x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 38 - SU WAYE SU

  • 111001 words
  • 114000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 179

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
wayar ta mayar da ita ma'ajiyar ta, sannan ta kuma zuwa gaban wani hoton tayi rubuce-rubuce kafin daga bisani ta fita daga ɗakin tare da rufe sa ta saka muƙulli ajiki, tana juya suka haɗa ido da Faheema, cike da ɗan sakin fuska tace "a'a ƴan mata an tashi?

Wani kallo Faheema ta watsa mata tana kawar da ido kana ganin idon ta kasan taci kuka ta ƙoshi, ko uffan bata ce mata sai ta kuma juyawa ta koma ɗakin da tafito, bin bayan ta da kallo Hajja Mama tayi tana sakin murmushin gefen baki, tare da jinjina kai, tana cewa "kin haɗa kanki da aiki yarinya indai nice, bari muga iya gudun ruwan ki..

Wani ɗakin ta nufa tana zuwa ta ta tura ƙofar dake daman a buɗe ɗakin yake, tana shiga Bilal na fitowa daga wanka, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai yana haɗe rai.

Murmushi ta saki tare da cewa tuba nake autan su, bansan zaka fito daga wankan ba ai, bari in fita idan ka shirya na shigo, banza yayi mata bai tanka mata ba.

Zaid dake kan gado ya diro yana watsa masa harara yace "banza me kama da mata to uban me zata gani dan ta shigo ko tsirara kake ai ba wani abun kalla da har zaka haɗe rai dan ta ganka da towel, ita ma abun haushi harda wani baka haƙuri.

Shima Bilal ɗin harara kawai ya watsa masa ya wuce abun sa bai tanka masa ba, yasan idan ya biye masa haka zai ta saka sa a gaba da takura, shi kuma baya son takura a rayuwar sa, shiyasa tasu bata zo ɗaya ba kullum cikin faɗa suke, shi bayason takura shikuma Zaid yana son ya takurawa mutum da kuma shiga abun da babu ruwan sa, ko baka saka da shi ba a zance sai ya shiga.

Ƙananun kaya ya ɗauka ya saka, yana feshe jikin sa da turare, har yanzu bai kula Zaid ba da yake ta cigaba da yi masa magana, ƙarewa ma da yaga ma sai ya fice abun da ya barsa a ɗakin, yana fita yaga Hajja Mama nakan dinning tana zuzzuba abinci, tsayawa yayi yana kallon ta.

Jin kamar ana kallon ta yasa ta ɗagowa, suna haɗa ido da shi ta saki murmushi tare da cewa "ƙaraso mana babana, zo ka zauna kaci abinci gashi na zuba maka..,

A hankali kamar baya so ya fara takawa tare da ƙarasa wajen da take, tun kan ya ƙaraso ma, ta tako zuwa gaban sa sannan ta kamasa ta ƙarasar dashi kan kujerar ta zaunar dashi, saida ya zauna ta matso masa da plate ɗin gaban sa, sannan tace bari inje in dawo kaci da yawa yanzu zan dawo.

"Wai ni dan Allah me kika mayar dani a cikin gidan nan, tunda bakya so na, ki mayar dani inda ake so na mana, kinzo kin kawo ni nan, shi kaɗai ne mutum kenan? Ni yunwar ta kashe ni babu ruwan ki da cikina?

Jinjina kai tayi tare da cewa; "Zaid kai de baka gajiya da jan magana ji nake yanzu na baka abincin kaima kuma bansan zaka ƙara bane shiyasa ban taso ka ba, nayi zaton ma bacci kake..

Ƙarasowa yayi yana maƙe kafaɗa tare da tallewa Bilal kai yana zama a kujerar gefen sa, sai loƙacin yace; "Bacci yanzu sai kace malalaci irin o'o ni ai namiji ne ba mace ba,

Cokalin dake hannun Bilal ya ƙwala masa shi akai tare da watsa masa lemon dake gefen sa, sannan yace; "Zaid ka ishe ni na rantse da Allah zan maka abun da baka tunani dan kaga ina ɗaga maka ƙafa ko to kaci gaba, Allah wataran na riƙe ka sai an rasa me ƙwatar ka anan gurin idan kana ganin kuma ƙarya ne ka cigaba I will show you my another colour.

