x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 8 - SU WAYE SU

  • 21001 words
  • 24000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 146

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
gaban mota da kuma waɗanda aka kaɗawa hantar ciki, su suna musu kallon me ya faru ne kuke jira baku fito da su ba, su kuma suna musu kallon meye kuke kallon mu me kuke so mu ce muku,

Me tuƙin ne ya matso kusa dasu yace; zaku fito ne ko jira kuke sai an fito daku,

Beenish tace dade yafi, inda hali ma ku bayan gadon bayan ku muhau ku sauke mu a ciki.

Cike da mamaki yake binta da kallo tabbas sai sunyi maganin fitsararrun nan sai sun sauke musu abun dake rawa akan su, juyawa yayi ya kalli HASHIM (wanda aka riƙewa hannu) sai yaga kawai ya sunkuyar da kansa, nan ya fahimci Something is wrong wajen tahowar su.

Zai juya kenan kawai ya tsinkayo muryar Ameela tana cewa "kaje kace Khamis Adam Ibrahim yazo ya shigar damu tunda shi yasa a kama mu akan jakin ɗansa kace masa idan ya isa yazo ya fitar damu da kansa shine zamu yarda ya cancanci muƙamin da yake kai,

Bashi kaɗai ba gaba ɗaya ilahirin ƴan gurin babu wanda be razana da maganar su ba, cike da ɗumbin mamaki da al'aji kowa ya zubo musu idanu wasu nason kallon fuskar su,

Dalla malamai ku daina kallon mu ko akwai wani abun kallo ajikin mu, mtsw Ameela ta daka musu tsaki ta ɗauke kai, harda ƙara miƙar da ƙafa tana gyara zama, suma sauran duk hakanne dan ita Babyn baby ma zamawa tayi ta kwantar da kanta akan cinyar Aunty Babba,

Hashim ne yayi sauran ƴan sandar alama da ido kowa yabar wajen, nan duk suka fara shiga cikin station ɗin saida yaga barin su wajen sannan yabi bayan su, suka barsu sukaɗai a cikin motar, shi nan yayi hakane dan yabasu dama su gudu dan shi yafi son tafiyar tasu akan zaman nasu,

Yana shiga duk ya tarar dasu a tsatstsaye kafin ma yace wani abu saiga DPO nan ya fito daga office ɗin sa cikin ɓacin rai, yana fitowa ya balbale su da faɗa kamar zai cinye su,

Sude babu wanda yace masa uffan har yakai aya sannan yabasu umarni da kowa ya ɗauki makamin idan basu fito ba yabasu go ahead suyi musu dukan tsiya a cikin motar sannan su fito da su su sakasu a sale a ƙulle su kuma minti goma yabasu, yana gama faɗa musu ya kira number commissiona ɗin ya sanar da shi halin da ake ciki...

Kan kace me kowa ya gyara shirin sa da waɗanda suka shigo da kuma waɗanda suke ciki haka suka haɗu wajen su goma sha shida, masu daukan kulki nayi masu ɗaukan gora wasu kuma sunce hannun su ya wadatar da su,

Hashim kam babu wani shiri da yayi inbanda dariya da yake musu a cikin rai dan yasan zuwa yanzu ai tuni sun fice daga gurin bazasu tarar dasu ba,

Hardayin layi sai kace zasu tafi farautar ƙartin maza,

Duk da haka Hashim ne a gaba saboda shine babban su, yana gaba suna binsa a baya har suka fito suka ƙara so wajen motar,

Gaban Hashim ne ya faɗi da yayi ido huɗu da su yanda yabar su haka ya dawo ya tarar dasu suna ta hirar su, shi babbar damuwa sa shine kar ayi musu wani abun su ɗauka shine suje su rama akan nasa iyalin shiyasa ya shiga tashin hankali da ya gansu, daga inda yake yaja burki ya tsaya su kuma ragowar suka fara raba kansu kowa ya tsaya a matsayar sa, aikwa sunyi kyau saida babu wanda ya riƙe bindiga saboda ba'abasu lasisin taba, mutum biyar suka nufi wajen motar suna shirin hawa, mutum biyu ne suka fara ɗanewa saidai suna takawa, suka jiyo jiniyar motar sa, hakan yasa suka dakata da shirin shigar da suke,

A guje suka shararo motocin su yana gana ana tuƙa sa sai motoci uku dake bayan sa, a jere sukayi layi sannan a kayi sauri aka zo aka buɗe masa yana fitowa duk suka ƙame kowa yana sara masa,

Bai kalli kowa ba saboda ɓacin ran dake cinsa, cikin ɗaga murya ya daka musu tsawa yace; ku wasu irin banzatar ne daman haka ake aiki, har yanzu ku tsaya zuba musu ido kukayi, su waye su da har suka gagare ku, saboda shirme har suka gaya muku abu kuma kuka kasa yi musu komai jira na kuke kenan to wallahi idan bakuyi wasa ba duk sai kun rasa ayukan kan ku, yanayi yana zazzare musu ido shima kamar zai rufe su da duka,

Cikin tsawa ya juya ya kalli ƴan sandan da suka zo tare, ya kuma cewa ku me kuke jira..!?

