sa a buɗe hakan yasa shi yayi saurin miƙewa daga gurin gudun kar wani yagan sa kan kujera ya koma ya zauna tare da rafka uban tagumi yana tunanin me kuma zai biyo baya daga ɓangaren Hammad......,
*(Duk me son in saka shi a group yayi min magana ta number ta a WhatsApp, dan Allah idan kasan ba karantawa zakayi ko zaka tambaye ni wani littafin to kar kayi min magana Please 🙏)*
*(ƴan facebook kuma da basa WhatsApp kuyi searching ɗin SU WAYE SU HAUSA NOVEL GROUP kuyi join anan zan ringa posting kullum amma idan kana wani group ɗin zaka iya ganin sa saidai baizama lalle kagani kullum ba kuma ba ajere ba.)*
___loƙacin da Beenish ta fito daga office ɗin sa direct can hole ɗin nasu ta nufa, tana ta sauri taje gurin su Babyn baby garin saurin bata kula ba tayi karo da wani wani saurayi da suke tafiya tare da abokan sa su biyu a bayan sa da sauri tayi baya tana shirin ta bashi haƙuri kawai ɗagowar da zatayi taji saukar mari a fuskar ta.
yana marin ta abokan nasa suka kwashe da dariya suna nuna ta da yatsa.
Cikin tsananin mamaki ta dafe kumatun ta, bata jira mamakin yagama sakin ta ba, itama ta ɗauke sa da nata marin kafin ya dawo hayyacin sa ta kuma sauke masa wani ta ɗayan ɓarin yana sake ɗagowa ta kuma wanka masa wani saida tayi masa guda huɗu zafafa, dan ranta yagama ɓaci da marin da yayi mata gani take har yanzu bata rama ba, tunda tayi masa na farko abokan sukaja baya cikin tsananin mamakin abun da tayi mishi,
Hannu ta ɗaga zata ƙara masa ɗaya daga cikin su yayi saurin riƙe hannun nata, ta watsa masa wani mugun kallo da idanun ta da har yanzu basu baje daga zan da sukayi ba tare da fusge hannun ta daga nasa, da sauri yaja da baya gudun kar yaje shima ta sauke masa marin,
Wanda ta mara ɗin da yaga haka shima bai daddara ba dan shima ranshi ya kai ƙololuwar ɓaci a zafafe ya ɗago hannu zai kaiwa wuyan ta shaƙa yaji an riƙe hannun, da sauri yabi hannun da kallo tare da sauke sa a kan fuskar ta, da wani irin kallo yake bin ta na uku saura kwata.
"Kayi na farko kayi na ƙarshe wannan shine dana sanin da zakayi idan kabari hannun ka ya kuma sauka a kanta sai kayi sha'awar dama baka zo duniya ba...
Duk da taƙaicin da yake ji hakan bai hanasa kwashewa da dariyar sheƙiyanci ba, yana dariyar ya matsar da fuskar sa daf da ita yana kallon ƙwayar idon ta, cikin karkatar da baki gefe ya ce; oh really idan kuma naƙi fa? Su waye ku waye uban ku a cikin garin dan da alamar ku baƙi ne ko bakusan ko ni waye ba.
Cike da jin haushin maganar sa ta tattaro yawun bakin ta ta tofa masa a fuska, hannun ta dake riƙe da nasa ta murɗe cikin ɗaga murya ta ce; Uban ka ne uban kuma da kake ikirarin bamu san kai waye sai me bamu sani ba kuma bama so mu sani kuma bazamu taɓa sani ba banza kawai ajawo, ka wuce banzan namiji lusari asararre kaje ka tambayi uwarka waye kai tunda ita ta haifeka, ita yafi dacewa da tasan kowa ta haifa, amma mu bama buƙatar sani, tana wannan maganar saiji tayi ƙas hannun sa da ta murɗe yabada sauti, amma duk da haka saida ta ƙara murɗawa sannan ta tura sa baya ya kuma faɗawa akan hunnun, ba shiri ya saki ƙara, kan kace me guri yagama taruwa da mutane daman wasu dasu aka fara faɗan wasu kuma sai yanzu hankalin su yayo wajen.
Da sauri Barazana ta ƙaraso wajen ita da Ameela, gurin Aunty Babba suka ƙarasa tunda suka ganta haka bama su tsaya tambayar ba'asi ba, sai ma jinjina mata da sukayi, sannan suka juya gurin Beenish da Babyn baby da suke tsaye hannun su riƙe da na juna, hankalin su ne ya tashi ganin fuskar Beenish kamar tayi kuka, da sauri Ameela ta ce; Me ya faru badai shi kika zubarwa da hawaye ba.
