hankalin su ya tashi wasu sai gumi suke, saboda tsoron kar su faɗi.
Agogo aka sa a gaban su ana kunna sa suna farawa, kowa ka gani sauri yake kawai wasu na zufa,
Beenish ce ta kalli Zee taga ta riƙe abun rubutun kawai taƙi rubuta komai, girgiza kai kawai tayi taci gaba da yin tata, ƙasa ƙasa tace Dan Allah Zainab kiyi please mana kar ki bari Ammu tasan baki rubuta komai ba.
Banza Zee tayi da ita ga nuna ma kamar bata ji ta ba, ta ci gaba da zaman ta, wani sojane ya zagayo ta gun yaga bata yi, ya daka mata tsawa "ke wasa kika zo yi ne me kike jira.
Abu kamar a saki fitsari da sauri ta shigayi batare da ta shirya ba, gashi ya tsaya akanta, kamar yasan bata son yi ne.
Saura kaɗan Ameela ta fashe da dariya tayi saurin riƙeta.
Time na cika akace kowa ya bayar nan wasu hankalin su ya tashi dan basu gama ba, sai akaci sa'a kuwa Barazana soja yasata gamawa da wuri, haka aka ware waɗan da basu gama ba, su kuma Waɗanda suka gama, aka kuma shiga wani guri da su, nan abun gasar ne, nan akai tayi musu wasu abubuwan ana cire wasu, har yanzu dai babu wanda aka cire a cikin su,
Nan ya rage saura matakin ƙarshe agama watsar da kowa dan mutane ashirin kawai za'a ɗauka, sannan a basu uniform sai kuma afara training, nan aka kuma yin na ƙarshe, still dai sunan su, na ciki Abu tayi mamaki da taga da sunan ta dan tana tayin abun da za'a cire ta amma ba'a cire ga ba, ashe abun da bata sani ko sun faɗi baza a cire su ba, saboda Ammu ta riga da tagama magana da meyin.
Bayan an gama ne aka nuna musu part ɗin da zasu zauna saboda saida safe, za'a basu uniform su fara training, nan suka runguma suka kuma shiga ciki, a ciki suka kwanta kuma babu komai a ɗakin kowa a ƙasa zai kwanta, babu yanda suka iya, Zee sai mita take musu sun jawo ta bala'i za'a binne ta da ranta loƙacin ta baiyi ba, babu wanda ya kulata dan kowa agajiye yake, ba ƙaramar wahala suka sha ba, dan badan wuyar da suka sha ba, babu wanda zai iya bacci a ɗakinnan gashi haɗe maza da mata saidai maza suka ware can gefe suma matan suka ware gefe.
Ƙarfe huɗu da rabi ko sallah ba akiraba, aka zo aka tashe su da ruwa, babu magana kawai watsa musu ruwan akayi, ba shiri kuwa kowa ya tashi yana yayyarfe hannu, Barazana kwa saida tayi Allah ya isa ƙasa ƙasa, sannan ta tashi zaune sai faman kumbura fuska take tana ciccin magani,
Fito da su akayi nan aka basu aiki suka share wasu ɓangarorin dake cikin gurin, sannan aka basu dama sukaje sukayi sallah, suna idarwa aka saka su suka fito, kowa kiran sa aka shiga yi ana basu kayan duk wanda aka ba sai yayi salute sannan zai juya cikin ɗakin, mata aka fara bawa damar suje su sako, sannan mazan ma sukaje suka sako, yanda aka ɗauke su daman maza sha uku mata bakwai,
Inda zasu fara training ɗin aka kaisu duk jeruwa sukay, aka sa kowa ya nutsu,
Cikin shigar shi ta sojoji ya fito yana takun sa cikin jarumta da mazantaka, kana ganin sa kaga dakaken soja, idon sa cikin glass a, kansa da p-Cap da yasaba sakawa a yawan loƙuta, gaban su ya tsaya yana bin ko wannen su da kallo, nan duk suka shiga sara masa kowa na ƙamewa tare saukar da kansu ƙasa kamar yanda aka sanar dasu anayi, su Beenish na can baya shiyasa basu gansa ba bai gansu ba.
