hannun ta wannan karon kwa sosai tayi murmushi har haƙoran ta na fitowa tace; "To basawa Sarkin ƙarfi, ga kuma masoyiyya....hakannan taitabin su tana murmushi tana shafa hotunan.....✍️✍️✍️
[3/5, 11:53 AM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
(THE WRITER OF 💅SARKI SAMEER 💅)
______________________________
*_episode 20💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
Bissmillah.....✍️
____Ta daɗe a gaban hotunan kafin ta matsa daga gurin, jakar ta kuma ɗauka sai ta nufi wani waje kai kace gurin bango ne kaɗai amma tana yaye wani abu a gun sai ga wata ƙofar ƴar ƙarama da bata fi wucewar mutum ɗaya ba, kuɗaɗe taf a cikin ɗakin jakar hannun ta ta buɗe sannan ta shiga irga kuɗin tana jere su akan wata kanta ɗakin babu komai a ciki kawai zagaye yake da glass anyi sa hawa hawa kuma ko wane hawa da kuɗi akai, jere su ta kumayi tsaf sannan ta maida ƙofar yanda take ta rufe,
Ɗaukar magen ta kumayi ta ɗorata a kafaɗa, sannan ta fita daga ɗakin, a falon ta tsaya tare da samun kujera ɗaya ta zauna, tana faman shafa bayan magen da hannun ta,
Sake miƙewa tayi ta nufi wani ɗan siririn corridor wanda jikin bangon duk glass batayi wata tafiya ba ta yaye wani maroon ɗin labule tare da zuge wani glass ɗaki ne tamƙameman gaske, sai gadaje a cikin sa hawa hawa kamar irin na ƴan boarding school saidai sun banban ta da irin su domin waɗannan masu kyau ne na katako kuma da girman su ba ƙananu bane duk guda ɗaya hawa biyu ne a saman sa, a ƙalla dai zasu kai wajen guda goma kowanne da hawan sa.
A hankali ta ƙarasa bakin wani gado dake can jikin bango, tsugunnawa tayi tana kallon sa tare da shafa kansa, tana ɗan murmushi, a hankali tace "sleeping boy, har yanzu ba'a tashi ba.
Kamar yasan me take cewa ya wani haɗe fuska alamar shagwaɓa tabi jiki, yana ɗan turo baki gaba, cikin baccin ya jawo hannun ta ya haɗa da filon dake hannun sa a riƙe ya haɗa su ya kuma ɗora kansa akai yana gyara kwanciya, tare da warwara ƙafafun sa sukayi ɗaiɗai duk girman gadon amma duk ya kusa cinye sa,
Kallon sa kawai take fuskar ta cike da murmushi, da dayan hannun ta ta shafa kwantaccen gashin sa da ya sha gyara sai sheƙi yake,
Ta daɗe agun bata tashi ba kafin ta samu ta lallaɓa sa cikin dabara ta zare hannun ta sannan ta miƙe daga gurin, gadon saman tabi da kallo sai suka haɗa ido da wanda ke kwance agun, gira ɗaya ya ɗaga mata yana mata murmushin gefen baki, daƙuwa ta jefa masa tace yaron nan ka rainani nace ka dena yi min irin wannan kallon kaƙi ka daina ko?
Girar ya kuma ɗaga mata yana miƙewa zaune tare da zuro ƙafafun sa, yana bin nakan gadon da kallo yana ya tsina fuska a hankali cikin taɓe baki ya ce; Hajja Maaa jifa yanda wannan yaron yake bacci gatan da kike masa ko a gidan su baya samu gatan yayi yawa ni kuma ko rabin sa bakya min to wallahi gida zan bar muku kun rabani da iyaye na kun kawo mu kuna azabtar dani to Allah sai kun maida ni gida kuma yau yau ɗinnan, tallaƙe masa ƙeya tayi tana cewa ai ƙofa a buɗe take sai ka dawo,
Haɗe rai yayi yana tutturo baki, ya duro kan gadon ƙasan, akan na kwancen ya faɗa yana danne sa da mugunta,
Bawan Allahn ka me makon ya tashi saboda nayin gardi da yaji sai kawai ya sa hannu bibbiyu ya rungumo sa,
Haushi ne ya kamasa ganin ya wani rungume sa sai kace mace, ya fara ƙoƙarin ɗaga sa, amma sai kawai ya kuma riƙo sa, yana magana ƙasa ƙasa....
