ta zama har wajen ƙarfe biyar babu kuma wanda ya shigo falon tun suna surutun su har suka gaji, sai da sukaji ankira sallar magriba sannan, Beenish tace suzo su fita loƙacin babu masu tsaro da yawa duk sunje sallah nan suka samu dama suka fito suka shiga motar su, tuni Beenish ta ɓalle abun da aka ɗaure ta dashi ashe daman ba'a ƙulle yake, ta kwa cire ta jefar dashi a wajen, sannan tace musu ita zata tuƙa sa, cikin ɓacin rai ta tayar da motar suka ja tunda kwa har suka shiga ai babu wanda zai hana su fita saboda su masu gadi basu san meke faruwa ba, suna zuwa kuwa aka buɗe musu suka fice daga gidan tunda ta hau titi kuwa take kwarara gudun hauka dan duk da haka a tsorace take ji take kamar zai biyo su ya kuma sawa a kamasu, saboda gudu saida ta kusan bugawa wata mota, ganin hakan yasa, suka dakatar da ita da tuƙin,
Barazana dake gefen ta sukayi exchanging ɗin guri ta karɓi tuƙin ita kuma ta koma gurin ta shima saida ƙyar ta yarda ta bata,
Ita ma dai kuma ba gudun hankali take ba da kaɗan nata ya ɗanfi na Beenish ɗin hankali, suna wannan gudunne na tsoro har suka ƙaraso unguwar tasu, sai kuma suka tarar da wannan abun.
Dalilin da yasa ƴan sanda suka kuma biyo su kenan bisa ga umarnin RK da ya basu umarnin su ɗauko su gaba ɗayan su, kuma idan sun ɗauko su, su wace masa da su barack ɗin sojoji ba gida zasu kai masa su ba, sai gashi kuma da suka zo suka kuma tarar da wata rigimar a ƙofar gidan, dan haka bayan sun gama saka yaran Bulama a mota, sai suka fara ƙoƙarin tura gate ɗin sukayi, saikwa ya buɗe nan suka fara tura kai ciki wasu suka shiga wasu kuma suka tsaya tare da yaran Bulama.....✍️✍️
*Kunga typing ɗin ku yafara ƙasa koh, to comment ɗin ku ne yayi ƙasa shima, kullum ragewa kuke yi, masu yi kullum ƙalilanne waɗanda de nasani ne, kuma daman nace yawan comment yawan typing 🤗*
[3/5, 12:25 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)
______________________________
*_episode 32💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
Bismillah..✍️
*PAID BOOK💸*
Loƙacin da suka shiga cikin gidan, a falo su Aunty Babba suka tsaya, nan suka ƙara gaisawa,
Aunty Babba ce ta shiga tambayar sa me yake son ci ta dafa masa, yace mata babu komai ba abun da zaici, ya hutar da ita..
Idon sa nakan Abulele yace "ya sunan ki, baku gaya min sunayen kuba sai ya wayance da tambayar su gaba ɗayan su, saboda Aunty Babba kawai suka basa amasa, ganin yanda Aunty Babba take ta kumma mannewa a jikin sa yasa Ameela miƙewa tace "mu basu waje mana, kuzo mu koma ɗaki, kamar jira suke tana faɗa duk suka miƙe, a kusan tare suka fara tafiya zuwa ɗakin su.
Suna Shiga Barazana ta fashe da dariya ƙasa ƙasa, tace kan Bala ba gashi wai wannan tsofe tsofen tsofen mutumin Auny Babba take so, kunga yanda take ta faman hauka akansa ko kunyar mu ma bataji.
