"Ya na ganki ke kaɗai, ina yarinyar da kika ce zaki taho da ita.
Watsa masa harara tayi batayi magana ba, ta wuce gaba, da sauri ya kuma bin bayan ta, amma bata tsaya ba saida suka ƙarasa bakin motar sa, yayi saurin buɗe mata ta shiga, sannan shima ya zagaya ya shiga, yana shiga ya tayar da motar yaja su,
Duk da haka bata kula sa ba har sukazo inda zasu sauka, sannan ya fito ya buɗe mata ta fito, cike da takunta da ta saba take takawa har suka shiga cikin gidan, babban falo ne da yaji duk wani abu da ake buƙata amma bana ƙasar nan ba,
Kujera ta samu ta zauna ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana girgizawa,
Da sauri shima yazo kusa da ita ya zauna, yana ɗan leƙen fuskar ta, ƙasa ƙasa yace; "Hajiya Dannar lafiya kuwa naga sai faman haɗe rai kike nifa bana son ganinki a irin wannan yanayin wallahi tsorata ni kike, bana son masifa daga cewa kizo sai kuma kizo kina cin magani irin haka, yana maganar yana sake leƙen fuskar ta, amma duk da haka bata sauya launin ta ba,
Hannu ta miƙa masa, batare da ta kalle sa ba,
Da sauri ya miƙe tsaye ya zura hannu a aljihu ya zaro wasu bandir ɗin kuɗi in dollars ya ɗora mata a kai,
Kallon kuɗin tayi tare da miƙewa tsaye, sai kawai ta watsa masa shi a jiki, da sauri ya kwashe su ya kuma zura hannu a aljihu ya ƙaro guda biyu sannan ya haɗa mata guda uku sai loƙacin ta karɓa shima a wani wulaƙan ce tana wani ya tsina fuska kamar ta karɓi kashi,
"Wane aiki za'ayi maka yanzu? Ta faɗa batare da ta kalle sa ba.
"Wani shu'umin murmushi ya saki yana kallon ta, yace; "Video"
"Angama" tana faɗar haka, tasa kai zata bar falon sai kuma ta ɗan dakata, batare da ya juyo ba, tace; "kafin naje ka turo min address ɗin" tana faɗar haka ta fice daga falon.
Bayan ta yabi da kallo yanayin wata iriyar miƙa yana lashe baki, duk sanda ya haɗu da hajiyar nan sai yaji yana fillings ɗin ta, amma yasan ko hauka yake baza ta taɓa yarda da shi ba, gwanda yaci gaba da lallaɓata har ya shawo kanta wani loƙacin yanzu dai taimakon ta yake nema dole yabi ta a hankali su rabu lafiya.
Shima fita yayi daga falon amma yana fita bai ganta ba, har ta bar wajen.
Shima motar sa ya shiga ya bar gidan.....
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
*Ɗan Ijje's hause*
Zaune suke duk sunyi jigum jigum kowa ya rafka uban tagumi, Hajiya Khattume da kuma Hajiya Jannat, sai yaran su maza da mata, da kuma wasu ɗaiɗai ku daga jikokin gidan, tun daren jiya suka nemi mai gidan su suka, tun suna jiran dawowar sa a daren har suka cire ran dawowar sa, gashi yanzu har yamma ta kawo kai, duk inda suke tunanin zasu jishi basu jishi ba, gashi kuma basa so su fitar da maganar har wasu suji,
Suna zaune kam kamar daga sama suka ganshi ya shigo waya manne a kunnen sa yana waya, yana ta faman dariyar sa, hankalin sa kwance.