Bace komai ba ya shiga wani waje dake gurin, ya ɗauko wasu littattafai,
Suna gurin kawai sukaji harbin bindugu kuma a inda suke, take duk suka ruɗe kowa ya fara neman hanyar guduwa duk suka tarwatse wannan yayi nan wannan yayi can, fara gudun su yayi daidai da fitowar sa, hannun sa ɗauke da littattafan, cikin rashin sani Beenish ta doshi wajen hankalin ta baya kanta tana zuwa bata san da fitowar sa ba, suka zabga karo take abubuwan hannun sa suka tarwatse bata bi takan sa, tayi gaba zata gudu, yana juyawa ya damƙo hannun ta tare da dawo da ita da baya, yana jawota ya ɗauke ta, da mari batare da yaga fuskar ta ba, cikin tsawa yace are you out of sense wannan wane haukane, murɗe hannun ta tayi dake hannun sa, take ta saki wata ƙara tana ɗagowa dan bashi haƙuri dan ita tashin hankali ma baisa ta gane muryar sa ba,
Cak ta tsaya tana zare hannun ta daga fuskar ta da ta ɗora, saida ya zaro ido batare da yasan yayi ba, da glass a idon sa dan haka batasan yanayin da idon sa yayi ba,
A hankali ya shiga zare glass ɗin dake idon dan ya ganta da kyau ita ɗince ko kuwa ƙarya idon sa yayi masa, Ido cikin Ido sukayi suna kallon juna, yayin da hannun ta ke cikin nasa a murɗe...✍️
*Duk meson na saka shi a group ɗin Su waye su yayi min magana, ta wannan nu
[4/19, 10:29 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)
08124226526*_______
*_episode 44💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*
Bismillah..✍️
A hankali ya shiga zare glass ɗin dake idon dan ya ganta da kyau ita ɗince ko kuwa ƙarya idon sa yayi masa, Ido cikin Ido sukayi suna kallon juna, yayin da hannun ta ke cikin nasa a murɗe...
Duk da dukiyar da take jin ta, amma yanzu ganin sa haka saida taji tsoro ya shige ta, dan atake zuciyar ta ta shiga bugawa, da sauri ta janye idon ta, ta mayar dashi kan hannun ta da ya murɗe, duk da a tsorace take da shi amma saida ta kuma dakewa ta shiga ƙoƙarin ƙwace hannun ta, shikam ƙara tamke fuskar sa yayi ganin tana ƙoƙarin ƙwacewa yasa ta kuma yi murɗe hannun sosai wanda yafi na da, ƙara ta saki da ta fi ta ɗazu, dan taji zafi sosai, juyawa tayi tabi yanda ya murɗa hannun ko zataji sauƙi amma tana juya shima sai ya kuma murɗa hannun ɗayan ɓarin, da sauri tayi ƙasa zata tsugunna sai ya kuma murɗa hannun sama dole ta dawo ta tsaya, tuni idon ta ya cika, da ƙwalla, murɗa shi ya sake yi akan nada saida yaji yayi ƙara sannan ya tura ta da ƙarfi, ta gaba ta kifa fuskar ta ta daki ƙasa, kasa tashi tayi saboda zugin da taji hannun ta yanayi kamar ma ya karye, da ƙyar ta iya miƙewa zaune tana tashi zaune ya kuma sa ƙafa ya tura ta sannan cikin tsawa yace ta tashi ta kwashe abubuwan da ta zubar masa, ai bata san loƙacin da ta fashe da kuka ba, ta kuma ɗagowa da ƙyar tana kallon hannun ta data ga kamar rawa yake, ashe da gaske dai karya mata hannun yayi, tabbatar da karyewa hannun yayi yasa ta kuma ƙara sautin kukan ta, ga hancin ta ta fara zubar da jinin haɓo sakamakon bugawar da tayi da fuskar, ga fuskar tayi dumu dumu da ƙasa, sai ta zama abar dariya abar tausayi.
Zagayowa yayi ta gaban ta, yana kuma cewa ta tashi ta kwashe masa abun da ta zubar,
Ƙara sautin kukan ta tayi tana cewa "wayyo hannun na, wayyooo hannuna ya kare.
Nan hankalin waɗan suka dawo gurin bayan gama harbin, hankalin su ya karkata kanta, da sauri wasu suka nemi zuwa gun amma sojan da yake agurin ya hana su, dan shi daman ba inda yaje yana gurin kuma duk yana kallon abun da ya faru.
