x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 20 - SU WAYE SU

  • 57001 words
  • 60000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 165

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
dawowar ɗan sa muke jira, indai ya dawo zamu ƙara samu power dole ma su fito da kansu a duk inda suka shiga..

Commissionana yace; shikenan ma duk komai zai zo mana da sauƙi kafin ma ya dawo ɗin ma duk zamu fara wasu shirye shiryen, akwai waɗanda zan nema muna neman taimakon su dan suma zasu taimaka mana sosai..

"SU WAYE SU!? Alhaji Ɗan Ijje ya tambaye sa cike da ƙara samun wata nutsuwar.

"Masu zaman kansu" Commisiona ya basa amsa,

Cike da rashin fahimtar maganar sa yace; "ban gane masu zaman kansu ba?

"Eh haka suke cewa kansu, kuma kusan hakanne dan basu da kowa, amma dai mubar wannan maganar yanzu ba loƙacin yin ta bane, kaje kawai zanne meka,

Sai loƙacin ya miƙe daga zaman da yayi tare da zaro kuɗin bandir biyu ya ajiye masa a gaban sa, sannan ya fita,

Yana fita daga ciki ƴan sandan wajen ma saida yayi musu alkhairi sannan yabar station ransa a sanyayye,

*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*

Ƙarar wayar ta ce ta tashe su daga bacci, tsaki Barazana taja tare da ɗallawa Ameela duka tace ke dalla malam kisaka wayar ki silent ba makarantar ma baza'a barmu mu huta ba,

Cikin magagin bacci Ameela ta jawo wayar ganin me kiran ta yasa ta ɗan buɗe idon tana ɗagawa, karawa tayi a kunne tare da yin shiru,

"Okay ƙarfe nawa? shiru ta kumayi kafin tace ba matsala indai taimako ne.... Kashe wayar tayi sannan ta tashi zaune tace; "kun san me Commissionana ne yake neman taimakon mu, kunsan dai shima ya taimake mu dole muje mu taimake sa indai har muna da halin yin hakan....

Duk tashi sukayi zaune, duk da ba gado ɗaya suke kwana ba amma indai ɗaya yayi magana duk zasu ji saboda kusa da kusa gadajen nasu yake.

Babyn baby ce kawai taƙi ta tashi duk da taji me akace amma sai ta ƙara gyara kwanciyar ta ma.

Nan dai duk da basu san taimakon da zasuyi masa ba, amma suka tashi masu gyaran gida suka shiga yi masu girki suka shiga, basu suka gama komai ba sai wajen ƙarfe sha biyu da wani abun sannan suka fito daga gidan, inda yace mata su haɗu anan suka dosa, suna zuwa kuwa already ya daɗe da zuwa gurin su kawai yake jira,

Suna ƙarasowa inda yake suka gaisa sannan suka zazzauna akan kujerun da ya tanadar musu....

Ɗan gyaran murya yayi sannan ya zayyana musu abun da ke faruwa da duk abun da ya faru loƙacin da akaje kai kuɗin..

Ameela ce ta ce;"Kayi haƙuri amma baza kasamu ko wane irin taimako daga gare mu ba indai akan wannan case ɗinne mun ma san ruwan da kake magana bawai bamu sani ba kuma zamu iya idan muka saka kanmu, saidai kasan me yasa bazamu yi b

Cike da kiɗimewa ya miƙe tsaye yana cewa "A'a, amma me yasa zakuyi mana haka ƴaƴan mu fa akayi kidnaping in baku taimaka ba meye amfanin taimakon da kukeyi,

