ta karɓi tasa sannan ta basa waccen yarinyar da ta mutu tace kafin su shigo kayi sauri kaje ka sanar da likitan cewar ta rasu in ba haka ba suma zasu iya tona maka asiri idan aka basu kuɗi, idan kun gama komai ka dawo ka same mu anan, basu dai wani tsaya doguwar magana ba ya karɓi ƴar hankalin sa duk a tashe yaje ya sanar da likitan nan kuwa suka yarda tare da karbar yarinyar, sai suka koma ɗakin da take kwance har yanzu bacci take,
Cikin sauri yayi kanta yana cewa likita zan dauke ta mubar asibitin ko kuma ku bamu wani wajen mu ɓuya koda a nan ɗakinne sosai ka ƙulle mu ta waje, wasune suke bibiyar mu nasan yanzu suna daf da shigowa koma sun shigo idan suka ganmu kashe mu zasuyi, dan Allah ka taimaka mana.....
Tunda ya fara maganar likitan yake binsa da wani irin kallon sama da ƙasa ko da yagama kuwa sai yace to shikenan zanyi tunani akai, amma idan zaka biya sama da kuɗin da suka biyani,
Cikin zaro ido yayi baya kamar zai faɗi tsabar razana da yayi, baisan loƙacin da caƙumi wuyan sa ba, ta shaƙe shi yana cewa me kake nufi da inbiyaka sama da kuɗin da suka baka SU WAYE SU eh su waye suka biyaka, me kake nufi....
Cikin dariyar rainin hankali yace "kamata yayi ka fara duba marar lafiyar taka sai kaga abun da nake nufi...
Sakin sa yayi cikin sauri ya juya ya koma kusa da ita kara kunnen sa yayi take kwa yaji bata numfashi hannun ta ya ɗaga shima yajisa a sake....
Wata mahaukaciyar ƙara yasaki tare da yin kukan kura ya damƙo likitan yana kai masa naushi cikin ɓacin ran da shi kansa baisan yana da shi ba, me yasa ka kashe ta me yasa wane irin rashin tausayi ne me yasa ka kashe ta me yasa ka kashe ta??? Duk yabi ya fice a hayyacin sa, hawaye na zubo masa.
Amma duk abun da yake masa saima wata dariya ta ƴan iska da yasakar masa yana cewa, me yasa na kashe ta saboda kuɗi kaji ko nace saboda da kuɗi itama jaririyar da bata mutu ba da kaina zan kashe ta Hhhhhh ya kuma sakar masa dariya duk da yana jin azabar riƙon da yayi masa amma hakan bai hanasa faɗar abun dake ransa ba....
Wata mahaukaciyar shaƙa yayi masa da a take yafara tari yana zaro ido da suka kaɗa suka jazur...
Saida yaga numfashin shi ya kusan ɗaukewa sannan ya sake sa yana ture sa gefe,
Gurin matar ya kuma komawa yana ci gaba da jijjiga ta yana kiran ta yana sumbatu dan sam baiso ta mutum ba, dan shi duk da tana maganganun ta na jiya bai taɓa kawo mata mutuwa ba, dan shi sauraron ta yake kawai azin zafin ciwo ne yasa take wasu surutan... Sosai yayi kuka kamar ransa zai fita...
yana gurin suka shigo cikin wajen saidai maimakon yaga waɗanda yake tunani sai yaga sabbin wasu fuskokin, su uku ne.
Yana ganin su ya miƙe yaje kusa da su yana binsu da kallo, cikin tsananin ɓacin rai yace "wallahi dukan ku sai kunyi nadama sai nasa kunyi da nasanin zuwan ku duniya kamar yanda muka rabata da farin ciki kuma sai nasa kun dawwama a cikin ƙunci wallahi sai na ɗaukar mata fansa kuma ko ban ɗauka da hannu na ba, wani na zai ɗauka sai na haifar muku da dana sani cikin rayuwar ku, Allah bazai taɓa barin ku ba, Sai Allah ya nuna muku ƙarshen ku gaba ɗayan k......
Tasss wani ga kwashe shi da mari ya ƙara taro sa ta ɗayan ɓangaren, tare da cewa kai kasan su waye mu da kake gaya mana magana son ranka, an kashe ta ɗin kuma kisa ma yanzu muka fara kaima kuma zamu kashe ka in yaso sai kafi jin daɗin ɗaukar fansar tunda har dakai idan kaje inda take sai ka faɗa mata zaka ɗaukar mata fansa, wani marin ya kuma kwashe shi dashi..
Amma duk da haka bakin sa bai mutu ba yaci gaba da cewa "an faɗaɗin ku kashe ni nima ku huta amma kusa aranku gaskiya zatayi halin ta ko ba daɗe ko bajima sai Allah ya tonu asirin ku sai kun girbi abun sa kuka shuka, da hannun, sai a loƙacin da kuke tunanin komai ya zame muku daidai a rayuwa, zaku ga sakayya kuje kuyi duk......
