Iso yayi masa zuwa cikin gidan, suna shiga ya ɗaga murya, ya ce; "Kubra kawo mana tabar ma munyi baƙo!
Daga can cikin ɗaki ita ma ta ɗaga murya tace "To ganin nan!
Ba jimawa ta fito daga ɗakin hannun ta ɗauke da tabarmar, in duka ta shinfiɗa musu, suka zauna, itama zama tayi daga ɗan gefe suka gaisa da baƙon sannan ta tashi tace bari a kawo mishi ruwa, ta faɗa tana miƙewa daga gurin....,
Da sauri wata ƴar budurwa tabi bayan ta inda zata ɗebo ruwan, cikin ƙasa ƙasa da murya tace "Uwar Abu wannan saurayi ga daga ina? Baƙon ki ne?
Ɗan hararar ta tayi tace "ke matsala ta dake gulma kullum cinki take, to nima ban sanshi..
Ɗan ɓata rai tayi ta ce; "kai Uwar Abu daga tambaya nifa ba gulma nake ba, kawai nagansa kalar ƴan birni ne kuma gashi yazo gurin ki, na sani ko Abu ce ta aiko sa...
Dungure mata kai tayi tace "Ni matsa min in wuce in son ji kike jeki tambaye sa mana nima basan shiba, kinji min ƴa daga zuwan mutum zaki wani tsare ni da tambaya, tana faɗan haka tayi wucewar ta ta bar ta agun...
Turo baki tayi tana ƙara kallon baƙon tana gunguni ƙasa ƙasa, tare da komawa wani guri ta zauna tana facing ɗin sa yanda zata fi kallon sa da kyau...✍️✍️
Yauwa free pages ya kusa ya ƙare, kowa ya fara shirin payment🤗
*Banjuuuuuuuu kina ina ki fara taru ko da biyar biyar ne dan sai na karya miki record ah to siye dole Aheeee😎😎*
____Turo baki tayi tana ƙara kallon baƙon tana gunguni ƙasa ƙasa, tare da komawa wani guri ta zauna tana facing ɗin sa yanda zata fi kallon sa da kyau...
Uwar Abu na ƙarasawa ta tsugunna ta ajiye musu ruwan tare da basu waje ta koma ɗakin ta.
Malam ne ya kuma gyara zama yana tura masa ruwan tare da cewa yaro sha mana, ya faɗa yana zuba masa idanu dan ya ƙagu yaji meke tafe da yaron.
Ɗan murmushi Khalifa yayi yana ɗaukan ruwan ya ɗan kurɓi kaɗan ya ajiye tare da gyara zaman sa, yana fuskantar sa da kyau kamar yanda shima yake kallon sa,
"Malam daman abun dake tafe dani abunne me mahimmancin gaske duk da bansani ba a wane matsayin zaka ɗauki maganar ba, an bani address ɗin gidan ka sakamakon wanda nazo nema ance baya garin saidai inzo wajen ka tunda mahaifin ka ne.
Jin abun da ya faɗa yasa Malam saurin haɗe rai laƙaci guda yanayin fuskarsa ya sauya launi.
Khalifa bai fahimci komai ba yaci gaba da cewa; "Ban sani ba ko kasan farkon zancen, nazo neman wata jaka ne dake hannun sa wacce ɗan uwanka yabawa mahaifinka ajiya, to yanzu buƙatar jakar ne ya tashi ake neman sa, dalilin da ya kawo ni garin kenan kuma akace ya tashi saidai inzo in sam...
Shiru yayi bai ƙarasa ba sakamakon ganin Malam ya mike tsaye tare da ɗaga masa hannun cike da tsantstsar ɓacin rai yace "Dakata da wannan banzar maganar taka tun kafin in irga maka uku ka tashi ka fice min daga gida in ba haka ba kuma sai ranka yayi mummunan ɓaci sai kayi danasanin zuwan ka garin nan.
Zunbur shima Khalifa ya miƙe mamaki al'ajabi tsoro da fargaba duk a loƙaci ɗaya suka saukarwa masa take wani irin gumi ya shiga tsatstsafo masa daga cikin kansa take jikin sa ya fara ɓari, muryar sa cike da rauni kamar me shirin fashewa da kuka yace "Malam dan Allah kar kace haka kar kamin haka duk da bansan me yasa kace haka ba bansan me yafaru ba amma dan Allah ka ka sanar dani meke faruwa? Kar ka koreni, ka taimake mu kamar yanda Allah ya taimake ka, wallahi matar nan tana cikin mawuyacin hali dole sai da taimakon ka zamu iya samun wasu abubuwan ka taimaka ka gaya min inda yak...
Kafita nace maka.!