Suma duk dariya sukayi ƙasa ƙasa yanda bazata jiyo su ba, Babyn baby ma tace "wallahi nima abun sai yaban mamaki tabb lalle so hana ganin laifi bare kuma muni ita a haka tagani take son abun ta,
"Nifa nama lura da mutum kamar ɗan duniya ne naga yanda yake kallon Zee kode ya sanki Zee? Cewar Ameela
"Wata uwar harara ta wurga mata tare da cewa "uwar sanina yayi ni a dangina babu masu zubin wannan halittar a gidan uban wa zai sani, nima naga kallon da yake min ɗan iska ne kawai, yaci darajar Aunty Babba da na tsige masa wannan matsiyacin gemun da hannu shege ni wallahi ma ji nayi kwata kwata banyarda dashi ba bai kwanta ba...
Beenish tace "wallahi nima haka ni abun mamakin ma yanda ya haɗo uban mutane ya taho dasu sai kace marar gaskiya ko kuma uban daba ya wani lodo mutane kamar yazo dambe ko gurin maza zaizo ai sai haka bare kuma yasan gidan mata ne.
Ke kwa kika sani ko anbasa labari yanda muke shiyasa ya taho da shirin sa, cewar Zee,
A can falo kuwa sai ƙara shigewa jikin sa take tana shafo gemun sa, neman haɗe bakin su ma take amma sai kakkaucewa yake yaƙi bata haɗin kai dan shi ji yake kamar ya ture ta ta faɗi dan ya gaji da abun da take masa, daman zaman da yake da ita dan saboda Abulelen sa na gun, dan haka hankalin sa na kanta, amma yanzu tunda ta tashi sai yaji kamar akan ƙaya yake abun Aunty Babba take masa duk sai ya kuma jin haushin ta da tsanar ta sun kama sa.
Ɗan hannu ya saka aljihun sa ya zaro wayar sa, sai yayi danne dannen sa ya kara a kunne yana wayar ƙarya, a loƙacin tasamu ya ɗan janye ta daga jikin sa, ya miƙe tsaye a hankali yace "sweetheart Bari in ɗan amsa waya ina zuwa.
Wani daɗi ta kumaji ya mamaye ta da ya kirata da sweetheart sai kawai tayi kwance akan kujerar tana ɗaga masa ka.
Ta gefen ido ya wurga mata uwar harara sannan ya nufi hanyar fita, yana buɗe ƙofar yaga sojoji sun nufo wajen da sauri ya koma sai ya juya ya kalli inda Aunty Babba take sai yaga ta rufe ido hankalin ta ba akan sa yake ba, lalbulen dake jikin ƙofar ya shiga ya ɓuya daga ƙarshe ta yanda idan aka buɗe ƙofar ba za'a gansa ba,
yana gurin aka turo ƙofar yanda kwa ya lissafa hakance ta faru, yana bayan ƙofar basu gansa ba da suka buɗe,
Da sauri Aunty Babba ta tashi tana cewa Uncle ka ga...... Ɗif tayi ta kasa ƙarasawa ganin sojoji ne suka shigo, batasan loƙacin da ta miƙe ta kwasa a guje ta nufi ɗakin su, kafin suyi yunƙurin kamata har ta rufe ɗakin tasaka muƙulli.
Sauran dake suke zaune akan gadon suna gulmar ta, ta shigo musu a haka, hakan yasa duk suka miƙe suka shiga tambayar ta lafiya me ya faru?
Cikin sauke numfashi da ƙyar tace "wallahi sun ƙara biyo mu fa, wannan mugun sojan shida wasu, kawai sai ganin su nayi a falo, yanzu haka sun taho nan ɗakin...
Duk tsuru-tsuru su kayi da ido kowa na tunanin meye mafita musamman Beenish da tasan ita ta aikata laifin, daman tasan za'a rina, to yanzu kuma idan ya kamata wace irin mugun ta zai mata kuma, tayi laifi kan laifi, sai yanzu take da nasanin tahowar da tayi.
Bam Bam Bamm sukaji ana ta bugun ƙofar da ƙarfi duk rasa abunyi sukai,
Beenish ce ta kalli Aunty Babba tace "dan Allah harda shi kingan shi da idon ki.