Bai ƙarasa ba sakamakon dukan da suka rufe sa dashi haɗuwa sukayi gaba ɗayan su suna dukan sa tun yana iya karewa har ya daina, ɗaya daga cikin sune yaje ya ɗauko wani ƙarfe ya buga masa a akai take ya zube a wajen yana sakin ƙara, ɗaya kuma ya samu ya daki ƙarfar sa da ƙarfi take kwa tayi ƙara, basu rabu dashi ba saida suka ga baya shurawa sannan suka rabu dashi...
Ganin zasu fito yasa mayar dake leƙen su tayi saurin janye wayar da take ɗaukan video da ita ta juya ta ɓuya a wani lungu saida taga fitar su har likitan sannan tayi saurin fitowa ta shiga ɗakin da sauri, saida ta shiga kuma sai ta rasa ma ta ina zata fara basa taimako..
Fita tayi ta koma can ɗakin su inda yakai musu yarinyar, da gudu ta shiga ciki tana kuka ta sanar dasu abun dake faruwa,
Namiji ɗaya ne sai wata mata sai kuma marar lafiyar da ta ke barci.
Fitowa sukayi gaba ɗayan suka shiga ɗakin kwance suka gansa da alama kuma kamar babu rai a tattare da shi, ga matar can ma itama kwance babu rai...
Namijin ne ya tsugunna a gaban sa tana sauraron ko da rai, da sauri ya miƙe yace "Mama da sauran rai a jikin sa fah, ya kamata muyi gaggawar yin wani abun....
Kallon sa tace to "Khaber yanzu meye abun yi, ya kake ganin za'ayi dasu, kar muce wani likitan yazo a duba sa ko da rai ajikin sa kuma suje su kuma yi masa lahani.
To ya Mama ya zamuyi dole mu kuma neman taimakonbwani ai ba duka aka taru a ka zama ɗaya ba, bazaiyiyu ace gaba ɗaya likitocin an haɗa baki da su, idan muka samu hujja ma har shi zamu iya sawa a kamasa..
"To kuma haka ne kaje ka gwada zuwa wajen wani likitan wanda de kake ganin da sauƙi sauƙi ko kuma abun da za'ayi ma kawai ka kira mana wannan likitar da take kula da Ruƙayya, kayi mata bayani koda ba ita zata duba mana ba sai ta faɗa mana wanda zai iya taimaka mana.
"Tom shikenan bari naje muga, yana faɗar ya fita daga ɗakin yabar su da jimami.,
Yana fita kuwa yayi sa'a itama ta fito tana ta sauri, shima da sauri ya tare ta yana cewa "Dan Allah wani taimako muke nema duk da naga kamar sauri kike...
Dakatawa tayi tana kallon sa "tace eh wallahi amma faɗi inji ko zan iya saida ya ɗan kakkali gefe da gefe yaga babu kowa, sannan cikin ƙasa-ƙasa da murya ya fara yi mata bayanin duk abun da suka sani suma..
Tayi mamaki batayi ba, ɗan numfasawa tayi sannan tace; "bawai bazan taimaka muku bane saidan kawa*78635i saboda aikina, taimakon da zan iya baku kaɗai shine ku fito da su ku same ni awaje in ɗauke ku a mota ta in kai ku wani asibitin amma yanzu gaskiya bana tunanin da wanda zai taimaka maka.....
Cike da mamaki yace to amma me yasa?
Kaga sauri nake kaidai kayi abun da nace kawai idan kuna so,
Babu yanda ya iya dole ya amsa mata da to sannan ya koma ciki ya sanar da su cikin gaggawa ya ɗauko sa, sukuma suka bi bayansa, a ɗakin suka bar waccen mayar kwance a mace....
Da ƙyar ya iya kaisa waje yasaka sa a motar da ta ajiye sa, shiga yayi sai mahaifiyar tasu ta shiga gaban motar ita kuma ƴar budurwar ta aka ce ta koma gurin yayar ta Ruƙayya ta zauna da ita su suje..
Har ta juya sai kuma tayi saurin dawowa ta raɗawa yayan nata wani abu sannan ta basa wayar hannun ta, sannan tabar wajen ta koma ciki, ita kuma likitar ta tayar da motar suka ɗauki hanya..
"Ke kwa dan Allah in tambaye ki mana, me yasa kika ce babu wanda zai taimaka mana acikin asibitin, shin idan aka sanar da kisan kan daɗaya daga cikin ma'aikafa yayi baza a hukun tasa ba ko me kike nufi wallahi abun yaban mamaki ne tun ɗazu nake tunanin abun a raina, cewar Kabeer.