Malam yakuma katsesa da tsawa me ƙarfi da saida tasa mutanen gidan leƙowa suga meke faruwa,
"Wallahi wallahi ka kuma cewa tak a gunnan zakaga me zai faru bana son jin komai daga gare ka kuma nima bazan faɗa maka koman ba kafice min daga gida kada ka kuma dawomin cikin gida har abada kafice nace!
Khalifa duk da haka bai daddara ba ya kuma yin yunƙuri zaiyi magana ya kifa masa mari fuskar sa cike da ɓacin rai yace "wai kai wane irin taurin kaine da kai nace ka fita ko! Ka fita nace bazan faɗa ɗin ba ka fita!
Tunda Khalifa ya dafe kumatunsa bai kuma cewa komai ba kamar mutum mutumin domin gaba ɗaya ma ji yake kamar ba a duniyar yake ba, ko inda takamin sa yake bai kalla ba a haka kawai ya shiga tafiya baisan inda yake saka ƙafar sa ba.
Yarinyar dake laɓe (wacce take tambayar Uwar Abu baƙon daga ina yake) da gudu ta fito tayo wajen takalman sa ganin yana shirin fita babu takalmin, saidai ta na tsugunnawa zata ɗauka Malam ya daka mata tsawa yace idan kika kuskura kika taɓa to idan kika bishi kar ki kuma dawo min cikin gida, sak tayi agun ita bata ɗauka ba kuma bata fasa ɗauka ba, hannun ta ya tsaya a tsakiya.
Uwar Abu ce ta ƙaraso gurin itama cikin sauri tace "Malam wai meke farune meye hakan? Ko ma meye ai kamata yayi kabari yasa ka takalmin s...
Wani banzan kallo ya watsa mata da yasata haɗeye guntun maganar ta tunda daman bataji me yake faruwa ba,
Kowa na gidan saida yazo gurin cike da mamaki suka tsaya suna kallon Malam a yanayin da basu taɓa ganin sa ba, mutumin da ko magana da ƙarfi bai fiya yiwa mutane ba amma yau shine harda irin wannan tsawar ga kuma ɓacin rai dake danƙare akan fuskar sa da ta nuna sosai, mutum ne wanda bai fiya faɗa sosai ba inka ga yayi faɗa ko fushi to ba ƙaramin abu bane zaisaka shi yi, ganin hakan yasa duk suka shiga taitayin su babu wanda yayi yunƙurin ƙara tambayar sa ko yin wata magana suka zuba masa ido har ya juya cikin fushi ya shiga ɗakin sa tare da bugu ƙofar da ƙarfi.
Khalifa tafiya yake kwai saidai da yaji ƙafafunsa sun kasa ɗaukar sa yasa shi zamewa jinkin wani gida yayi zaman dirshen a ƙasa tare da haɗa kai da gwiwa baisan loƙacin da hawaye ya shiga sauko masa ba ji yake kamar ance bazai taɓa cikawa matar nan alƙawarin da ya ɗaukar mata ba, yanzu da wani ido zai koma gida ya kalle ta yace ba'a dace ba ya faɗa mata irin korar wulaƙancin da yayi masa gashi dare yayi baisan ma inda zai dosa ba daga nan, abun ba ƙaramin tsaya masa arai yayi ba to meyasa Malam zaiyi masa haka me yasa bazai faɗa masa ba me yasa yanayin sa ya sauya sosai daga jin maganar me yake faruwa?
Sai faman tambayoyi yake jerowa kansa da bashi da amsar su,
Inuwar abu yaji akansa da sauri ya ɗago dan ganin ko waye, mace ya gani akansa a tsaye hannun ta riƙe da takalmansa sai yanzu ya tuna ba takalmi a ya fito, yarinyar ce ta biyo shi ganin baban nata ya shiga ɗaki.
Kallon ta yake itama zuba masa idanu tayi tana kallon sa, saida ta gama kallon nasa sannan ta tsugunna ta ajiye masa takalman sa tare da zama a gaban sa, tana kallon sa tace; "kayi haƙuri da duk abun da mahaifina yayi maka wallahi ba halin sa bane, naji tattaunawar ku saidai bangane ba kuma bansan komai ba saidai idan baza ka damu ba idan zaka kuma yi min bayani indai nasani to ko ta wace irin hanya ce zan taimaka maka ina fatan banyi maka shishshiga b?
Jinjina mata kai kawai yake sosai ya ɗanji sanyi da zuwan ta da kuma abun da tace masa,
"In Sha Allah zan taimmake ka kar ka damu ka sanar dani dan Allah,
"Saida yaja ɗan loƙaci kafin yace "kin san inda kakanki yake ma'ana mahaifin mahaifinki?