"Eh mana nagansa da ido na, kema kin san dole yazo ai tunda shi mu ka yiwa laifin.
"Na shiga uku to yanzu me zamuyi nifa gaskiya bazan yarda in koma ba wallahi nasan abun da zaimin sai yaci uwar na farko, dan haka nidai bazan fita ba, tana faɗar haka ta nufi wajen wardrobe ɗin su tace Babyn baby zo ki rufe ni idan na shiga, ki ɗora min wannan bargon.
Dariya suka saka mata duk da halin da suke ciki bana dariya bane amma saida sukayi ganin abun da take shirin yi,
Haɗe rai tayi ta tsaya tana kallon su kamar zatayi kuka, tace "au dariya kuke min kunma maida ni mahaukaciya kenan ko dan kunga baku za'a kama ba, shikenan tunda haka abun yake na fasa shiga bari inje inma kashe ni yayi sai kufi jin daɗin dariyar, tayi magana cike da dakewa tana haɗe rai dan har cikin ranta take wannan maganar dan sun bata haushi..
Duk da haka maimakon ta basu tausayi amma dariya ta kuma basu saidai yanzu basu bari ta fito ba kowa ya ƙunshe abar sa sai dai ƴar kallon kallon da suke suna ƙara riƙe dariyar su, gudun ƙara tunzurata dan sun lura ta canza gaba ɗaya a tunzure take abu kaɗan sai ta sauke fushin ta akan su,
Da sauri duk suka tari gaban ta suka shiga bata haƙuri, Aunty Babba tace haba masoyiyya ai baza'ayi haka ba ba haka muke nufiba, muje in ɓoye ki kawai, kinga ma fah ƙofar da muƙulli ba iya shigowa zasuyi ba ki kwantar da hankalin ki, duk kinbi kin sauya bansanki da tsoro bafa jaruma Beenish, ma yayi miki da har kika fara tsorata da shi wallahi dakewa zakiyi ke ko shi, shima zaiji shakkar ki amma idan kina nuna tsoro haka ai sai yayi galaba akanki kuma ya rainaki, gwanda kema ki nuna masa jaruma ce ke, duk ina jarumtar taki kin mata da maza nawa muke faɗa sai yanzu guda ɗaya ne zai gagare mu har ta ɗaga mana hankalin ƴar uwa ai dole muyi shiri na musamman akan sa koh ya kuka ce? Ta juya tana kallon su,
Duk jinjina mata kai sukayi alamun haka ne.
Buɗar bakin Beenish kam sai cewa tayi baku da hankali gaba ɗayan ku wallahi nutumin da yake faɗa da mutane sama da ɗari shi kaɗai shine zaku haɗa kanku da shi ku da kuke faɗa da spray ne barkono in kun isa kuje gurin sa a haka kar ku tanadi komai kuga yanda zaiyi da kasusuwan ku, dan bai dake ku bane shiyasa kuke wannan maganar da ƙafa fa kawai ya ɗan taɓa ni saida na bar inda nake na koma ƙasan gado, hmmm idan na faɗa muku yanda naji bazaku gane ba wallahi har yanzu jin dukan sa nake ajikina gaba ɗaya jikina ciwo yake min, ai ƙarfin mu ba ɗaya ba, mu ƙarfinmu dabara ce kawai, amma idan kunga zaku iya dashi bismillah bada ni gaɗa a lahira, dan wallahi bazan yarda mu sake haɗa hanya da shi ba, tana maganar ta nufi hanyar banɗaki ta kuma ƙulle kanta dan har ga Allah ta gama tsorata da shi duk abun da take faɗa da gaske take.
Su fa ko a jikin su dan wallahi tana shiga banɗaki suka kuma kwashewa da dariya, suna mamaki wai yau su ake cewa basu da hankali Beenish tayi nisa...