Shiru tayi kamar bazata yi magana ba, taci gaba da tafiya batare da ta tanka musu ba, saida ta daɗe kafin ta numfasa tace....
Yanzu haka ma angan sa loƙacin da yake kisan saidai babu wanda ya isa yayi magana, an daɗe anayin hakan domin duk wanda ke cikin asibitin nan yasan halin asibitin nan sannan ba a gina sa dan bawa ko wane marassa lafiya lafiya ba, kawai dai sirri ne amma kowa yasan me a keyi kuma ba daidai bane amma idan kafa ɗa kana cikin matsala daga kai har dangin ka ma zaka iya jefaku cikin halaka, saidai ka gani ka nuna ba kaga komai ba, sannan ba kowa suke ɗauka aiki ba, duk wanda ka gani yana aiki anan da wata manufa yake yin ta, sannan dan taimakon marassa lafiya anayin saidai ba kowa ba sai wanda a kaga dama...✍️✍️
*Kuyi malej da wannan dan gaskiya page ɗin ba'a nan naso in tsaya ba, wataƙil gobe ɗorawa zamuyi akan wannan page ɗin wallahi naje wani biki ne munci rawa mun ƙoshi🤣 nagaji da yawa, wannan ɗin ma Allah yasa nayi sa tun safe kafin in fita amma da kun lashe yaseen*
[3/5, 12:03 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
💧💪Jajirtattu writers association 💪💧
______________________________
*_episode 26💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
Bismillah....✍️
__Yanzu haka ma angan sa loƙacin da yake kisan saidai babu wanda ya isa yayi magana, an daɗe anayin hakan domin duk wanda ke cikin asibitin nan yasan halin asibitin nan sannan ba a gina sa dan bawa ko wane marassa lafiya lafiya ba, kawai dai sirri ne amma kowa yasan me a keyi kuma ba daidai bane amma idan kafa ɗa kana cikin matsala daga kai har dangin ka ma zaka iya jefaku cikin halaka, saidai ka gani ka nuna ba kaga komai ba, sannan ba kowa suke ɗauka aiki ba, duk wanda ka gani yana aiki anan da wata manufa yake yin ta, sannan dan taimakon marassa lafiya anayin saidai ba kowa ba sai wanda a kaga dama.....
Daidai loƙacin suka ƙaraso wani asibitin shiga ciki sukayi suna fito dashi kuwa aka tare su da gaggawa aka zo aka ɗauke sa, aka nufi emergency dashi...
Suma duk fita sukayi likitar har tana shirin jan motar ta matar tayi saurin leƙawa tace "yarinya ban tari numfashin ki ba, kuyi haƙuri ki ƙarasa bamu labarin waye me wannan asibitin kuma hukuma batasan dashi bane, da aka kasa ɗaukar mataki akai....
Shiru tayi tana nazari kamar bazata ce komai ba sai kuma tace ku shigo daga ciki to, saboda tsaro nasan zasu kula da wancen koda ba kwa gurin...
Kowannen su komawa yayi gurin sa ya zauna suna maida hankalin su gare ta batare da ta kalli inda suke ta ci gaba da cewa.....
"Hmmm ko watan da yawa wuce ansa mu wani da ya fahimci wani yayi ƙoƙarin fitar da maganar amma koda ya faɗa sai aka ƙaryata sa koda hukumar tazo bincike sai aka tanadi komai da zai hanasu samun hujja shima kuma bashi da hujja tunda da ido yagani shiaysa babu wanda ya ɗauki mataki ko kuma yaci gaba da bincike, daga baya ma kuma aka kashe shi, shiyasa duk wanda yake son rayuwar sa baya faɗa nima da na faɗa muku bawai bana son ta bane, saidan kawai nima ankamani da wani abun yanzu haka wani bincike ake akai na ana gano gaskiya za su kashe ni, na faɗa muku dan wataran koda zaku iya dakatar da wannan rashin a dalcin da sukeyi, daman neman wanda zan faɗawa nake sai kuma Allah ya haɗa ni daku tunda naji taimakon da kuke son shiyasa naji na yarda daku kuma inaji ajikina zakuyi wani abun saidai kuma maganar gaskiya koda kunyi nasara akai ankama ku to rayuwar ku tana cikin wani hali ba lalle su barku kuci gaba da rayuwa ba...
Maganar gaskiya nima ba halina bane kuma ban taɓa kashe wani ba, inadai gani anayi ko nawa aka bawa mutum suna kashe shi ba sabon abu bane a wajen yawancin likitocin, fahimtar bana kashe kowa yasa suka fara zargin ko nakai munafurcin su, shine suke zargin hakan, dan indai kai farkon zuwa ne bazaka taɓa fahimtar me ake aikatawa ba, sai ka kula sosai, nima fahimtar danayi sunyi wani meeting ne isu isu banda ƙananun maiakata, anan najiyo duk wani sirrin su na fara bincike akai na gano har tarihin su, shiyasa suke ta kuma bincike akan nagano wani abun nasu ko bangano ba da zarar sun gano gaskiya bazasu taɓa bari na ba, dan haka wannan asibitin gaba ɗayan sa babu gaskiya a cikin sa...