Dariya Zaida ya sanya harda tafawa, yana dariya yace; "Gaskiya ne maza, yau maza na magana, to in baka fasa ba, daman kai har wata kala ce dakai, gaya min wace iri ce fara ko ja ko baƙa?

Tsaki Bilal ya daka masa yana ƙoƙarin tashi ya bar masa gurin dan ji yake kamar ya shaƙe shi dan wallahi ya ishe shi ya takurawa rayuwar sa, shikaɗai ne matsalar sa da zaman gidan kuma dole ya bar gidan ko araba musu ɗaki,

Da sauri Hajja Mama ta ce "Auta babu ruwanka da shi zauna kaci abinci ka ka rabu da shi zanyi maka maganin sa,

Kamar zaiyi kuka cikin langwaɓar da kai yace; "kina fa ganin abun da yake min wallahi nagaji da zama dashi, ki mayar dani gurin Dadyna kince min zaizo amma har yanzu baizo ba wai kode kidnaping ɗinmu kikayi ne?

Wani dammm Hajja Mama taji gaban ta ya faɗi, bata son ya ringa tambayar saboda duk loƙacin da yayi mata tambaya makaman cin haka da ƙyar take iya haɗa ƙaryar da zata kwantar masa da hankali yabar zance, to amma tambayar yau tafi bata mamaki na cewa kode kidnaping ɗinmu ki ka yi ne? Bata san kuma ta inda zata kuma ƙaƙalo wata ƙaryar ba.

"Eh kidnapping ɗinku tayi muma ɗauko mu tayi, ƴar kidnapping ce duk abun da zata gaya muku ƙarya take muku!

Duk juyawa sukayi suna kallon ƴan mata biyun dake tsaye hannun su riƙe da na juna, da mamakin ganin su da kuma mamakin abun da suke cewa yasa su Bilal mutuwar tsaye.

Ran Hajja Mama ba ƙaramin ɓaci yayi ba da wannan maganar tasu, tuni fuskar ta ta koma yanda take babu ɗigon annuri a tattare da ita, su kansu basu taɓa ganin ta a irin haka ba.

Jikin Bilal ne yayi wani irin sanyi a hankali ya juya ya kalli Hajja Mama, ya ce; "da gaske ne ke ƴar kidnapping ce daman?

Kallon sa tayi fuskar ta babu annuri tace; "duk yanda tunanin ka yabaka, idan ka yarda da maganar su hakane sai ka ɗauki mataki idan kuma baka yarda ba nan zaku iya ɗaukar matakin da kuka ya dace gaba ɗayan, duk wanda ya shirya fita ƙofa a buɗe take, daga su har ku ɗin, tana faɗa ta juya zata bar wajen.

Cikin tashin hankali Bilal ya shiga gaban ta, hawaye har ya fara cika masa ido yace, dan Allah ki faɗa mana gaskiya me mukayi miki me yasa kika kawo mu nan, ko ba kidnapping ɗinmi kikayi ba amma meye dalilin ki na kawo mu nan, kin rabamu da kowa namu, duk da bakya musguna mana kina bamu kulawa yanda ya kamata amma meye dalili, suma kuma waɗannan su waye su da suke cewa sato su kikayi?