Ameela ce ta koma kan gadon tace "tsoro ne kawai da ta bari ya shiga zuciyar ta har take irin waɗannan maganganun, kalli ƙofar ma fa a rufe take amma duk tabi ta tayar da hankalin ta harda ƙara shiga banɗaki ko wa yace mata shigowa zasuyi...
Daga waje kam tun sojojin nan na budu har suka gaji sai kawai suka fita daga gidan ma gaba ɗaya kuma suna fita suka tafi da waɗancen mutanen batare da sun kira RK sun sanar dashi abun da ya faru ba kuma basu gaya masa babu ƴan matan ba sukayi tafiyar su a haka.
Bulama saida ya tabbatar da sun tafi sannan ya iya fitowa daga inda yake yana sauke ajiyar zuciya harda dafe ƙirji ganin basu gansa ba duk da baisan me ya kawo su ba amma a tunanin sa shi suka zo kamawa shiyasa ma ya ɓuya amma da yasan ba gurin sa suka zo ba bazai ɓuya ba.
Maryama na ganin tafiyar sojojin ta sauke ajiyar zuciya tare da nufar cikin gidan tana tura ƙofar taji ta buɗu dan haka ta danna kai ciki ta shiga, saɗaf saɗaf take tafiya, tana ɗan jujjuyawa sai taji kamar ana binta, a haka har ta ƙarasa bakin ƙofar falon nasu, itama tura ta tayi, a hankali ta fara saka ƙafar ta ciki.
Jin an turo ƙofar yasa Bulama saurin juyowa a tunanin sa sune suka dawo, karaf kwa idon su cikin na juna, kowa saida ya razana da ganin ɗan uwansa.
"Doctor Maryam! Bulama ya kirata cike da ɗan mamaki duk da de angaya masa tana raye amma saida yayi mamakin ganin ta.
Hannu ta ɗaga masa tare da cewa "me kazo yi cikin gidan nan?
cike da basarwa ya saki murmushi yana tafa hannun sa sai ya fara takowa zuwa gaban ta, bai kuma daina murmushin da yake ba na ranin hankali,
Saida yazo daf da ita sannan ya tsaya yana kallon ta ido cikin ido, tare da ɗage mata gira ɗaya, yace yadai ko da magana, gani a ciki in kuma zaki fitar dani to ko kuma ki kuma ɗaukan rahoton da kika saba, nan ma nazo nayi aikin da na saba, Hajiya Maryam ashe dai kina raye nayi farin ciki da ganin ki wallahi nasan buƙatata zata biya ki ban haɗin kai a karo na biyu....
Wata uwar harara ta watsa masa, tana matsawa daga kusa dashi, sannan ta daka tsaki tana ƙarasa shiga cikin falon, tace "kayi gaggawar fita daga cikin gidan nan idan ba haka ba zan sa su fita dakai, fita ta wulaƙanci dan idan nagaya musu duk abun da ka aikatawa iyayen su babu wanda zai barka sai sun wulaƙanta ka a gurin nan sannan baza su taɓa bari ka fita da rai ba daga cikin gidan nan, saidai a fita da gawar ka, dan haka kayi gaggawar fita daga cikin gidan yanzu yanzun nan, in ba haka ba zaka ga aiki da cikawa dan wannan karon babu ɗaga ƙafa.
"Hhhh au dan Allah fa, babu ɗaga ƙafa, to tsakanin ni da ku aga wanda za'a ɗagawa ƙafa, taso ta gama nata nema kinzo da naki salon tom muzuba mu gani nima zanzo muku da nawa salon na daban, kin gane koh? Ya ƙarasa yana kuma ɗage mata gira tare da sakin mahaukaciyar dariya..
Da ƙarfi tace "Bulama! Ya ishe ka haka ka fita daga cikin gidan nan tunkan kowacce ta ganka idan ba haka ba, kuma nagaya maka abun da zai faru..
Yanda suke sa'insa da ɗaga murya yasa su Aunty Babba sukajiyo hayaniyar su hakan ya sa suka fara ƙoƙarin fitowa.