Kabeer yace "waye me asibitin?
Ɗan numfasawa tayi kaɗan kafin tace "wani mugun mutum ne ya buɗe gurin akan wani banzan ƙudurin sa kwata-kwwta babu Allah a ransa mugunta kawai yasa gaba bashi da tausayi bashi da imani, tun kan ya fito daga gidan yari yake aikata kisan kai, daga baya ma saida ya san yanda yayi ya gudu a gidan yarin, tunda ya fito kuma bai tsaya ba yaci gaba da cin zalincin mutane daba fashi haka yaringayi yana tara kuɗaɗe daga haka har ta samu ya gina asibitin ko karatun arziƙi baiyi ba kuma baida masani akan harkar likitancin ko sunayen magunguna bai sani ba, amma ya gina shi, sannan yasa mutane a ciki irin sa, daga farko ma yanda yake yi idan aka kawo marar indai a buge yake sai ya ƙulle ɗakin ya biya buƙatar sa, sai ya gama sannan yasa a duba ta, saboda akwai likitoci waɗanda suka iya aikin saidai kawai rashin aiki da abun da suka iya ɗin sai su biyewa son zuciyar su, amma abun da na fahimta daga baya shine duk wannan abun da yake bashi kaɗai bane akwai sa hannun hukuma ko kuma masu manyan muƙami da suke faɗa aji hakan yasa suke duk abun da suka ga dama ba tare da anyi bincike akan su ba an hukunta su an barsu a haka suna ta tsulla abun da suke so, ni nasan tawa ta ƙare domin dole su gano gaskiya yanzu haka ma saurin da ku kaga inayi shi yake kirana kuma idon sa yana kaina duk inda ma naje zai nemo ni, kuma hukuncin da zai min ma sai yafi haka, dan haka ina so daku da ku tsaya tsayin daka ku kawo ƙarshen abun nan, amma ta bayan gida zaku ɓullo musu, kar ku bari su fahimci kunsan wani abu kuma fara tabbatar da cewa wanda zaku gaya shima zai iya taimaka muku kar ku samu wanda baida tausayi, idan aka bashi kuɗi zai iya juya muku baya, sai kunyi shiri sosai kafin ma ku tadar da maganar sannan ku cigaba da samun wasu shedun daga cikin asibitin ta yanda zaku samu ƙwaƙƙwarar hujja da babu dama su kare kansu, zan baku address ɗina kuje gidan mu, dake unguwar Narewa ku tambayi inane babban gida za'a nuna muku, idan kun shiga sai ku tambayi wace Khabirat za'a nuna muku ita, sai kuce ta baku ajiyar da na bata, zata baku wata jaka, a kwai system ɗina duk wani abu yana cikin flash ɗina shi kaɗai zaku ɗauka duk sauran bayanai da abun da nayi bincike da hotuna da muryoyin su da na ɗauka duk zaku samu a cikin sa shi kaɗai ma hujja ce amma dai ku kuma samo wasu hujjojin saboda gudun matsala, daso samu ne ma da yanzu ma nake so kuje ku karɓa saboda indai naje muka haɗu dasu zasu lalubo gidan mu kuma zasu binciko wani abun gwanda kuje ku karɓa ta yanda ko sunje baza su samu abun da suke so ba.
"Yanzu to kina da tabbacin basu ganmu ba loƙacin da muka taho kar su biyo sawun mu su san munyi magana dake,
Girgizar kai tayi tace "saida na tabbatar da wanda yayi masa hakan ya fita daga asibitin tare da waɗancen mutanen, shi kuma me asibitin baya nan, sauran kuma ba wanda hankalin sa zai kawo wani abun, dan haka babu wata matsala kuje kawai sannan ku kula sosai, ni yanzu zan tafi wajen sa idan na dawo da rai zan nemeku idan kuma sun kashe ni shikenan Allah ya baku sa'a ku kuyi nasara babban burina nidai koda na rasa raina, a samu a dakatar da su sudena ɗaukar rayukan ƴan uwa musulmai, da ai tayin asarar rayuka da yawa gwanda ayi asarar rai guda ɗaya, sannan bayan shi nasan wata mata da yake yawan zuwa wajen sa alamu kuma sun nuna mun itama tana da hannu aciki amma ita bangama gane inda take ba...
Cike da ɗanjin tsoro matar tace "a'a kibar wannan maganar kema zaki rayu baza ki mutu ba, in