Daga nesa wasu suka tsaya duk suke kallon ta cike dason jin abun da yafaru, itakam sai faman kuka take tana wayyo hannun ta,
Shi kam ko ajinkin sa, daɗi ma yaji da ya ganta a wannan yanayin, sosai zuciyarsa tayi fari, tsugunnawa yayi a gabanta kamar abun arziƙi zaiyi, amma sai ya cire hular kanta, yakama gashin ta, da ƙarfi ya damƙa ya shiga jijjiga mata shi, idan ya girgiza shi gaba da baya, sai ya girgiza shi gefe da gefe, har wani cije baki yake yana girgiza ta da ƙarfi, Allah sarki ita kuma sai dai ta kuma fashewa da kuka dan bata da ƙarfin da zata iya dakatar da shi, saida yagama wujijjiga mata kai ya hargitsa mata ƙwaƙwalwa dan har saida taga duniyar na juya mata, tana ganin mutane hurhuɗu, yana sakin ta kuwa ta kuma faɗawa ta baya dan bazata iya zama ba, ranshi fari tass ya tashi duk halin da take ciki amma haka ya kuma ce mata yabata minti biyar ta kwashe abubuwan ta kawo masa, yana faɗa mata haka ya juya, ya koma inda ɗayan sojan yake,
"Kallon ƴan gurin yayi yace "ina sauran a haka kuke shirin zama sojojin daga jin harbin binduga shine duk zakuyi wannan haukan, so this is the first time da ku kuma yin wannan abun If not I will punish you akan wannan abun, jin abun da yake cewa dan da ƙarfi yake maganar yasa waɗanda suka ɓuɓɓuya a wasu guraren suka shiga, fitowa, duk gurin su suka dawo zuciyoyin su na ɗarɗar,
Ameela da Fashion ne ƙarshen fitowa suna daga bayan sojan dake gurin, a hankali Barazana take tafiya,kamar ɓarauniya dan gaba ɗaya a tsorace take har yanzu, har sunyi gaba, RK ya ce "ke!
Fashion daman ƙiris take jira tana jin wannan tsawar ta kwasa aguje saima ta rasa inda zata dosa duk tabi ta kiɗime, saida taba wasu dariya suka shiga a hankali, Ameela kam juyowa tayi itama a tsorace, tana juyowa suka haɗa ido, duk da wani abu baitaɓa haɗasu ba, amma saida taji gaban ta ya yanke ya faɗi, bata san loƙacin da ta zaro ido ba cike da tsoron ganin sa, kana kallon ta zakasan a mugun tsorace take.
Bayan wata mota dake gurin Barazana taje ta ɓuya gabanta nata dukan uku uku.
RK da mugunta ta gama cika masa ciki, yana ganin su ya gane su, hakan yasa yabi Barazana inda yaga ta tsugunna, a hankali yake takawa har yaje gurin sai ya zagaya ta bayan ta, yana tsaye a ba ceyan ta, yaga ta daddafe motar tana ɗan tashi a hankali da niyar ta leƙa taga babu wanda ya biyota, tana wannan leƙen RK yaɗan dafa ƙafaɗar ta, ihu ta saki tana juyowa a tsorace, tozali da fuskar sa yasata ƙamewa dan numfashin ta ne ya ɗauke gaba ɗaya, saida yayi saurin girgiza ta, sannan ta dawo hayyacin ta tana kuma sakin ihu zata kuma guduwa, ya damƙi hannun da ƙarfi ya shiga janta sannan ya saki hannun ya shiga tura kanta, kamar zata kifa haka yake turata har suka ƙarasa gurin, Ameela kam na inda ya barta mamaki ya ƙamar da ita agun,
Duk ihun da Beenish take dake gurin ɗan tazara da tsakanin su, gashi kuma basa cikin hayyacin su yasa duk babu wanda ya hankalin sa yakai ga jiyo sautin muryar ta.
Yana kawo ta gurin ta ya koma inda yake ya tsaya yana haɗe rai tare da cire p-cap ɗin kansa yana miƙawa sojan gefen sa ya riƙe masa, cikin ɗaga murya ya ce "oya get ready, then, prepare to move out and hold the line!
Saurin gyara tsayuwar su sukayi kowa na saita kansa inda aka saka shi, yanda sukayi tsayiwar layin farko su bakwai sai na tsakiya shida ɗayan gefen ma seven, Barazana dai da Ameela a rikice suke har yanzu musamman ma Abu da jikin ta har karkarwa yake.
Ameela ce ta samu ƙarfin halin duddubawa taga ina Beenish amma har ta gama duba ko ina bata ganta ba acikin gurin, hankalin ta ya kuma tashi ta shiga tunanin ina take to, kode tayi wani wajen loƙacin da suka gudu, sai bayani yake musu amma hankalin ta gaba ɗaya baya gun sai dube dube take.
Gurin babban guri ne haka nan aka sa kowa yabi layi zasuyi gudu su zagaye sa sau goma,
RK yace "kuyi dividing ɗin kan ku into 4 groups, any group zai zama we have 5,5 members,
Group 1 suka fara ware kansu mazan uku uku mata kuma zai kama bibbiyu amma wani group ɗin sai dai asaka maza huɗu mace ɗaya, kasancewar su, matan su bakwai ne idan suka raba kansu a huɗu wani group ɗin bazai samu mace ɗaya ba, su kuma mazan suma idan suka raba kansu gida huɗu ɗaya zaiyi ragowa saidai ya shiga cikin group ɗin da yake da mace ɗaya,
Saida suka raba kannasu sai suka ga group ɗaya maza huɗu ne kawai babu macen ɗaya da zata shiga cikin su, tunawa sukayi da inda take nan suka kalli gurin sai suka ga bata gurin, ɗaya daga cikin matan da suka shiga group ɗaya da Ameela ta tambaye ta, ina ƴar uwar su da ta gansu tare, tayi maganar ƙasa ƙasa da sukaɗai suka san me suke cewa, karkaɗa mata kai kawai Ameela tayi alamun bata san inda take ba itama, daman itama so take ta samu damar da zata tambaye ta gashi kuma ita tafara tambayar ta,
RK ne yace "group A u can start!