Duk miƙewa sukayi a kusan tare cike da mamaki, yayin da fuskar su kuma ta ɗan saki daga damuwar da suka tsinci kansu,
Guri ya samu ya zauna yana waya amma idanun sa yana kan su, katse wayar yayi yana saka ta a aljihu,
"Haba Alhaji ina ka shiga tun jiya gaba ɗaya hankalin mu ya tashi,
Ɗan murmushi yayi, yace; "kuyi haƙuri ban sanar daku ba, wallahi wata fitar gaggawa ce ta kamani, ku kwantar da hankalin ku, sannan kuma ga wani abun farin ciki da yasame mu, BILAL zai dawo har magana munyi dashi,
Gaba ɗaya ruɗewa su kayi su na tambayar sa, a ina?
Dariya yayi yace; "wanda ya ɗauke sa ne suka kira suka ce indai ana buƙatar ƴaƴan nan to a tura musu billoin goma sha biyar......
Ai bai gama rufe baki ba gaba ɗayan su suka zaro ido cike da mamaki,
Jannat ce tace; "What...? Me kake nufi yanzu akan yaron nan ka tura musu 15 billoin bafa million ba billoin kuma shabiyar amma hankalin ka yana kwance meye hakan kayi kana kwa cikin hankalin ka, yaron da bashi da uwa ma, ka barshi su kashe shi mana sai me idan ya mutu amma kayi mana asarar kuɗaɗe masu yawa har hak.......
Tassssss...Tasssssss...Tasssssss.......... Kawai ƙarar saukar maruka kake ji ta ta cika falon, saida ya sauke mata kusan guda goma sannan ya dakata, waɗanda basu aka mara bama saida suka dafe kumatun su.
"Jannat...! ya kira ta da ƙarfi cikin daka mata wata uwar tsawa me tafe da tsananin ɓacin rai,
"Kuɗin uban ki ne ko na uwar ki? Su suka bani kuɗin ko su suka nema min, ƴar gidan matsiyata ko angaya miki wannan wani abunne a cikin kuɗaɗe na, to ki sani kamar kece da nera dubu ki cire biyar a ciki haka waɗannan kuɗaɗen suke a waje na, ba komai bane, da kike cewa uwar sa ta mutu shine ya mutu, to kaf ƴaƴana nafi son sa akan sa zan iya bada raina, kuma zan iya rabuwa da kowa in zauna dashi, dan haka duk wanda baya son shi to nima bazan taɓa son shi ba har abada, dan haka minti biyar na baki, kizo ki fice min daga gida kuma bance ki ɗaukar min ko tsinke ba tunda ba uban ki ne ya kawo ki da su, loƙacin ki ya fara daga yanzu idan mintuna suka cika baki fita daga gidan nan ba, saidai a fitar da kasusuwan ki, munafuka ashe duk son da kike nuna masa ba ƙaunar sa kike ba mutuwar sa kike jira...
Wayyo Allah na! Na shiga uku! Wallahi Alhaji ba haka bane ko kaɗan wallahi sharrin sheɗanne duk abun da na faɗa ƙarya nake bansan ma na faɗa ba, ka gafar ce ni, ta zube a gaban sa tana kuka wiwi kamar ranta zai fita,
Matsawa tayi daga wajen, ya nufi wajen kayan wuta, wata wayar wuta ya jawo ta ƴar yawo, ya nufo ta, da duk a tunanin ta da wasa yake batai tunanin zai dake ta ba, amma da taji saukar ɗaya saida fitsari ya kuɓuce mata, batasan loƙacin da ta miƙe ba, ta nufi waje ko mayafi babu a jikin ta, a haka ta fita har can waje.
Sauran kuwa gaba ɗayan su shan jini jikin su sukayi harda masu karkarwa dan gani suke kamar yana gamawa da ita zai dawo kan su,
Juyowa yayi a fuska ce cikin ɓacin rai yace; "Daman duk bamai ƙaunar sa a gidan nan, duk munafukai ne ku, ita da take nuna tafi kowa son shi ga abun da tace ina ga ku, da bakwa nuna hakan, me Bilal ya tsare muku a gidan nan, me yasa bakwa son shi eh...? Ya ƙarasa maganar cikin daka tsawa, ƙara rikicewa sukayi suna neman hanyar ɓuya,
Saura kaɗan ya rufe su da duka, amma sai yayi saurin saita kansa, amma dai ya firgita su iya furgitawa, babu wanda bai tsure ba, dan sun sanshi da masifa amma basu taɓa ganin yayi irin ta yau ba.
