x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - SU WAYE SU

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 145

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
inda muke kuma bamu da hujjar kare kanmu, dole mu amshi hukunci zaman mu yazama abanza.

Dukan su jigum jigum sukayi kowa jikin sa yayi sanyi tare da tunanin rayuwar da zasu kuma faɗawa nan gaba, domin wannan rayuwar kamar ba zata zo musu da sauƙi ba,

Nan kowa ya shiga faɗar ta bakin sa suna ɗan tattaunawa de.....

Aunty Babba ce takai tashar labarai, tana kaiwa kunnuwan su na jiyo musu cigiyar da ake musu harda hotunan su loƙacin da suka juya baya suka ɗaga hannun su anan aka samu wani yayi musu hoto da basu san waye ba, tsayawa sukayi suna sauraron labaran...✍️
[3/5, 11:28 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________


*_episode 5💧_*


💧💦محمدالرسوالله...!💦💧

Bissmillah.....✍️


*News*

"A yau ranar Laraba an tashi da ɓatan ɗan gidan commission of police na jahar Kano KHAMIS ADAM IBRAHIM akan hanyar dawowar sa gida akayi kidnapping ɗin sa, to bincike kuma ya nuna ana zargin wasu ƴan mata da suka shigo garin bayan fafatawar da sukayi da ƴan sanda akan ɗan gidan Alhaji Ɗan Ijje da suka sace shi, bayan kamasu kuma suka ƙi yarda a kama su har sukayi nasara tserewa ƴan sanda aka rasa inda suke tode yanzu ga hoton ƴan mata kamar yanda kuke gani yanzu dai hukuma tana neman su ido rufe ga duk wanda ya gansu sai yayi saurin sanar da hukuma domin.........,

Ɗif tvn ta ɗauke sakamakon kashewar da aunty Babba tayi, tare da jan tsaki,

"Tabb babbar magana.. meye mafita?

"Mu miƙa kanmu...

Dukan su zuba mata ido sukayi cike da mamakin faɗar hakan.

"Beenish kinsan kwa me kika ce?

"Eh, Aunty Babba, ina ganin kamar hakan shine mafita, tayi maganar cikin sanyin murya,

Zee ce tace "Beenish baza'ayi hakan ba, wannan maganar bata taso ba kefe kike ƙarfafa mana gwiwa bai kamata wannan abun yasa ki fara karaya ba tun yanzu, idan muka miƙa kanmu bazasu taɓa yarda bamu bane saboda duk wata alama da zatasa a gane mune munriga da mun nunata, dan haka bazai yiyu mu nuna kanmu tun yanzu ba,

"Nima dai abun da nagani kenan idan mukayi haka zamu iya jefa kanmu cikin cakwakiya, suna da kuɗi duk yanda zasuyi su ɗora mana laifin zasu iya bazamu taɓa kare kanmu ba ko abun da mukayiwa ƴan sandan da kuma ɗauke sa da mukayi tun farko dole sai sun hukunta mu akan hakan....

Maganar ki gaskiya ce "Ameela, ko an ajiye maganar kidnapping bamu bane, amma dukan nasu shima laifi ne da kuma ɗauke shin da mukayi tun farko mun wahalar dasu, dan haka baza su barmu ba hakannan, cewar Babyn baby,

"Barazana tace "yanzu de ai babu wanda yaga fuskar mu, dan haka mafita itace zamu dena fita da motar mu sannan dole mu ringa ƙoƙarin rarraba kanmu kar mu ringa yawan nuna guri ɗaya muke,kar agane kanmu a haɗe yake, idan mun fita mu ringa raba hanya, ko ya kuka gani?

'Hummm to kusan hakanne mafitar amma kuma fitar muma ɗaiɗai kuwa zata yiyu kuna ganin babu matsala,

"To in bahaka ba ya zamuyi gwanda mu fara gwada hakan zuwa wani loƙaci kafin mu samowa kanmu mafita....