Suma miƙewa sukayi cikin fushi fushi Beenish tace; bazamu taɓa yi ba kuma kuji abun da ake ji, a duk watan duniya tun shekaru da yawa da suka wuce, ana yin irin wannan abun baku taɓa ɗaga murya ba kunce zaku nemo inda suke ba sai yanzu da aka taɓa naku, ka gaya mana sau nawa kuka taɓa bibbiyar case makaman cin haka na tsawon wata guda ma akan ku fito da waɗanda akeyin kidnaping ɗin su a ƙasar nan sai yanzu da akazo kanku, kaman ta loƙacin da muka kawo maka ƙara tun matsayin ka ma baikai haka wacce irin amsa ka bamu? Zaka iya tuna adadin cases ɗin da ka fuskan ta akan ɓatan mutane da akeyi kama ga yara manya mata da maza? Masu kuɗi da talakawa, amma hukuma babu abun da take yi akai shin su waɗanda ake ɗauke musu basu da gata ne ko me? Ko faɗowa sukayi daga sama? Ko babu zuciya a jikin su da zasu ji ba daɗi idan suka rasa ƴaƴan su, indai akan ɗan kane ƙwalli ɗaya kake wannan haƙillon to bazamu taɓa taimaka maka ba har abada saboda kaima baka taimaka wa wasu ba alhalin haƙƙi ne akan ku amma bakwa taɓa saukewa kanku nauyin da kuka ɗorawa kanku, kai bakaji kunya ba ma akan yaro ɗaya zaka zo neman taimako gurin mu, ai kaɗan ma kuka gani kowa sai yaga sakaya ɗaya bayan ɗaya duk sai Allah ya tonu asirin ku..................✍️✍️

(Barkan mu da dawowa daga hutun salla da fatan kowa yayi salla lafiya......)

*Waɗanda suka ban Barka da salla ina godiya sosai Allah yanar zumunci, waɗanda ma basu bayar ba duk ina godiya*

My WhatsApp number 08124226526
[3/5, 11:54 AM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*

(THE WRITER OF 💅SARKI SAMEER 💅)

______________________________


*_episode 21💧_*


💧💦محمد لرسول الله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

Wani irin gumi ya ringa tsatstsafowa commissionana daga goshin sa, a loƙacin da suke gaya masa wannan maganar tare da tambayoyin da suke masa da ba shi da ƙarfin amsa ko guda ɗaya a halin da yake ciki yanzu, sosai ya sha jinin jikin sa, yasan tunda suka ce sun san gurin kuma in suka sa kansu zasu iya yin abun da yake so ya san zasu iya ɗin kamar yanda suka faɗa ɗin amma yanzu kuma babu hali dan tunda suka ce baza su yi ba to baza suyi ɗin ba,

Ameela ce ta katse masa tunanin sa ta hanyar cewa; "ko ka manta mu tuna maka, kayi babban kuskure ai kuma kasani kamar yanda muka gaya maka a baya loƙacin na nan zuwa wannan muƙamin da kake taƙama dashi sai ya zama bana ka ba sai mun sa an kore ka korar wulaƙanci ma, duk wani abu da kake taƙama dashi sai ka rasa su ɗan ka kuma ko munsan inda yake baza mu taɓa fito maka dashi ba indai ta hanyar mune.

"Ya isa yace ya manta bakiga zufar da yake ba saboda an taɓa masa yaro guda yake tada jijiyoyin wuya, ashe ɗa baifi ɗa ba mtsww dan kuzo mutafi danni raina ƙara ɓaci yake wallahi da nasan wannan taimakon yake neman mu ba zai taɓa ganin mu ba" cewar Barazana tana daka tsaki ta juya tare da jan hannun Babyn baby suka bar wajen.......

Commissionana na tsaye a gun kamar mutum mutumi yakasa ko motsawa daga inda yake bare ya yi yunƙurin yi musu magana kawai da ido yake binsu yana kallon su amma bakin sa ya kasa furta ko word ɗaya.

Suma juyawa sukayi suka barsa a gun tare da ƙara faɗa masa maganganu son ransu.