"Banza mahaukaci marar imani wanda baisan meye tausayi ba a rayuwar sa ka gama da iyayen su shine zaka kuma lallaɓowa gurin su to wallahi duk sun fi ƙarfin ka babu sa'arka a cikin su, saidai kaje ka nemi uwar ka da baka san darajar ta ba,
Fesa ya kwashe ta da wani gigitaccen mari, yana saukewa hannun sa yaji shima an sauke masa wani marin da bai taɓa tsammanin jin sa ba, ana yi masa kuma aka kuma taro sa ta ɗayan ɓarin, cike da mamaki ya dage fuskar sa yana juya ɓarin da yaji an mare sa, sosai razani ya bayyana akan fuskar sa.
Cikin nuna sa da yatsa muryar ta na rawa tace; "Nima a shirye nake da yin komai, komai ma zan iya yi akan waɗannan yaran muddun zakayi ƙoƙarin taɓa su to bazan taɓa ƙyale ka ba, dan haka idan kana son zaman lafiya ka fita harkar su gaba ɗayan su bawai iya jikata ba har suma sauran duk ƴaƴana ne!!!
Bashi kaɗai ba hatta Maryam saida tayi mamakin jin kalaman Rabi...
Cikin zafin nama ya kaiwa Rabi shaƙa zai shaƙe ta tayi saurin riƙe hannun sa tare da kaiwa wuyansa shaƙa, shi kansa saida yayi mamakin yanda ta shaƙe sa kuma yakasa ƙwacewa.....
Daidai loƙacin kuma su Ameela suka gama bayyana a falon duk tsayawa sukayi suna kallon ikon Allah,
Tuni Aunty Babba tayi kukan kura tayi kan Rabi zata kai mata naushi itama, Maryam tayi saurin tare ta, tana cewa "rabu da su kar kishiga tsaƙanin su, ki barshi shiɗin mugune kuma zuwa yayi ya cutar daku shiɗin duk da sa hannun sa wajen kashe muku iyaye duk abun da kuka ga ya faru daku shine sanadi...
Wani irin kallo Aunty Babba ta ringa binta dashi na baki da hankali, bata gama faɗa mata ba, ta tayi wani cilli da ita saida ta faɗi a ƙasa, ta ƙwace daga riƙon da tayi mata, huci kawai take ta shiga riƙe hannun Rabi tana ja, amma ina Rabi taƙi saki saida taga yana shirin mutuwa sannan ta sake sa dan kanta....
Tari ya farayi idon sa ya kaɗa yayi ja na azaba, Aunty Babba kamar tayi kuka ta kama yi masa sannu, tana tattaɓa wuyan sa, ranta in yayi dubu to duka ya ɓaci da ganin wannan baƙar ranar abun soyuwar ta ake so aga bayan sa, duk wanda yayi gagancin hakan kuwa dole shima ya ɗanɗana kuɗar sa,
"Sannu Uncle sorry, itama gaba ɗaya ta fita hayyacin ta juyawa tayi ta kalli su Beenshi cikin ɓacin rai ganin yanda sukayi burus suna kallon ta babu wanda yazo kusa da ita,
"Wai duk bakwa ganin abun da yake faruwa ne babu wanda zai ya taimaka min nikaɗai zaku bari babu wani abun da zaku iya yi, kuna kallon ana ƙoƙarin kashe shi amma babu wacce tayi yunƙurin yin wani abun, Ku kama wannan matar mana da take shirin kashe shi bawai ku tsaya kuna kallon su ba, zasu rabani da farin ciki na...
Duk tsuru-tsuru sukayi babu yanda suka iya dole suka matso kusa da ita suka shiga bata haƙuri shima suna yi masa sannu,
Rabi da taga Barazana a gaban ta kuma daman ita tazo ɗauka dan haka sai kawai ta kamo hannun ta, batare da ta kalli kowa ba tace wuce mutafi.