Zama yayi yana sauke ajiyar zuciya, "bani ruwa"
Ai kusan gaba ɗayan su suka nufi fridge suna rige rigen ɗaukowa, amma mutum biyu ne sukayi nasara suka kawo, masa ƙin karɓa yayi ya tsaya yana kallon su, Ma'aruf me da Hafsa suka miƙa masa ruwan, hannun Ma'aruf sai faman karkarwa yake, dan a kwai shi da tsoro,
Hannun nashi yabi da kallo, sai kawai yaji tausayin su ya kamasu, maimakon ya karɓi ruwan sai kawai ya jawo hannun Ma'aruf gaba ɗayan sa, ya ɗora sa kan cinyar sa, ita kuma Hafsa ya jawo ta ya zaunar da ita gefen sa, kallon Ma'aruf yayi yace; "wannan tsoron fa sai kace kaga dodo,
"Dad ai kaga fa yanda ka koma kasan dole mu tsorata,
"Sorry raina ne ya ɓaci, amma ai kun san bazan iya dukan ku ba, juyawa yayi ya kalli Hafsa da ta sunkuyar da kai, "Kema matsoraciya ce har haka,
Ɗan murmushin ƙarfin hali tayi, amma fa duk da haka wallahi a ɗan tsorace take dashi,
Nan ya ringa jansu da hira kamar bashi ne yanzu ya canza kamanni ba, amma har ya sauko, kuma duk dan saboda farin cikin yaran sane, amma haushin Jannat da yake ji har yanzu yana jinsa aran sa, a fili baza kace yana da wata damuwa ba, yanda yake nunawa yaran, amma a baɗini ba haka bane, ranshi in yayi dubu duk yaɓaci ɗaya bayan ɗaya, amma ya danne saboda nasu farin ciki, haka kwa suka zauna, harda cin abinci yana bawa wasu a baki suma suna bashi tuni ya mantar da su duk wani abun da ya faru a yanzu.........,
Bayan ganawar su ne ya ce mu su bari yaje ɗaki ya ɗan huta,
Ɗakin sa ya nufa tare da rufewa yasaka key a jiki, a gurin ya tsaya tare da jingina da jikin ƙofar yana dafe ƙirjin sa, yana runtse idon sa, shi kaɗai yasan halin da yake ciki,
Ya daɗe a gun yakasa tashi, can kuma kamar an tsikare sa ya miƙe tsaye da sauri, katifar sa ya ɗaga, ya kuma yaye wani abu dake kan karagar gadon, wani abu a ƙulle ya ciro sai ya kunce ta, saiga wata jaka baƙa me ɗan faɗi bata da wani girma sosai, guri ya samu ya zauna gefen gadon a hankali ya shiga zuge ta, wasu tsofofin hotuna ya zaro daga jiki, hotunan wasu yara ne ajiki sai wata babbar mata me ciki, da wata sarƙi, da abun gashi, haka dai tarkace fal cikin jakar, ya daɗe a gun yana kallon abubuwan kafin daga bisani ya haɗe su ya mayar inda ya ɗauko, ya kuma komawa ya zauna,
Miƙewa ya kuma yi ya ƙarasa kusa da ƙatotan hoto dake jikin bangon ɗakin, hoton Bilal ne, yana sanye da ƙananun kaya a kwance ya rungume wani fillo me shap ɗin heart hoton yayi kyau sosai ya ɗan ɗago da kansa gashi ya ɗan zuzzubo masa gaba kaɗan,
Hoton ya ƙurawa ido ƙwalla na cika masa ido "Bilal ka yafe min ina cutar dakai da yawa na rabaka da mahaifiyar ka gashi ni yanzu nakasa riƙe ka, nakawo ka inda ba'a sonka babu wanda yake son ka, sai ni kaɗai, gashi yanzu sakaci na yasa ansace ka, duk ƴaƴa na babu wanda aka ɗauka sai kai kaɗai shin kode duk duniya ma, bata son ka, ina zanga mahaifiyar ka inne mi yafiyar ta, ina zan ganta? Ina take? Ina ta shiga? A faɗin duniyar nan na neme ta na rasa bansan yanda zanyi da alhakin ka ba, ta mutu ko tana raye......??