Suna barin wajen ya daki bencin wajen yana girgiza kai, da ƙarfi yace "never! Ƙarya kuke wallahi kunyi kaɗan da ina rabuwa daku ne kawai bisa wani dalili amma kun taɓo ruwan daka kanku, ko ni ko ku amma sai naga bayan ku, Sai huci yake yana huhhura hanci sama, cikin tsananin ɓacin rai ya zaro wayar sa buɗeta yayi ya shiga contact ɗin sa ya lalubo wata number da naga an rubuta magana ɗaya da haka akayi saving ɗin number, danna masa kira yayi ana ɗagawa ko sallama baiyi ba yace "ya Magana ɗaya ina son ganin ka yanzunnan, ka same ni a guest house shiru yayi yana sauraren sa kafin daga bisani yace yauwa kayi sauri ina jiran ka.

Wayar ya sauke daman gurin da yake kamar irin gurin sha ƙatawa ne, cikin sauri ya fito daga wajen shima ga shiga motar sa daman shi kaɗai ya taho ya hana kowa biyo shi, a 360 yaja motar yabar wajen, baiyi wata tafiya ba sosai ya ƙaraso unguwar da gidan masa yake, yana sauka sai ga mashin ɗin mai magana ɗaya nan ya kwararo sa a guje yana zuwa bakin wajen ya cake sa yana ɗaga taya sama, yayi wani juyi sannan ya taka burki amashin ɗin tare da jefar da tsinken sigarin dake bakin sa yana hura hayaƙin sama, kallon motar commissionanan yake da yaga shima zuwan sa kenan kuma bai fito ba, cikin takun shegun kannan da suke ganin sunkai gwatsane a rashin ji da ganin duniya yake tafiya yana harhaɗa hanya, wata iriyar tsayuwa yayi a gaban motar yana masa kallon ƙasan ido....

"Yauwa kaga mun ƙaraso ma a tare ɗan zuge mana gate ɗin ga muƙulli ya faɗa yana miƙa masa...

Shikam ƙin amsa yayi sai ma zura hannun sa da yayi a cikin aljihun wando ya zaro mandula tare da ƙyasta mata leta sai da ya zuƙa batare da ya fitar da hayaƙin b, cikin wata irin murya ta ƴan shaye da zuƙe zuƙe ya ce; "Ɗan aiki ka samu nifa ba gate man bane kasan waye ni, dan haka inajin ka, yi maganar ka kai tsaye zan wuce dan ina da ajenda da wata shuka ta kar in ɓata mata rai, yana maganar yana rangaji da kai yana kuma zuƙar Mandular sa yana masa kallon tara saura kwata.

Wani irin numfashi commissionana ya sauke ransa babu daɗi amma babu yanda ya iya yasan halin sa yau ƴan rashin mutuncin ne akan sa ya sha tayi masa yawa, dolen sa ya kashe motar ya fito da kansa sannan ya buɗe gidan yace su shiga maganar baza tayiyu a waje ba,

Gaba yayi shikuma mai magana ɗaya yabisa cikin tafiyar sa ta ƴan duniya da suka riƙa suka fi kuɓewa riƙa.

A farfajiyar gidan suka zauna akan kujerun da suke gurin,

"Inajin ka kusa cinye loƙacin ka, ka faɗi komai a cikin minti biyar tana cika zan tashi daga nan gurin kuma kasan sai ka biyani kuɗin zuwan da nayi maka koda buƙata bata biya ba, loƙacin ka ya fara, ya faɗa yana karkarɗa masa yatsa.

Yauwa nasan ka da magana ɗaya baka wasa da aikin ka, wani ɗan ƙaramin aiki zakayi min akan wasu yara ƴan mata ne guda biyar,

Zabura yayi yana zaro ido sai kuma yayi dariya yace "abun kuma kam mata ya dawo to faɗi inajin ka,

"Naga yanzu sauri kake amma zan tura maka da address ɗin su da number ɗin su ina so kasa mutanen ka su kwashe su gaba ɗayan su sannan ku lalata musu rayuwar su gaba ɗaya kuyi rapping ɗin su sannan ku lalata musu fuskokin su, so nake idan aka kalle su sau ɗaya mutum bazai so ya ƙara ganin fuskar su ba, kagane me nake nufi ko nawa kake so zan baku yanzu zan tura maka da 5 million idan kun gama kuma ka faɗi ko nawa kuke so zan baku sanna.......

