ya kasa ko motsawa, gaba ɗaya ya ɗauke wuta, dan ba shida abun da zai iya cewa, so yake ma ta kashe shin ko zai huta.
Sai sunbatu take tana zazzagin sa da faɗar munanan abubuwa akan sa, wani abun ma batasan ma tana faɗa ba, dan bata hayyacin ta, da ƙyar aka samu aka cire hannun ta daga jikin wuyan sa, shima aka janye sa,
A ranar dai baiyi bacci ba dan saida aka ɗauko sa daga wajen ma aka mayar dashi gida,
Kwana biyu dayin mutuwar gaba ɗaya ya canza ya fita hayyacin sa, itama kuma bata cikin hayyacin ta har yanzu dan har buge buge take yi wani loƙacin, ƴarta kuwa sai fita akayi da ita daga gidan.
Ranar sadakar uku aka tashi da mutuwar Alhaji Yunusa Sarkin noma, anan hankalin sa ya kuma tashi dan yaga alamun da gaske suke, mutanen gari ma kowa sai magana yake akan wannan mutuwar, hakan yasa zargi ya kuma ƙarfi akan Jambo ne yake yin su, dan anfara daina zargin Labaran.
Ƙara ɗauko Labaran sukayi a karo na biyu ganin zargi yana ƙarfi a kansu kuma hukuma ta shiga ciki domin ƴan gari sunkai ƙarar sa, har an fara neman sa, a police station, hakan yasa suka ɗauko shi suka kuma yi masa barazana da sauran rayukan da zasu kashe,
A wannan karan kuwa baiyi musu ba yace musu zai amsa indai zai rabu da sauran shi kuma zai amsa laifin kisan...
Ranar da aka zo ɗaukar Jambo sai ya tubure yace ai shi baza'a tafi sashi shi kaɗai ba, dole sai an haɗa da labaran saboda matar sa tace shi ya kashe mata mahaifi sun samu saɓani a tsakanin su yace sai ya kashe shi kuma gashi ya kashe shi dan haka dole a haɗa dashi,
Ƴan sanda kwa da sukaji haka sukaje ɗauko sa ranar sadakar ukun mahaifin sa, haka ƴan uwan sa da mahaifiyar sa harda sauran ƴan gari da dama sun bada shaidar bazai aikata ba, kar su ɗauke sa, amma babu yanda suka iya dole aka kwashe su aka kaisu police station, kwana biyu da kaisu aka ɗaukaka ƙara zuwa koto,
Ranar da aka tsayar da Shari'a, aka fara gudanar da ita ana tambayoyi kamar yanda akeyi a koto, lauyan Jambo na kare sa shikam Labaran baida lauya ma, bayan angama da su Jambo aka dawo kan labaran,
Alƙali yace; "Malam labaran me zakace a bisa tuhumar ka da ake da kisan kai na Malam Rabo da kuma Alhaji Yunusa Sarkin noma, me zaka iya cewa koto.
Shiru yayi yana ta nazari ya amsa ko kar ya amsa, ɗagowa yayi ya kalli mahaifiyar sa da ƙanwar sa da kuma ƴan uwansa da mahaifiyar matar sa, dan ita batazo gurin bama, duk da koto tana son ganin ta, amma halin da take ciki yasa aka barta a gida, sai kuma ƴar sa da take hannun kakar ya, da sauran ma munatan gari da duk suke masa shedar arziƙi da kuma fatan a gama Shari'a batare da ance shiɗin bane, kowa de nagurin fatan nasara yake masa juyawa yayi ya kuma kallon Alƙali sannan ya juyo ya sunkuyar da kai cikin muryar sanyi yace; "EH NI NA KASHE MALAM RABO DA HANNU NA......!
Kusan gaba ɗaya mutanen gurin saida suka miƙe tsaye ciki da ɗumbum mamaki, shi kansa Alƙalin saida ya cire glass ɗin idon sa yana kallon sa.....✍️✍️✍️
[3/5, 11:49 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________
*_episode 15💧_*
💧💦محمدالرسوالله...!💦💧
Bissmillah.....✍️
Kusan gaba ɗaya mutanen gurin saida suka miƙe tsaye ciki da ɗumbum mamaki, shi kansa Alƙalin saida ya cire glass ɗin idon sa yana kallon sa....,
Nan guri ya nemi hargitsewa suna cewa bashi bane wasu suna mamakin kowa dai na faɗan albarkacin bakin sa, saida Alƙali ya buga gudumar sa sannan kowa yayi shiru ya koma ya zauna, mahaifiyar sa kuwa sai aikin kuka take,
"Hmm Alƙali yace yana me jin mamakin mutuin, jin bai wahalar da shari'a ba ya amsa laifi cikin sauri haka, maida glass ɗin sa yayi sannan ya ɗau alƙalamin sa yayi rubutu sannan ya kuma ɗagowa yace; "ko zamu iya jin dalilin ka nayin waɗannan kisan kai ciki harda mahaifin da ya haife ka,
Kowa zuba masa ido yayi ana jiran jin ta bakin sa,
Shikam yayi shiru, ya daɗe a haka kafin yace; babu wani dalili hakannan na kashe su saboda inajin haushin su bana son ganin su,
Tsit kake ki kamar ruwa ya cinye duka mutanen wajen haka kowa yayi ɗif.