Shiru tayi tana nazarin kafin ta ɗan numfasa tace "gaskiya bansan inda yake ba da gida ɗaya muke zaune dashi a yanda babar mu taban labari saidai tace rana tsaka kuma yabar gidan aka neme sa aka rasa a cikin garin amma dai mahaifin mu yasan inda yake saidai yaƙi gayawa kowa dan ko antashi za'a neme sa sai yace a daina yana zaune lafiya kuma zai dawo tun anayi har akadaina daga baya ma idan aka tambaye sa sai yace ya rasu amma su basu yarda ba, saidai babu yanda aka iya dole aka haƙura akabar zancen tun loƙacin... Kaji iya abun da nasani kenan saidai kayi haƙuri ni yanzu zanci gaba da bibbiyar lamarin nasa zan gano gaskiyar lamarin in Allah ya yarda amma sai kaban loƙace yanzu ka tafi in ka dawo nan da wasu watannin duk yanda ake ciki zan sanar da kai.
Wani dogon numfashi yaja dan ba haka yaso ji ba, amma ya zaiyi dole ya ƙara gwadawa ta hannun ta saidai watanni da ta faɗa yayi masa nisa.
"Tom nagode da hakan ma amma watanni da kika ce basuyi nisa na, in kina da waya kiban number ki sai in ringa kiranki inajin yanda ake ciki tunda kinji dai abun da mahaifin ki yace kar na kuma dawowa duk da bana jin zan iya haƙura ɗin,
"Hmm gaskiya banda waya amma bari inje gida in ɗauko biro da takarda kaban taka idan nasamu waya sai in kiraka, kuma watanni da nace bawai dole sai abun yakai wata ba kawai dai bansan yanda lamarin zaizo bane zan samu abun da wuri ko bazan samu ba, amma yanzu indai da number to duk yanda muke ciki zakaji ni da wuri.
"Ok thanks a lot, yanzu kije ki ɗauko ɗin in baki.
Tashi tayi da sauri tace "to ka jirani dan Allah ko da zakaga na daɗe dole sai na saci hanya zan fito, ai anan zaka kwana ko.
Ɗaga mata kai kawai yayi dan besan me zaice mata ba, shi da ba wanda ya sani a garin a ina zai kwana.
Harda gudu gudu take haɗawa wajen tafiya tana tafiya tana waigen sa, dan tausayin sa takeji hakannan.
Tana ƙarasawa gidan ta shiga ciki da saurin ta, turus tayi ta tsaya ganin duka ƴan gidan ma tayi a tsakar gida ga mahaifin ta da saida ta firgita da suka haɗa ido, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa take taji zuciyar ta ta tsinke shikenan yau kashin ta ya bushe gashi kuma ta cewa saurayin ce ya jira ta yanzu ya zatayi idan aka hanata fita da ta sani ma cewa tayi ya faɗa mata ta haddace akanta amma batayi wannan tunanin ba a loƙacin.
Tana wannan tunanin taki saukar bulala akan ta, ihu ta ƙwala tana shirin juyawa ta fita ya jawo hannun ta, ɗakin sa kawai yayi da ita, tana ihu amma babu wanda ya dakatar da shi har ya shiga da ita ya rufo ƙofar, ihun kukan ta kawai kake jiyowa saida ya gaji da dukan ta sannan ya rubu da ita tare da fitowa daga ɗakin sannan ya ƙulle ɗakin ya samu guri ya zauna abakin ɗakin yana maida numfashi...
$$$$$$$$$$$$$$$$$$$
*Barack*
Babban Barack ne da ya amsa sunan sa sai cike yake da sojoji ta ko ina kowa nayin aikin gaban sa duk da kasancewar ba masu laifi bane a ciki amma kowa riƙe da binduga wasu kuma tana saƙale a jikin su,
Wasu kuma suna bakin gidajen dake cikin gurin na manyan ma'aikatan su,
Tunda Rk ya aika su su ɗauko masa su ya wuce Barack tunda yaje ya kasa tsaye ya kasa zaune yana cikin wani falo da ya gaji da haɗuwa daga gani dai nasane duba da yanda hotunan sa dake manne a kowa ne kusurwa bangon falon, jiran ƙarasawar su kawai yake daga ƙarshe ma fitowa yayi daga cikin falon ya fito hara bar Barack ɗin, nan ƴan sandan dake bakin part ɗin sa suka shiga sara masa suna tambayar sa abun da yake buƙata ɗaga musu hannu kawai yayi alamar ba komai, ya daɗe yana jiran su kafin su ƙaraso, suna shigowa ya zubawa motar tasu ido baya ko ƙiftawa.
Da gudu suka firfito tare da fito da mutanen da suka taho dashi yaran Bulama duk tsugunnar da su sukayi agaban, batare da sunce masa komai ba duk da saida suka tsorata ganin sa a tsaye a bakin wajen dan sai yanzu ma suka gane sunyi babban kuskure da basu taho da yaran nan ba duk da saida yayi musu gargaɗi akan su ɗauko su,
Duka tsaye sukai suna sara masa tare da sada kansu ƙasa babu wanda yayi gangancin haɗa ido dashi kuma basu ce komai ba.
