ta juya zata fita har taje bakin ƙofar fita ta tsinkayo muryar sa yana cewa "kiyi ɗayan aikin kibar case ɗin SMA If you want to be alive, If not I don't care, yayi maganar tare da taɓe baki irin wanna ke ta shafa.
Cike da mamakin furucin sa ta juyo tare da cewa "I don't understand you, what do you mean, I don't know what you're trying to say, I need more explan, please explain to me! Na kasa yarda da abun da kunnuwa na suka ji min, tayi maganar tana kuma takowa zuwa inda yake, kana ganin fuskarta zaka mamakin dake shimfiɗe akanta.
"Just go!
Yana faɗar haka ya tashi daga inda yake ya shige toilet abun sa, yabarta tsaye da mamaki, tasan tunda yace haka bazai kuma tanka mata ba, hakan yasa ta juya ta fita amma kuma dole yayi mata cikakken bayani game da wannan maganar da yayi, hartabar barack ɗin mamaki bai sake ta ba tana ta tunani akan maganar tasa, babban abun da yake tayi mata yawo ma akai shine "If you want to be alive" to yasan waɗanda sukayi hakan kenan ko me yake nufi, dole ta gano gaskiyar lamarin.
$$$$$$$$$$$$$$$$$$
*Five star ⭐*
____Beenish da Babyn baby sun daɗe suna kuka daga rungume da suke da ƙyar su Ameela suka samu suka shawo kansu suka rarrashe su kafin suka tsagaita da kukan da suke.
Da ƙyar suka iya tashi suka koma ɗaki, a ɗakin ma saida su Ameela suka ɗan kuma kwantar musu da hankali da basu haƙuri, memakon kowa ya kwanta anasa wajen tare suka kwanta gado ɗaya batare da suncewa junan su komai ba.
Barazana ce ta kalli gadon Aunty babba tare da jan tsaki a fili tace "shigiya baƙa mu zaki juyawa baya akan wani ɗan iskan ƙaton kwarto mutum tsofe tsofe da shi sai wani maƙalƙalesa kike marar kunya shashasha kawai.
Ameela ce tace "dan Allah ki bar mana zancen ta zatagane shayi ruwa ne badai namiji ta zaɓa ba, zata dawo da ƙafar ta,
"Ai wallahi bata isa ba tunda ta tafi ta tafi kenan saidai tabi wani sarkin amma mukam tayi hannun riga damu, cewar Barazana.
Beenish na jin su bata iya tsoma bakin ta ba domin bata da wani kuzari dan Babyn baby har zazzaɓi yafara rufe ta, saida ta sha magani sannan bacci ya ɗauke ta da ƙyar, Beenish kuma kanta ne yake sara mata kamar zai rabe haka take jinsa tana daga kwancen amma ki take kamar zai faɗi tasa hannu biyu ta dafe kan.
Suna cikin wannan surutun suka kuma jin ana musu bugun hauka.
Da sauri Beenish ta damƙe idon ta danji tayi kamar a cikin ƙwaƙwalwar ta akeyin bugun.
"To fa waye kuma cikin darennan yake mana irin bugun, cewar Barazana.
Ameela tace "zo muje mu gani Allah ya sadai ba sojojin nanne suka ƙara dowawa ba,
Barazana tace "haba dai su dawo suyi mana me kuma, nifa sun fara ban haushi wallahi na tsani soja.
Suna wannan maganar suna ƙarasowa cikin falon daidai loƙacin itama Maryam ta fito daga nata ɗakin cikin maganin baccin da bai daɗe da ɗaukar ta ba tace "Su waye ne wai? Take tamabayar su Ameela.
Cike da rashin sani suma suka bata amsa yayin da Ameela ta ɗan leƙa ta wata ƙaramar ɓulla, ɗagowa tayi tana dafe kanta tace "wallahi sune!
Barazana ta dafe ƙirjin ta tare da cewa mun shiga tara bamu ƙarasa goma ba, me zasu yi mana kuma?
Ameela tace "wa ya sani ai bazamu buɗe ba idan sun gaji sa tafi.