Ɗayan sojanne ya irga musu 3, su kuma acikin minti ashirin ake so sugama zagayewar, ɗayan group ɗinne suka fara yi, sannan group B wanda Barazana ke ciki, suna suka fara nasu, tun a zagaye na biyu Zee ta zube agun, dan daman ba iyawa take ba, kaɗan kaɗan takeyi, babu wanda ya kula ta saidai suka gama, sannan RK yace nasu baiyi ba, sai sun sake nasu, haka Zee ta ja musu saida taga ya tunkaro ta sannan ta tashi taci gaba dayi, da ƙyar ta iya gamawa, tana gamawa ta zube a ƙasa tana maida numfashi dan ji take kamar numfashin ta zai ɗauke, group C ne suka fara group ɗin su Beenish, suna gamawa na ƙarshe zasuyi nasu, zasu fara kenan RK ya dakatar da su, cike da rainin hankali sai kace baisan me ya faru ba, yace "ina cikon group ɗin?
Ɗayane yace "Sir tana cen gurin ɗazu yanzu kuma munga bata gurin, bin gurin yayi da kallo shima kansa yayi mamakin rashin ganin ta agun, amma bai bari mamakin ya bayyana ba, kawai yaba su go ahead ɗin su fara sunayi yana kallon su amma zuciyar cike take da tambayar ina tayi daga gurin ko wane ne gangancinne ya yi masa shishshigi ya taimake ta, batare da sanin sa ba.
Suna gama nasu aka kuma basu wani horon na tafiya akwance, babu wanda bai gajiba sannan aka sallame su suje su huta kafin a juma su ƙara fitowa wani horon, yana gama sanar da su ya juya yabar wajen, ɗayan sojan ma bayan sa yabi.
Sukam yawancin su kasa tashi sukayi daga gurin Zee kam in banda kuka tanayin Allah ya isa babu abun da take yi, dan ita ko takan rashin ganin Beenish bai dameta ba,
Ameela ce ta ce "ke kam dan Allah kiyi shiru wallahi kar ya dawo ya jiki, yauwa ke wai ina Beenish ne, kowa fa yace bai ganta, kamata yayi ma mu tashi mu duba inda take.
"Wallahi babu inda zani tama ɓatan ina ruwana ai duk ita tajawo mana wannan bala'in da masifar ko me ya same ta ai ita tajawa kanta, wallahi Allah ya isa na Beenish Allah bazan yafewa yarinyar nan ba abubuwan da take min na zalinci, sai zuba take tana share hawaye, idon yayi ja tsabar jigatuwar da tayi.
Ameela bata kuma ce mata komai ba, dan tasan komai zatace ba sauraron ta zatayi ba, ita da wata mace, tayiwa magana tace dan Allah ta rakata su zagaya gurin ko zasu gano ta a wani wajen.
Tafiya sukayi suka bar Fashion a gun tana ta faman zubar da hawaye tana goge wa da hannu.
Fita sukayi daga gurin suna ta zagayen neman inda take.
RK sosai abun shima ya basa mamaki dan har saida ya kasa jurewa suna cikin tafiyar ya tsaya tare da kallon, ɗayan sojan,
yace "ko yaga inda yarinyar nan tayi daga gurin da take?
Jinjina masa kai yayi tare da cewa "eh naga wani soja ya ɗauke ta akafaɗa saidai banga fuskar waye ba.
Haɗe rai yayi yace "why u shouldn't tell me?
"To ai banga wani abuba wataƙil ko ɗata daga cikin masu kula da lafiyar sune yaganta a cikin halin shiyasa ya ɗauke ta.
Kawai kallon sa yayi yana jinjina kai yayi gaba, yabar sa, a ransa yana ayyana cin mutuncin da wanda yayi masa wannan shishshigin ko waye bazai ƙyale sa ba.
Can cikin wani guri ya dosa, inda masaukin su yake, cikin zafin nama yake tafiya saboda ya matsu yaje ya cire kayan jikin sa zafi yake ji.
Yana shiga tundaga falo ya shiga ɓalle botiran rigarsa, hakannan yaji ransa duk adagule, saboda zafin da yake ji, a galon ya jefar da rigar tasa, ya