Hannu ya ɗaga masa yana miƙewa tsaye ya ce; "Angama nagane komai kawai naji alart a yau zamu ƙaddamar maka da aikin ka na barka lafiya ya faɗa yana haɗa hanayen su guri guda yayi masa irin ta ƴan India sannan ya juya abun sa yana tafiya yana fito tare da ƴar waƙar sa "tuu turu tuu turu tuturuturuuu ehh yau zamu kwashi romo yau zamu kwashi daɗi hhhhhh..... Yana ta haukan sa har ya fita daga cikin gidan.

Commissionana baiyi wani ɓata loƙaci ba ya zaro wayar sa ya tura masa duk abun da yace zai tura masa sannan ya miƙe daga gurin yana sakin murmushi tare da furta ƙarshen ku yazo dan kunga ana lallaɓaku kun ɗauka bazan taɓa iya ɗaukar mataki akan kuba, gwara nayiwa tufkar hanci tun yanzu sai muga da yanda zaku sa a kore ni finally komai yazo ƙarshe yanzu, kana kallon fuskar sa kasan farin cikin har cikin ransa yake jin sa, ya daɗe agun yana surutan sa shi kaɗai kafin daga baya ya shiga cikin gidan.

*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*

Bayan su Beenish sun bar gurin Commisiona suka nufi wajen wani super market a bakin mall ɗin sukayi parking ɗin motar su, sannan suka shiga ciki rabuwa sukayi kowa na ɗaukan abun da yake so tare da cefanen abun da suke buƙata, sun daɗe a gun suna ɗibar abubuwa.

Babyn baby ce ta taho wajen Ameela da sauri tana cewa Ƙawa kinga abun wannan yayi insiyawa Baby, wani agogone me kyau da tsada,

Murmushi tayi tace kai auta yayi mana indai kina so ki ɗaukar masa mana, indai kina so.

"To wannan kuma fa ta nuna wata leda da taga tana ɓoyewa a hannun ta, ƙara ɓoye ta tayi a bayan ta tana murmushi tace "Sirri ne na baby ne amma babu me gani, tana faɗa ta juya tana cewa bari na dawo wani abun zan ɗauko,

Haka suka daɗe suna siyayyar su sannan suka taho wajen biyan kuɗin, gaba ɗaya aka tattara musu abun da suka siya, suka bada atm aka ciri kuɗin sannan a kwa kwasar musu kayan suka fito waje.

Suna fitowa sukayi karo da Faheema cikin washe baki ta farayi musu magana, Sunan Ameela ta kira, Barazana ce ta fara gane ta tace "laa Faheema koh?

"Eh nice ashe kin gane ni, hannu ta miƙa musu duk suka gaisa suma ba yabo ba fallasa suka sakar mata fuska suna gaisawa, basu wani jima ba suka ce bari su wuce, har sun ɗanyi gaba tace "wait!

Tsayawa sukayi gaba ɗayan su tare da juyowa suna fuskantar ta, da sauri ta ƙaraso gurin tana saka hannun ta a jaka wani kati ta zaro guda biyu tace "ga wannan number ta ce wanna kuma dan Allah katin gayya ta ne zamuyi taro a gidan mu gobe da yamma ɗan Allah kuzo ina gayyatar ku....

Kamar baza su karɓa ba saidaga baya de kawai Beenish ta karɓa tace "to shikenan ba matsala zamu shigo indai ba wani ƙwaƙwalwaran ɗalil ba zamu zo kar ki damu.

Sosai ta faɗaɗa murmushin ta tace na gode sosai dan Allah kuzo ko kuban number ɗin ku ma sai inne me ku ko kuma ma ku ban address ɗin ku sai inzo mu taho tare in babu damuwa,

"Kar ki damu zama muzo tunda muka ce zamu zo to zamu zo" cewar Barazana.