Harɗe hannun sa yayi a chest ɗin sa yana aika musu da wani mugun kallo sai ya kalle su sai ya kalli mutanen dake gaban sa, jin sunyi masa shiru yasa ransa ya kuma ɓaci yace su kawo masa mata amma yaga sun kawo masa maza and then they didn't say anything to him.
Ganin gurin yayi shiru kuma sun san su yake jira suyi masa bayani yasa ɗaya daga cikin su yayi ƙarfin halin cewa "we are so sorry Sir, there was a problem and we were unable to pick up the ladies, nan suka shiga bashi labarin abun da ya faru da suka je ɗin saidai kuma basu kai ƙarshe ya dakatar da su,
Cikin tsawa yace musu ya jefa musu tambaya"where are they? What did I tell you, I told you to bring me the stupid girls, you brought me the men, why?
Yayi maganar yana zazzare musu idanu.
Sorry Sir!
f**ck you then I don't care about that just go back and take me the bastard girls, I'll gave you ten minutes to bring them, if not I'll kill you.
Dan kunje sunƙi buɗe ƙofar why baku fasata ba zaku zo min wannan silly maganar eh? Why?
Babu wanda ya kuma magana haka suka juya cikin sauri suka kuma komawa motar suka bar Barack ɗin.
Kallon mutanen dake gaban sa yayi ya watsa musu kallon banza kawai ya juya saida yaje bakin ƙofar da zai shiga falo yace da wani soja yaje ya kwashe su a ƙulle su.
Yana faɗa ya shige ciki yana shiga ya hau cire kayan jikin sa yana watsar da su a ƙasa sannan ya samu kujera ya zauna yana maida numfashi sosai zuciyarsa take masa zafi ya rasa dalili inbai hukunta yaran nan ba hankalin sa bazai taɓa kwanciya ba.
"Moohad!
Ya ƙwalawa wani kira da sauri ya amsa yana fitowa daga wani ɗaki, gaban sa ya ƙaraso yana kallon sa danjin me zaice,
"Bani ruwa" kawai yace da shi,
Zuwa yayi ya ɗauko masa ruwan ya buɗe masa ya miƙa masa, yana karɓa ya kafa kai bai tsaya ba saida ya shanye shi tas ya jefar da robar.
Moohad ne ya zauna gefan kujerar yana kallon sa kafin ya ɗan numfasa yace "ya kamata kaman ta da yarannan koda zaka musu wani abun kabari saida daga baya yanzu muyi abun dake gaban mu, muna fa da aiki sosai bai kamata ace mun zuba ido mun bar maganar Sir SMA yakama muyi gaggawar gano inda yake da kuma waɗanda suka ɗauke sa amma ka tsaya kan..
"Moohad! Ya kirasa da kakkausar murya tare da miƙewa daga gurin ya nufi ɗaki.
Moohad bai kuma magana ba yasan me yake nufi da kiran sa da yayi dan haka sai ya tashi ya fice daga falon ya fito waje yana mamakin ganin yanda yaƙi nuna damuwar sa sosai akan ɓatan SMA ɗin baisan me yasa ba, ga abun da ya dace yayi amma ya tsaya zai biyewa mata har yana ɓatawa kansa rai akan su.
Shi kuma yana shiga ɗaki ya faɗa kan gado tare da jawo wayar da dake gefe daga kwancen ya dannan kira tare da saka wayar a handsfree bugu uku aka ɗauka shiru yayi bayan ya ɗaga,
Ana ɗagawa yace ki same ni a ɗaki right now, Yana gama faɗa kuma ya kashe.
Baidaɗe da kashe wayar yaji ana nocking baice komai ba kuma aka buɗe aka shigo,
Wata ƴar budurwa ce doguwa me dan jiki sanye take cikin kayan sojoji ko mayafi babu a jikin ta ta ɗaure gashin kanta kawai hannun ta kuma ɗauke wasu takaddu,
Tana shigowa ta tsaya saida ta gama ƙarewa surar jikin sa kallo harta shagala ma saida taji yaja wani dogon tsaki yasa tayi saurin ɗauke kanta tana ƙarasowa kusa dashi ta samu gefen gadon ta zauna.
"Na same ka lafiya?
Shiru bai motsaba kuma bai bata amsa ba.
Daman tasan ba amsar zata samu ba musamman da taga kamar ransa a ɓace yake, memakon ta ajiye masa a gefe saita ɗora masa takaddu akan ƙirjinsa, har yanzu bai kalle ta ba, saida ta gaji dan kanta sannan ta miƙe tsaye tana cewa ni zan wuce gida duk wani bayane yana ciki abun da baka gane ba sai ka kirani