Nan dai sukai ta tattaunawa kowa yana kawo tasa shawara har suka tsaya a matsaya ɗaya, wajen ƙarfe goma duk suka tafi suka kwanta, kowa yana ƙara saƙa wasu abubuwan aransa,

***********************

*Waye Alhaji Ɗan Ijje..?*

'"Alhaji Ɗan Ijje, Babban mutum ne dan a ƙalla shekarun sa zasu iya kaiwa hamsin, mugun me kuɗi ne kuɗin sa har sun kai yawan dash kansa baisan adadin su ba, saidai kuma abun tambayar ga sauran mutane ƴan gari babu wanda yasan tsayayyiyar sana'ar saidai ya kasance mutum me yawan shiga wasu ƙasashen wataƙil a can yake gudanar da kasuwan cin sa shiyasa babu wanda yasan me yakeyi da har yatara maƙudan kuɗaɗen nan haka, Alhaji Ɗan Ijje ta wani fanni yana da kirki ya iya zama da mutane idan yaso kuma idan kabishi sau da ƙafa sannan yanaso yaga kowa yana jin tsoron sa, saidai yana da son kuɗi matuƙa sannan yana da son yara akan ƴaƴan sa baiƙi yasa a kashe mutum bama baya so a taɓama masa ƴaƴa, ya ɗaure musu gindi kowa yana abun da yaga dama acikin garin babu wanda ya isa ya takasu shiyasa suma suka taso basu da mutunci ko kaɗan, daga masu bin mata sai ɗan shaye shaye dan wasuma acikin su idan suka bushi iska sai subar ƙasar ma gaba ɗaya sai su shafe watanni kafin su dawo gida, acikin su kuma babu wanda yake sana'a makaranta ma kuma sai sunga dama suke zuwanta, yana da mata uku, Sabeena, Khattume da Jannat, yana da yara guda biyar, Shuraim, Bilal, Ma'aruf sai mata guda biyu Abeeda da Hafsa, Sabeena itace mahaifiyar Bilal da Shuraim, sauran kuma ƴayan Khattume ne matanne manya sai autanta Ma'aruf, ita kuma Jannat bata da ɗa ko ɗaya, shiyasa bayan rasuwarsa Sabeena sai ya auri Jannat to ita ta riƙe Shuraim da Bilal tun suna yara, dan ko da suka taso ma babu wanda yasan ba itace ta haife su ba, saidaga baya suka sani,

"Hajiya Jannat itama tana da zafi sosai dan daga Alhaji Ɗan Ijje a waɗanda ake tsoro acikin gidan sai ita amma duk zafin ta indai Ɗan Ijje yana gida to dole ta ajiye nata dan bata isa tayiwa yaransa maganar da bata dace ba ko ta zagesu ko ta ɗaga musu murya ba itama sai nata ran ya ɓaci, amma aganaban sa tana nuna masa matuƙar ƙaunar da takewa yaran sa musamman waɗanda take riƙewa yanda take nuna yanda take matuƙar ƙaunar su da nuna kulawar ta agare su kai kace ma itace ta haife su, musamman Bilal tafi ji dashi saboda shine ƙarami kuma Bilal yana da shiga rai daman agidan kowa yana yin sa musamman mahaifin sa yanda yake basa kulawa shima kamar shikaɗai ɗansa aduniya yafi ji dashi fiye da kowa acikin ƴaƴan sa, ba komai yasa kuma suke sonsa ba saidan cutar da yake da ita ta Sleeping skines(cutar bacci) kuma yana ɗauke da asma baida cikakkiyar lafiya de, dan ko abinci ma sai anyi da gaske yake cinsa in bahaka ba kuwa sai ya kwana ya wuni baici ba,

