x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 52 - SU WAYE SU

  • 153001 words
  • 156000 words
  • Out of 175942 words

Category: Love Stories

Views 176

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
mutsa fuskar sa yayi kamar an yaɓa masa kashi haka yajita a jikin sa, amma a haka ya daure yayi huging ɗin ta back yana ta faman tattaɓe baki, a hankali yace I'm very sorry dear.

Wani irin daɗi taji ya mamaye ta, jin ya bata haƙuri daman tasan fushi ne yasa yayi mata abun da yayi mata, amma yanzu wataƙil yaje yayi maganin matsala shine hankalin sa ya kwanta, tunda gashi har ya bata haƙuri, ƙara narke masa tayi ajiki, cikin shagwaɓa tace "it's ok dear, am sorry too, nima nasa ka ƙara jin haushi, sannan kayi haƙuri akan abun da ya faru, wallahi ka tsorata ni da ganin yanayin da ka shiga ɗazu, dan Allah kar ka kuma fita ka barni gashi tun safe nake jin yunwa banci komai ba har cikin ya fara murɗawa ciwo yake min sosai.

Sakin ta tare fuskar sa ɗauke da yaƙe yace "sorry, shi kaɗai ya iya furtawa sannan ya miƙe tsaye yana watsa mata banzan kallo ta ƙasan ido, danji yake kamar ya shaƙeta wallahi, da wata ƙatuwar muryar wai nan shagwaɓa zatayi abun ko kyan gani babu, "mtsww ya furta a fili batare da yasan yayi ba.

Jin tsakin da yaja yasa ta ɗago tana kallon sa, sai kawai ya sakar mata murmushi yaƙe, yana cewa duk rainane a ɓace da na barki haka babu abin ci, kuma ke bakiyi dabarar ki dafa ba zaki zauna haka da yunwa, da yunwar ta kashe ki fa.

Langwaɓar da kai tayi tana turo zabga zabgan laɓanta tace "to baki ne kaƙi kula ni ba, kuma ai na duba banga kitchen ba anan.

Fakar idon ta yayi ya harare ta sannan ya taɓe baki yace "taso in nuna miki yana ta cen kwanar, ya nuna wani ɗan guri da yayi kwana acikin falon, ita kuma hankalin ta kwata kwata baikai gurin kodan ba a cikin kwanciyar hankali take ba.

Kasa tashi tayi, sai kawai ta girgiza masa kai tace "wallahi ina tashi faɗuwa zanyi gaba ɗaya jikin ba ƙwari ko girkawa bazan iya yi ba, dan Allah ka bayar a siyo min koma a ina ne, shima idan aka daɗe zan iya mutuwa.

Tsaki yaja a ransa yace ai da nafi kowa jin daɗi da zaki mutun, a fili kuma sai yace ki daina wannan maganar bazama ki mutu ba, amma yanzu tunda hakane bari in bayar a siyo miki, yana faɗar haka ya fita waje, baya so ta mutu batayi masa abun da yake so ba, hakan yasa dole zai ɗan kula da ita na zuwa wani lƙcn.

Inda ya barta nan yazo ya same ta kujera ya koma ya zauna yana kallon ta ta ƙasan ido, rarrafowa tayi daga inda take ta dawo gaban kujerar da yake daga ƙasan ta zauna sai ta ɗora kanta akan cinyar sa, ji yayi kamar ta ɗora masa bulo, saboda nauyin da yaji, tana ɗorawa kuma ta riƙo ƙafar sa cikin soyayya, riƙon da tayi masa saida yasa Bulama ɗan zaro ido dan saida yaji zafi ji yayi ta damƙa da ƙarfi, kasa jurewa yayi ya ɗan sunkuyo da kansa, yana leƙen hannun yaga da salon mugunta tayi masa ne, ko kuwa dan yaji riƙon bana wasa ba, ganin ta yayi tama lumshe idon ta kuma hannun ta babu alamun irin tana sane ta damƙe ƙafar ba.