Shiru sukayi danjin me yake cewa sai kawai sukaji yana cewa; "Please one more please don't leave me again, kiss me kiss me yana faɗa yana jawo fuskar ƙato zaiyi masa kiss.
Shi kuma cikin zaro ido da mamaki duk yama fara kiɗimewa yana ƙoƙarin ƙwacewa amma ya kasa, Hajja Maa kuwa babu abun da take musu sai dariya da take ƙunshewa.
Bai ankara ba kawai yaga yayi juyi dashi ya koma ƙasan gadon shi kuma yana ƙoƙarin hayewa kansa, har ya hau kansa idon sa a rufe kuma baidai sambatun da yake ba,
"Beab Please don't go don't go, yana faɗa ana sake kai bakin sa kan fuskar sa,
Ganin dai da gaske yake bashi da hankali in ya zauna a banza gardi zai sumbace sa, daddagewa yayi da iya ƙarfin sa ya buga masa duka a damtsen hannun sa yana tura sa baya, ya faɗi kan gadon, sai loƙacin ya ware idon sa akansu yana sakin ƴar ƙaramar ƙara yana ɓata fuska kamar zai fashe da kuka...
"Banza ɗan iska wallahi da ka sumbace ni sai na kashe ka kama rasa wanda zaka danne sai ni ban girme ka ba, yana maganar yana kai masa duka,
Hannu yasa yana karewa dan ba ɓata loƙaci ƙwaƙwalwar sa ta zayyano masa duk abun da yayi shi kansa saida yaji kunya ta kama sa, ga Hajja Mama dake kansu tana musu dariya,
"Wallahi Bilal bazan yafe maka ba Allah ya isa dan ka cuce ni banza me kama da mata, ɗan daudu kawai,
Dafe kansa kawai yayi cike da taƙaicin kansa bai iya cewa komai ba sai kawai saukowa daga kan gadon da yayi yana ya mutsa gashin kansa, yana sakin tsaki,
"Wallahi Hajja Mama kin lalata yaron nan taɓarar sa ta fara wuce gona da iri aure yake so tunda har ya fara mafarkin ƴan mata,
Sosai take dariya ta ce; "Allah ya shirye ka Zaid baka da kirki ai kane da tsokana ni yamin daidai da yayi maka haka, gobe ma sai ka kuma danne sa, sai kaje wataran ka karya masa ƙafa ma da wannan shegen jikin naka irin na ƴan can garin....
Haushi ne ya ishe shi ya tashi fuuuu ya nufi hanyar banɗakin da Bilal ya shiga, takun sa biyu ta sa hannu tajawo sa ta baya ta mayar da shi kan gadon tace; "Allah ka taɓa sa ni da kai ne sai naga me ƙwacen ka a cikin gidan nan....
Tunda ta fara maganar kawai hannun ta yake kallo da ta jawo sa da hannu ɗaya duk girman nan nasa ya ɗanyi mamaki amma sai ya basar ya danne mamakin a ransa.
"Kana mamaki ko to kaɗan ma ka gani inka shigo hannu na dakan sakwara sanyi maka...
"Lalle kin so ki ziyar ci lahira loƙacin baiyi ba, faɗa da ni ai ba duk kai ba,
"Hmmm kawai tace masa tana girgiza kai aranta tana cewa yaro yaro ne, a fili kuma sai ta ce; "ka tashi muje ka ɗauko muku abincin ku, kuma kar ka sake ka taɓa min Boy ɗina, komai ya wuce.