Cikin hanzari suka sake sara masa sannan suka nufi wajen motar gadan gadan tunkan su ƙarasa ma na kusa da motar suka rigasu shiga,

Sunje daf da motar kawai waɗanda suka shiga suka dawo da baya tare da faɗawa kansu suma duk sai da suka zube a ƙasa.

Waɗanda basu faɗi bane da sauran suka tunkari ciki da sauri, saidai kuma suna shiga suka gansu a tsaye riƙe da hannun juna ko waccen su da spray a hannun ta, nan suka feshe musu fuska suma tare da sa ƙafa suka hankaɗo su waje, haka sukai tayi musu duk wanda ya shiga sai sun jefo sa ƙasa har saida suka ƙare.

Commisiona da DPO ne suka ƙaraso wajen baki sake, ƙara sowar su tayi daidai da tsalan da sukayi suka duro daga cikin motar basu dire ko ina ba sai gaban su, a kusan tare suka razana gana ɗayan su tare da ɗan ja baya, tunda suka saukko idon Commisiona ke kansu ya kasa koda ƙiftawa bare yayi motsi.

DPO ne ya shiga nuna su da hannu murya cike da mamaki yace "Dama kune.....!?

*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
[3/5, 11:44 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________


*_episode 8💧_*


💧💦محمدالرسوالله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

____DPO ne ya shiga nuna su da hannu murya cike da mamaki yace "Dama kune.....!?

Gaba ɗayan su suka zuba masa ido, suna jiran jin karin bayani game da wannan tambayar da yayi musu.

"Juyawa yayi ya kalli Commissiona cike da son gaya masa ko su waye su, yace; Sir waɗannan sune waɗanda suka ɗauke ɗan gidan Alhaji Ɗan Ijje, kuma su ake zargi da sace ɗanka da ake zargi, suma su biyar ne kuma abun da sukayi amfani da shi yanzu wannan spray ɗin da shi sukayi amfani wancan karan ma, halanne ya tabbatar da cewa sune, dan haka yanzu kamasu za'ayi kawai a miƙa koto su, daga jiya zuwa yau kalli yanda duk kowa ya sha aiki akan neman su, dole a haɗa musu da hukuncin wahalar da hukuma da kuma dukan ƴan sanda wannan babban hukunci ya kamata a yanke musu.

Juyawa yayi ya watsa masa kallo tare da kallon sa sama da ƙasa sannan ya kuma juyawa ya kalli ƴan mata dake tsaye ƙeƙam a gaban su, ganin yanda suke kallon sa yasa yayi saurin janye idon sa akan su, batare da ya kalli kowa ba yace; "DPO bana son inji kowa ya ƙara wata magana kuma ni basu suka ɗauke min yaro ba shima ɗan gidan ɗan ijje basu bane dan haka abar maganar anan ka jawa sauran kunne kar wanda ya kuma tada maganar case is closed...

Yana kaiwa nan bai ya juya yabar wajen ba tare da ya yarda sun haɗa ido da kowa ba.

Har ya ɗanyi nesa dasu, Ameela ta ɗaga murya tace "Wa kake so ya maida mu?

Cak ya tsaya yana damƙe idon sa ji yake kamar ya tona rami ya nutse agun haka yake ji, baice komai ba kawai yayi gaba motar da yazo da ita yaje ya buɗe baya sannan ya zagaya ya kuma buɗe wajen me zaman banza, sannan ya dawo ya shiga driver seat ya zauna, ya tayar da motar.

Ameela ce tayi gaba su kuma suka bi bayan ta suna takun su cikin kwanciyar hankali kamar masu tausayin ƙasa a tare suke tafiya takun wani baya wuce na wani tare suke ɗaga ƙafar su, kuma su sauke a tare.

Yau DPO ya ganewa kansa abun da yafi ƙarfin sa, dan kamar soko haka ya koma, yanda suke tafiya haka yake binsu da kallo baki sake, har suka ƙarasa wajen motar Ameela ce ta zagaya ta shiga gaban motar su kuma suka shiga baya tare da rufewa.