Wani banza kallo Hajja Mama ta kuma watsa masa tana ya tsina fuska, tace; "ni ba kidnapping ɗinku nayi ba dan babu abun da zanyi da kuɗaɗen ku, kai ka taɓa ganin anyi kidnapping ɗin mutum kuma ambarsa haka, dan haka idan zaku kwantar da hankalin ku ku cigaba da zama ku kwantar idan kuma bazaku kwantar ba ku cigaba da ɗagawa kanku hankali dan babu me fita daga nan gurin, matsa min, bani hanya in wuce, sannan duk wanda yayi yunƙurin fita daga falon nan ma, sai ya ziyar ci lahira kana saka ƙafar ka awaje to ku sani kamar ka jefa kanka cikin kabarin kane, dan babu abun da zai hanani kashe mutum, kana mutuwa kuma zamu bawa karnuka gawar ka, dan haka duk wanda ya shirya mutuwa a cikin ku ya iya fitowa yanzu ma basai anjima ba. Tana kaiwa nan tayi ficewar ta...,

Duk saranda sukayi babu me ƙwaƙƙwaran motsi, dan sunma rasa abun cewa, musamman Bilal da Zaida su jin sune ma ya bar gangar jikin su, dan jin abun suke kamar almara kamar ba gaske ba, basu taɓa tunanin hakan daga gare ta ba.

Faheema ce ta samu damar cewa; "daman wannan matar daga ganin ta bazatayi mutunci ba kana ganin ta kasan muguwa ce, kuma wallahi kidnaper ce ita, ni da har cikin gidan mu taje ta ɗauko ni.

Da sauri Zaid ya ƙarasa gaban su cike da rashin kwanciyar hankali, yace "dan Allah da gaske kike to taya ta ɗauko ku, nidai bada haka ta ɗauko ni ba, wasu ne suka biyo ni ta taimake ni tundaga nan kuma ban sake sanin inda nake ba, sai anan gidan, kuma tace min zata mayar damu ai tana tsoron mu fita ne mutanen da suka biyo ni su kashe ni, shiyasa take son na zauna anan zuwa wani loƙaci, ashe duk ƙarya take min.

Ɗayar ce ta kalle sa tace "haka take yi dan nima kusan hakan tayi mun, muna tafiya ta sa aka ɗauko ni, dan Saida suka fara ƙwace min mota ma sannan ta sa aka ɗauko ni, mu biyu muke tafiya da ƙawata amma ni kaɗai suka ɗauka, dan sunga mahaifiya ta tana da kuɗi shiyasa ɗayar kuma da suka san babu abun da zasu samu idan sun sato ta ai basu ɗauko har ita ba...

"Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un kawai Bilal yake maimatawa ƙafafun sane suka shiga rawa da sauri ya zauna agun danji yake yana shirin faɗuwa ƙafafun sa bazasu ɗauke sa ba, take shima ya shiga tunanin yanda ta ɗauko sa daga cewa zata taimaka masa ta fito da shi daga rufewar da ƴan matan nan sukayi masa tana fito da shi tasaka sa a mota da sunan zata kai sa gida, shima dai kuma daga haka dai farkawa yayi ya gansa a gidan koda ya tashi ya tambaye ta sai cewa tayi ai bacci yayi suna tafiya ta tashe shi yaƙi tashi da har zata sauke sa saiga wasu nan sun biyo su suna cewa ta basu yaron dake cikin motar ta ta, hakan yasa ta tayar da motar da gudu har ta ɓacewa masu binsu shiyasa kawai ta kawo sa gidan ta, amma sunyi waya da mahaifin sa yace zaizo ya ɗauke sa ta ajiye sa agun ta har sai yazo kar ta bari ya fito saboda mutanen da suke neman sa kashe sa zasuyi, shiyasa ya tsorata sosai da abun da kunnuwan sa suka jiyo masa....

*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*

*COMMISSIONANER*

Tun ranar da abun ya faru aka ji masa ciwo a ƙafa hakan yasa ya zame da ƙyar ya sha zuwa gida,, dan harda saran wuƙa a gefen hannun sa, hakan yasa shi zaman jinya a gida, koda ya fara jin sauƙi baiyi gaggawar fitowa ba, gashi wayar sa ta faɗi a gun so yake ya nemi Magana ɗaya suyi magana da shi akan batun ƴan matan da shi har yanzu ƙidurin sa yana nan na ɗaukar fansa akan ƴan matan musamman yanzu da suka sake yi masa illa ta sanadin su, gashi kuma sun haye ba tare da komai ya same su ba, shiyasa yake so ya sake shiri na musamman akan su, dan alƙawari ya ɗaukar wa kansa sai ya tarwatsa rayuwar su gaba ɗaya...