Ƙura mata ido yayi ko ƙiftawa bayayi har ta gama bayanin bai ɗauke idon sa akan ta ba, saida ta kai ƙarshen zancen nata sannan ta lura da kallon da yake mata, sai ta haɗe rai tana watsa masa hararar tace "Zaid.! Zaid.!! Zaid.!!! Sau nawa na kira sunan ka?
Bai amsa mata ba kuma bai daina abun da yake matan ba,
"Wallahi ka fita a ido na in rufe wai yaushe kamin sannin da har ka rainani haka,
"Tun ranar da kika sato ni.
Duka takai masa ya goce yana dariya ya miƙe tsaye yana jan hannun ta suka fita daga ɗakin.....
Bilal daman fitar su yake jira, suna fita kuwa ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, koda ya shigo dakin kan gadon ya koma ya zauna, har yanzu jikin sa bai dawo normal ba, dafe kansa yayi tare da ce wa; "Why you want to come my dream ba dama inyi bacci sai kin addabe ni, mtsww ya ɗanyi tsaki, yana furzar da iska daga bakin sa, "Bea ya kuma furtawa a hankali, tare da lumshe idanun sa yana sake buɗe su, can kuma sai ya saki murmushi tare da kuma faɗawa kan gadon ya kwanta yana sake rufe idanun sa, a haka yana ta tunani bacci ya kuma yin gaba dashi daman ya lafiyar kura bare ta ƴayan ta... (Kunsan yana tare da cutar bacci ga kuma shauƙin Bea da bamu san a inda ya samo ta ba)
Zaid ne ya shigo ɗakin cikin sauri yana shigowa yayi turus yaja ya tsaya yana kallon sa, cikin sakin baki ya ƙaraso gurin yana cewa Allah yaye maka Bilal daga fitowa sai komawa bacci ko abinci ma bazaka tsaya kaci ba, duka ya ɗala masa a cinya zumbur kuwa ya miƙe zaune yana sosa gurin, idon sa har ya ɗan cicciko da ƙwalla cikin murayar kuka yace "Zaid wai meye matsalar ka dani ne ka takurawa rayuwa ta, to Allah ya isa kaje kai da Allah yana faɗa ya mike tsaya yana cika yana batsewa, dan sosai yaji zafin dukan da yayi masa,
"Banza me sumbatar namiji jarabar taka har baka tantance wanda ka riƙe macece ko namiji, sai ka faɗa kace kai aure kake so ayi maka aure tunda har kakai munzalin ka fara mafarkin ƴan mata...
Banza yayi masa har yagama kwakwazon sa da surutan sa bai tanka masa ba, daga ƙarshe ma yana saka gajeren wando wandon da ƴar singlet ya fice yabar sa a ɗakin.....,
Yana fita shima yabi bayan sa yana bambamin yaƙi kula sa, har saida Hajja Mama ta dakatar dashi sannan ya rabu dashi,
Zama yayi akan center capet ɗin dake tsakiyar falon, Hajja Mama ce ta zuba masa abinci sannan ta ɗauki cokali da kanta ta ringa basa abaki, saida taga Zaid ya zuba musu ido sannan tayi murmushi tace kaiɗinne ka girma shiyasa bana baka zo ka karɓa.
Watsa mata harara yayi yace; "sai yanzu kika tuna dani bana ci... Tashi yayi daga gurin yana kiran KITI..! KITI..! da gudu wannan kyakkyawar magen ta taho gurin sa tsugunnawa yayi ya ɗauke yana mata wasa ya nufi wani ɗaki da ita dake cikin falon.....