Jin maganar da sojojin sukaji ne yasa suka kuma ƙara ƙarfi wajen bugawar kamar zasu ɓalle ƙofar, daga wajen kuma suke cewa baza ku buɗe ba sai mun sa muku boom agidan,
Taɓe baki Ameela tayi tace "kun daɗe baku saka ba, ai wallahi saidai ku ɓalla ƙofar nan amma babu wanda zai buɗe muku mugaye kawai.
Cike da rashin fahimta Maryam take tambayar su abun dake faruwa nan suka ɗan gaya mata abun da ya haɗa su.
Ɗan murmushi Maryam ta saki sosai dan har haƙoran ta suna fitowa.
Mamaki sukayi ganin tana murmushi.
Ameela tace "lafiya kike kuwa?
Da sauri ta ɗan daidaita kanta tare da cewa lafiya mana, kawai abun da kukayi ne ya ɗan so bani dariya, to ku buɗe mana kuji da me suka zo baza ku iya dasu bane?
Barazana tace "a'a wallahi baza mu iya da su ba, dade ba gun a hannun su shine amma hakannan mu buɗe su fasa mana ƙwaƙwalwa da hanjin ciki, inaa wallahi bazai yiyuwu ba, bangaji da rayuwar duniya ba da saura na, ko aure banyi ba.
Yanzu murmushi Maryama tayi,
Suna cikin haka Beenish ta fito hannu dafe dakai ta yafa ɗan ƙaramin mayafi, har wani haɗa hanya take saboda yanda take jin kanta da jikin ta kamar zata kifa haka take ji idon ta duk yayi ja.
Tana zuwa babu wanda tayiwa magana kawai ta nufi ƙofar zata buɗe danji take kamar kanta zai rabe idan suna buga ƙofar,
Da sauri Barazana ta tari gaban ta tace "in kinayiwa Allah kar ki buɗe dan Allah ki rabu da su zasu haƙura ne su tafi, kin manta abun da mugunnan yayi miki ga shi kuma laifin da mukayi muka gudo, wallahi idan kika buɗe sai sun fasa mana ciki da bindiga, Allah shawara ki rabu dasu,
Cikin yanayin damuwa da ciwon kan Beenish tace "Dan Allah bani waje banajin daɗi,
Ameela ma saida ta hanata amma duk yanda suka so su hanata ƙin yarda tayi, itadai Maryam bata hanata ba dan tama fi son a buɗe ɗin daman,
Cike da dauriya Beenish ta janye Barazana daga gabanta tasa hannu ta buɗe ƙofar,
Ai ana buɗewa basuyi wata wata ba kawai suka danno kai cikin falon saura kaɗan su buge Beenish tayi saurin matsawa.
Su Barazana kama neman gurin ɓuya suka shigayi saidai babu wanda yayi yunƙurin arziƙi suka cinmasu, duk suka riƙo su.
Wani ne ya damƙo hannu Beenish tayi saurin ƙwacewa tace kada ƙazamin hannun ka ya kuma taɓani ko baku riƙe mu za muje ku kaimu duk inda kuka ga dama in ma kashe mu zakuyi kuyi aikin banza kai mstww taja tsaki tana fita daga falon,
Su Ameela kam ko mayafi babu a jikin su haka suka tisa ƙeyar su suka fita dasu, basu bi takan Maryam dan ba'ace musu har itaba, tunda sunga ita ta manyanta, kuma basu nemi sauran biyun ba sude tunda su samu damar kamasu shikenan.
Har suka fito suka saka su a mota suka fara tafiya Barazana take zazzagawa Beenish masifa,
Barazana tace "Narantse da Allah Beenish bakiyi ba wallahi kin cuce mu, nidai Allah na mutu kece sila saida muka ce kar ki buɗe amma kika ƙi jin magana sai ɗan iskan taurin kan masifa yanzu wa yasan me zasu yi mana, kai kai wallahi Beenish Allah ya isana nidai daman duk ke kika ja mana wa aike ki yiwa baƙin mugun mutum rashin kunya muna zaman zaman yanzu zaki sa suje su rataye mu su jefar da gawar mu acikin daji ƙarshe mu ƙare a bakin karnuka ku mu ruɓe, ai ko mutuwar ce gwanda kayi me kyau ayi maka sallah akaika amma yanzu irin wannan mutuwar ai abar ƙyama ce.