Mmurmushi Beenish tayi tare da dafa kafaɗar ta ta ce; kar ku wani damu bashi bane abune ya faɗan a ido dalilin haɗuwar mu dashi kenan ban lura da shi ba, bai jira na bashi haƙuri ba kawai ya.....,
Barazana ce ta dakatar da ita da cewa shikenan kawai ai mun gane maimaita saɓo saɓo ne, dan wallahi zuciya ta a kusa take hmmm.
Kan kace me magana ta karaɗe makaranta duk wanda yaji labari sai yazo ya ganewa idon sa, da sauri abokan sa suka ɗauke sa suka saka shi a mota suka fita dashi daga cikin makarantar.
Wata ƙawar Ameela ce da suke ɗan gaisawa amma sama sama ta matsa kusa da ita tace; Ameela wai me ke faruwa?
Da kamar bazata kula taba, sai dai ta ce; "Nasan tunkan kizo kinji labarin komai bansan kuma me kike son ji daga gurina ba, tana faɗar haka ta kawar da kanta ta juya gurin Aunty Babba da tayi tsaye kamar soja taƙi ko motsawa jira take kawai wani ya kawo musu wurgi ta ƙarasa sauke abun da take ji a kansa,
Haushi ne ya kama ta jin yanda ta bata amsa, yanzu isakan cin nasu yafara wuce gona da iri, a wannan karan sun taɓota dole ta ɗau mataki a kai tunda suka taɓa mata abun son ta....
"Wai su waye su? Naga kamar zaƙewar su tayi yawa, Wata ce take tambayar wannan wacce tayiwa Ameela magana, ɗan juyawa tayi ta kalle ta, sannan ta ce; "To nidai bazan ce nasan su ba kuma bazan ce ban san su ba, wannan abun da kika gani ma kaɗanne sa basu tarar masa su duka ba, amma dai abun mamaki bisa ga dukkan alamu basu san waye ba, nasan da baza suyi masa haka ba duk jiji da kansu, daman ance rana dubu ta barawo rana ɗaya ta mai kaya, yau zasu kwashi kashin su a hannu kenan sun jawo ruwan dafa kansu.
"Nima dai nayi mamaki da naji ance wai wata ta karya ɗan gidan Commisiona of police, shiyasa nazo inga su waye masu wannan aika aika to amma a ina suke danni yau nafara ganin su....
"Bahiyya!
Ameela ta kira sunan ƙawar tata da take wannan maganganun ashe duk tana jinta...
A wani wulaƙance ta ɗago ta kalle ta, zaro ido Ameela tayi ganin kallon da tayi mata na raini da wulaƙanci tundaga nan ta fahimci inda maganganun ta suka dosa, ta kowa tayi tazo har gaban ta, itama a wulaƙancen ta kalle ta tace; "Wannan ya zamana first and last da zaki min irin kallon nan in bahaka ba wallahi sai na tsiyayar miki da ido inga ubun da ya tsaya miki...shiru tayi na ɗan wani loƙaci sannan ta cigaba..
"Ke kiji da abun dake damun ki, ki rufawa kanki asiri kamar yanda tsohuwar ki take son rufa miki, ke yanzu ina ke ina shi hanyar jirgi daban ta mota da ban, abun ba haɗi, shawara zan baki son maso wani baida amfani ki bari ya gani ya yaba, har kike kirari akan sa to be san kinayi ba abun kunya, kin dage kina hauka akan wanda bai san kinayi ba ƴar gidan malam Shehu wallahi in ban tona miki asiri a gurin nan ba kice a shegiya nazo duniya wacce bata san inda yake mata ciwo ba... Maganar kuma bamu san ko waye shi ba, koma waye ba damuwar mu bace sanin hakan baida amfani a gare mu, wannan ke ta shafa indai ke kin sanshi ai shikenan mtsawww ta doka tsaki tabar wajen.
Iya shaƙa ta shaƙa ga mutane wasu na mata dariya, saboda irin masu rawar kannanne da son nuna su masu shine alhalin na mota ma da ƙyar take samu amma sai ƙaryar arziƙi, ji tayi kamar ta shaƙota amma tana tsoron kar taci gaba da yi mata ɓarota shiyasa zata ɗaga mata ƙafa amma tayi alwashin sai tasa tayi danasanin abun da tayi mata a gaban mutane.
'Wiwiwiwiwiwiiiii nan kallo yafara komawa inda ake jiyo jiniyar ƴan sanda, motar ƴan sanda ce ta shigo cikin gurin da gudu har inda dandazon mutanen suke.
Wacce aka kira da Bahiyya ta saki wani irin murmushin farin ciki harda tafawa sa hannu, tana kallon su Ameela, ta fara takawa zuwa wajen su cikin jin daɗi tace; To yanzu zaku san ko shi waye koh, angaya muku kowa ake taɓawa a kwana lafiya, in wani yayi rawa an basa kuɗi to a wani wajen idan kayi duka zaka sh.......,
Bata kai ƙarshe ba Barazana ta kwashe da mari tare da caƙumar wuyan ta ta shaƙeta da hannu ɗaya hannu ɗaya kuma tana kifa mata mari dashi....