Faheema tace "gaskiya naji daɗi nagode sosai, amma duk da haka kuban number in case...

"Tawa kike so a baki? cewar Aunty baba.

Kallon su tayi tace "kai ni wallahi da zaku ban ta dukan ku ma ina so...

"A'a ɗaya zaki zaɓa, inji Babyn baby tana yi mata dariya.

A ranta so take tace ta Beenish take so amma tana kamar bazata bata ba, dan ita tafi burgeta ko ace babu maganar yayan ta, a ranta ma tafi son ta...

Tana wannan tunanin kawai taji an karɓi wayar hannun ta, hakan yasa ta dawo daga tunanin da take, mamaki ne tayi ganin wayar ta a hannun Beenish kamar tasan tunanin da take, hamdallah tayi a ranta dan taji daɗi sosai.

Beenish ce tace naga kin tafi tunani ga yawa nan zan saka miki sai ki kirani inyi saving ɗin ta, miƙa mata tayi aikwa da sauri ta karɓa tana sake godiya, ji take kamar yau sallah a wajen ta...

Har suka juya suka shiga mota tana gurin tana ɗaga musu hannu saida suka tafi sannan ta daka tsalle tana murna, da gudu kamar ƙaramar yarinya ta nufi wajen da motocin su suke, ashe tare da Aveed suke, tana zuwa ta fara ɗaga masa hannu tana nuna masa number dake jikin wayar ta, shima da sauri ya buɗe ya fito daga motar yana fusgar wayar a hannun, tare da zaro tasa wayar hannun sa har yana karkarwa wajen ɗaukar number ya shigar da ita cikin wayar sa sannan ya bata wayar ta, yace nasan halin ki da shirme yanzu sai kije ki goge ta bakiyi saving ba..

Shiga shiga mu tafi kar suyi mana nisa, tace; "kai yaya tunda ga number su ai shikenan mubi komai a hankali mana kuma fa zasu taron na basu katin sunce zasu zo, mu jira kawai suzo ɗin, duk kabi ka rikice haba control your self,

"Never I can't control my self, you know that, dan haka kawai muje ni sai hankalina yafi kwanciya,

"To ai sai kai tayi dan yanda naga ma suna gudu wallahi ba ganin su zakayi ba, saidai kasamu muyi wahalar banza....

Kumatun ta yaja yana lakace mata hanci yace naji koma me zaki ce nidai tunda kikayi min wannan aikin kinga ma yi min komai, sannan ki faɗi duk abun da kike so insiya miki, yana faɗa ya tayar da motar suka fara tafiya.

Murna kamar ta kashe Faheema wayar ta ɗauko tayi saving ɗin number, tana cewa mota zaka sauya min kawai ka gama yi min komai...

"Kin samu indai mota ce ko tawa kike so zan baki wallahi.

"Wuuuu wayyo daɗi dan Allah da gaske kake zaka ban motar ka?

"Eh wallahi indai kina so.

"Kashhh kasan me kabari amma sai Ya Rk ya koma sai kaban dan nasan halin sa yanzu sai ya kawo min cikas ko sa yaji dalilin da yasa zaka ban.

"Eh kuma fa hakane, kinga manta da wannan ma, ɗan kira ta yanzu mu tabbatar da number ɗin ce,

Ɗan taɓe baki tayi tace; "yanzu idan na kirata me zance mata kar kasa su fara zargina mana, mu bari sai zuwa goben mana kawai wallahi zasu zo.

"Ke banza ce kawai haka zaki ce mata kece tayi saving ɗin taki number...

"Hhhhh to ai munyi hakan tun kan na taho na kirata taga number tawa nasan yanzu tayi.

"Mtsaw baki haɗu ba, amma dai koma meye tunda ka number komai me sauƙi ne, sai faman sakin
End Ads