Tun safe ya tashi ya fara shirin fita aiki, yayi shirin sa tsaf, yana shirin fita daga ɗakin matar sa ta shigo ɗakin bakin ta ɗauke da sallama amma kana ganin yanayin ta kasan ba lafiya ba.

Tsayawa yayi yana kallon ta tare da cewa "lafiya kuma me ya faru naga yanayin ki haka, takardar dake hannun sa ta miƙo masa, cike da damuwa tace; "sun ce na baka sannan kuma wai awa 24 da huɗu suka baka.

Karɓa yayi ya shiga warware ta, a razane ya ɗago ya kalle ta yana zaro ido kamar zasu faɗi ƙasa, sakin takardar yayi a hankali yana kuma binta daɓas ya zauna a ƙasa, a hankali ya fara furta Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un, ya furta ta tafi sau biyar hular dake kansa ya zare ya ajiye ta gefe, take gumi ya shiga tsatstsafo masa ta ko ina sai muzurai yake da idanu yana rarraba ido.

Matar ce ta ɗauki takardar itama karantawa tayi tana gama karantawa ta ɗora hannu akai "na shiga uku, Abban su me kayi haka wane laifin ka aika ta aka kore ka daga aiki, Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un ina zamu shiga idan suka kore mu daga gidan nan ina zamu koma mun shiga uku Abban su kayi wani abun mana ka tashi kaje ka basu haƙuri kar su kore ka, basu san baka da lafiya bane baka basu san da hutun da ka ɗauka da dalili ba, me yasa zasu kore ka saboda rashin imani ma da tausayi kana zaune kana jinyar babu wansa yazo ya dubaka, sai ranar da kake shirin komawa, za'a wani aiko maka da takardar dakatar da aiki me yasa ma baza su bari kaje can gurin nasu ba, sai kawai ayims aike saboda rashin ɗaukar ka da muhimmanc.....

A zafafe ya miƙe tsaye cikin daka mata tsawa yace "ke Malama kimin shiru haka, ya isa haka!

Cikin sauri ya hau cire kayan aikin nasa ya sanya na gida, a cikin minti da baifi ɗaya ba zuwa biyu ya gama shiryawa ko kallon inda take bai kuma yi ba ya fita fuuuu... binsa kawai take da ido bata kuma gigin yi masa wata maganar ba.....,

*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*

*LAUTAI*

Khalifa da ya fito daga gidan, can gida ya koma, Allah ya taimake sa babu kowa a gidan dan haka yana shiga shiryawa yayi ya ɗauki duk abun da zai ɗauka, ya kuma fita daga cikin gidan cikin sauri, dole ya bar motar sa a gida saboda baisan garin ba dole saidai yayi tambaya yaje tasha ya hau motar haya, saida ya sake komawa gidan da ya ajiye Fateema ya tambaye ta garin sannan ya kuma fita.

Tasha yaje ya hau motar Kano a daren, basu suka sauka ba sai wajen ƙarfe, biyar na safe loƙacin anata sallah, baisan ko ina ba baisan kowa ba, haka ya zauna a masallacin da su kayi sallahr, sai da gari ya fara haske sannan ya fito da tambaya ya kuma samun inda zaije ya hau motar garin da zaije, ko karyawa bai tsaya yayi ba ya kuma tarar wata ya hau kai tsaye aka wuce garin Lautai da shi, bayan sallar azhar suka sauka, nan ma dai saida ya sha wahala kafin ya samu ma aka kula sa, da ƙyar ya samu aka kaisa wani gida, saida da ya ɗan fara bayani sai aka ce masa ba gidan bane, nan yaci gaba da tambaya amma bai samu ba, har wajen ƙarfe huɗu yana garari bai samu inda aka sanshi ba,

Masallaci yaje yayi sallah la'asar, yunwa ce ta fara damun sa hakan yasa ya fara neman abun da zaici, yaga ana siyar da abincin siyar wa amma bayajin zai iya ci, wata ƴar kasuwa ya ƙarasa inda yaga ana siyar da abubuwa da yawa, nan ya samu ya siyi gurasa kawai ya samu guri yaci, ya sha ruwa,

Tunani mafita ya farayi dan ya cire rai kuma baya so ya koma gida ba tare da ya samu labari ba, ganin yamma nayi masa yasa ya kuma tashi har zai koma cikin garin sai yaji ƴan acaɓa na cewa "Lautai ta biyu, kai ƴan mata ina zaku? Kuzo ku hau mu tafi.