Ƙara buga guduma yayi sannan yace; "akwai me magana ko faɗar wata sheda akan hakan ko mu yanke masa hukun ci kawai.
"Akwai...! Ta faɗa tana sunkuyar da kai, tace ya me girma me Shari'a a bani dama.
Gaba ɗaya gurin suka maida kallon su ga inda sukajiyo sautin muryar ta.
Alƙali ya kuma yin rubuta sannan ya ɗago ya kalle ta yace; zaki iya fitowa koto ta baki dama.
Fitowa tayi daga inda take kowa na binta da kallo har taje gun da ake tsayawa ta tsaya,
Bayan tsayuwar ta ta kuma durƙusar dakai tace; "ya me girma me shari'a ina neman koto da taban dama domin wanke me laifi da yake shirin ɗora kansa laifin da bashi ya aika ta ba.
Kowa da mamaki yake kallon ta,
Da sauri lauyan Jambo ya miƙe tsaye yace; "ya me girma me Shari'a ina da jaa wann....
Ɗaga masa hannu yayi ya dakatar dashi tare da cewa koto bata baka dama ba,
Cike da taƙaici ya jinjina kai yana komawa ya zauna,
Alƙali yace mata muna sauraron ki,
"Labaran bashi ya kashe su ba, Jambo ne, ni yabawa abu na zubawa malam Rabo yaci ya mutu da yaga haka kuma......nan ta kwashe duk yanda suka tsara ta bada labarin komai,
Jambo da borin kunya ya fara hauka yana ƙaryata ta yana faɗin sai ya kashe ta, babu wanda ya isa ya kamasa, da ƙyar jami'an gurin suka kama sa, direct aka fita dashi waje sannan aka yanke masa life in prison,
Kowa yayi farin ciki da haka, Khadija kuwa sa taji haka saida tayi da nasanin duk abun da tayi masa, kuma tayi tayi ya maida ita amma fir yaƙi shima, dan ji yayi gaba ɗaya garin ya fitar masa a rai, ko wata baiyi ba, ya ɗauki mahaifiyar da ƙanwar sa, suka koma, can wani gari dake kusa da Zamfara me suna Lautai, haka rayuwa taita tafiya, duk da yarinyar sa tana ransa amma bai taɓa zuwa ganin ta ba, ko sau ɗaya,
Itama kam ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba ba uwa ba uba, mahaifiyar ta na gidan yari, mahaifinta kuma na inda ba'a dawowa, a hannun ƙanin baban ta take, shikuma matar sa bata da mutunci, zaman haƙuri kawai take gashi ta nemi inda labaran yake a faɗin garin ta rasa inda ya shiga,
Bayan wasu shekaru, aka samu da ƙyar tayi aure, inda mutumin kuma akayi sa'a ɗan garin Lautai ne, kuma layin su ɗaya, dan haka basu wani daɗe ba suka haɗu da juna, sai ta basa ƴarsa mahaifiyar sa taci gaba da kula Abu,
(Bari dai inyi muku a gurguje naga zai ɗauke ni loƙaci)
A taƙaicce dai,bayan wajen shekara goma, Jambo bai canza hali daga gidan yarin yake ƙula duk wani abu da yake so, tare da taimakon mahaifin sa sa ya goyi bayan ɗansa suka ci gaba da neman inda suke a haka har sukayi nasarar gano inda suke, saboda mugunta me garin ya koma can garin da zama gaba ɗaya tare da iyalen sa duk dan ɗaukar fansa. A haka suka kadawa garin gaba ɗaya garin da mugunta dake ƙaramin gari ne kuma ƙauye yasa basu da ilimi na boko da na zamani, hakan yasa me gari mulke ƴan garin, ake ta zuba mugunta duk dan ayi nasara akan su Labaran. Kamar yanda suka tsara saida suka kashe mahaifiyar da ƙanwar sa, da Abu taga haka sai ta ɗauke ƴarta taci gaba dayi musu magani ita sa ƴar dan mahaifinta da zai mutu a rubutun takardar ya sanar da ita duk yanda zatayi wasu magungunan sannan ya bata wasu acikin jakar da ya cilla, ta tsinceta loƙacin da ta rataye zanin wanka ya faɗa baya, bayan ta gama shiryawa da wasu kayan sai ya zagaya ɗauko sa anan taci karo da jakar.