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
*Hajiya Dannar*
Kamar yanda ta tsara haka kuwa tayi kwanan ta biyar a London ta dawo Nigeria, bata wuce meduguri ba ta wuce Kano ta hanyar address ɗin da Safwan ya tura mata, ta nan tabibiya ta sauka a unguwar da ya kwatanta mata,
Saukar dare tayi dan haka ta wuce hotel ta kwana, ba tashi ba sai wajen ƙarfe sha ɗaya, tana tashi ta shiga wanka bata daɗe ba ta fito, wata shegiyar dogowar a tamfa me tsadar gaske, kalar ta, yellow ce sai adon jikin ta da a kayi da baƙi tayiwa farar fatar ta kyau sosai sai ta kuma fito da hasken ta, zama tayi ta tsantsara kwalliya manyan idanun ta suka ƙara fitowa da tasaka kwalli sai suka kumayin haske, taci uwar ɗauri ya mata kyau shima ta ɗauko wani glass baƙi ta ɗora a idon ta, bayan gwala-gwalan dake jikin ta, ta ɗau jaka da takalmi, dama ƴar jakar da tashi go da ita kayanne kaɗai a ciki, dan haka ta rataya ta kayan da tazo da su kuma ta bar su a gun ta fito waje.
Ɗai ɗai take takun ta, ta fito wajen harabar hotel ɗin, duk inda tayi mutane sai kallon ta suke idan ta gifta kwa ta wajen aka daɗe baka dena jin ƙanshin turaren ta ba, daman tun a daren jiya ta kira drivern ta da yazo.
Tana fitowa kuwa ta hange sa can nesa, shima yana ganin ta ya taso yazo kusa da motar ya buɗe mata, tana ƙarasowa ta shiga, ya rufe, sannan shima ya zagaya ya shiga yasu suka bar hotel ɗin.
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
*R, K, D, UNIVERSITY KANO*
Ameela ce da Barazana suka fito daga lecture, dan haka gurin hutawa suka nufa suna jiran fitowar sauran, suna hirar su, suna ta dariya abun su.
Wata ƴar matashiyar budurwar nan ta ƙaraso gurin, fuskar ta ɗauke da murmushi,
"Assalamu alaikum"
Ɗagowa sukayi suna kallon ta dan basu ga tahowar ta ba, saida tayi musu magana, amsa mata sukayi suma fuskar su a ɗan sake.
"Zan iya zama anbani izini?
Murmushi Barazana ta ɗan saki tare da cewa; "Izini kuma? Har sai mun baki, gurin da bana Ɗahiru da Sa'adu ba,
Murmushi ta kumayi ta ce; "Me yayi zafi haka duk da bansani ba ina tunanin dai sunan iyayen ku ki ambata a haka gaya ba sakayawa, ina laifin ma kice Baba Ɗahiru da Baba Sa'adu,
Dariya sukayi mata, Ameela tace; "wa yace miki Baba muke ce musu sai kace munzo daga can garin, au ashe fa su o'o daga can ake,
Haɗe rai Barazana tayi tana kai mata dukan wasa da littafin hannun ta,
Dariya tayi tace; "kai sisters har kun ban dariya wallahi, sai kace wasu ƙananun yara, nidai ba faɗa nazo na haɗa ba,
Ɗan nutsuwa sukayi kaɗan, amma duk da haka Barazana bata bar hararar Ameela ba.
Ameela ce tace; "baiwar Allah daga ina mun baki izinin ga guri zauna.