Tsayawa yayi yana kallon masu mashinan, nan dai yaji suna ta cewa Lautai ta biyu sai kawai tunanin sa ya basa ko ya gwada zuwa indai har akwai wata Lautai ɗin to ai inajin ma ita ce, kenan wannan ta ɗaya ce waceen ta biyu, tunawa kuma da maganar da tayi masa bata san garin ba kawai sunan sa ta sani zai iya yiyuwa kenan bai gaya mata ta farko ba ko ta biyu. hankalin sa ne ya kwanta da hakan da yaje kawai ya gwada zuwa can ɗin ko zai dace.

Juya akalar sa yayi ga zuwa wajen ƴan mashinan, yana zuwa suka ce "Malam ina za'a kai ka?

"Lautai ta biyu.

Nan ya hau mashin ɗin mai mashin ɗin yaja suka tafi, saida sukayi tafiya sosai sannan ɗan acaɓan yace "malam wace unguwar zaka sauka?

"Wallahi ni baƙo ne bansan ko ina ba wani gida de nake nema idan ka sani sai ka kaini, gidan Ali Bashir yana da ɗa Shu'aibu.

Shiru ɗan azaɓan yayi yana tunani, sai can dai yace "gaskiya bansani ba saidai ko in tambaya zamuyi, nan suka fara tambayar mutane wasu suna cewa basu sani ba, daga ƙarshe dai da me mashin ya gaji sai yace bari inkai ka gidan me gari in yaso sai yaba da cigiyar sa ko acan cikin gari yake, ko kuma shi yasan shi, da to ya bishi kawai dan bashi da zaɓin da ya wuce hakan.

Nan ya kai sa gidan me gari ya sallame sa ya juya, da ƴar jakar sa ya ƙarasa wajen mutanen dake wajen, yayi musu sallama daga haka ya faɗa musu gurin me gari yazo nan akai mishi iso har gaban sa.

Bayan sun gaisa ya sanar da shi abun dake tafe dashi, take kuwa wani dake gefen me gari yace "ai ɗan nasa ya mutu ko? wanda yake aiki a Kano daga ƙarshe kuma yayi aure bayan auren nasu aka kashe shi shi da matar da ƴar su guda ɗaya koh.

Cike da jin daɗi Khalifa yace "Eh...Eh. shine kuwa.

Nan ƴan gurin na suka fara ɗaukar maganar kowa ma ya gane wanda ake magana, sai da suka gama kace nace ɗin su, sannan me gari ya kalle sa ya ce; "yaro saidai gaskiya wanda kake nema ya daɗe da barin garin nan kuma babu wanda yasan inda ya koma, amma yanzu dai za'a raka ka gidan ɗan sa akwai ɗan sa guda ɗaya da ya rage again nan, za'a raka ka inyaso daga nan sai su faɗa maka inda yake, ina fatan dai lafiya ko?

Khalifa yaji daɗi baiji daɗi ba, da sauri yace "Ehh lafiya ƙalau.

"To...To Masha Allah bari ayi sallah sai a raka ka ko?

"To nagode"

Bayan anyi sallar magriba aka raka sa gidan, saida suka tura yaro yayo musu sallama da Malam.

Tare suka fito da yaron, nan yaron ya tafi, shima wanda ya rako sa ya juya ya tafi cike da rashin sanin juna, Khalifa ya gaida shi.

Da fara'ar sa ya amsa sannan yace "yaro mu shiga daga
End Ads