Daga nan suka kafawa Labaran da abubuwa da dama amma sunƙi yin nasarar kashe shi, dan haka sai kawai suka ɓillo masa ta wata hanya, suka jinginar dashi bashi da wani amfani kallo kawai yake amma baya magana, kuma baya tafiya, yana kwance ko da yaushe,
Babu yanda Abu ta iya dole ta taimaka masa da magunguna da kuma kula dashi, mijin da yaga haka sai ya dakatar da ita da cewa idan bata daina ba, sai ya sake ya, haka ta haƙura saidai ta saci idon sa ko kuma ta aiki Abu ta kai masa wani abun ko ta taimaka masa, loƙacin shekarar ta sha uku, sosai take tausayin mahaifin nata kuma a haka take taimaka masa, shi kaɗai me a gidan shiyasa wataran take kwanciyar ta kusa dashi,
Suna shan wahalar rayuwa dan duk abun da ta samu a kansu yake ƙarewa, amma duk da haka batayi ƙasa a gwiwa ba, ga karatu da tasaka yarinyar dake can cikin garin su Islama da boko.
Loƙacin da Abu ta cika shekara ta ashiri, ta gama secondry school sun kusa sauka a karatun Qur'ani, loƙacin ne su kaji wani mummunan labari cewar Jambo ya fito daga gidan yari,
Hankalin su ya tashi dan har aiko musu yayi tunda bai auri uwar ba sai ya auri ƴar ta ko tana so ko bata so,
Ita dai tasan bai isa yayi mata komai ba, saidai kuma tana tsoron abun da zai yiwa ƴar da kuma labaran dan haka ta roƙi mijin ta da yabar ta ta dawo dashi cikin gidan sa, a wani ɗan ƙaramin fili, sake cikin gidan amma yaƙi yace saidai ta siya haka ya saka masa kuɗi me yawa ta siya ta biya aka gina, mata sannan ta maidashi ɗakin, Abu taci gaba da kula dashi,
Tashin hankali dai da yayi yawa taga indai yarinyar ta tana cikin garinnan bazai taɓa ƙyale ta ba sai ya cika ƙudirin sa akan ta kamar yanda yayi alƙawari,
Da kanta ta ɗauke ta tare da kayan ta ta baro garin da ita suka shiga garin Kano batasan ko ina ba, amma a haka ta ringa yawo tana nemawa ƴarta gidan aiki, a haka suka samu, bata bar garin ba saida ta samu ta siya mata ƙaramar waya itama ta siya tare da layika, aka saita musu komai da nuna musu inda basu sani ba, kwanan ta biyu a garin ta dawo ƙauyen su,
Tundaga nan ta samu salama domin kuwa duk bala'in Jambo har gidan yazo amma ba yanda zai yi da ita dan tafi ƙarfin sa, ya nemi Abu ya rasa, kuma shi duk da be taɓa ganin yarinyar yarinyar ba yaji yana sonta kuma da aure, amma gashi ya rasata, daga ƙarshe ma haka aka ce masa ta mutu dan har gawar ƙarya aka haɗa da taron mutane duk dan ya yarda, wasu sun yarda amma duk da haka loƙaci zuwa loƙaci yana zuwa ya tayar da hankalin ƴan garin, saidai yayi ya gama ba wanda yake kula sa, duk da yaji labarin Labaran bai mutuba shima nemansa yake ido rufe.
Tun yana zuwa har ya daina zuwa, tajishi ɗif gaba ɗaya ma baya garin, kullum sai tayi magana da Abu duk halin da suke ciki sai sun sanar da junan su, duk wata tana turo mata kuɗin ta na wata idan an bata, duk sanda zasu haɗu saidai su haɗu a ɓoye... Bari mu dakata anan, sauran labarin ma ƙarasa sa acikin labarin, nasan dai yanzu kowa ya fahimci asalin Zee Barazanar, Zee Fashion, zamuji inda ta samo wannan sunan ya akai da ga Abu ta koma barazana.