Saida ta gama basa yaci ya ƙoshi sannan ta rabu dashi ya kora da ruwa, zama sukayi suna ta hira agun tana janye shi da zance saboda kar ya koma bacci, daga baya ma shima Zaid dawowa yayi suka ci gaba da hirar tare kamar ma wani abu bai faru ba, saida sukayi sallar magriba da isha'i sannan ta sa duk suka koma ɗakin su ta tura musu magen, tace su kwanta amma gobe da safe baza su ganta ba, sai wajen yamma zata shigo duk abun da suke buƙata zata sa a kawo musu... Badan sun so ba haka suna gani ta fita daga ɗakin kuma ta ƙullo su ta waje daman haka take basa fitowa sai tana nan,
Tana rufe su ta fita daga falon gaba ɗaya, wata hanyar ta sake nufa, wani ɗaki ta tura shima kamar yanda wancen yake haka yake saidai shi gadajen su na ƙarfe ne kuma basu da girma, ga mutane ne da yawa a ciki duk sun kwanta sakamakon dare da yayi, ƙofar ɗakin tasu ta ƙarfe ta samu wata guduma dake gefen gurin wajen ajiye ta, buga musu tayi da ƙarfi sai wajen huɗu ai ba shiri duk suka farfarka wasu na durowa daga gadon, daman sun san ita ce dan haka duk suka zube a ƙasa suna sunkuyar da kai, duk maza me kuma matasa wasu ma yara ne a cikin su,
Kamar ba ita ce wacce tayi dariya ɗazu ba ta haɗe rai sosai tace; "Waye yayi ƙoƙarin guduwa wancen satin?
Gana ɗayan su suka shiga nuna wani matashi da kana ganin sa kasan zai aika ta, wuri wuri ya farayi da ido yana muzurai.
Takowa tayi tazo har gaban sa, ta ɗago sa da gashin kansa tana kallon fuskar sa cikin shouting tace; "Kai ƙaramin ɗan iska da har kake tunanin barin gidan nan, to kasani wannan gida ƙaddarar kace tunda ka shigo sa babu fita saidai a fita da gawar ka, duk wanda ya shigo gidannan ya shigo kenan har abada bazai fita, kasa wannan a ranka, ta'addancin ka babu inda zai kaika duk abun daka kake taƙama dashi gidan kazo, tana gama faɗar haka ta tofa masa yawu a fuska, ta nuna wasu majiya ƙarfi dake cikin ɗakin tace ku hukunta sa daidai da abun da ya aikata, tana faɗar haka ta juya ta bar ɗakin....
Wani ɗakin ta kuma shiga duk de the same da sauran, amma su kuma mata ne, kuma basu kai mazan yawa ba, tana shiga da sauri duk sukayi kanta suna ce wa; Hajja Mama Raliya na na kuda tun ɗazu da safe tana buƙatar taimako ki taimaka a fita da ita kar ta rasa kanta dan Allah ki taimaka.
Tsayawa tayi tana binsu da kallo tare da nazarin su ɗaya bayan ɗaya, saida suka gama sukayi shiru dan kansu, sai loƙacin tace; "kowa ya koma ya kwanta, badan sun so na duk jikin su babu ƙwari suka ja da baya suka koma inda gadajen su suke,
Ƙarasawa tayi gurin gadon matan, tana kalle ta sama da ƙasa, sannan tace; "waye yayi miki cikin?
Inda inda ta fara ta kasa bata amsa.
Saidai ta daka mata tsawa ta maimai ta mata tambayar sannan cikin fashewa da kuka tace; "Ƙanin mijina ne.!
Kika kashe mijinki ki ka kwanta da ƙanin sa ko saboda jahilci.
Shiru tayi tana sunkuyar da kanta ƙasa.