Yana jin sun rurrufe yaja motar yabar police station ɗin,

Nan suka bar DPO baki sake yakasa koda motsawa daga inda yake yakai wajen 6 minutes agun bai janye idon sa daga kallon gurin kamar ance masa suna gurin, da ƙyar ya janye ya mayar da idon sa kan ƴan sandan dake kwance wasu kuma duk sun tashi zaune saida idon nasu dishi dishi basa iya gani da kyau, a ƙalla sunkai kusan su ashirin amma ace wai mata ne sukayi musu haka, amma abun da yafi komai bashi mamaki abun da Commisiona yayi abun ya matuƙar ɗaure masa kai har na ya rasa wane kalar tunani zaiyi akan wannan lamarin wazai fara tunkara da wannan maganar....

*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*

Sallama ɗauke a bakin sa ya shiga tamƙameman falon da ya gaji da kayan duniya da ƙyale ƙyale ga wasu shegun kujeru haɗaɗu ƙirar Japan kalar white and butter milk, sai wasu shegun stairs triple ƴan uku da suka taho daga mahaɗa ɗaya tare da rarrabewa ko wanne ya kalli gurin sa, gasu a wani malmalkwaɗe jikin benan kalar butter ne sai wasu fararen fulawoyi da aka zagaye sa dashi, shi kansa saman falon da kuma fitulun dake jikin sa abun kallo ne dan zama zayya na muku shima ɓata loƙaci ne, kawai ya gaɗu iya haɗuwa ƙarshen haɗuwa, komai na falon abun kallo ne,

Ƴan mata ne su biyu kacal a falon duk girman nan nasa, sunyi rashe-rashe suna kwasar waku(abinci) jin sallamar sa tasa su dakatawa da cin abincin tare da maida duban su gare ɗaya ce ta amsa masa ɗaya kuma tayi saurin gyara zaman ta da kyau tanaƙara fuskan tar sa tare da tsayar da idanun ta akan sa kana ganin kallon in ka lura kamar ace kaza nayin ƙarƙara, bata ɗauke ba har ya ƙarasa shigowa ya zauna amma bai kalli inda take ba,

"Ya Aveed me ya same ka haka na ganka so week like ka fita aikin wahala,

Banza yayi mata dan yasa isgilanci take son yi masa, dan haka yayi mata shiru saima hannu da ya miƙa ya ɗauki lemon dake gaban ta ya fara sha,

Ɗayar ce tace; "Yaya sannu da zuwa ba magana,

"Yauwa sannu abun da ya iya ce mata kenan,

"Bro wai yau kuma dame aka haɗu ne naga sai wani shan shan ƙamshi kake ana magana kanayin shiru,

"Please FAHEEMA ina son munyi wata magana mai muhimmanci dan Allah, bansan wasa is serious talk.

Yanda yayi maganar is serious ɗin tasan dagaske yake, dan haka ta bashi attention ɗin sosai ta ƙara nutsuwa tare da fuskan tar sa face to face, sannan tace; Bro what do you want to me? Ina sauraron ka ɗan naga alama like U are fall in bad mood ban saba ganin ka shigo a haka ba, wa yayi attempting ɗin shiga rayuwar.

A jiye kofin dake hannun sa yayi sannan ya kamo hannun ta, ya ɗago ta ta dawo kan kujera ta zauna, tana kuma ƙara nazartar yanayin sa,

"Kayi shiru, kafaɗi anything what do want to say,

"Fahima daman ina son kiyi min...Sai kuma ya ƙara yin shiru,

"Oh my gosh! Ta faɗa tana dafe goshin ta da yatsun hannun ta, cike da zaƙuwar son jin a bun da yake son gaya mata.

Kallon fuskar ta kawai yake, yakasa gaya mata.

"Oya tell me don't worry da abun da zaka faɗa free me kasan banda any problem right?

Jinjina mata kai yayi alamar tabbas ta ƙasan ido ya kalli ɗayar dake ƙasa tana ta cin abincin ta amma itama hankalin ta yana kansu jira take taji me zai faɗa,

Hakan yasa Faheema fahimtar FADWA wace ta hana sa yin maganar dan haka sai kawai ta ɗan yi gyaran murya tare da cewa "Uhmm Fadwa Please we need space,

Wani abu taji ƙudum a ranta watakon bazaiyi maganar agaban taba kuma basu zasu tashi ba saidai ita ta tashi ta basu waje.

"Fadwaaa...!
Faheema ta kuma kiran sunan ta me cike da tuni.

"Okay, kawai tace sannan ta tashi ta bar gurin da plate ɗin abincin ta, tana ƙunƙuni a ranta har ta haye upstairs.

"You know what?

"Sai ka faɗa, ta basa amsa, tana gyara zaman ta,

"Taimako nake son kiyi min a gurin RK kinji,

"Na me?