Jinjina kai yayi kawai ya mayar da kansa yana mamakin irin wannan ƙarfin da take gwada masa, tuna yanda ɗazu ma ta rungume sa har yakasa ƙwacewa, anya kuwa ita kaɗai ce bata tare da jinnu, masu ƙarfi, da nauyi, ji yayi bazai iya ɗaukan loƙaci a haka ba tare da ita, ai sata sagar masa da ƙafa, hannun sa yasa zai ɗaga kanta, sai ta kuma wawuro ƙafar tana kuma danna kanta kan cinyarsa, tare da cewa "Please dear kabarni har akawo abincin idan ina jikinka ina samun releaf da yunwar da nake ji, tana faɗa tana kuma gungura masa kai a cinya, tana kuma jawo ƙafar sa tana rungumeta a ƙirjinta da kyau.

Kasa motsawa yayi dan taƙaici shifa ko feelings baya ji da ita, anya ma tana da lafiya ta taɓa shi amma kamar ba mace bace ta taɓa shi, ji yanda take naniƙarsa amma kaɗan baiji komai ba, tunawa yayi loƙacin da ya riƙo hannun Zee ɗin shi, yanda yaji hannun ta laushi da daɗin taɓawa, amma wannan ko daɗin taɓawa babu, yanzu da Abu ce tayi masa haka ai da tuni ya manta da kawowa, dan shi ko ganin ta yayi sai yaji shi a up, to ina ga tayi masa haka, wayyo gaskiya Abulen sa duniya ce yarinyar akwai kaya kamar uwarta ai dole ma ya auri Abu dan bazaiyi 2-0 ba ko ɗanɗanta ne na kwana ɗaya wallahi sai yayi bare ma yasan idan ya same ta bazai taɓa barinta ba, wannan tunanin da yake yasa yaji shi cikin annashuwa dan har ma ya manta da abun Rabi tayi masa, ƙoƙarin meƙewa ya farayi dan zuciyar sa gaba ɗaya ta kuma karkata ga Zainabun sa sai hango ta yake yanda ya ganta jiya, tana masa wannan masifar shi sai yaji ta kuma burgesa saboda ko me takeyi kyau take daɗawa, ya manta da wace akan sa saida yaji ta kuma dakatar dashi daga yunƙurin tashin da yake sannan ya maida kansa gare ta, baisan loƙacin da yace "ke dusa ɗag... Da sauri ya katse maganar tasa jin abun da yake shirin faɗa, sai ya shiga cewa "uhm uhmm wannan banzar matar nake tunawa, me kama da dusa, babu abun da tasani dai akuyanci sai na bata dusa taci wallahi tunda tana kama da su, bata wani kama da mutane, shegiya duk tabi ta addabe ni ta takurawa rayuwa ta naniƙe min kuma ba wani daɗin aiki gare ta ba, bata iya komai ba, bata da ɗanɗano ko kaɗan wajen girka abin ci, bata inda zaka ji daɗi da ita komai sai ta ɓata maka rai.

Aunty Babba takasa gane inda maganar sa ta dosa amma saboda yunwar da take ji bata damu da sai ta gane wa yake magana ba akai, tadai san wataƙil da matar ɗazu yake, to amma sarautan da yake ne yasa bata fahimci komai ba.

Hararar kanta yayi tunda ta kifa ba kallon sa take ba, a ransa yace kaga jaka duk wannan bayanin nasan babu abun da ta gane, da wani jikin ta kamar ta macen alade ko mata sun ƙare me zanyi dake, abu lami babu sugar babu maggi, ta kwanta akaina kamar gardi ne ya kwanta.

"Kayi haƙuri ka daina min maganar ta dan nima raina ɓaci yake yi, duk ita tajawo min wannan masifar da tuni munanan muna shan soyayyar mu amma tazo tayi cikas.

"Uhm wallahi kam, Baby ɗan ɗagani zanyi fitsari yanzu zan dawo, badan taso ba ta ɗaga sa, tana ɗaga sa yaji wani sanyi har saida ya ɗan saki ƙaramar ajiyar zuciya.