Ganin hakan yasa ƴan sanda sukayi saurin yowa kansu........✍️✍️
Please comment and share and likes hakanne zaisa kuna ganin update da yawa.
*(Duk me son in saka shi a group yayi min magana ta number ta a WhatsApp, dan Allah idan kasan ba karantawa zakayi ko zaka tambaye ni wani littafin to kar kayi min magana Please 🙏)*
*(ƴan facebook kuma da basa WhatsApp kuyi searching ɗin SU WAYE SU HAUSA NOVEL GROUP kuyi join anan zan ringa posting kullum amma idan kana wani group ɗin zaka iya ganin sa saidai baizama lalle kagani kullum ba kuma ba ajere ba.)*
[3/5, 11:43 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________
*_episode 7💧_*
💧💦محمدالرسوالله...!💦💧
Bissmillah.....✍️
_____Bata kai ƙarshe ba Barazana ta kwashe da mari tare da caƙumar wuyan ta ta shaƙeta da hannu ɗaya hannu ɗaya kuma tana kifa mata mari dashi....
Ganin hakan yasa ƴan sanda sukayi saurin yowa kansu........✍️
Maven ƴar sanda ce take ta fara jan Barazana amma ko gezau ba tayi ba kuma bata fasa abun da take ba, nan aka shiga ƙoƙarin rabasu amma aka kasa saida ƙyar aka iya ɓanɓare Bahiyya daga hannun Barazana, Barazana sai ciki take tana batsewa tana watsa mata kallo ji take kamar ta kuma shaƙota,
Ƴan sandanne suka jata zuwa motar su babu musu ko wata garda ma ta shige tana shiga suma su Beenish suka bi bayan ta ƴan sanda sunyi mamaki dan su a tunanin su wacce suka tarar tana ƙoƙarin kashe wata ita ce me laifin da ta daki ɗan gidan Commisiona of police, shiyasa kawai basu wani tsaya jin ba'asi ba tunda idon su ya gane musu no need su tsaya tambayar wacece,
Da sauri wani ɗan sanda ya tari gaban su su duka huɗun, tun kan yayi magana, Ameela tace; mu duka muka aikata dan ni na karyawa tsinanne hannu dan haka dukan mu zaku kama, ba ita kaɗai ba, tana gama faɗar haka tabi gefen sa ta haye kan motar da kan ta, yana gurin kamar gunki duk suka raɓa ta gefen sa suka haye kan motar, shidai tunda yake yau ce rana ta farko da ya haɗu da irin waɗannan shi sa ko maza sukaje kamawa sai kaga suna tsoron a kamasu amma su suna mata ba tsoro a tattare da su, da kansu ma zasu shiga motar, aikwa dole ya nuna musu ko su waye ƴan sanda sai ya sanya musu tsoro a zuƙa tansu, daga yau ko jiniyar ƴan sanda suka gani sai su gudu bare kuma suga ƴan sandar da kansu...
Ƴallaɓai.!
Wani ɗan sanda ne ya katse masa tunanin da yake yi,
Shima shiga yayi suka saka su a a tsakiya, aka tada motar da gudu suka bar cikin makarantar da su.
Saida suka fita sannan ƴan gurin suka fara gulmar su wasu su faɗi alkhairi wasu su faɗi a kasin haka, Bahiyya dai saida taimakon wasu ta iya miƙewa daga gun, jikin ta ya gaya mata, dan wuyan ta sai raɗadi yake mata, numfashin ta kam har yanzu fitar sa bata gama saituwa ba,
Tunda suka fara tafiya su Barazana suka kafa hira a cikin motar police, har shewa,
Wannan ɗan sandanne ya daka musu tsawa,
"Dalla malamai kuyi man shiru wallahi zanci muku mutunci anan gurin ko an gaya muku nan gurin sheƙeyan ci ne, ku shiga hankalin ku, if not, I swear Then you should regret what you are doing. Ku kama kanku or I should shoot you,
"Banza sukayi masa kamar ma basu san da halittar sa ba acikin gurin sukaci gaba da abun da suke,
Wani abune yazo masa wuya ya tsaya dan ta ƙaici, a harzuƙe ya ɗaga hannu su zai kaiwa Babyn baby mari dan ita ce a kusa da shi, sai kawai yaji hannun sa a cikin hannun mutum huɗu dan duk atare suka cafki hannun nasa, kuma damƙa bata wasa ba, ɗayan ɗan sandan dake bayanne ya yunƙura zai shima a zafafe dan kawai ƙyale su yayi saboda ogansu na gun shiyasa yayi shiru duk abun da suke bai tanka musu ba,
Cikin ɗaga murya yace; "Kai..!