*Ci gaban labarin*
Wash nagaji hannuna ya ƙage sai gobe😟😅🤣
[3/5, 11:50 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________
*_episode 16💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
Bissmillah.....✍️
*Ci-gaban labari*
____Sun daɗe suna binciken yanda zasu gano tracking information na inda number take amma network ya hana su saboda ƙaranci network dake garin, sunyi sunyi amma da ya fara sai ya katse sun kasa har wajen ƙarfe biyu suna yin abu ɗaya amma ya gagara dole suka haƙura suka barwa gobe,
Washe gari a subar fari suka bar garin, basu tsaya ko ina ba, sai a garin kano loƙacin da suka wajen sha ɗaya, dan haka makaranta kawai suka wuce basu tsaya ko ina ba,
Shigar su ke da wuya sukaga pastocin hotu nan su, gaba ɗayan su, ganin hakan saida gaban su ya faɗi, kasa fitowa sukayi daga cikin motar,
Da ƙyar sukayi ƙarfin hali suka fito suna bin duk inda suka ga hoton su da kallo, suna gurin daman kamar su ake jira sai gashi ɗan aike yazo musu wai Dr.Aveed yana neman su,
Ko kallon ɗan aiken basu yi ba suka nufi office ɗinsa har zasu shiga aka ce musu baya nan yana can wajen da suke meeting a can a ke neman su, direct suka nufi can ɗin,
Suna shiga bakin su da sallama duk amsawa sukayi suna duban ƴan matan da akace sun daki lectura guda, saboda tsaurin ido irin nasu basa tsoron abun da zai biyo baya,
Sunkuyawa sukayi suna gaida ƴan wajen kawunan su duk a sunkuye,
Sir Suraj kuwa sai washe baki yake yana binsu da kallon mugunta,
Dr. Aveed ne yace; "kun aikata wani babban laifi sosai kuwa domin faɗa da lectura ba abu ne me sauƙi ba, duk da a kan gaskiyar ku kuke bai kamata kuyi masa haka a gaban mutane ba, kamata yayi kuyi masa a gefe ko kukai ƙarar sa gaba tunda akwai manya a gaba ko ba haka ba?
Nan mutanen wajen kowa ya shiga jinjina kai cike da gamsuwar maganar da,
Sukam shiru sukayi kansu a ƙasa suna sauraron duk abun da yake cewa.
Sir Suraj kam tunda yaji yace akan gaskiyar su suke, gaban sa ya faɗi, sai faman zuba ido yake akan ko wannen su,
"Saƙo daga me wannan makaranta yace kar ku kuma yin haka kuma ya yabawa ƙoƙarin ku nason kare wa mata incen su bisa ga ɓaya garin malamai kuma yace ku cigaba da saka ido akan duk wanda baiyi daidai ba ko ya taka mana doka, ko soyayya bamu yarda lectura yayi da wata yarinyar ba a cikin makarantar nan koda kuwa soyayyar gaskiya suke su bari in sun fita waje sa yi, me wannan makaranta yace in miƙa godiyar sa gare ku, sannan saboda yazama izna ga sauran wanda yaga zai daina ya daina wanda yaga kuma bazai daina ba, bismillah muna nan idon mu akan sa.
"Wata takada ya ɗauko a envelope yazaro wata takardar yayi ƴan rubuce-rubuce, sannan ya miƙawa Sir Suraj yana cewa "ga wannan kayi singing.
Sir Suraj karɓa yayi hannun sa na karkarwa yayin da zuciyar sa take dukan uku-uku, baisan takaddar mece ba, amma a haka yayi singing ya miƙa masa, sai ya ajiye ta ya ɗauki wata shima yayi singing ajiki ya miƙa masa yace; "takardar korar ka daga aiki ne, daga yau ka gama aiki muddin ƙarƙashin wani ne, domin yace duk makarantar da kaje sai yasa ankoreka, saidai kaje kayi kasuwanci...
Miƙewa yayi cikin sauri, ransa yagama ɓaci, cikin jin haushin maganar sa, yace; "wannan wane irin shirme ne yaza ayi yara suyi min ƙazafi su dake ni kuma ku goyi bayan su dan rashin adalci, ni zaku kora a aiki wallahi baku isa ba, sai nasa duk an ɗaure ku sai kunyi da nasanin wannan abun da kukayi, kuma baku isa kun hanani ba zanci gaba da koyarwa kuma anan makarantar ko kuma in sa a ƙulle ta, gaba ɗaya, sai na jefe rayuwar ku cikin ƙunci,
Dr. Aveed ne ya miƙe tsaye shima cikin ɓacin rai yace; "it's enough for you kar ka kuma wata maganar banza anan If not sainasa an ɓalɓallaka anan gurin, ka fice mana daga nan gurin duk abun da kake son yi kaje kayi bamason hauka anan gurin,
Da sauri Sir Suraj ya ƙarasa gaban sa yana jifan sa da wani