Yana tashi akayi musu nocking ɗin ƙofar fara zuwa yayi ya buɗe, ledojin take awaya ne wajen guda uku, ɗan aiken ya miƙo masa, karɓa yayi yana rufe ƙofar sannan yazo ya ajiye mata biyu ya ce "gashi fara ci kafin na fito, yana a jiye mata ya wuce sama.

kamar kura taga nama haka ta hau buɗe ledar ko godiya batayi masa ba Allah Allah takeyi tayi ta fara ci, dan ji take kamar kawai ta buɗe cikin ta ɗura abincin basai ta tsaya tunawa ba, leda ɗaya dambu ne da ya sha haɗe harda hanta aciki yaji uban zogale sai ƙamshi yake, ɗayar ta kuma buɗewa ita kuma fried rice da gasashshiyar kaza, ga kuma lemuka masu sanyi, tukan ta fara ci taji yawun ta ya tsinke, sai ta rasa da wanne ma zata fara, ai ɗaga dambun tayi kawai ta haɗe da shinkafar da taga abun bazai cinye ba sai ta rage a leda, kazar kuma ta ɗauke ta ta ajiye ta gefe tare da yago wajen rabin ta hau yayyagata da duka hannunwan ta biyun, inda taji yayi mata tauri sai ta yaga da baki, sannan ta haɗe sa da abincin ta cakuɗe, ta fara zura lumo kan ta cinye na bakin ta ta kuma kwaso wani, haka ta dinga ci hannu baka hannu ƙwarya.

Bulama na shiga wanka ya farayi cikin sauri dan so yake ya fita ga ba waya a hannun sa, yana gamawa ya zauna ya ɗan ci abin cin kaɗan, sannan ya ɗauko ragowar ya fito dashi, mamaki ne ya kamasa ganin yanda tayiwa gurin kaca kaca gashi ta cinye duka kuma a haka ta baje ta fara bacci a gurin, jinjina kai yayi tare da cewa "kan bala'i lalle riƙon mahaukaci sai sarki uwar ki ma haka take da wannan cin ajinin ku haukan yake ashe, haka ya tsaya ya gama zage ta tsaf sannan ya ajiye mata ragowar dan yasan zata kuma buƙata shi nan daman a nashi lissafin da ya kawo mata guda biyu taci ɗaya yanzu in taji yunwa da daddare ma taci dan bazai ma kwana a gidan ba yau bare taje ta karya masa wani ɓari najikin sa, dan wannan cikin dare idan ta danne sa ai sai ta Allah dan haka gara ya bar nata gidan da safe ya ringa leƙota dan wallahi ko ganin ta baya son yi, dan ba yanda zaiyi ne da ita sai ta biya masa buƙatar sa amma da mayar da ita zaiyi inda ya ɗauko ta, dan a hakan ma baya jin zaiyi zaman sati biyu da ita suna zaune gida ɗaya, ficewar sa yayi daga gidan yanzu ma still ƙulle ta yayi ta waje yayi tafiyar sa, ma'aikatan sa ne suka zo suka buɗe masa ƙofa, wani drivern zai shiga gaba yace "a'a ya barshi shi kaɗai zai fita baya neman ɗan rakiya, haka suka rabu da shi ya shiga ya tafi, wajen siyan waya ya fara zuwa ya siyi wata, saka sin ɗin sa yayi ya ɗan sassaita wasu abubuwan sannan ya lalubo number Rabi, bugu uku ta ɗauka.

Tana ɗagawa yace "gani na zuwa garunku, zanzo gidan ki, badai kinyi naki ba, to saura nawa, in ba tsoro ba kar ki sake kibar garin ki jira zuwana, yana gama faɗar haka ya kashe batare da yaji daga gare ta ba, daganan ya tayar da motar ya ɗau hanyar garin Sokoto....



$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$


____*HAJJA MAMA*


Tana kwance a ƙasa hannun ta da ƙafar ta duk a ɗaɗɗaure sai mutsu mustu take kamar tsutsa tana so ta kunce ɗaurin da akayi mata amma ba hali, dan an ɗaure ta da kyau,

Tana cikin wannan abun wani babban mutum fari ƙal ya shigo cikin gurin fuskar sa ɗauke da wani irin shu'umin murmushi kana ganin sa kaga kuɗi dukiya jin daɗi da duk wani abu de da mutum ke nema a duniya zaka ce ya same sa, takalmin sama kaɗai abun kallo ne, banda suturar dake jikin sa, irin ta ƴan ƙasar Algeria ta masu kuɗi.

