauƙi ne ai kaide ka jira kaga me zai faru sun riga da sun tsara duk yanda zamu shiga sai sun fara shiga zamu shiga mun gama komai ƙarasowar sa kawai muke jir............
Bata kai ƙarshen zancen taba, suka jiyo ƙarar jinyar motocin su alamun sun ƙaraso kenan......
Wani murmushin ta kuma saki me ƙayatar wa har haƙoran ta na bayyana a waje...
A hankali ta furta "You are welcome" tana bin motacin da kallo ta cikin glass.
A yanda suke motocin haka suka fara shiga cikin gidan a layi amma ba duka suka shiga ba saboda gurin, na baya duk sai suka tsaya basu kai ga shiga cikin gate ɗin ba.
Baba ɗaga gurin shiru ya ɗauka kowa ya maida idon kan motocin,
"Ameela!!
Beenish ta kira sunan ta, a hankali,
Matsawa tayi kusa da ita cikin raɗa raɗa tace kun shigo mana da kayan dai ko, daman nasan hakan zata faru, baku lura da kallon da commissionanan yake mana ba tun ɗazu, duk ɗagowar da zanyi sai mun haɗa ido, yanzu kuma da na kalli wajen naga baya gurin, yanzu kuma kinga da suka shigo ya dawo wajejan mu naga suna ta magana da ido da wani shegen ɗan sanda, kawai jikina yaban akwai abun da suke shiryawa, bana tunanin za'agama taron nan lafiya duk da naga akwai tsaro awajen sosai.
"Ashe bani kaɗai na fahimci hakan ba, gaskiya da abun da commissionanan yake shiryawa zamuyi maganin sa, daman nasan bazai bar mu haka tunda muka ƙi basa haɗin kai, nasan dai iya kaci yace zai mana sharri ko ya wulaƙan tamu a gaban mutane, cewar Aunty Babba.....,
"Wallahi yayi yunƙurin tada husuma agunnan saida a ɗau rayuka anan gurin dan nasan waɗannan bundugun da suka riƙe tsaf zasu fasa kwanyar mutum, kuma wallahi sai inda ƙarfin mu ya ƙare dan bazamu ɗauki duk abun da zai yi mana ba sai mun casa shi a gaban mutane saidai duk a harbe mu ko kuma a rabamu da ranmu.....✍️✍️✍️✍️✍️✍️
More comments more typing🤗
Daga ƴan facebook har ƴan WhatsApp bakwason yin comments to yaseen duk group ɗin da ba'ayi zakuna jina shiru sai nayi muku yaji aiki gobe😌😌
[3/5, 11:55 AM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
(THE WRITER OF 💅SARKI SAMEER 💅)
______________________________
*_episode 22💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
Bissmillah.....✍️
____Wallahi yayi yunƙurin tada husuma agunnan saida a ɗau rayuka anan gurin dan nasan waɗannan bundugun da suka riƙe tsaf zasu fasa kwanyar mutum, kuma wallahi sai inda ƙarfin mu ya ƙare dan bazamu ɗauki duk abun da zai yi mana ba sai mun casa shi a gaban mutane saidai duk a harbe mu ki kuma a rabamu da ranmu" cewar Barazana.
Suna cikin wannan zancen Faheem ta ƙaraso gurin da ɗan saurin ta, cike da saurin magana, ta ce; "yazo kuzo muje kusa da can inda familyn mu suke.
Beenish ce tace; "A'a Faheema mu ai ba familyn ki bane abokai ne dan haka kije kawai zamu zauna a inda kowa yake zaune mun gode da hakan ma"
Yanayin fuskar Faheema ne ya sauya dan bataji daɗi ba da ta faɗi hakan, kamar zatayi kuka tace; "to shikenan nima anan zan zauna ɗin idan munshiga daga ciki ma gaisa, amma ni a matsayin ƴan uwana na ɗauke ku ba abokai ba, tayi maganar tana ɗan tutturo baki dan ta samu kujerar gefan su ta zauna tana kawar da kai gefe ita a dole sun ɓata mata rai.
Murmushi kawai Beenish tayi tace; "Kema na fuskanci kin iya neman rigima koh gata ne yayi miki yawa wallahi, kinga ki tashi kije gurin ƴan uwan ki naga ana ta kallon inda kike kar kisa azo a kama mu...
Da sauri ta kalle ta yace "to taso muje ƙawata ta faɗa tana miƙewa tsaye zata kamo hannun ta, Beenish yayi saurin riƙe ɗayan hannun itama tare da cewa; Baby dawo ki zauna, ke kuma Fasheema tun muna shaida juna ki bar wajen nan,
Yanzu kam da gaske ta haɗe rai da maganar da Beenish tayi, murna sai ta koma ciki, maimakon ta tafi sai kawai ta kuma komawa inda ta tashi ta zauna.
A can wajen baƙon mu kuwa, an buɗe masa ƙofar motar ana jiran fitowar sa amma yaƙi fiyowa, alhalin kuma yasan kowa shi yake jira,
Saida yaga dama dan kansa sannan ya zuro ƙafafun sa, a hakan ma saida yajawa mutane rai sannan ya ƙarasa fitowa, yana fitowa duk ƴan sandar da sauron sojojin na gurin kowa ya ƙame ga sara masa, shima sara musu yayi sannan aka bashi hanya ya nufi wajen da tawagar ƴan uwan sa suke, gurin mahaifin sa, ya fara zuwa yana zuwa duk sukayo kansa sai ya rasa ma me zaiyi musu takan wa zai fara amsa gaisuwa, mahaifin sa kawai ya miƙawa hannu sukayi musabaha sannan yayi hugging ɗin mahaifiyar sa, duk sai washe baki suke na farin cikin ganin sa amma shi ko ajikin sa duk dade fuskar sa na rufe amma yanayin kamar baya nuna farin ciki kamar yanda suke nuna masa...