Khattume kuma salihar matace babu ruwan ta da shiga sabgar da ba'asata aciki ba, kuma tarbiya tana iya ƙoƙarin ta waje bawa ƴayan ta, saidai kuma ko ta yi mahaifinsu sai ya wargaza mata, abun na damunta, amma duk da haka suna ɗan jin maganar ta basa iya aikata komai agaban ta musamman matan tana matuƙar kula dasu dan ganin basu lalace tana basu tarbiya yanda iya yanda zata iya kuma alahamdulillah basa ɗauko mata magana ko aikata abun da ba daidai ba, saidai kuma suma basu da mutunci idan suka fita musamman idan suka haɗu da ƴaƴan talakawa akwaisu da wulaƙanci anan gurin amma sunsan mutuncin kansu, basa huɗɗu ma da samari saidai ƴaƴan masu kuɗi irinsu....ɗanyan yaron kuma Ma'aruf ya fitta zakka da sauran danshi akwaishi da fara'a ga barkwanci kowa nasane baya wulaƙanta mutane, ya iya zama da mutane bakamar sauran ba danshi ko masu aikin gidan zai iya zuwa ya zauna sutayin hira babu ruwansa, Yanzu haka matakin karatun sa yana level 2 inda yayyan sa kuma suke level 3 da ɗaya suka fisa, su kuma sauran Shuraim yagama karatunsa bama aƙasar yayi ba, amma yana gamawa mahaifinsa ya ɗauki babban kamfanin yabasa kyuta saidai kuma shi ba aikinne a gaban saba duniyanci yasa a gaba, Bilal kuma yafara karatu amma baigama ba ya dakatar dashi tun a level 2 saboda ko yaje sana'ar tasa yake ta bacci baya kwaso komai sai asarar kuɗi ake shiyasa daga baya kawai ya dakatar da karatun gaba ɗaya hakannan yake rayuwarsa ba aiki ba karatu,

Duk kuɗin Alhaji Ɗan Ijje bai yarda wani yajasa a mota ba duk inda zashi shikaɗai yake tafiya saboda bashi da yarda ko ɗigo, baya barin kowa ya raɓe sa bare yasan halin da yake ciki ba wanda yake jin cikin sa ko yasan wasu tsare tsaren da yake duk abun da zaiyi shikaɗai yake abun sa ko matansa baya sakawa a ciki, ƴanƴansa dai kowa yana da masu basu kariya saboda abun da suke yasan idan yasake su haka wasu zasu iya kawowa ƴayan farmaki ko su cutar dasu shiyasa duk inda zasu da bodyguard suke zuwa kuma Bodyguard ɗin ma ba ƴannan ba saboda bayason munafurci a lamuransa yasan kuma idan ya zuba ƴaƴan hausawa zasu iya basa matsala shiyasa yake ɗaukar wasu yaren da ko hausarma basaji sosai kuma su ba hausawa bane, zama cikin garinne yasa suka iyata, yanason abawa nasa ƴaƴan kulawa da kariya amma shi yafison ya tafi shikaɗai duk inda zashi........,

***********************

*LAUTAI*

.........To ku kama sana'a mata, to ku kama sana'a mata, ku kama sana'a mata duk macen da bata sana'a aurace lale..lale maraba da samun kasuwa, ta ƙarasa maganar ta tura ɗaurin kallabin da tayi ture kaga tsiya dashi, tare da tsugunnawa tanaci gaba da suyar ƙosan ta, tana watsawa ta gefen ta harara ta ƙasan ido,

Matar dake gefen ta taɓe baki tare da cewa "Anyi ba ai ba wai me niƙab tayi wawan zama,

"Hhhhhh magana ake ta masu iya magana anayi muna shan shayi.. wani namiji da yayi zaman dirshen gaban me ƙosan yana ƙara washe baki,

"Yanzu naji bugu wai an daki kwarto da sket......me suyar ƙosan taƙara faɗa idon ta nakan kaskon da take suyar,

"Tunkan a haifi uwar me sabulu balbela take da farin ta, tana faɗar haka ta miƙe daga gurin ta shige ɗaki,

Ahhhhhaye ayyiri yiri yiri...."kin mana maganin ƴar sa ido..

"Karime yo ba dole ba, baƙin ciki ai bazai barta ta zauna ba, mace sai agefen sa ido sai kace ita ta yankewa sa ido cibiya....

"Kallo sai kace mayya.