"Hhhhhh ya kwashe da wata irin mahaukaciyar dariya yana tsugunnawa agaban Hajja Mama, "kinyi babban ganganci na shiga rayuwa ta, waya ce miki anan shiga gona ta, ko waɗanda kike ganin mu tare babu wanda yake ƙoƙarin shiga harkata, uban gidan naki bai gaya miki waye ni ba, bai baki cikakken labarina ba ko da yake shi kansa baisan waye ni ba, duk yanda lissafin ku da tunanin ku yake na wuce haka, ƙwaƙwalwa ta ba irin taku bace lissafina ba irin na mutane ba ne, ke nan har wani jinki kike wata ko, nan kin lissafamu zaki haɗa kanmu ki kama mu to banƙi ba shi zaki iya kamawa tunda baida kaifin tunani da har ya kasa fahimtar wace ce ke, ya kasa fahimtar aiki nawa kike a ƙarƙashin shi, to ki sani duk wani motsinki da kike a ƙasar Nigeria babu wanda bansani ba, da ɗauke ƴaƴan mutane da kike, to bari na miki wani albashir dake da kike farauta ta da shi uban gidan naki, duk zan haɗa ku na kashe sai na kawo ƙarshen duk wani shiri naku, sannan abu na gaba gidan da kuke tara kuɗaɗe da mutane a yau ɗinnan zansaka a cinna masa wuta duk wani abu da kuka tara da naki da nashi komai sai ya ƙone har mutanen ciki Hhhhhh, sannan kuma ki jira next plan ɗina da zanyi akan jinin Sardaunan da kike kirari dashi, bincike ɗaya ya rage min in gano jinin nasu suma ɗaya bayan ɗaya sai na kashe kowa, in kin isa ki dakatar da hakan dan kece ƙarshen kashewa sai kinga komai da idon ki!

"Dalla can kayi kaɗan ka kawo ƙarshen abunnan saidai kai kaga komai da idon ka, mayaudari maci amana, karasa wanda zaka yaudara sai matar ka to abun da baka sani ba kasani ka kashe miciji baka sare kanba, ɗan zaki ya girma, kun kashe kunama amma ƙarinta na nan kuma shine me cutarwa, bari nima na sanar dakai wani abu shin kasan ƴar gidan Dhuhar tana raye? Ma'ana ƴarka?

Yayi mamaki amma sai ya kwashe da dariya yace tana zuwa duniya muka mayar da ita, da ita da uwarta, da ubanta kuma, babu wani sauran abu da ya rage mana ke kaɗai ce kuma kema kin zo hannu nake ba fita, mission completed!

"Never, mission incompleted!


Waken da ka shuka yana ta yaɗo kuma zaici gaba yaɗo har ƙarshen duniya, kaga nima daman dakwai abun da bansani ba nake kokwanto akai to yanzu na sani, daman a kullum mamaki na taya za'ayi Musbahu ya iya aikata wannan abun ni nasan saidai asaka shi Musbahu zuciyar mutum ce dashi ba irin taka ba, kasa Dhuhar ta mutu da ciwon ganin mijin ta ya yaudare ta ta mutu da baƙin cikin shi, ashe ashe kaine munafikin Allah ta'ala to ko uwar ka idan ta gane gaskiya zakaga me zatayi maka, ka jira nan gaba sai duniya gaba ɗaya ta juya maka baya sai duniya ta tsaneka, hatta ƴaƴan ka sai sun tsaneka, kuma da yardar Allah jinin daka tsana a duniya shine ajalin ka, shi zaiga ƙarshen ka, abun da kaso binnewa tunda ransa to bai mutu ba yana acikin rami da ransa,

Bata ƙarasa ba ya caƙomo wuyanta ya buga da jikin bangon gurin ya dawo da ita sannan ya kuma buga mata goshi take goshin ya fashe.