"Suma ɗaga masa muryar sukayi tare da daka masa tsawar da tafi tashi dan har saida drivern dake tuƙa su yaja burki yana juyowa dan su da suke gaba basu san me yake faruwa ba. amma dake basa gani su sai kawai ya tayar da motar suka ci gaba da tafiya.
Shima baya ya ɗanyi, dan saida yaji muryar tasu har cikin ranshi,
Aunty Babba ce tace; ku nan a tunanin ku kun isa kuyi mana wani abun, har kana da damar da zakayi mana tsawa to wlh kayi ta farko kayi ta ƙarshe, in ba haka ba yanzu kaga haƙoran ka a ƙasa idan kuma kana ganin wasa ne ka kumayi kagani wallahi sai na gurje maka baki anan gurin, ta ƙarasa maganar tare da wurga masa mugun kallo, tana hararar sa,
Gum yayi da bakin sa, dan ya fahimci kamar basu kaɗai bane, wataƙil da wani makamin a jikin su, gashi su kuma basu da wani a bun da zasu kare kan su, idan suka biye musu zasu iya sawa suji kunya, dan haka yaja bakin sa yayi shiru,
Tunda suka riƙe masa hannu ya haɗiyi wani mugun yawu daskararre da ya wuce da ƙyar dan saida yaji riƙon kamar ta ciki suka riƙo ƙashin sa gashi sunƙi sakin da,
Kai kuma da kake shirin fuskar ta, Sa'ar ka ɗaya kana matsayin ɗan sanda amma wallahi kaga yanda muka riƙe maka hannun nan kowa sai ya ɓalla inda ya riƙe amma munɗaga maka ƙafa matsayin na me muƙami bawai dan munajin tsoron ka ba dan haka ka iya bakin ka ba ruwan ka da rayuwar mu, ka tsaya a matsayin ka in kuma kana ganin zaka iya ja da mu bismillah,
"Barazana ce ta ɗan ƙara damƙe inda ta riƙe da ƙarfi sannan tace; AHMADU da SIRAYYA, nasan kuma inda SAHU me wake take da kuma unguwar mabuga. To kasani jayayya damu kamar jayayya da rayuwar su ne, sai ka zaɓo aikin ka ko su?
A mugun razane ya ɗago jayayen idanun sa da sukayi kama da na ƴan masu zuƙe zuƙe, ya tsorata da maganar da Barazana ta faɗa, yayi maki jin sunan ƴaƴan sa da matar sa, a bakin ta, to hakan me yake nufi shida ko a gurin aikin sa ba kowa ne yasan inda iyalan sa suke ba, amma gashi yaji sunayen su a wajen da bai taɓa tsammani da tunani ba, to su ɗin wai su waye su, a ina suke shidai baitaɓa jin labarin su bama bare ya gansu amma gashi har address ɗin sa sun sani anya kuwa basa aiki da aljanu da suka gaya musu ko kuma su ɗinne aljanu, wata zuciyar tace ko aljanun ne ma to su waye su meye haɗina dasu me nayi musu Kum......
Maganar da Barazana tayi masa ne yasa shi dawowa daga tunanin da ya tafi bai shirya ba,
Dariya ta kwashe da ita ta sake shi tana tafawa da hannu, can kuma sai ta haɗe rai kamar ba itace tayi dariya yanzu ba, sannan ta kuma cewa, yadai naga ka tsora ta daga jin ɗan wannan abun, to kaɗan ma ka ji idan kace zakai damu mu zauna lafiya in kuma ka kawo mana iskan ci sai mun nuna maka a bakin tasha aka haife mu,
Suma ragowar duk sakin sa sukayi, jikin shi a mugun sanyaye yayi baya, bakin sa yayi masa nauyi dan ya rasa ta cewa; ga tarun tambayoyi dake cikin ransa amma ba halin yinsu dole ya koyawa kansa hankali yabi su a sannu su rabu lafiya dan da ta shine ma da tun yanzu zasu rabu, matsalar kawai de dan ɗan gidan Commisiona suka taɓa amma da ba abun da zaisa yaci gaba da tafiya dasu guri ɗaya, yana cikin maganar motar ta tsaya alamun sunzo,
Tunda yayi baya bai yarda ya sake ɗagowa ba bare su haɗa ido dashi yana jin su suka ci gaba da hirar su kamar suna ɗakin uwar su hankalin su kwance.
Sum sum sum yayi ya fito daga motar shima ɗayan da sauri ya fito suna fitowa ƴan ƙasa dasu suka hau yi musu salute,
Har na gaban motar suka fito wanda yake tuƙasu da kuma macen dake gefen sa, amma suna ciki basu fito ba, kuma kamar basu da niyar fitowar.
Kallon kallo suka shiga yi a junan su, tsakanin ƴan sandan da suka fito daga