"Babar Abu wlh kinmin daidai da kika yi mata haka, naga tunranar da kika fara sana'ar nan kina fara suya zata zauna agun kuma naga ba siya zatai ba,

"Rabu da ita Karime, wannan zaman da kikaga tanayi, da Baban Abu ya dawo zataje ta fayyace masa duk abun da yafaru har waɗanda suka shigo gidan nan sai ta lissafa masa da duk adadin cinikin da nayi sai yaji labari, ai daga yanzu bazata ƙara zaman gurin nan ba wallahi duk sanda ta zauna sai na koreta shigiyar mata me ƙashin tsiya tunda aka auro mana ita aka auro mana tsiya muke fama da talauci,

"Tsiya ta ƙare akanki da dangin ki, amma badai niba, wallahi KUBURA ki kiyaye ni ki fita harkata tun muna shaida juna kafin gari ya ɓaci....tana daga bakin ƙofar ɗakinta ta ɗaga labule take maganar....

"Kanki ake ji, wai mahaukaci ya faɗa rijiya, yace ku barni ni wanka na nakeyi..... Wacce aka kira da Kubura ta bata amsa kuma itace me suyar ƙosan....

""Hhhhhhh hhhhhhh Hhhhhhhh..ƴan gurin gaba ɗaya suka kwashe da dariya wasu harda masu tafawa,

Baƙin ciki ne ya gama cika ta fam ta cika kamar ta fashe saboda dariyar da sukayi mata, hakan yasa ta wawuro wata uwar ashar ta narka musu gaba ɗayan su,

A zafafe Babar Abu ta ɗago zata mayar mata da martani, ta tsinkayo muryar mijin su, yana cewa "Kubura ya isheki haka koma me tayi miki kukujawa kanku kar kisake nasake jin muryar ki anan, kuma wallahi bazakici gaba da haddasa min masifa acikin gida ba, Tunda kika fara sana'ar nan faɗan yau daban na gobe daban, To wallahi in baki shiga hankalin ki ba sai kin ajiye sana'ar inga ta tsiya, jiyama duk angaya min abun da yafaru ɗaga miki ƙafa kawai nayi, to kinkaini ƙarshe tundaga bakin hanya ake jiyo dariyar ku sai kace zararru to kishiga hankalin ki......

"Kai malam dakata kaji wallahi bazaka zo kaɗagan hankali ba ita baka ga me tayi min ba, amma laifina kake gani to wallahi bazan daina sana'a taba,tunda bakai kaban jarin ba, anfiso kullum mutum ya zauna ahaka baci gaba, to wallahi da sake dan bazan lamun ta ba, bazamu yarda anringa wulaƙan tani ba koda yaushe.....

"Au haka kika ce ko....

"Abun da kunnen ka yajiye maka ta faɗa ƙasa ƙasa tana murguɗa baki tana cigaba da juya ƙosan ta, sauran kuwa kowa shiru yayi babu wanda ya ƙara buɗar bakin sa saboda magana ce ta masu gida,

"Me kika ce..!?

"Ni ba magana nayi ba...

"Hmmm muzuba mu gani zakiga abun da zai biyo baya.... Yana maganar yayi gaba wajen waccen matar,

Yana zuwa daf da ita ta fashe da kukan munafurci, cikin kuka tace "kaji tade haka suke sani agaba daman ina gaya maka tunda ta fara sana'ar nan kullum haka suke sani agaba zagi da cin mutunci ba kalar wanda basa yimin haka zasu haɗu suyi ta zagina har iyayena suke zagewa, kaima bakaji kalar zagin da take saka agaban su tana zaginka su kuma suna tayata, idan nayi magana kuma saboda kishin ka da nake sai ta dawo kaina......,

"Ransa ne yaƙara dugunzuma amma sai kawai ya shiga bata haƙuri ya jata cikin ɗakin, shi kaɗai yasan hukuncin da zai mata,

"Na rantse da Allah wannan matan sai taga danyen hauka ni zata yiwa haka, zanci ƙafar uwarta, bazan kulata ba yanzu tagama shirya nata, in tasan wata ai bata san wata ba, kura ma tasan gidan me babbar sanda.....,

*************************

"Washe gari......