Mahaifin sa ne da kansa yayi masa jagora zuwa inda aka tana da saboda shi, har saida ya zauna sannan masu tsaron suka ɗan jajja baya suka ci gaba da kulawa dashi.
Mic ɗin da aka ajiye masa a gaban sa ya jawo sa daidai saitin bakin sa bayan ya gama kallon dukkan mutanen dake gurin dama da hagun sa na gaban sa babu inda bai kalla ba. Ya gama saita abun kenan zaiyi magana kawai sukaji ƙarar bundiga a cikin gidan sautin ta kuma kamar ma daga saman gidan aka sake ta, mutane basu gama tantancewa ba, suka kuma jin harbin har sau biyu, da gudu wasu sojojin suka nufi cikin gidan kowa na mamakin daga me ya faru daga ina kuma me yake faruwa.
Wasu na shiga ciki sai kuma suka fara jin wani da aka rasa daga ina, kan kace me guri ya hargitse jama'a na neman hanyar fita, gurin da yake kuma da sauri sojoji suka zagaye sa gudun kar wani abu ya sake sa, shikam ko ajikin sa daga yanda yake a zaune ko motsawa baiyi ba bare yayi yunƙurin yin wani abu,
Wasu na ƙoƙarin guduwa sai kawai sukaji harbin ya ɓalle ta waje wasu ƙarƙashin kujeru suka fara shiga, wasu kuma duk aka buɗe musu motoci suka shiga.
Commissionaner ne ya kalli ya jinjinawa, magana ɗaya hannu alamun aikin su na tafiya, shi kuma magana ɗaya yana mamakin jin harbin dan shidai yasan ba shirin shi bane ayi harbi ta sama ya dai san yace su saki har bi ta waje ta yanda hankalin mutane zai koma waje shi kuma sai yasamu damar kwashe su, yanda suka tsara kenan...
Faheema duk ta ruɗe ta ƙanƙame Barazana dake gefen ta, gashi tana tsoron ta tafi gurin ƴan uwan ta, a harbe ta, duk da harbin baizo harabar wajen ba, amma kowa cikin sa ya ɗuri ruwa...
Babyn baby ma an ruɗe, tana ƙoƙarin shiga ƙasan kujerar itama kawai taji an damƙo kanta mayafin jikin ta har sai da ya cire, ƙarar da ta saki ne yasa hankalin su gareta dan suma hankalin su ba a kwance yake, ba shiyasa ba su ankara da zuwan sa ba, har saida sukaji ƙarar ta, da sauri Beenish ta kai hannu ta damƙi nasa hannun, kuma tana damƙa ta murɗe sa har saida yayi ƙara agun, da sauri ƴan sandan da Commissioner ya tanada ya siye, yace kawai su saka hannu akamasu, idan anyi magana agun suce sun kama su ne da rashin gaskiya,
Cikin muryar sa me amo da ta zagaye duka wajen ta cikin loudspeaker.
"Stop shooting the guns, don't let anyone shoot at that place, close the gate, yayi maganar yana zaune batare da ya motsa daga zaman da yayi ba.
Daman kuma harbin a waje kawai ake jiyo ƙarar sa, na saman ma da akayi ba'a kuma yi ba, sojojin dai na can suna bincika lungu da saƙo na saman...
Duk da yayi magana amma gurin bai dawo daidai ba daga masu koke koke sai matakan tsaro da suke ta faman gudu wasu na ƙara haurawa sama, wasu kuma na fita wajen dan ganin anmagance wannan tozomar da basu san ta ina ta ɓullo ba,
Ƴan sanda sai zagaye suke agun wasu kuma na kusan tar inda su Beenish suke tsaye suna watsa idon su ta ko ina dan kar akawo musu hari basu ankara ba....
Cikin zaro ido Barazana da ta haɗa ido da commissionaner tace "Katumar babbar bara'uba, ran mata ya ɓaci ganin commissioner na turo musu wasu ƴan sandan, ai babu shiri duk suka sake ɗaura ɗamara, babu ruwansu da abun da ke faruwa suka tsaya cikin shirin su,
Ba zato ba tsammani kamar daga sama sukaji Commisioner nacewa ku kamasu basu da gaskiya ƴan ƙwaya ne ku duba jakunkunan su, akwai coken a ciki yana maganar yana nufo su yana nuna su da yatsa,
Gaba ɗayan su mutuwar tsaye sukayi dan saida kansu ya ƙulle amma na wani ɗan loƙaci, dan take tunanin su ya dawo gangar jikin su, jakunkunan su da suka ajiye akan table ɗin Ameela ta shiga dubawa cikin hanzari tana duba jakar Babyn baby kuwa saiga hodar koken ɗin aciki, mayarwa tayi ta rufe tana me mamakin yaushe aka saka musu, suma dukan su ita suka zubawa ido suna kallon hodar, ba ƙaramin mamaki sukayi ba kafin suyi wanni yunƙuri, ƴan sandan sun fara kai hannu kan jakunkunan nasu zasu duba, suna ɗora hannu akan jaka ɗaya Babyn baby