Dalla malama ki daina yi mana wannan mummunan fatan in Sha Allah bazamu mutu ba ke angaya miki mutuwa wasa ce ai ba yanzu zamu mutu ba, ni wallahi bana jawa kaina mutuwa yanzu, saidai ke da kike nemanta kike jawa kanki Allah ya kawo miki ita muna zuwa ko kafin ma mu ƙarasa dan kawai sun ɗauke mu sai ki fara jawo mana wannan alkaba'in to wallahi ki gani a kanki amma banda mu.
"Amma Allah ya isa tsakanina dake Ameela ni zaki ringa yiwa wannan muguwar addu'ar to wallahi kema harda ke, yo Allah na tuba ko gani nayi zan mutu ai na jawo ki mun tafi tare bazan mutu ni kaɗai ba.
Ameela zatayi magana kenan Beenish tace dan girman Allah kuyi mana shiru wallahi kamar a cikin kaina kuke wannan maganar wai bakuga halin da nake ciki bane, dame zanji da damuwata ko da ciwon kan koda surutun ku, haba dan Allah tunda muka taho kunƙi kusawa bakin ku linzami mtssww, ta ƙarasa maganar tana ƙara ɗora kanta akan cinyar ta, kamar ta fashe da kuka haka take ji har wani bibbiyu bibbiyu take gani idan ta ɗaga kanta.
Cike da hasala Barazana tace "daman ba dole kice haka ba ai ba abun dake damunki da da akwai da baki buɗe musu ƙofar nan ba, wallahi nidai banzan fasa magana ba, ga mari ga tsinka jaka ai abun sai yai yawa shige da hauka.
Ameela ce tace "dan Allah ya isa haka kuma ki mana shiru dan Allah tunda de kinga yanayin ta bata da lafiya ko kin manta me yafaru ɗazu ne.
"Hmmm" kawai Barazana tace dan batajin zata iya yin shiru da bakin, dan wallahi ita in batayi magana ba bakin ta har motsi yake shi kaɗai, bata so tayi shiru, yawan shiru ai warin baki yake sawa.
Motar shiru ta ɗauka shima sojon dake gefansu wallahi sun ishe shi kawai dai yayi musu shiru ne dan bai manta abun da Aunty babba tayi masa ba loƙacin da yakawo su gida ya tsaya yana kallon su, shiyasa yanzu kawai yayi shiru ya rabu dasu, amma aransa yana ayyana indai hardashi a punishment ɗin da za'ayi musu, sai ya rama...
A haka suka ci gaba da magana saidai jefi jefi Barazana sai tayi magana dan bazata iya ɗin ba kamar yanda tace ɗin, saidai ba ta samu ana kulata ba, Ameela ma ta rabu da ita, idan ta gaji dan kanta tayi shiru...
$$$$$$$$$$$$$$$$$$$
*COMMISSIONER*
___Yana fitowa daga gidan sa ya shiga motar da gudu kawai yake kwararawa kamar zai tashi sama, saida ya ƙaraso wani tanƙameman gida sannan ya doka horn ana buɗe masa ya danna kai cikin gidan ko gama parking beyi ba ya fito daga cikin gidan.
Wajen shiga falon ya dosa yana zuwa bakin gurin kuma aka sanar dashi cewa wanda yazo nema baya nan.
Ji yayi kamar ya shiga dukan su ya huce akan su, tambayar su yayi ina yaje, suka ce masa basu sani ba amma dai ba daɗewa zai yi ba.
Motar sa ya koma tare da ɗaukan wayar sa ya shiga daddanawa ana ɗagawa yace gani a gidan ka yaushe zaka dawo?