"Koda safe da suka tashi da wuri suka shiga shiryawa a tsanake yau suka shirya dan saida suka karya ma sannan suka mimmiƙe suna shirin fita,

"To yanzu ya zamu kasa tafiya muyi bibbiyu ko ɗaiɗai ya zamuyi, cewar Ameela,

Beenish tace "dani da Babyn baby da Aunty Babba sai mu fara yin gaba ku kuma sai ku taho daga baya, ai hakan yayi ko, idan munje makarantar ma haɗe, ko ya kukace,

"Hakan ma yayi, muje kawai kunga goma har ta kusa, 10 zamu shiga lecture,

A tare suka fita daga cikin falon, suna fitowa gaba ɗayan su sukayi mutuwar tsaye tare da ƙamar da idon su awajen, suna me mamakin hakan,

Beenshi Cikin mamaki da ɗan tsoro atattare da ita tace "What am I seeing? Even if my eyes are cloudy?

"A new car..!? Aunty Baba itama ta faɗa cike da zaro ido,

Barazana tace "me hakan ke nufi? Who is following our lives!? Tayi tambayar idon ta yana kan motar kuma babu wanda ya bata amsa.

Da gudu Aunty Babba ta tafi gurin gate ɗin su tana cewa "Woo, Olorun mi, Baba, kilode ti o fi n pa mi, Baba, kilode ti o fi n ṣọ mi?"(Wayyo Allahna Baba me gadi kana ina? Baba me gadi kana ina...,)

Da sauri ta ƙarasa baki ƙofar ɗakin sa ta tura ƙofar wayam taga ɗakin babu kowa aciki kuma babu kayan sama a ciki,

A rikice ta kuma fitowa daga ɗakin tana sauri tuɓur tuɓur tana tafiya amma komai najikin ta rawa yake,

Suma duk gurin nata suka nufo cikin sauri suna tambayar ta yana ina,

Girgiza kai tayi tana nuna ɗakin da hannu tace "Baba me gadi is not here, wallahi he is not inside, he has taken all his clothes ɗakinfa babu komai aciki, hannu ta kuma ɗorawa akai tace Igba yen ni tiwa pari,

Duk saranda sukayi kowa yana tunanin what is the solution, what is going to happen to them like this, who wants to come into their lives like this......????

*Announcement! Announcement!!*

*Sanarwa Ku tsaya ku karanta kar kuzo kunace min bakuga wani page ɗin ba, maganar gaskiya yawan sharing ɗin littafin nan yana bani wahala dan haka ba kullum zakuna ganin saba a kowanne group ba, musamman ƴan facebook, duk me son karantawa kullum na buɗe group kuyi searching ɗin SU WAYE SU HAUSA NOVEL kuyi join anan zan ringayi saboda groups sunyi min yawa ina gajiya da tutturawa,*

_*Ƴan WhatsApp me son group yayi min magana in saka sa, (kawai kace min group nasan me kake nufi) dan bazan ringa share ɗin sa tare da link ba saboda bana son mutane su ringayi join batare da karantawa zasu yi ba, gwanda duk wanda yasan karantawa zai yi sai yayi magana ta number ta 08124226526 dan Allah Dan Annabi idan kasan ba karantawa zakayi ba kar kamin magana, abun taƙaici wai duk bayanin da nayi amma wasu sai suyi min magana wai suna so in turo musu da wasu littattafan bayan Ni kuma haka nace idan kana son karanta wannan littafin kayi min magana amma wasu sai a hankali*_

*Sannan a sati zan ringayin posting sau biyar Monday to Friday banda Saturday and Sunday*

Sannan duk ƙarshen sati ko kuma sau uku ko sau biyu in sha Allah zanna baku shawarari da abun da ya shafemu mu mata, kamar de ƴar lecture zanyi muku sadaka, bari in baku misali a nayau,

*Gyara*
"Namiji ko bamai gyara bane yanason mace me gyara, to bare mh if me son gyaran ne wanda yasan darajar gyara
Kunga gyara,gayu tsafta,kwaliya should be the first priority in your marriage,
End Ads