Duk da haka bakinta bai mutu ba, tace "raina yafi ƙarfinka baka isa kaga bayana ba,

Bakin ta ya kuma makewa shima ya fashe,

Da ƙafarta dake ɗaure itama ta miƙa ta taɗosa ta kifar dashi ƙasa, yana faɗuwa tabi sa da baki ta fara cizon sa tana buga masa kai, duk inda tasamu ciza take, kunnen sa ta kama saura kaɗan ta cire masa kunne da haƙori, yayi saurin turata gefe ya miƙe duk ta ɓata masa kaya da jini cikin sauri ta kuma tashi zaune tace "in ka isa ka kunce ni kaga yanda sanyi dakai agunnan wallahi sai na kashe ka, mugu taɓaɓɓe jahili wanda babu komai a kwanyarsa, munafiki in Allah ya yarda mutuwarka bazatai kyau ba sai kayi mutuwar wulaƙan ci, nan gaba kare ma sai ya fika gata, duk kuɗin da kake taƙama dasu sai sun zame maka bala'i da masifa, kuma nan gaba baza su taɓa yi maka amfani ba, shegen matsiyaci wanda tsiya tayi wa kamu, kana wani taƙama da kanka kana ji da kuɗi, to har yanzu matsiyaci ne kai baka da komai kabari kayi taka dukiyar da zaka nemeta da halak ɗinka bata mutane ba, duk kuɗinnan sai ka ɗauke sa da hannun ka ka damƙawa masu shi cikin kunyata a idon duniya, jaki acinkin jakan ma kai jakine daƙiƙ....

Wani irin mari yakaimata wanda saida yasa ta fita hayyacin ta na wucin gadi, yana sauke ya kamo kafaɗunta ya miƙer da ita tsaye, cikin ciccije baki yana zazzaro ido ya shiga bubbuga kanta da bango, yana cewa "bari in aika ki inda suke sai ki yi musu albashir ɗin a can, buga kanta yai tayi har saida yaga ta dena motsi sannan ya jefar da ita baya tana faɗuwa yabi ta ya murje mata yatsun ƙafa shima saidai yaga ya fashe sannan ya rabu da ita, ƙafar tata ya jawo ya ringa janta a ƙasa yana yawo da ita acikin ɗakin saida yayi mata kaca kaca da jini yaga ko numfashi batayi sannan ya ciga da janta ya fito da ita waje, dajine wajen sai yaran sa dake bakin wajen suna guiding, ci gaba yayi da janta saida yayi tafiya me tsawo sosai sannan ya kawo bakin wani ruwa, da ƙafa yayi ball da ita zuwa cikin ruwan.

A bakin gurin ya tsaya saida yaga ta lume a ciki, sannan ya wara hannun sa yana kwashewa da wata mahaukaciyar dariya cikin dariyar yace "Hhhhhh yanzu kin yarda mission completed! Ƙarya kike na daɗe da kashe ahalin Musbahu, mutum ɗaya ne ya rage a duniyar nan da masana yana raye kuma yana sonsa kuma rabu dashi, shine mahaifiyarmu, uban mu ma na daɗe da aikasa inda na turasa, Hhhhhh babu wanda ya isa yayi jayayya dani kaf faɗin duniyar nan, Ni Menasara ne a ko da yaushe,nasara tawa ce!!!!

Shikaɗai sai zuba yake saida ya gama haukansa sannan ya juya ya koma can gurin yana zuwa aka buɗe masa mota drivern sa, ya jashi suka tafi zuciyar sa fal da farin ciki, daman yana ta jiran ranar da matar nan zata kawo kanta har inda yake, gashi kuma ranar har tazo, tama wuce, daga nan direct yace akaishi airport, yana zuwa yayi duk abun da zaiyi yabada kuɗi aka basa kujerar da jirgin yanzu zai tashi, ba ɓata loƙaci aka gama komai jirgin ya ɗaga zuwa Nigeria,




$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$
[4/25, 12:52 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
End Ads