Akan wannan lecturing ɗin da nakeyi I swear I'm so tired of this Allah kullum cajin da ake min da ban, kice ya taimaka yayiwa Dad magana ya sauya min aiki,

Dariya ta sanya tare da yin tsaki tace da wannan ɗan abunne yasa duk kayi haka me kuma ya ƙara faruwa a cikin school ɗin, yau ban samu na shiga ba banda lecture, nasan hakannan baza kazo da wannan maganar ba, kaifa kace kana so kuma yanzu kazo kace baka so how comes, how did you think Dad zaiyi accepting ɗin wannan maganar taka without for any reason.

Yakamata dai kayi tunani but any way zan taimaka maka I will try my best, bana so inyi encouraging ɗinka amma da sai ince kayi haƙuri kawai kaci gaba hakan ai ba faɗuwa bane ka daina tunanin matsayi mulki ko kuɗi a part from this nifa a tawa shawarar kenan, amma idan baka so wallahi zan gwada tambayar maka Allah ya sa a dace.

"Ameen yace a sanyaye a ransa yana tunanin yanda zai fara yi mata maganar ladies ɗin can da suke niyar rikita masa ttunani,

""Tunanin me kake inayi maka magana kayi shiru,

Ɗan numfasawa yayi sannan ya ce; Fasheema akwai wani aiki da nake son kiyi bayan wancen, dan nama fi son sa a kan wannan...

"Ɗazu muna cikin lecture wata yarinya ta saka mana ihu a ciki......nan ya kwashe labarin komai ya gaya mata har faɗansu da ɗan gidan Commisiona duk saida ya bata duk abun da a kayi a kan idon sa a kayi, loƙacin kuma da aka ɗauke su a motar ƴan sanda yabi bayansu yana shirin idan sun shigar da case ɗin yaje yayi canceling ɗin sa yafaɗi abun da yasan gaskiya ne a bashi belin su, dan shi sunyi masa daidai da sukayi haka, saidai yanda yaga sunyi da ƴan sandan kuma suka fita tare da shi kansa commissiona ba tare da yayi musu komai ba, hakan yasa abun yake tayi masa yawo akai dan sosai yakeji har ransa yana son gano ko su waye su,

"Kai Bro wannan maganar taka kuwa gaskiya ce? Mata fa kace.

Dungure mata kai yayi yace "Ni sa'anki ne me kika maidani zan miki ƙarya ne ko na saba yi miki, nima kaina abun yaban mamaki wallahi,

"For serious a bun yazo min unexpected, gaba ɗaya sai naji uncomfortable akan maganar nakasa gasgatawa,

"Zaki ji labari ai idan kinje gobe,

"Tabb, to ni yanzu me kake so inyi maka korar su kake so ayi ko kuma kamasu za'ayi ayi musu hukunci ko Dad ne zai ɗau mataki ko ya RK me kake so ayi danni dai bazan ma haɗa hanya dasu ba, suna yiwa mutane irin wannan murɗa haka ni da nake yage yage da ni kamar a hure,

"Ke dalla can matsala ta dake wallahi wani loƙacin ke banza ce,

"Niɗin kake gayawa haka to sai kaci gaba da maganar da banza ta faɗa tana shirin tashi daga wajen yayi saurin mayar da ita yana cewa; sorry just da wasa fa nake miki, kin san aiki da zakiyi min,

Shiru tayi masa tana kawar da kai gefe,

Bai damu ba da hakan da tayi, sai ya ɗan muskuta yace; "Ni duk wannan abubuwan da kika lissafo babu ko ɗaya da nake so, abun da nake so shine ina so kishiga jikin su ku saba har mu gano su waye su nima kuma zan sauya taku a makaranta so nake mu saba sosai dasu ki jawo mana su cikin gidan nan ni kuma daga nan zanji da komai in kikayi min haka kin gama yi min komai...

*$$$$$$$$$$$$$$$$$$*

Suna cikin tafiya Ameela tace "Sauke mu anan burki yaja ya tsaya batare da ya juya ya kalle ta ba duk da yanaji a jikin sa kallon sa take,

Su Beenish ne suka buɗe suka fita daga motar, ya rage daga Ameela sai shi a cikin motar, shiru motar tayi babu wanda ya cewa ɗan uwansa ƙala,

Sai daga baya Commisiona da yagaji da zama da ita yace; me kuma kike so bayan haka, kuma ina kuka kaimin ɗana I need more information, duk maganar da yake bai juyo ba hasali ma window yake kallo,

"Kana tambaya ta me nake so, to kai nake so zan iya samu?

"Ameelaaaaa..!

Ya kirata cike da jan sunan nata kamar irin zai fusatar nan,

"Babyyyyy.....!

Itama ta kira sa da haka kamar yanda ya kirata,

Damƙe ido yayi cike da taƙaici ya kuma cewa "Maganar ɗana nake miki ba wata maganar da banba,

"Wanne daga ciki, me yasa kake tunanin za mu ɗauke maka ɗanka, kayi mana abun da bai dace bane a matsayin ka
End Ads