Shiru yayi yana jiran amsar sa, sannan ya kuma cewa ina jiranka dan akwai matsala kayi sauri sai kazo zamu tattauna na, kashe wayar yayi yana jefa ta kana kujera yana dafe kansa tare da furzar da isa ka daga bakin sa, da ƙarfi yace "ƙarya kuke wallahi sai nayi maganin baku isa kusa a kore ni daga aiki ba, ni! Ni! Wai ni za'a tonawa asiri a koreni daga aiki koma waye da wannan aikin ya jawo kansa sai kun gane kuren ku daku da kuka faɗa ɗin da wanda ya dakatar sani ɗin duk sai na koya muku hankali, harda min barazanar in bar cikin gidan nan da 24 hours wallahi babu inda zani ina nan babu wanda ya isa ya fitar dani daga cikin sa kuma babu wanda ya isa ya koreni daga ai ko ko waye shi ƙaryarka kaima,
Sai surutai yake faman yi shikaɗai ya daɗe a gidan har yana shirin tafiya sai kuma yaji anbuɗe gate ɗin da sauri ya kuma buɗe motar ya fito, yana jingina da jikin motarsa, har waccen motar ta ƙarasa shigowa ta nufi can parking lot saida aka ajiye ta sannan suka shiga fitowa daga motar, shi ya fara fitowa sai ya zagayo ya buɗe gaban motar tare da miƙa mata hannu tana murmushi ta ɗora nata hannun akan nasa tare da miƙewa tsaye.
Kasa haƙuri commissioner yayi yata ji cikin sauri dan ya same sa a inda yake, yana ƙarasowa gurin, yayi daidai da ya kamo hannun ta sun juyo suka haɗu da shi.
Da sauri Commissioner yaja baya yana binta da kallo itama cike da mamakin take kallon sa.
Ƙayataccen murmushi mutumin ya saki yana shafa gemunsa yace "sarki rigima me kuma ya faru muje daga ciki koh?
Cike da ɗumbin mamaki Commissioner yace Bulama meyi haɗin ka da wannan yarinyar da na ganka da ita.
Murmushi Bulama ya kuma yi sannan yace "abun mamaki koh kaga baka taɓa gani na da mace ba ko? Ka muje ciki wannan long story ne.
Commissioner ya kasa ɓoye mamakin sa ga yanda Aunty babba ta wani basar kamar bata taɓa ganin sa bama, sai faman narkewa take yi ajikin Bulama.
Commissioner ya kuma cewa "karde kace min itace wacce kake so kake nema tsawon loƙacinnan?
"Eh itace mana, Bulama ya faɗa yana ƙaƙalo murmushin yaƙe saboda tana gurin a ranshi kuwa cewa yake Allah ya kiyaye me sanyi da wannan abun,
Jinjina kai yayi zai kuma tambayar sa kenan, Bulama yace "wai a tsaye zamu gama maganar ne Madam fa ta gaji mu shiga daga ciki nace.
Commissioner badan yaso ba dan abun yagama ɗaure masa kai, amma ba yanda ya iya dole ya bisa yanda yake so.
Aunty babba kam daɗi ya gama kashe ta jin abun da commissioner yace ashe dai da gaske ne tana ran masoyin ta kowa ma yasan yana nemanta gaskiya taji daɗi sai taji ta kuma zama wata sarauniyar mata, amma ko da wasa batama kalli commissioner ba bare ta nuna ta taɓa ganin me kama dashi kamar sanshi ba haka tayi, hannun ta cikin na Bulama ta saƙalo sa har suka ƙarasa shiga cikin falon, shidai commissioner kamar jela haka yake binsu a baya...
$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$
*GHAMBURJ*
*Hajja Mama*
__Bayan ta gama yiwa su Bilal barazana ta fito daga cikin ɗakin tana fitowa tayi hanyar ɗakin da ta ajiye SMA, tana shiga yadaɗe da farkawa yana zaune ya zabga tagumi cike da mamakin abun da ya faru dashi.
__Ganin yasa yayi saurin tashi yana mamakin ganin ta, itama shiɗin take kallo tare da ƙaƙalo murmushin rainin hankali loƙaci ɗaya kuma ta haɗe rai tana aika masa da kallo me cike da fassarori kala-kala.