Cikin ki watan shi takwas ina lissafe ƙarya kike ba na ƙuda bace, kinyi na farko kinyi na ƙarshe da zaki pretending ɗin naƙusa kike yi dake da masu goya miki baya duk zanyi maganin ku, kunci sa'a ina da uzuri yanzu amma da sai kunyi na damar aikata hakan da kukayi, useless kawai tana kaiwa nan ta juya ta fice daga ɗakin cikin sauri....,
Wani ɗakin ta kuma shiga, saidai wannan ba mutanene a ciki ba kayayyaki ne a cikin sa, bindugu kala kala da wuƙaƙe ga kayan sakawa nan a rarrataye da fuskoki cike dai yake da kayyaki kala kala wasu ma bansan sunan sa ba,
A cikin gurin ma akwai wani ɗan ƙaramin ɗaki ta shiga amma cikin shi gaba ɗaya duhu ne, zuwa wani ɗan loƙaci ta fito daga ciki tayi shirin doguwar abaya sai tayi rolling da mayafi sai tasaka face mask sannan ta kuma ɗora niƙab akai, wata ƙatuwar jaka ta jawo Wuƙaƙe biyu ta ɗauka ta ɗaga rigar ta tasa ka su ajikin wandon jikin ta, jakar kuma ta loda wasu kayan a ciki har da bindugu ta haɗa, rataya ta tayi abayan ta, sannan ta fita daga, ɗakin nidai binta kawai nake bansan inda ta dosa dan hanyar da ta biyo ɗazu bata nan ta bi ba, wayar dake hannun ta shiga daddanawa sannan ta kara a kunnen ta, "Hello komai ready gani nan na fito mu ku tabbatar da komai ya daidai ta kar ku bari wata matsalar ta faru wannan ce damar mu ta ƙarshe kowa ya tsaya cikin shiri na taho da kayan aiki, ku ankare sosai... Kashe wayar tayi daidai loƙacin da ta ƙaraso inda wani ke kan mashin, hawa tayi tana hawa ya tayar da mashin ɗin suka ɗauki wata miƙaƙiyar hanya........
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
*Alhaji Ɗan Ijje*
Alhaji Ɗan Ijje ya zama kamar tsohon mahaukaci a cikin police station tun safe yake zarya yana jiran su kawo masa ɗan shi ,sai aka samu kuma suka zo masa da wannan mummunan zancen na antafi da kuɗi kuma babu yaron sa,
"Alhaji dan Allah kayi haƙuri duk inda ma suka shiga zamu nemo su, yanzu abun da zamuyi shine dole mu samu waɗanda suka iya shiga ruwa, duk yanda akayi suna da kusan ci da kusa da ruwan nan, nidai a nawa tunanin indai kuma ba bayan tafiya mu ba tsohuwar ta fita ta canza hanya.
"Wacce magana kuke haka sai da nace muku ku basu kuɗin kar kuyi wani yunƙurin kai musu hari, ni kuɗi ba damuwa ta bace, wallahi ko kusa a fito min da yaro ko kuma ku dawo min da adadin kuɗin da na baku in bahaka ba kuma kowa sai ya raina kansa,
"Wai zakai faɗa da hukuma ne kaf nan akwai inda zaka je ka kai ƙarar mune muma fa akan aikin mu muke ko ɗanka ne kawai ɗa nima da yaro na, dole mu bi komai a hankali mu lalubo inda suke nasan bazasu kashe mana yara ba kawai dai ka tanadi wasu kuɗi nasan zasu ƙara neman mu, anan zamu bi diddigin inda suke koda kuwa sun kira da privet number akwai wacce zata iya bibbiyar mana inda number take ko ma a wacce ƙasar ne, kaide ka bar komai a hannun mu, dole mu kamasu muyi musu hukuncin abun da sukayi bayan wahalar da hukuma da sukayi ga shi sun ɗauki ɗan commissionana laifi kan laifi....
Shiru Alhaji ɗan Ijje yayi yana nazarin kafin daga bisani yace; "Me zai hana a samu ƙarin wasu ƴan sandan daga wasu jahohin ayi musu runduna guda aje, idan baza su bayar da su ta salin alin ba sai a ɓullo musu ta bayan gida..
"Eh hakan ya kamata muyi banzaci abun nasu yakai haka ba, amma yanzu sun kawo ni ƙarshe dole mu ɗauki mummunan mataki a kansu.
Alhaji ɗan Ijje yace "wannan gaskiya ne, munyi magana ma da tsohon governor daman jiran