Ta matsa mata gefen ta, zama tayi, har yanzu fuskar ta bata ɗauke daga murmushin da take ba,
"Sunana Faheema" wallahi kawai kuna burge ni ne, tun ba yanzu ba nake son in muku magana ina tsoron kar naje, a cire min wata gaɓar a jiki na, yanzu ma dan naga baku da yawa shiyasa nazo Allah yasa dai zaku aminta dani..?
"Kan Bala ba gashi to me kika maida mu, cewar Barazana,
"Masu cirewa mutane gaɓoɓi su siyar, cewar Ameela.
"Laaa kunji ku wallahi ba haka nake nufi ba, da wasa nake muku,
"Barazana tace; "a'a wannan maganar taki babu wasa a cikin ta sai zallar lagwadar gaskiya, dan haka bari inje inkira sauran sai kiga aiki da cikawa, ta ƙarasa maganar tana miƙewa kamar zata tafi, Faheema tayi saurin riƙeta tana dariya, tana bata haƙuri...
Suna cikin hakan ma su Beenish suka nufo wajen, a gajiye suka ƙaraso wajen,
Babyn baby ta langwaɓe ta faɗa kan Ameela tace; "ƙawa nagaji da yawa wallahi tun ina ɗauka har na dena ɗauka, gashi cikina yana tayin wani abu,
Shafa kanta Ameela tayi tace; "to auta me kike so, ko de goya ki zanyi, mu tafi gida,
Kai ta ɗaga mata alamar "Eh"
"To shikenan, Zee bamu mayafin ki mu yi goyo.
"Kun daɗe bakuyi ba, ke dalla tashi daga nan, wallahi sai na gayawa Baby kar ya sake ya kula yarinya, babu abun da ta iya kuma bakya son aiki da karatu duk sai na gaya masa, turo baki tayi kamar zatayi kuka, ta fara shirin tashi a hankali.
Ameela ta mayar da ita tace, ke rabu da ita, kishi take yi, kuma saidai ɗan baƙin ciki ya mutu, nan gani nan bari ɗumamen tuwon mayya,
"Wannan pha, Aunty Babba ta zuguri Barazana tana tambayar ta ƙasa ƙasa.
"Badai kyau munafurci" cewar Beenish da take gefen Aunty Babba tana jinsu itama gajiyar ce ta hana ta magana,
Barazana ce tace; "yauwa dama jiran ku nake kuzo muyi mata rufdugu zagin mu take, tana ce mana makasa masu cirewa mutum gaɓ.......
Shiru tayi bata ƙarasa ba sakamakon idon ta da ya gano mata abun da take tunanin kode mafar ki take.
Jin shirun ta yasa suka kalle ta Aunty Babba tace "wai da gaske kike? ganin hankalin ta baya gurin su, hakan yasa wasu suka kai duban su ga inda suka ga tana kalla,
A kusan tare duk suka miƙe tsaye cike da mamaki.
Wani irin ƙayataccen murmushi ta saki da ta saba yin a mafi yawan cin loƙata tanayi tana tunkaro su cikin takun ta na masu kuɗi...✍️✍️
My WhatsApp number 08124226526
[3/5, 11:51 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________
*_episode 18💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
Bissmillah.....✍️
___A kusan tare duk suka miƙe tsaye cike da mamaki.
Wani irin ƙayataccen murmushi ta saki da ta saba yin a mafi yawan cin loƙata tanayi tana tunkaro su cikin takun ta na masu kuɗi.....
A dai-dai gaban su ta tsaya, hannu ta sa ta zare glass ɗin dake idon ta, kyanta ya ƙara fitowa, tana niyar yin magana kenan.
Ta ɗaga mata hannu tare da cewa; "me kika zo yi min kuma, waye ya baki address ɗina, bana son jin ko wacce magana dan Allah ki juya ki tafi inda kika fit......
"A'a hakan ba dai-dai bane bai kamata ba, uwa ce fa, kamata yayi ki fara tsayawa kiji da me