Yau ga shugaban sojoji agaban shugabar ƴan aiki, kayi mamakin yanda hakan ta faru ko to uban gidan naka ne yasa aka ɗauko ka, baisan kuma daman nemanka muke ba, sai gashi kazo cikin sauƙi, shida tasa manufar yasa aka kawoka kuma badan yayi maka komai ba, saidan cikar wani nashi burin, saidai baisan kura ya kawowa ajiyar nama ba, a hankali zamuyi amfani dashi duk mukama magauta mu shi muka sani shi kuma ku yasani ta hanyar sa zamu gano ku duk inda kuke ɗaya bayan ɗaya sai munsa kun kwashi kashin ku a hannunku kun cinye shi kuma! ta ƙarasa maganar tana ɗaga masa murya.
Shima hayyaƙowa yayi zaiyi kanta yana naɗe hannun sa zai kai mata naushi tayi saurin gocewa tana kaimasa nata naushin da ƙafa, wani irin juyi yayi bata ankaraba ya kaiwa wuyan shaƙa yana haɗa ta da bango, cikin zazzaro ido da jajayen idanun sa da suka juya suka koma na sojoji, kana ganin sa kasan an fafata da shi.
"Idan kika kuma yin wata maganar banza anan sai na kashe ki, kuma kin san na kashe banza, ƙarya kike Boss bazai taɓa sawa ku ɗauko ni ba, kuma ina me ƙara tabbatar miki duk loƙacin da Boss ya san ke wace sai kinyi dana sanin kasancewar ki a raye har yanzu, kuma ki sani baza ku taɓa ɗaukar fansa kanmu ba, ki ɗau fansa a matsayin ki nawa eh daman ƴan aiki zaki yi wannan shishshiga kibar masu gida suyi, ko su babu wanda yayi magana sai ke zaƙwaƙura, tun laƙacin babu wanda yayi magana sai yanzu zaki taso da maganar to wallahi na lahira sai yafiki jin daɗin muddun suka san kina raye.
Duk da Hajja Mama taji shaƙar nan dan har karin amai ta fara, amma haka ta daure bata bari ƙarantar ta ta bayyana ba, ƙarfin ta tasaka ta tura sa baya tana shafa gurin da ya shaƙeta ba ƙarya taji zafi, cikin fusata itama tace; "banzar ƙwaƙwalwar ka ce take baka zancen ya mutu amma kullum rai ake ƙara masa nan da wani loƙaci duk zaku gane kuren ku, dan baku ci bulus ba, wallahi ko babu jinin Sardauna a raye to ni sai na zama saina rama masa daidai da abun da abun da kuka aikata bare ma jinin Sardauna ya yawaita ƴansa suna nan tare da jikokin sa da kuma ƴan amana! Yanda kuka hana familyn sa sakewa kuma duk sai mun tarwatsa ko wannen ku,
Yunƙurowa yayi tayi saurin zato wata wuƙa daga ƙasan ƙafarta tace "wallahi ka kuma yi min hauka anan takan ka zan fara dan sai nayi gunduwa gunduwa da naman cinyoyin ka bazan kashe ka yanzu ba saika ɗanɗan jin ɗaci raɗaɗin da kuka sanya mu mukaji, ba wanda zamu kashe amma kowa sai jikinsa ya gaya masa dan sai kunfi zaɓar mutuwar ku akan abun da zamuyi muku, musamman wancen wawan lusari da duk ƙwarewar tasa yakasa gane wace ce ni, har yake haɗa kai dani, in baka sani ba kasani ba bari in sanar dakai shiɗin da kake taƙama dashi baitaɓa zama dakai da zuciya ɗaya ba bakasan me yace ayi maka ba ne, shiyasa har kake ikirarin idan ya gano gaskiya bazai barni ba to tunanina yaci uwar nasa sai nagama kwashe komai daga gare sa na jefa rayuwar sa cikin ƙunci, kuma gida nashi ne amma ni nake da ikon juya duk abun da naga dama ta hanyar maida shi mahaukaci taɓaɓɓe wanda baisan komai ba marar tunani! Tana kaiwa bata jira cewar sa ba ta juya ta fice daga ɗakin tare da ƙullo sa ta garƙama ƙwaɗo.
SMA ji yayi kamar ya kurma ihu tabbas ya tsorata da abun da tace duk da bai nuna mata ba, bai taɓa kawo wannan ranar cikin gaba